Showing 12001 words to 13756 words out of 13756 words

Chapter 5 - MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1 By Aliyu Abubakar Sharfadi .pdf

zan

rabamaku wannan rikici, ku bani kwari da baka zan harba ta duk wanda a cikinku ya
fara dauko ta, ya kawo mani ita nan to wannan hular tazama tashi.


Wadannan yan uwa biyu suka amince da abinda ya fada, suka bashi kwari da baka
gami da hular ya rike a hannunsa.

MAALIKUS-SAIF ya harba kibiya duk mutanen
suka saki dawakansu suka bazam neman kibiya, suka barshi a tsaye da hula a hannun
sa, can bayan wani lokaci sai MAALIKUS-SAIF ya hango daya daga cikin mutanen
nan ya dawo a sukwane, kafin ya karaso sai MAALIKUS-SAIF ya raya a zuciya sa
cewa To niko in gwada wannan hular in gani in gaskiya suka fada mani akan wannan
hular, sai MAALIKUS-SAIF ya saka Wannan hular.


Koda mutumin ya qaraso wajen
sai ya rinka kwada kira yana yakai wannan alkali namu ina kashiga gani na dawo da
kibiyar, yayita diri diri.


Koda MAALIKUS-SAIF yaga mutumin baya ganinsa sai
yace a zuciyarsa "To lallai na yarda da lamarin wannan hula idan kasa mutum baya
iya ganinka, yanzu saura na gwadata akan aljani nagani, can sai ya tuna ai AKISA
aljanace bari yaje ya gwadata akanta.


MAALIKUS-SAIF yai tafiyarsa yabar wannan mutumin yanata diri-dirin neman
sa, daya fito ne ya iske AKISA tana tsaye tana jiransa yazo gabanta ya tsaya amman
duk bata ganshi ba, saiya kira sunan ta *Ya 'yar uwanta AKISA". AKISA tayi wani
turus! "Tace kana ina ne Dan Uwana, kardai ace kasamo hular nan ta Malam
AFLADIN? MAALIKUS-SAIF yace kina ganina?


"Tace A'a bana ganin ka kana
inane?" Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai ya godema Allah daya bashi ikon
mallakar wannan hula, Sannan ya cire hular da hanninsa sai AKISA ta ganshi a
gabanta, ya kwashe labari kaf game da yanda akayi ya mallaki wannan hula ya fada
wa AKISA.


"Ai manyan sarakuna da dama na samu labarin sun rasa rayukansu akan
neman wannan hula, amman kai gashi ka sameta a sama" AKISA take bashi labari,
taci gaba da cewa MAALIKUS-SAIF to yanzu saika shirya na tafi dakai izuwa birni

na biyu.

MAALIKUS-SAIF yace to yanzu karbi hulata ki ajiye mani, tana karba yace
da ita to muje na shirya.
MAALIKUS-SAIF da AKISA suka kama hanyar birni na biyu nan ma dai AKISA
ta saukeshi a kofar shiga gari yai mata sallama ya tinkari kofar shiga garin, da shigar
MAALIKUS-SAIF garin sai jama' ar garin sukayiwo kansa suna ga bako! Ga
bako...!Suka taso masa zasu kamashi sai rigima ta barke a tsakaninsu suna dukanshi
shima yana dukansu, ahaka hardai sukaci karfinsa suka kamashi suka kaishi wajen
Sarkin su.

Shi Sarkin wannan gari sunan sa Sarki DUHANI, ita wannan qasa suna da
wani zobe wanda duk wanda ya mallaki wannan zoben to shine zai zama Sarkin
wannan gari, saboda shi wannan zoben shi suke bauta mawa, sannan idan aka nuna
mutum da wannan zoben sai kanshi ya guntule y fadi qasa, a wannan lokaci Sarki
DUHAN shiya mallaki wannan zoben, saboda haka ya zama Sarki.

Sarki DUHAN ya
dubi MAALIKUS-SAIF yace "Kai ko mai ya kawoka qasata?" MAALIKUS-SAIF
yace "Nazo ziyara ne da kuma yawon bude idanu." Da Sarki haka sai yace Shine
kuma kazo ka fara fada da mutanena harka kashe mani wasu daga ciki.


Sarki yayi
umarni ga wani babban bawansa da ya tafi da MAALIKUS-SAIF gida yayita gana
masa azaba har sai gobe da safe a dawo bakin kogin dake gaban gidan Sarki a fito
dashi a kasheshi. BULAKI ya kama MAALIKUS-SAIF ya tafi dashi ya kaishi cikin
wani daki yayita azabtar dashi har dare ya raba sannan ya koma dakinsa ya kwanta.




MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 10
post by Shuraih 99%
.
Can bayan wani lokaci, MAALIKUS-SAIF yana a daure sai yaga BULAKI ya
shigo dakin ya fadi gabansa yace ka gafarceni ya Sarkin Sarakuna MAALIKUS-
SAIF Dan ZIYAZINUN ka gafarceni.

Koda MAALIKUS-SAIF yaga haka sai yace
"Ya ya haka kainefa kayita azabtar dani dazu kuma yanzu kazo mani da wannan

maganar."

BULAKI ya nisa yace "Ai yanzu cikin baccina naga Annabi HALLIRU ya
musuluntar dani kuma yace dole na kubutar dakai.

Nan da nan BULAKI ya kwance
MAALIKUS-SAIF, ya kawo masa abinci yaci ya koshi sannan ya kawo masa ruwan
sha, sannan ya kara jadda musuluncinsa a gaban MAALIKUS-SAIF.


A wannan dare BULAKI yabi duk mutanen gidan ya musuntar dasu sai wata baiwa
kwaya daya data ki musulunta, akayi akayi amman taki. Nan BULAKI ya kamata ya
daure yace "Gobe Zan je ya jefata ruwa a mainakonka." MAALIKUS-SAIF yace


"Tunda kai yanzu musulmine Zan canja maka suna daga yau ka koma Abdussamad."
Gari na wayewa Abdussalam ya fito da wannan kuyangar lullube dan ayi tunanin
MAALIKUS-SAIF ne, yazo da ita bakin kogi ya tsaya. Jim kadan sai Sarki ya leqo ta
taga, yai Umarni da Abdussamad daya kashe MAALIKUS-SAIF shi a tunaninsa
kenan amman baisan ba MAALIKUS-SAIF bane.


Bayan Abdussamad ya kashe
wannan kuyanga mai taurin kai. Sai Sarki yayi nuni da hannunsa daya jefa gawar
cikin ruwa. Abdussamad ya jefa gawar cikin ruwa ya koma gidansa.


A lokacin da
Sarki yayi nuni da hannunsa da a jefa gawar cikin ruwa bai saniba ashe a wannan
lokaci zobensa ya subuto ya fada cikin ruwan.

Zoben na fadawa cikin ruwa sai wani
kifi ya hadiyeshi a tinaninsa abinci ne.
Da isar Abdussamad gida sai yace da MAALIKUS-SAIF "Mai kake da sha'awa
yanzu na kawo maka?" **Yace kifi nakeso naci yau domin naji ina marmarinsa.


Abdussamad yace Kash! Sai dai babu sauran kifi a gidan nan amman bari na fita nayi
fatsa na kamo maka.

Da MAALIKUS-SAIF yaji haka Sai yace kaga kuwa nima ina
da sha' awar fatsa bari mu tafi tare. Abdussamad ya yarda da hakan suka tafi wannan
kogin da suka jefa wannan kuyangar, can suna fatsa sai suka kamo wani katon kifi

ganin kifin yana da girma sai suka hakura suka taho dashi kadai gida.


Abdussamad ya
yanka cikin kifin a dafa, koda ya kwaso kayan cikin sai yaga zoben Sarki. Nan da nan
ya mika wa MAALIKUS-SAIF zoben nan yace Kaga wani zobenan cikin kifin nan
koda MAALIKUS-SAIF ya gogeshi, sai Abdussamad yace duk yadda akayi wannan
zoben Sarki ne ba makawa.


Nan dai ya kwashe labarin wannan zoben yabawa
MAALIKUS-SAIF labari yakuma fada masa cewa Duk wanda ya mallaki wannan
zoben to ba makawa shine Sarki wannan gari.

Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai
yace ba komai Allah ya kaimu gobe zanje fada na tunbike wannan mushitikin Sarki
naku.


Gari na wayewa MAALIKUS-SAIF da Abdussamad suka kama hanya suka doshi
fada, da isarsu sai suka ga fada ta cika makil Sarki DUHAN yana bisa kan karagar
mulkinsa anata fadanci.


Da shigar su fada Sarki ya cika da mamaki yace "Ya kaida
nasa a kasheka kuma naga ka dawo." MAALIKUS-SAIF ya dubi Sarki yayi dariya
sannan ya daga wannan zoben ya nuna wa Sarki da Duk jama'ar dake fadar.


Koda
jama' a suka kyalla ido sukaga zoben, sai suka kama cewa "Aiko zoben sarki ne ai
shine. ai tunda ka mallaki wannan zoben ba makawa kaine Sarkin mu, dama
ka'idarmu kenan ta samun sarautar wannan gari."


Koda Sarki DUHAN yaga haka sai
ya mike yana hargagi yana karyata MAALIKUS-SAIF yana cewa wannan zoben na
karyane ba zobena bane nawa na barshi a gida.


Rufe bakinsa keda wuya sai
MAALIKUS-SAIF ya nunasa da hannunsa mai zoben nan take kansa ya gutsire ya fadi kasa
matacce. Sarki DUHAN tasa ta kare makomarsa ta munana aka gaggauta

zuwa da ransa jahannama.


Bayan ya gama da Sarki DUHAN sai MAALIKUS-SAIF yace yanzu bautar wuta
ko zobe ta kare kowa ya zai koma bautawa Allah da manzon sa Annabi Ibrahim
Halilullah, in kuma kukaqi in halakaku gaba dayan ku.


Jama'a gaba daya suka yi
mubayia. MAALIKUS-SAIF ya zauna dasu har tsawon wata biyu yana sanar dasu
hanyoyin bautar Allah.


Ranar da MAALIKUS-SAIF zai bar garin sai ya dora Abdussamad bisa gadon
sarauta ya umarci Jama' ar garin da yi masa biyayya.


Daga nan Jama'a suka yi masa
rakiya har bayan gari sannan suka juya suka koma cikin gari. Shi kuma ya doshi inda
yabar AKISA tana jiransa. Da zuwansa sai ya iske AKISA tana jiransa.


Koda ta
ganshi sai tace ya Dan Uwana na ina kallon lokacin da mutanen wannan qasa sukaso
halaka ka, inaso na taimakeka amman bani da ikon shiga garin tilas haka na hakura
ina gani zasu kasheka.


MAALIKUS-SAIF yace ashe kin ganni, ai yanzu gashi Allah
ya kubutar dani, ai yanzu saiki daukeni ki kaini birni na uku. Koda jin haka sai
AKISA tace "A'a Dan Uwana bazan iya kaika ba, ina gani a cutar dakai domin kuwa
suma birane biyar din bazan iya shigarsu ba, saboda haka koda hallaka za'ayi inaji
ina gani babu yadda zanyi, kaga kuwa ya za'ayi na rika kai Dan uwana ga mahallaka
bani da ikon taimaka nmasa."


Da MAALIKUS-SAIF yaji haka sai ya fusata ranshi ya
baci yace kidai ki kaini mana ina ruwan ki. Itako AKISA da taga ran MAALIKUS-
SAIF ya baci sai tayi masa dabara tace haba ya dan Uwana kada rudin duniya ya
shagaltar dakai abinda kafito nema mana littafin tarihin NIL, koda jin abinda AKISA
ta fada sai hankalinsa ya karkata izuwa gida, ya tuno da SHAMATU abar begensa.

Sai ya umarci aljana AKISA data daukeshi ta mayar dashi birnin KAIMARA yayi
amfani da hularsa ya dauko wannan littafin tarihin.


AKISA ta daukeshi sukayi sama
bata zame ko ina ba sai bakin wannan rijiyar data fito dashi.


AKlSA ta mika masa
hularsa BADUHU wadda ya samo Sannan tayi masa adduar Allah yasa ya dauko
wannan littafin na tarihin NIL.

Sukayi sallama AKISA ta tashi sama, ta tafi shi kuma
ya tsaya yana tunanin yadda zai shiga garin KAIMARA yana cikin wannan tunanine
can kuma Bokanya AKILA ta hangosa a madubin tsafinta..

YANZU SHIN MAALIKUS-SAIF YANA SHIGA GARIN KAIMARA NE HAR
YA DAUKO LITTAFIN NAN KO KUWA HAKURA YAKEYI YA KOMA GIDA?

IDAN KUMA YANA DAUKO LITTAFIN TO YA YAKE A SHIGA GARIN
TUNDA SUNADA GUNKI MAI TONON SILILI.

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login