Showing 9001 words to 12000 words out of 13756 words

Chapter 4 - MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1 By Aliyu Abubakar Sharfadi .pdf

shidai wannan bako
gashi mun ganshi cikin duhu kuma kifi ya hadiyeshi, ga kuma wani tsuntsu ya
ratayoshi, da sarki yaji haka sai yace wannan wace iriyar maganar banza ce kuke fada
haka mara ma'ana.


Sai Bokanya AKILA tayi farat ta rufesu da fada tace na fada
maku cewa ku daina cin abinci da yawa domin yana hanaku kuyi aikin ku yanda ya
kamata amman kunqiji ai ga irinta nan yanzu kun binciko wa Sarki shirme.


Koda
Sarki yaji haka sai ya fusata yasa hauni ya sare wa Bokaye biyar kawuna, sannan aka
tashi daga fadanci.


Koda Bokanya AKILA ta koma gida sai ta fito da MAALIKUS-
SAIF daga cikin rijiya ta fito dashi daga cikin kifin sannan ta kwance mashi tsutsun
data daura masa, kana ta kwashe duk abinda ya wakana a fada ta fada mashi.


MAALIKUS-SAIF yace lallai kina da yawan hikima, badan kinyu mani haka ba da
da tuni bokayen nan sun gano ni, haka sukayita fira da Bokanya AKILA tare da yarta
DAMATU har dare ya raba sannan suka kwanta bacci.



Da gari ya waye a rana ta biyu, Bokanya AKLA ta samo wata barewa ta daura
mata fuka-fukan tsuntsu, sannan ta sa MAALIKUS-SAIF ya durkusa
gaban
barewar ta daura mashi ita ta kuma daura wata igiyar ta raba qafafun barewa da qasa,
ta shirya ta yafi fada.

Da zuwan ta fada sarki ya umarce ta data sa bokayen nan da su
buga gasa su nemo inda baqo yake.


Nan da nan bokayen nan suka tsundum aikı, can
sai bokayen nan suka dago sukace sun ganshi.

Cike da zumudi Sarki ya tambayesu
yana ina? suka kada baki sukace ai gashi can wata barewa ta tashi sama dashi, nan da
nan Sarki ranshi ya qara baci yace me yasa kuke kawo mani wasa ne? Kun tabajin
ance yau ga barewa da fuka-fukai?, wannan ai rainin hankali ne yasa aka kuma yanka
bokaye biyar nan dai fada ta tashi.


Bokanya AKILA ta tafi gida tana dariya, taje ta kwance MAALIKUS-SAIF suka
cigaba da hira.


A rana ta uku Bokanya AKLA ta samo wata babbar tasa, ta yanka wata dabba ta
juye jinin a cikin wannan tasar, ta kuma samun wata tasar da dora a cikin tasar da ta
zuba jinin, Sannan ta umarci MAALIKUS-SAIF daya shiga cikin tasarnan zauna,
bayan ya shiga ya zauna.


Sai ta kama hanya ta nufi fada, isarta keda wuya ta umarci
bokayen dake karkashinta akan su fara aiki. Nan suka dukufa, bayan wani dan lokaci
suka dago sukace munga wannan baqon a cikin wani kogi na jini, sannan banda
wannan kogin da yake ciki akwai wani kogin wanda shi babu komai a cikinsa, jin
haka sarki ranshi ya qara baci ya umarci hauni daya kara sare kawunan bokaye
goma, sannan yace da bokanya AKILA ke ya kamata ki duba mana inda wannan
baqon yake tunda su sun kasa,

bokanua AKILA tace to tunda yau saura kwana biyar
bikin mu na shekara to a ranar zan kawo maka wannan baqo, koda jin haka sai fuskar
Sarki ta fadada da murshi a haka aka tashi daga fada.


Bayan kwana biyar yaune Bokanya AKLA tayiwa Sarki KAMARUNU alqawarin
kawo masa baqon daya shigo wannan gari nasu. Tunda sanyin safiya MAALIKUUS-
SAIF ya fara jin hayaniyar mutanen wannan gari, cikin firci ya tashi yace mekuma
yake faruwa ne tace ai na manta ban fada maka ba yaune muke bikin shekarar mu
kuma a cikin dakin da wannan littafin yake anan muke bikinmu, saboda haka kayi
zamanka acikin gida nida hannuna zan kawo maka wannan littafin.


Nan fa
MAALIKUS-SAIF yanuna shi sam baiyarda ba saidai ta tafi tare dashi, dole kuwa
hakan tayi tatafi tare dashi amman kafin haka saida ta bashi wani bakin ruwa na tsafi

tace ya watsa qa jikinsa, watsarshi keda wuya yaga ilahirin jikinsa ya zama baki
kamar yadda fatar 'yan garin suke, Bokanya AKILA ta bashi jakarta ta bokanci ya
rike, tana tafe yana binta a baya har suka fito daga cikin gidan.


Fitowarsu keda wuya
suka tadda bokayen nan dake qarqashin Bokanya AKILA a bakin gidanta suna jiranta
tana qarasawa inda suke suka dunguma sai dakin bauta,


koda suka kusa shiga sai
MAALIKUS-SAIF ya qarasa kusa da Bokanya AKILA ya miqa mata jakarta, ita
kuma cikin rada ta qara jadda mashi kan cewa kada ya kuskura yayi yunqurin daukar
littafin nan ya amsa mata da to amman badan ya yarda da shawararta ba.


Koda Bokanya AKILA ta isa cikin dakin bautar sai gaba daya mutanen dake dakin
bautar sukayi wa littafin sujjada bayan Sarki KAMARUNU ya fito dashi daga
maboyarsa ya dorashi bisa wani taburi, ganin sunyi sujjada ga wannan littafin yasa
MAALIKUS-SAIF ya taho a hankali cikin sanda, yazo inda littafin nan yake ya miqa
hannu da niyyar ya dauko shi sai kawai yaga littafin ya fado qasa tim! Ya fara
zagayeshi.


Jin qarar fadowarshi yasa Bokanya AKILA; Sarki KAMARUNU da
sauran jama'ar dake wannan dakin bautar suka dago daga sujjadar da suka yi, aiko
sukayi ido biyu da MAALIKUS-SAIF, nan fa suka hau dukansa baji ba gani,
MAALIKUS-SAIF shima ya hau dukansu,


kasancewarsu suna da matukar yawa sai
wani daga cikin.dakarun ya zagayo ta bayan MAALIKUS-SAIF ya sammaceshi ya
bugesa a tsakiyar kai, nan take MAALIKUS-SAIF ya baje a kasa baiko shura ba,
koda ganin haka sai Sarki KAMARUNU yayi godiya ga wannan littafi sannan ya
umarci wasu dakarunsa dasu je su jefa MAALIKUS-SAIF cikin wata tsohuwar rijiya
dake a bayan gari.


Bayan sun dauki gawar sun jefata a wannan rijiyar ne suka dawo
suka sanar da Sarki KAMARUNU. Sannan Sarki KAMARUNU yace da jama'a aci
gaba da shagalin biki.

Ita kuwa Bokanya AKILA koda taga an kashe MAALIKUS-
SAIF sai hankalita yayi mugun tashi kasancewar tasan irin son da yarta "DAMATU
takewa MAALIKUS-SAIF saboda haka ta sulale ta koma gida ba tare da sanin
kowaba.


Koda tafada wa DAMATU abinda ya faru a dakin bauta, kuka °DAMATU
ta dinga yi da qyar Bokanya AKILA ta shawo kanta.
******
Alamarin MAALIKUS-SAIF kuwa ashe ba mutuwa yayi ba lokacin da aka

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 8
post by Shuraih 99%
.
dokeshi a tsakiyar ka suma yayi, yana cikin wannan hali na suma wata aljana ta
bayyana tsulim! A cikin wannan rijiyar koda ta daga hannunta sama sai wani ruwa ya
dinga fita daga wannan hannu yana jiqa fuskar MAALIKUS-SAIF, jim kadan sai
MAALIKUS-SAIF ya farfado daga suman dayayi, nan fa ya fara tariyo abinda ya
faru dashi a dakin bauta,


bai gama tunanin dayake ba yaji anyi sama dashi anfito
dashi daga wannan rijiyar.
Anan MAALIKUS-SAIF yayi godiya ga Allah madaukakin Sarki daya kubitar
dashi daga cikin wannan rijiyar, to bayan ya gode ma Allah, sai ya tambayi wannan
mutumin daya fito dashi yace kai kuwa wane ne kai? Mutumin ya dubi MAALIKUS-
SAIF yace ni ba Namiji bane ni mace ce, kuma aljana, na kasance diyace a gurin
Sarki fararen aljanu mai suna ABAYARU ni suna na AKISA, nan da nan ta juye ta
koma budurwa.


Kuma nazo nan ne domin wani taimako da zakayı mani.
MAALIKUS-SAIF ya dubeta yace wane taimako kikace zan maki? Aljana AKISAA
tace ya Dan uwana akwai wani bakin aljani mai suna MUTTADI'U.


Shi wannan
aljani kafiri ne mukuma musulmai ne, mun samu musuluncin mune a wajen wani
bawan Allah mai suna Shehu Abdussalam. Wata rana wannan bakin aljani mai suna
MUTTADrU ya sauka a Garinmu yace yazo ziyara, duk da karfin mulkin mahaifina
amman yana tsanananin tsoron wannan bakin aljanin, saboda haka mahaifina ya

saukeshi suka zauna afada suna fira.


Can nazo wucewa da bakin aljanin nan ya
dubeni sai yace yana sona, saboda tsananin tsoronsa da mahaifina yake sai yace masa
ya bashi ni, ni kuma banason sa, saboda ba musulmi bane, hankalina sai ya tashi, nayi
iya tunanina naga babu mai iya kubutar dani daga wannan bala'i da nake ciki, sai na
yanke shawarar na tafi wajen wannan bawan Allah Shehu Abdussalam wanda ke
garinmu, na fada masa halin da nake ciki na nemi ya taimaka mani.


Da Shehun yaji
haka sai yace Ai duk duniyar nan babu mai iya kubutar dake daga hannun wannan
bakin aljanin sai wani mutum kuma Dan uwane gareki mai suna MAALIKUS-SAIF
Dan ZIYAZINUN.


Sai na tambayeshi inda zan sameka sai ya ce mani Inkoma wajen
babata zata gaya mani inda kake. Dana koma Gida sai na tambayi uwata shine take
bani labarin cewa ai yanzu wasu aljanu daga kasar KAIMARA suke bata labarin
cewa gashi can a jefashi a cikin wata rijiya, maza jeki ki kubutar dashi to shine
kaganni nazo to kaji abinda nakeso ka tainmakeni ka kubutar dani daga wannan baqin
aljanin.


Da MAALIKUS-SAIF ya gama jin wannan batu daga bakin AKISA sai ya shafa
bulalarsa yaji tananan, sai yace in sha Allahu zan kubutar dake daga hannun wannan
bakin aljanin.


To amma kuma naji kina cewa ni Dan uwanki ne, ya akayi ni ina
mutum ke kina aljana har na zama Dan uwanki?.


AKISA tace uwata ta sanar dani cewa ai kaima danta ne domin tare ta shayar dani
da kai nono lokacin muna jarirai.


MAALIKUS-SAIF yace to ya sunan babar taki?
AKISA tace DASUKATU. Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan suna sai yace na
yarda ke yar uwata ce, to yanzu saikiyi maza ki kaini wajen wannan uwa tamu.

Kafin ya rufe bakinsa sai ga DASUKATU ta dira dif! a gabansa yana ganin haka
ya rungumeta, yana ce Mata mai yasa kika rabani da ku shekaru da dama.


DASUKATU tace ya Dana munyi maka haka ne domin zamanka a wajenmu bazai
yiwuba saboda dabi'un mu da naku na mutane sun banbanta, shiyasa ya zama mana
dole muka mayar dakai ga mutane yan uwarka, yanzu maza ka hanzarta domin
kubutar da yar uwarka. Da gama wannan magana sai tayi masu sallana ta tafi.


MAALIKUS-SAIF ya kalli AKISA yace To yanzu sai ki daukeni ki kaini wajen
wannan aljani.

AKISA ta dauki MAALIKUS-SAIF ta tashi dashi izuwa qololuwar
sama tayita tafiya dashi, can sai AKISA ta tsaya da tafiya ta sakko kan wani dutse, ta
nuna masa wani tsauni ta ce Kaga wancan tsaunin to akansa gidan wannan aljanin
yake.


MAALIKUS-SAIF yace "To shiken an tsaya anan ni na shiga na fito", yakama
hanya, daya isa gindin tsaunin nan yai zagaye ya rasa inda zai kama ya hau, yana
cikin haka sai yaji ana kiran sunan sa daga saman tsaunin nan, ya daga kansa sai yaga
wasu yan mata ne suke dago masa hannu suna kiran sunan sa.


Sai suka zuro masa
igiya ya kama, suka jashi harkan tsaunin nan.

Da MAALIKUS-SAIF ya hau kan dutsen nan sai yaga yawan yan matan nan yakai
su Arba'in,kuma dukkansu yan matane kyawawa, sai daya daga cikin su wadda
kamar itace shugabarsu mai suna NAHIDA tace ai jiya a cikin baccina naga Annabi
HALLIRU
laihissasatu Wassalam, yace inbada Gaskiya akan addinin Annabi
Tbrahim Alaihissasatu wassalam, ya musuluntar dani Sannan ya fada mani cewa yau
akwai wani mutum mai suna MAALIKUS-SAIF zai zo ya kubutar damu, ya kuma
fada mani cewa ni ina daya daga cikin matayen da zaka Aura, shine na fito ina baiwa
wadannan yan uwa nawa labari sai muka leko muka ganka.


MAALIKUS-SAIF ya tambayi yan matan nan ku kuma me ya kawoku nan?
NAHIDA tace ai mu duk nan daka ganmu yayan Sarakuna ne, ganinmu da kayi anan
wannan aljanı shiya kwasomu ya kawomu nan, dama shi dab1arsa shine duk inda
yaga yar Sarki kyakkyawa to sai ya daukota ya kawota nan, ahaka duk ya taramu

anan.


Da MAALIKUS-SAIF yaji wannan bayani sai ya tuna lokacin dashi wannan aljani
yaje zai dauke SHAMATU ya sare masa hannu daya, suna cikin haka sai suka ji wani
rugugi da hayaqi ya tunkaro su, sai matan nan suka ce wa MAALIKUS-SAIF ya
gudu ya nemi wajen buya domin ga aljanin nan ya dawo.


MAALIKUS-SAIF ya ce
Ku barni dashi babu inda zani, yan matan nan suka shige cikin wani daki suka bareshi
tsaye a waje.


Jim kadan sai ga aljanin nan ya bayyana, koda yaga MAALIKUS-SAIF
sai yace yauwa daman kaine ka taba sare mani hannu yau gashi kazo har gidana, kaga
sai na rama na kasheka nima.


Koda gama fadin haka sai aljanin nan ya miko hannu d nufin ya kama
MAALIKUS-SAIF. Cikin zafin nanma MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya zaro bulalar
sa ya tsula wa aljanin nan. Nan take aljani ya kama da wuta yana kururuwa yana ihu
yana ya kasheni! Ya kasheni...! Cikin lokaci kankani aljanin nan ya qone kurmus,
ya baje kamar turbaya.


Da yan matan nan sukaga haka sai suka fito a guje suna murna, shi kuma ya yi
kiran AKISA ta taho ta shigo wajen. Koda taga ya kashe wannan aljanin sai tace Ya
Dan Uwana na gode wa Allah, na gode maka daka kubutar dani daga sharrin wannan
aljanin, ni kuma babu abinda zanyi na saka maka illa kawai na rika maka hidima.


MAALIKUS-SAIF ya umarci AKISA da ta dauki yan matan nan duk ta mayar dasu
kasashensu kuma idan ta mayar dasu ta sanar da iyayensu cewa shine ya kubutar
dasu.


Nan da nan AKISA ta rika daukar yan matan nan tana mayar dasu qasashensu,
sannan tayi bayanin kamar yadda MAALIKUS-SAIF ya fada mata, da haka har ta
kwashesu kaf ya rage saura NAHIDA kadai.

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1

part 9
post by Shuraih 99%
.
AKISA tazo zata dauketa amman sai taqi. MAALIKUS-SAIF yace Ki tsaya mana
ta daukeki ta mayar dake wajen iyayenki.


Sai tace "Ai ni tunda Annabi HALLIRU ya
fada mani cewa ina daya daga cikin matan da zaka aura to ba inda zani ina tare da kai
duk inda zaka kuwa".


Da MAALIKUS-SAIF yaji wannan magana ta NAHIDA sai ya
tambayeta yace "Ke mutumiyar wace qasa ce'?" ta amsa mashi da cewa "Ita
mutumiyar birnin Sin ce, kuma ubana shiyake mulkin wannan kasa". MAALIKUS-
SAIF ya amsa da cewa "Naji kuma zan Aureki to ammanfa ki sani bazan aureki ba
har saina auri SHAMATU DA 'DAMATU tukunan.


Saboda haka yanzu ki koma
qasar ku". Tayi nacim duniyar nan amman yaqi, koda ganin yaqi yarda sai tayi masa
wata addua tace "To tunda kaki insha Allahu duk lokacin da zaka shiga garinmu,
dagakai sai wando zaka shiga". Shikuma sai yace "Ni kuma insha Allahu lokacin
kina a makance zan shiga, bazaki ganni a tube ba" Dukkansu kuwa sa aka amsa
masu adduarsu.


MAALIKUS-SAIF ya umarci AKISA data dauketa ta mayar da ita kasarsu.
AKISA ta kaita ta dawo da AKISA ta dawo sai tace da MAALIKUS-SAIF to ya Dan
Uwana in kanaso zan kaika birane bakwai mafiya kyau a Duniya?MAALIKUS-SAIF
yace "Eh inaso ki kaini nayi kallo, amman kafin nan inaso ki kaini wajen Shehun nan
na garinku nayi masa ziyara.


AKISA ta daukeshi suka tafi. Da zuwansu, sai
MAALIKUS-SAIF yaga wata hasumiya. AKISA tayi sallama sai sukaji daga ciki an
amsa masu da cewa Barka dai MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN.


Suna tsaye sai
wani Tsoho ya fito. MAALIKUS-SAIF ya tambayi AKISA yace Shikuma wannan
Tsohon wanene shi? AKISA tace "Ai shine Shehu Abdussalam din da nake baka
labari". Suka yi musabiha shida MAALIKUS-SAIF yajashi ya shiga kogon dashi

yana fada wa MAALIKUS-SAIF wasu nauoi da sigogi na zikirin Allah.


Bayan sun
kammala ne Shehun yace ka zauna ka kwana anna ni gobe zan mutu, bayan na mutu
kayi mani wanka ka daga kasan shirmfida ta zakaga likkafani sai ka lillibeni dashi.


Sannan sai ka fita waje kofar hasumiyar nan kayi kira sallah, zakaga mutane ta sama
da qasa sunata zuwa kar kayiwa kowa magana, kuyi zana' ida tare da mutanen nan
bayan kun gama, zakaga ba kowa a cikin mutanen nan.


Sai kaima ka binneni ka kama
gabanka. Haka kuwa akayi gari na wayewa Shehun nan ya cika. MAALIKUS-SAIF
yayi jana'idar yadda Shehun nan ya fada masa.


AKISA tazo tace Ya Dan Uwana idan ka shirya to zan kaika birno na farko,
MAALIKUS-SAIF yace Na shirya. AKISA ta daukeshi suka samu Kamar sa'a daya
a suma suna tafiya, sai suka isa ganuwar wani birni AKISA ta sauka tace "To dan
uwana gamu a qofar birni na farko, yanzu sai ka shiga ka fito ni bani da ikon shiga
wannan birnin, domin akwai kafi wanda zai iya koneni idan har nayi kuskuren shiga.


MAALIKUS-SAIF ya kama hanya ya shiga cikin wannan birni na farko. Da shirsa
sai yaga nmanyan gine gine masu matukar kyau, sannan da Abubuwa masu balain
kyau, yaita yawo yana kallo. Can sai ya iso wani fili yaga wasu mutane sunata fada.
Koda suka ganshi sai duk sukayo kashi, daya daga cikin su yace "Yakai wannan
baqon sai ka raba mana rikicin dake tsakanin mu.

MAALIKUS-SAIF yace Wane
rikici zan raba maku? babban yace nida Dan Uwana mahaifinmu ya kasance shine
baban malami a wannan birni, sunansa Malam AFLADIN, ya mutu ya barmana
gadon wata hula, wadda ita wannan hula ta tasance indai ka sakata to mutum ko aljan
babu mai ganin ka.

To shine muketa rigima akan ko wannenmu yanason ace shine ya
gaji wannan hula, dama kafin kazo mun yanke shawarar duk wanda yazo ya samemu
to shi zai Yanke hukunci a garemu, sai kuma gashi kazo, to muna so yanzu ka raba
mana wannan rigima tamu.

Da MAALIKUS-SAIF yaji haka sai yace "To

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login