Showing 3001 words to 6000 words out of 13756 words
Chapter 2 - MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1 By Aliyu Abubakar Sharfadi .pdf
Koda jama' a sukaji haka mafiyawancinsu basu
yarda ba, amman saboda zafin mulkinta sai sukayi shiru domin sun san lallai idan
suka karyata zancenta, to lallai zasu dandana kuransu. Kuma gashi duk mutanentane
a majalisar, wann dalilin ne yasa suka bita a yanda tace.
Shi kuwa jinjirin da aljana ta dauka yayin daya cika shekara biyu a fadar Sarki
AFAYARU, sai aljana ta yayeshi tare da yarta, kuma tanemi izini a gurin mijinta kan
cewa tanason maidashi gun Sarki AFARA"'U. Da Sarki AFAYARU yaji haka sai
yace da ita tabar yaron nan a wajensu, ya cigaba da cewa yaron yana da alamura masu
girma, domin kuwa dan Sarki ne, kuma shi zai kubutar da yarki daga wata masifa a
nan gaba, kuma wannan yaro shine zaiyi yaki duniya baki daya kuma yayi nasara,
saboda wannan girman lamari nasa nake ganin bai kamata mukaishi wajen mutane
yan uwansa ba domin zasu iya cutar dashi.
Koda DASUKATU matar Sarkin aljanu
AFAYARU taji haka sai tayi na' am da wannan magana amman kuma sai ta tuna ai ta
daukarwa Sarki AFARA'U da matarsa alkawari kan cewa zata maido dashi.
Anan sai tace da mijinta eh ta yarda da maganarsa amman itama tana da shawara. Ya
tambayeta yace to fadi shawararki muji.
DASUKATU tace Kaga mu ba mutane bane,
saboda haka halayyarmu data mutane ba iri daya bace zaifi kyau mu mayar dashi
gurin mutane yan uwansa domin ya samu taebiyya irin tasu.
Sarki AFAYARU ya
yarda da wannan shawara ta matarsa, yakuma yi mata izini data mayar da yaro gurin
Sarki AFARA'U da matarsa, amman ta ja masa kunne kada ya yarda wani abu ya
tabasa.
DASUKATU ta dauki yaro ta mayar dashi ga Sarki AFARA'U da matarsa
kamar yadda tayi alkawari kuma ta gargadeshi Kamar yadda mijinta ya fada mata.
Sarki AFARA"U ya karbi yaro ya shiga dashi cikin gida cike da farinciki ya kira
matarsa DAHASHANATU ya mika mata yaron koda ta ganshi sai tayi wuf! ta
karbeshi, ta rungumeahi tana kuka domin farinciki da murna da suka kamata.
Sannan
ya fada mata duk sharuddan da aljana ta fada masa. Anan Sarki da matarsa suka sama
wannan yaro suna WAHASHINFALA.
Bayan an samu kwananki Kamar kwana Arbain da dawo da WAHASHINFALA
wurin Sarki AFARA'U sai matar Sarki ta sami ciki, murna kan murna wurin Sarki
AFARA'U da matarsa DAHASHANATU basai an fada ba, gashi suna murna aljana
ta dawo masu da WAHASHINFALA gakuma DAHASHANATU tana da ciki.
Duk
gari akayita taya Sarki murna. Hakadai lokaci yayita tafiya har lokcin haihuwar
DAHASHANATU yyi tahaifo ya mace aka saka wa yarinyar suna SHAMATU.
Ita
wannan yarinyar farace kuma sai ya zamto Kamarsu daya da WAHASHINFALA.
Wannan lamari ya baiwa Sarki AFARA"U tare da duk sauran mutane mamaki saboda
sudai gasu bakake amman gashi sun haifi farar mace, balarabiya, kuma gashi tayi
kama da wannan yaro WAHASHINFALA, haka dai sukayita manaki.
A lokacin da WAHASHINFALA yakai shekara bakwai, sai ya bukaci yanason ya
fara hawa doki, sarki yasa aka dauko masa wani dan karamin doki, da
WAHASHLFALA yaga wannan dokin sai ya rainashi yace shi bazai hau wannan
karamin dokin ba, shi babba yake so. Sarki yasa aka mayar da wannan dokin aka
kawo masa wani baki ingarman doki mai digo-digon fari a wuyansa da kirjinsa.
WAHASHINFALA yace wannan doki yayi masa, yayi tsalle ya dare kansa yayi
sukuwa a gaban jama'a yana dawowa gabanSarki yana tirjiya.
Daga nan
WAHASHINFALA ya fara koyon yaki da takobi kuma cikin kankanin lokaci ya
kware a harkar fada da takobi yazama kaf yaran dake sa' anninsa bawanda zai iya ja
dashi har manyan ma.
Ganin haka yasa Sarki AFARA'U ya dinga alfahari dashi
kuma ya ware masa masu yimasa hidima.
Wata rana Sarki yana zaune a fadarsa da yan majalisarsa ana fadanci can saiga
bokan Babban Sarki mai suna SAKARAJUNA ya shigo fadar sarki da yan majalisa
suka mike domin girmamawa ga wannan boka saboda sanin matsayinsa a gurin
Babban Sarki wato SAIFURRA'ADU wato shugaban Sarki AFARA'U.
Boka
SAKARAJUNA ya zauna, bayan sun gaisa da sarki ne sai boka SAKARAJUNA
yace masa yazo kasarsa ne ziyara, daga haka akaci gaba da fadanci daga can sai Boka
SAKARAJUNA yaga WAHASHINFALA zaune kusa da Sarki.
Sai Bokan nan ya
tambayi Sarki cikin rada mai ya kawo wannan farin yaron nan, kuma mai yake yi a
cikin kasarka? shin baka da labari cewa irinsu ne zasu mulki duniya kuma su
maidamu bayinasu bayan sun karkashemu.
Nan take Sarki AFARA'U ya fadawa
bokan nan maganganu masu sanyaya zuciyar Boka SAKARAJUNA ya yarda, da
suka nitsa ne cikin hira sai Sarki AFARA'U yake bawa boka labarin cewa ai matarshi
ta haihu shekaru biyar da suka wuce ta haifa masa "ya mace.
Nan da nan boka ya
bukaci da akawo masa yarinyar ya ganta, Sarki yasa aka kawo masa SHAMATU dan
boka ya samata albarka.
Da boka ya daga ido ya kalleta sai yaga ai fara ce balarabiya,
kuma gashi tayi kama da wannan yaro WAHASHINFALA wanda Sarki yace ba
dansa bane.
Nan da nan boka yayi tsafinsa ya gani cewa lallai wannan yarin ya
SHAMATU yar Sarki AFARA'U ce kuma wannan yaro ba dansa bane. Sai ya umarci
daya mayar da wannan yaran cikin gida.
Sarki ya tura SHAMATU da WAHASHINFALA suka koma cikin gida. Nan dai
Boka ya sake buka rairayi sai yaga ita wannan yarinya wanda zai aureta farin mutum
ne, kuma shine wanda zai mulki duniya, sai ya zaci ko WAHASHINFALA ne, sai ya
fusata yace wa Sarki ya zama dole ya kashe wannan yaron WAHASHINFALA in
kuma yaki to zai aika wa Dan uwansa Boka SAKARADUSA, ya fadawa Sarki SAIF
ce wa "Sarki AFARA'U ya ajiye wani farin yaro kuma idan ya taso to duk zai
halakar damu ne, sannan kuma ya mayar da wasun mu bayi.
Boka SAKARAJUNA
ya kare da cewa kaga kuwa idan Sarki SAIF yaji wannan batu to labudda zai halaka
ka da ki da jamaaar taka baki daya."
Koda Sarki AFARA'U yaji wannan magana daga bakin Boka SAKARAJUNA, sai
hankalinsa yayi kololuwar tashi saboda yasan indai har wannan magana taje kunnen
Sarki SAIFIRRA'ADU to kashinsa ya bushe.
Koda gama wannan tunani sai yace da
boka SAKARAJUNA daya bashi nan da kwana biyar zaiyi shawara, boka ya yarda
da hakan.
Boka yayi wa Sarki sallama ya nufi masaukinsa, yayin da shikuma a
bangaren Sarki AFARA'U ya zurfufa kogin tunani na neman mafita, yana cikin
wannan haline na tunani Wazirin sa mai suna HARISU ya fado masa arai.
Waziri
HARISU ya kasance mutum ne mai hangen nesa, saboda sanin yakamata da kuma
hangen nesashi ne yasa Sarki AFARA'U ya nadashi Wazirinsa.
Wanda ada yake da
mukamin Sarkin gida.
Koda Sarki AFARA'U yazo nan a tunaninsa, sai ya kira wani barde yace yayi
maza gidan Waziri HARISU ya kirashi yanzu yanzu.
Bardennan ya amsa da angama
ya shugabana. Ya haye dokinsa ya sukwaneshi. Lokacin da barden nan ya dawo shida
Wazirin HARISU Sarki yana cikin turakarasa.
Saboda haka shima Waziri sai ya
zarce inda turakarsa Sarkin take. Bayan ya nemi izini Sarki ya bashi, ya kunna kai
cikin dakin. Koda shigar sa sai Sarki ya bashi labarin duk yadda sukayi Boka
SAKARAJUNA akan WAHASHINFALA. Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi
na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron
numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan...
Zamu cigaba
MALUKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 3
posted by Shuraih Usman
@ https://dlhausanovels.com.ng
Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi
na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron
numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan wannan lamari
tunda kaidai kanason yaron nan bakason rabuwa dashi ko kadan.
Mezai hana mu jewa da wannan boka kalamai masu sanyaya rai da kwantar da
hankali, muyi masa alkawarin cewa Indai har wannan yaro ya girma mukaga
take taken shi nason rushe mana masarauta da kuma hanamu bautar zahalu to sai mu
kashehi."
Koda Sarki AFARA'U yaji wannan zance sai yace "Maraba da fasihin
Waziri, hakika hakan za'ayi".Da haka Waziri yayi wa Sarki sallama ya tafi gida.
Bayan kwana biyar Kamar yadda Waziri HARISU yayi wa Sarki AFARA'Uu
bayani, cikin sa'a kuwa suka shawo kan boka SAKARAJUNA.
Sannu a hankali soyayyaya mai karti ta kullu tsakanin WAHASHINFALA da
SHAMATU ba tare da Sarki AFARA'U ko boka SAKARAJUNA sun sani ba.
Bayan wasu yan shekaru kowa a cikin wannan garin saida ya fahimci soyayyayar
dake tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU saboda haka boka
SAKARAJUNA ya fara kokarin rabasu ta hanyar alqalaman tsafi amman abu ya
farkara.
Ganin haka ya shirya mashi makirci ta qarkashin kasa.
Sannu a hankali manema suka fara fitowa neman auren SHAMATU, cikinsu kuwa
harda WAHASHINFALA wanda shine kan gaba.
Saboda haka Sarki AFARA'U ya
nemi shawarar boka SAKARAJUNA, koda boka yaji harda WAHASHINFALA sai
yayi dariyar qeta yace "Inaso gobe a tattatara mani manemanta a kofar fada".
Daga
haka Sarki AFARA'U yasa aka rubuta takardu zuwa ga masu neman auren "Yarsa
SHAMATU. Yakira wani bafadensa ya aikesa.
Washe gari tunda sanyin safiya masu neman auren SHAMATU suka fara bayyana,
bayan wani lokaci, suka gama bayyana a bakin fada, cikin mutanen nan kuwa harda
WAHASHINFALA dashima ya shiga layin manenan SHAMATU.
Bayan wani
lokaci suka fara jin bugun tabura gami da busar algaita hakan ya tabbatar masu da
cewa Sarki yana tafe. Haka kuwa akayi Sarki AFARA'U ne sanye cikin alkebba,
daga damansa Wazirin sa ne mai suna HARISU Sannan daga hagunsa kuma boka
SAKARAJUNA.
Koda ya karaso bakin fadar, bayan yayi masu barka da zuwa saiya
umarci boka SAKARAJUNA daya fada masu abinda ake buqata ga duk wanda
yakeson SHAMATU.
Boka SAKARAJUNA ya fara magana kamar haka "inayi wa
bakinmu barka da zuwa, dalilin dayasa muka taraku anan shine, duk wanda yake son
auren SHAMATU to sadakinta shine zai kawo mana kan Shahararren dan fashin nan
wato SA'ADUNUJJANJI, koda wadannan jaruman da yayan attajirai dake neman
auren SHAMATU sukaji haka sai suka fara sulalewa, cikin kankanin lokaci wajen ya
zama fetal ba kowa sa WAHASHINFALA.
Koda ganin haka sai boka yayi
murmushin keta yace da WAHASHINFALA jarumtarka ta burgeni sai ka shirya
nanda jibi ka kama hanya.
Daga haka suka juya izuwa cikin gidan sarautar.
Bayan kwana biyu WAHASHINFALA ya shirya cikin bakin sulke, yayi wa
SHAMATU da Sarki AFARA'U sallama y kama hanya cike da kewar garinshi da
kuma masoyiyarshi SHAMATU.
Alamarin SHAMATU kuwa tunda masoyinta WAHASHINFALA ya tafi ta shiga
damuwa kasancewar bata da tabbacin cewa ko zai dawo da rai.
Ahaka ta kwana ta
wuni a rana ta biyune tana bacci tayi mafarki da annabi HALLIRU alaihissasatu, yace
mata ai ita taimakon WAHASHINFALA yana hannunta.
Cike da mamaki ta kalleshi tace taya ya? Sai yace da ita a gidan akwai wata matattala ita
wannan matattalar ta
kasance idan ka taka ta farko lafiya ta biyu bazakata lafiya, yacigaba da cewa saboda
haka ya zama maki dole kije ki sanar dashi.
Koda SHAMATU ta farka cikin dare
bata zame ko ina ba, sai bargar dawakai, cikin sanda ta kanto doki ta haye cikin sa'a
kuwa ta tadda masu gadin kofar sunata sheka baccisu.
Ba tare da tsoron komai ba ta
bude kofar ta fice.
Kasancewar WAHASHINFALA be dade da lafiya ba ita ta bi bayansa koma dokin
data dauko irin na musammanne wanda ba koda wane lokaci ake fani da suba,
tadauki lokaci tana tafiya cikin kurmumun daji ba tare da tsoron komai ba.
Aiko cikin
sa'a ta fara hango WAHASHINFALA wanda yana gab da shiga cikin gidan
shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI ta kwala masa kira, koda yaji
ankwala masa kira sai yayi turus yaja ya tsaya ba tare daya waiwayo ba.
Ganin shirun
yayi yawa yasashi ya waiwayo koda ganin wadda ta kirasa sai fuskarshi ta fadada da
murmushi.
Ya tabayeta keko meya sa kika biyoni? SHAMATU tace Zan baka labari
amman ba yanzi ba.
WAHASHINFALA shida SHAMATU sukayi kokari suka shiga cikin gidan
kasurgumin dan fashin nan SA'ADUNUJJANJI can suka hango wata matattakala,
nan take WAHASHINFALA ya doshi inda matattalar nan take ya mika kafa ya taka
ta farko ya kuma taka matattala ta biyu daga takawarshi sai ya rufta ciki wasu
wukake guda biyu masu matukar kaifi, da tsini tare da suka nufoshi zasu rabashi biyu
cikin azababben sauri SHAMATU ta rugo da gudu ta rikeshi sannan tayi wuf ta
jawoshi waje.
Ai koda ya ganta sai ya cika da matukar mamaki ya tambayeta ya akayi
kikasan haka? Nan ta kwashe labari kaf ta fada masa.
Da yaji haka sai yace gashi
yanzu adduarki taci. Nan dai SHAMATU ta ci gaba da bashi labarin wannan
matattala tace Ita wannan matattalar idan ka taka ta farko lafiya to tabiyu ta Sharri ce
dan haka idan ka taka ta farko to saidai ka tsallake ta biyu ka taka ta uku. To haka
sukayi har suka isa can sama da suka isa sai suka riski wata katuwar kofa ta baki
karfe saboda haka sai MALUKUSSAIF ya leka ya hango wani mutum baki, kato,
mai manyan idanuwa gasu jajaje tamkar garwashin wuta, gashi da katon hanci kamar
gwangwani, ga katon kai Kamar mangala Sannan ga manyan labba kai kace fata aka
shinfida.
Daga gefen damansa mutane arbain ne haka ma bangaren hagunsa. Koda
WAHASHINFALA yaga haka sai ya dawo bayan wannan kofar ya labe, koda ganin
haka sai SHAMATU tace da WAHASHINFALA shi wannan mutumin na tsaki baki
mummunan shine SA"'ADUNUJJANJI.
Suna zaune can sai SA'ADUNUJJANJI yace
da mutanensa kai kutsaya nifa kamar motsi nake ji fa? Inaga daya daga cikin mutanen
da kuka kamo ya kwance, daya daga cikin ku ya tashi ya duba.
Yana gama rufe
bakinsa, daya daga cikin Sadaukan nan ya tashi domin ya dubo yana zuwa daidai
inda kofar nan WAHASHINFALA yayi wuf ya sare masa kai, ita kuma SHAMATU
ta janyeshi ta boye gawar, da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yaji shiru sai ya kuma
turo wani barden nan ma dai WAHASHINFALA ya sare masa kai kamar yadda yayi
wana farko, haka SA'ADUNUJJANJI yayi ta aiko da mutane har akazo kan na biyar
nan fa kowa tsoro ya darsu a zuciyarsu aka rasa Wanda zai tashi shikuma
WAHASHINFALA dayaga anjima babu wanda ya sake fitowa sai ya kutsa kai ya
shiga cikin dakin ya tsaya gabansu koda SA'ADUNUJJANJI yaga
WAHASHINFALA sai yace kai kuma wannan karamar halitta daga ina haka? Kuma
maiya kawoka nan harka halaka mani mutane?
WAHASHINFALA ya amsa masa da
cewa babu ruwanka daga inda najo, kuma dalilina na zuwa na wajenka shine nazo ne
na kasheka, Sannan na tafi da kanka a matsayin sadaki.
Koda SA'ADUNUJJANJI
yaji wannan magana sai ya bushe da dari sannan yace kai yanzu wannan yaro har
MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 4
post by Shuraih 99%
zaka iya fada dani? Dubeka fa ka dubeni na ninka ka sau goma, yanzu kaiko wannan
saurauyin wane ne ya turoka ka aikata wannan abu gareni? WAHASHINFALA
cikin bacinrai yace ba'a sani ba idan zakayi shirin yaki kayi.
SA'ADUNUJJANJI
yace zo mu shiga cikin gidana akwai fili isasshe wanda zai ishemu ni da kai.
SA'ADUNUJJANJI ya tashi yaransa suka biyoshi a baya, WAHASHINFALA ma
ya biyo shi a baya, suka shige wasu manyan soraye guda uku suka riski wani fili, da
suka isa wannan fili sai SA'ADUNUJJANJI ya juyo wajen mutanen sa yace idan
muna yaki da wannan yaro kar wanda ya kawo mani dauki koda kuwa kunga yana
kokarin samu galaba a kaina ne, ku tsaya kawai kuyi kallo.
Koda yaran
SA' ADUNUJJANJI sukaji haka sai su dukansu suka babbake da wata mahaukaciyar
dariya, domin sun san cewa ba ta yadda za' ayi wannan karamar halittar ya iya kai
shugaban nasu kasa ko yazo da matemaka bare ya zo shi kadai.
Suka amsa da sunji
sun yarda.
Can kuma SHAMATU data ga sun shiga wannan gida, sai ta fito daga inda take
boye ta hau kan wani dutse inda zata iya ganin karawar da za'ayi tsakanin
SA'ADUNUJANJI da saurayinta.
SA'ADUNUJJANJII ya yiwo kan WAHASHINFALA yana gurnani tamkar zakin
dakejin yunwa ya hango nama, WAHASHINFALA shima ya zare tashi takobin yayi
dauki kan sa suka kaure da yaki bají-ba-gani har dare yayi rana ta take.
Can suna
cikin wannan dauki ba dadi dine sai WAHASHINFALA ya taka wani karamin dutse
ya durkushe kasa.
SA'ADUNUJJANJI ya daga takobinsa ya kawo wa
WAHASHINFALA wani wawan sara koda SHAMATU taga haka sai ta tabbatar da
cewa indai har saran nan ya dira a kan masoyinta to saidai wani bashi ba.
Sai tayi
wuf! Ta zaro wani gariyo daga cikin sulkenta ta wulwuloshi ta jefi
SA'ADUNUJJANJI dashi, sao gariyon ya sare shi a hannu wanda hakan yayi sanadin
faduwar takobin dake hannunsa.
WAHASHINFALA ya rike takobinsa a hannu yayi
niyyar sarewa SA'ADUNUJJANJI kai amman sai ya fasa yace tashi ka dauki
takobinka muci gaba da yaki, domin bazan kasheka ta hanyar yaudara ba, sai kuma
ya juya ya fuskanci dutsen da SHAMATU take tsaye yace jinjina gareki ya
ma'abociyar bege.
Koda SA'ADUNUJJANJIl yaji haka sai ya tashi ya dauki takobinsa
suka ci gaba da yaki, haka suka cigaba da wannan gwabzawar har tsawon kwana uku
a rana ta ukun ne shuka tsaya domin su huta, ko wannensu ya samu guri