Showing 1 words to 3000 words out of 11892 words
Admin 004
Sardaunah Novel
GIDAN MATI
By Rufaydah Umar..
Young Writters Fanz
Page 1
Buguzum-buguzum ta sanyo kai cikin gidan tana wak'a.
"Ahayye iye nana..."
D'if ta dakata gami da sakin baki adalilin abinda ta hango a tsakar gidannasu.
Maigidansu Mati a k'ofar d'akin kishiyarta Abulle zaune su na hira da dariya. Ganinta ya sanya
Mati yin tsuru da idanu yayin da ita kuwa Abulle ta washe baki, cike da dabara ta fiddo takardar
naman da ta 6oye a bayanta ta warware ta d'auki tsoka d'ayan da ya rage ta jefa a baki ta na
tauna gami da fad'in. "Maigida kana burgeni, kana kawomin irin wanda na ke so."
Mati ya watsamata kallon muguwar mace, shaf a tunaninsa dagaske ta yarr da takardar tsiren,
ashe makirar abinda ta shiryamasa kenan. Ya numfasa gami da share zufa ya na duban Nene
batare da ya ce uffan ba.
Nene wacce zuciyarta ta gama kaiwa bango ta fisge mayafin kanta ta had'iye miyan da ya taru
a bakinta tsabar na ranta ya biya ta ci d'amara ta hau tafa hannu.
"Allah na godemaKa da ka nunamin abinda ke faruwa a bayan idona! Ashe daman cuta ta ake
yi ana dawowa idan bana nan? To yau dubunku ta cika Mati, yau sai an bambance tsakanin aya
da tsak'uwa!"
Jin haka ya sanya Mati mik'ewa ya hau fad'an k'arfin hali da borin kunya.
"Ke ya isa! Yimin shiru dak'ik'iya kawai! Kin shigo gida ba sallama ba komai sai wak'en banza
sannan ba ki tsaya kin ji dalilin dawowata ba yanzu kishi zai kaiki ya baro ki!"
Kafin Nene ta samu bakin magana, Abulle ta saki wata dariya irin ta wadanda duniya ta yiwa
dadi.
"Kai namiji, namiji akace buhun k'aya. Sannunka munafuki, inace mun fi awanni biyu tare? Duk
dai abinda za'ayi sai dai a yi don ba na tsoron kowace mai yanayin kul6a, miji ne mun yi
aurenmu na soyayya muna zaune lafiya yana kawomin kayan mak'ulashe koda kuwa ba kwana
na ba, sai a mutu!" Da jin haka Nene ta zabura ta yi kanta ta na faman surfa ruwan ashariya.
"Yau sai na nakasa ki tsohuwar bazawara mai bin maza, saidai wannan tsohon gurgun ya k'ara
haifar wata."
Ai sai su ka shiga kokawa, Nene ta daddage ta ba ta kyakkyawan cizo a mamanta wanda ya ke
fata ce kawai. Wani ihu Abulle ta saki gami da fad'in.
"Kan uban can!" Ta cafki jan gashin kan Nene mai kama da gemun ɗan Bunsuru ta hau ja da
k'arfi, ta kuwa shiga ihu har zaninta na fad'uwa sai ga ta zirr babu ko d'an bante. Mati ya tafi da
gudu ya d'auki zanin ya na kokarin suturceta ganin magulmatan makwaftansu wato Gidan Delu
da Gidan Shafa har sun soma lek'e ta Katanga.
"Menene haka? Ke Abulle don iyayenki sakarta!"
Wani turi da Abulle ta yiwa Nene sai kuwa ta jefata jikin Mati su ka yi kyakkyawan zubewa a
k'asa abinka da siririn mutum. Da sauri Nene ta mik'e ta suturta jikinta ta na huci.
"Shegiya mai kalar mayu zan yi maganinki a gidannan, za ki san kin shigo gidan Nene."
Wani banzan harara Abulle ta watsamata sa'ilin da ta ke gyara zaman rigarta.
"Yanzu aka fara tashin hankula a gidannan muddin ba za ki fita a harkata ba. Mace ba ta ajiye
komai ba sai ta ci ta yasar da k'aton kashi a masai! Gwara ni, tunda ko ba komai na yi 6ari an
ga shaida!"
Nene ba ta jira komai ba ta nufi wajen girkinsu ta rarumo ta6arya ta taho a guje, ai Abulle na
ganin haka ta fad'a d'akinta, ga shi ta kasa d'aga labulen kaban k'ofar d'akin hakanan kawai ta
turo kyauren.
Nene ta tsaya ta na huci ganin Mati ya sha gabanta.
"Shegiya kai, ashe ke 'yar iskar k'arya ce, yo ki tsaya mana idan ban nakastaki ba anan."
"Haba Nene, ya isa hakanan, muje daga ciki ki ji."
Fad'in Mati hankali a tashe don shi har ya rasa ma yanda zaiyi ga makwafta 'yan gulma na
kallo.
"Haba ke kuwa Nene, ki yi hakuri mana."
Fad'in Delu kenan cike sa tsegumi.
Wani banzan kallo Nene ta watsamata, sai lokacin ta lura da tarin magulmatan makwaftansu da
ke lek'e.
"Kai! Allah Ya tsaremu da munafukai, mutane ba su ajiye komai ba banda munafunci da gulma,
dadin abin dai mijina bai ta6a jibgata ba kuma bai ta6a haikewa wata ba."
Delu wacce tasan ita miji ke jibga ta ja tsaki ta ce.
"Oho dai! Duk acikin so ne." Daganan ta bar lek'en tare da yanmatan yaranta uku. Ita Shafa
salin alin ta sauka ba ta ce uffan ba, to ina bakin magana tunda tasan da gaske mijinta kwarto
ne na a kwantanta.
Dakyar dai Mati ya kashe rigimar tare da alk'awarin zai kawomata na ta k'unshin tsiren. Abinka
da kwad'ayyiya kamar Asma'u a gari, ba musu ta hak'ura.
*** *** ***
Abulle ta ta6e baki.
Mati bai ko kula ba ya ci gaba da maganarsa.
"Sanin kanki ne dai Inna ba ta damu da zuwa k'auyen nan ba tunda Baban su Ladiyo ya
d'and'ana mata zaman birni, yanzu kuma musamman don ni za ta zo ayi zumunci. Don Allah
Abulle, ke ce k'arama, ke ce kuma ba ta sani ba, ki taimaka ku zauna lafiya har ta tafi. Sannan
inda hali inason ayi wani abu." "Menene shi?"
Ta fad'i da sauri.
Ya yi shiru sai kuma ya numfasa ya sassauta murya.
"K'aryar ciki."
Gaba daya ta zaro idanu ta na dubansa. Ta murza bajajjajen hancinta.
"Yi min gwari-gwari dai."
Ya hau bayani.
"Inna ta sanarmin cewa muddin ta tarar kema ba ki da ciki to lallai za'a samu matsala don kuwa
sai na sake ki na yi wani auren. Ni kuma kinsan dai ina sonki ina son zama da ke, don.."
"Tsaya tsaya Mati, shi ke nan wannan abu mai sauk'i ne zan yi, sai dai menene ribar? Wace
kyautar bajintar za ka samu bayan hakan don nasan halinka, ba ka aikin banza."
Ya yi 'yar dariya ya shafi sumarsa.
"Kai kai Abu tawa ta kaina, kina da saurin fahimta kam. To bari ki ji, akwai wata tafkekiyar gona
ta Inna da kuma gida da ta ke bayar da haya ana biyanta balas duk karshen wata, ba yanda
ban yi ba akan ta bani gonar ta k'i, to ta tabbatarmin za ta bani har da k'arin gidan nan ya zama
mallakin jikanta." Abulle ai sai ta hau tsallen murna da sakin gud'a.
Mati ya hau rufemata baki a tsorace.
"Ke ki rufamin asiri kada waccan ta ji."
Tunanowa da Nene da ta yi ne yasa ta saurin sai ta kanta.
Page 2
Daga waje kuwa Nene na jin haka sai ta yi wuf ta fito daga maɓoyarta, can baya take zagayawa
ta hau kan ɗan dutse tana kasa kunne a ƙaramar tagar ɗakin Abulle. ta na yi tana leƙa bayanta
ko wani zai taho wucewa kasancewar daga nan ana hangen waje a dalilin gajartar katangar.
. Ɗakinta ta shige da saurinta, jiki na rawa ta hau sauke kwallayenta tana faɗin; "Idan sammako
ku kayo, ni asubanci na yi."
Ta fiddo wani maganin gargajiya wanda tayi mugun tsanar warinsa, sannan ta mai da kayan ta
afka garin kusan rabi a baki. Kan ka ce mene wannan cikinta ya murɗa ga yunƙurin amai da ta
soma. Ai a guje ta fito ta isa gaban makwararar ruwa ta hau sheƙa aman iyakar ƙarfinta tana
nishi yanda ta tabbatar za su tsinkaya... "Ni fa kamar kakari nake ji." Cewar Mati yana kallon Abule.
"Kai fa daɗi na da kai har yanzu baka bambance kukan Jakinka dana Akuyar Delu."
"To idan ma itan ce kinyi zaune salon tamin ta'adin da ta saba?"
Ya faɗa yana mai mi'kewa tsaye, itama da sauri ta mi'ke tana mai rufa masa baya.
Ita ɗin ma ta wajen jin tahowarsu ya sata zubewa gefen kwatamin tana mai ri'ke cikinta da faɗin
"Wayyo! Mati..."
Da gudansa ya 'kara so wajen yana mai janyeta gefe.
"Ikon Allah! Nene ashe ke ce. Sannu me kika ci ne haka?"
"Ba komai tun safe nake jin tashin zuciya da rashin jin daɗi."
Ta faɗa da ƙyar tana sauke numfashi.
"A'a irin wannan ciwon ai ba na shiru ba ne Nene, karki manta da haka Sahura ta mutu da irin
shirun nan."
"To Mati ana ta kai wa yake ta larura? Taimaka min zakai Abule ta dubomin 'Yar Magaji, ji nake
kamar ana daka yaji a kirjina."
"Huu'umm!" Abule ta faɗa tana tafa hannu.
"Ai wallahi da aiken kishiya gwamma na jibgi Uwar miji. Kai ni ban ma yarda da wannan ciwon
ba. Saboda Allah Mati baka ji warin tazargaje ba?"
Ta faɗa tana mai ɗaɗɗaga hanci sama.
"Me kike nufi ne? Kinga Abule ban san fitina, ya mutum na halin ciwo kina kawo shashanci. Idan
na isa dake to maza ki je ki dubomin 'Yar Magaji."
. Mintuna kaɗan Abule ta dawo da 'Yar Magaji biye da ita ta rataya wata tutturna jaka me
kama da ta wazirin Sarkin kutare.
Kallo ɗaya tama Nene maƙaryaciyar zuciyarta ta kisa mata menene,
dan haka ta kalli Mati da murmushi.
"Malam ai ba wata larura ba ce mai girma, ƙaruwa ce zaku samu, a taƙaice dai Nene ciki gare
ta har na tsawon wata biyu."
"Kan babban bala'in can! Alkur'an wannan ƙarya ce."
Abule ta faɗi tana mai buga tsalle gefe, kafin kuma ta yi ɓarin da Nene ke kwance.
"Ke Nene ki ji tsoron Allah, ina ce ba shekaranjiyar nan muka gama rikici kan tsumma na da
kika yaga kikai kunzugu da shi ba?"
"Wayyo Ni Abule! Yau na ga abinda yafi 'karfina, wai cikin ma har kinsan ya yi wata biyu sai ka
ce wacce kika haɗa iri da Mayu. ke kam 'Yar Magaji anyi tantiriyar ma'karyaci wallahi. Matar da
ake raɗe-raɗen Aljanu sun sace mata mahaifar ne ke da ciki?"
"Ke! Ke! Abu kin cika mana kunne da shegen karaɗi. Ki tsayamana abu abin a sannu idan ma
ƙaryar ce ai 'Yar Magaji za ta faɗi.
"Wane irin bi-sannu Mati? Ai fa magana ta riga ta ƙare, Nene dai ciki gare ta, maganar ganin jini
kuma wanann a bayyane yake, ko Magaji ka tambaya zai idar maka wannan zance. Lalle ne
akwai Matan dake jini da ciki. "
"Ke kuma Abule da kika haɗa Ni da Maita ina jin dai tsohonki shi ne Bazawari na? Dan haka
bushiya dai ba zata wa Kunkuru gorin ƙafa ba , ko zaki mutu dai Nene ciki gare ta na wata
biyu."
"Kai kuma yanzu ya rage naka sai ka dinga mata abinda take so. Ni kaga tafiya ta."
Page 3
"To ai sai ki kauce daga samanmu tunda dai shegen baƙin cikinki ya jawo kinji abinda Tsohonki
ke aikatawa a waje."
Mati ya faɗi yana hararar Abule da tayi tsaye hannu bisa ƙugu tana jinjina maganar 'Yar Magaji.
"Oho dai, daɗin ta Bazawari aka ce ba Ɓarawon Jakai ba."
Ta faɗa tana hararar Nene dake yatsine-yatsine.
.
"Kyale ta kinji Nene uwargidan Mati, muje na raka ki ɗakI ki kwanta, daga yau ko tsinke ban
yarda kin ɗage a gidan nan ba, wanda ba zai iya gani ba yayi zuciya mu gani a ƙasa." Ya faɗa
cike da lallami.
Ita ɗinma miƙewa tayi cike da kwarkwasa har da riƙe rigar Mati. Gab da zata ɗaga labulen kabar
ta ne ta waigo ta kalli Abule fuskarta ɗauke da murmushin kaɗan kika gani.
Dogon tsaki itama taja tana hararar ɗakin bayan shigewarsu. "Wai Kura ce ta samu damar miƙe
ƙafa, ayi dai mu gani, muna nan za ka zo kana min 'yar murya. Har yaushe ma akai daren?" Jin
shiru ba su amsata ba sai tashin dariyarsu da take ji ne ya sata juyawa a fusace zuwa na ta
ɗakin. Kwana biyu gidan shiru daga uhumm sai hu'umm wai uwargulma tayi cikin shege. Duk san
Abule na ta gane gaskiyar cikin Nene abun yaƙi yiwuwa. Sai ma barinta da takaicin arba da
ledar Burodi da Tsire da take yi kullum safiya. Idan ma ta yi dakon hana ido barci dan a kasa da
ita Mati baya shigowa gidan sai dare ya raba, kafin ta gama barcinta ya kaɗa na sa Jakan yayi
gaba tsabar rashin gaskiya.
Sauri take ta isa gida, dan ta fara gwada maganin saka laulayin da Gwaggonta ta bata ta dinga
shansa duk dare, bayan ta sanar mata da abinda ke faruwa a gidansu. Ta tsinkayi muryar Delu
na kwaɗa mata kira.
Kamar ba za ta tsaya ba, sai dai taja tunga ganin Delun harda ɗan gudunta.
"Uhm! Tunda na taho nake Addu'ar Allah ya sa na ganki, dan kuwa ba za ai wannnn cin Amanar
a gaba na ba."
Gabaɗaya ta mai da hankalinta kanta
"Me ya faru Delu? Na sanki baki maganar banza."
"Ke dai Allah ya raba mu da Miji mai ɗabi'ar hankaka. Mati na gani yanzun nan gun 'Yarbaiwa
mai Fara ya sai har ta Naira Hansin wai Uwargida ke kwaɗayinta, baki ganta ba fal ledar..."
"Fara fa kika ce? Farar da tunkan muyi aure yake min alƙawarin cinta?" Ta tari numfashinta.
"Idan ƙarya nake miki wannan zance tsawar bana ta sauka gonar Malam Alkur'an."
"A'a me na jan masifa? Zai yi fin haka ko dan ya nunan shi Namiji ne kwandon zawo, barni da
shi, yau ko zai mutu ba za ta ci Farar nan ita kaɗai ba. Ke har ke sai kin ɗanɗana, na gode miki
Delu, bari na ƙarasa gidan.
Da sallamarta gidan ta yi jifa da kallabin kanta gefe, luma yatsunta ta yi cikin gashinta ta fara
wargaza shi, kan kace mene wannan ta tada hankalin gashinta ya yi tsaitsaye tamkar gemun
Mahaukaci da ya shekara ana jifansa. Nene dake gefe ana ƙoƙarin sai ta kai, sai gani tayi Abule
ta zube tana wani nannaɗewa, doka ihun da zata yi sai ga shigowar Mati yana mai da aljihunsa
baya. Ganin Nene jiki na ƙyama ya sashi yin wurin Abule yana salallami.
"Karka ƙaraso! Kana ƙarasowa idan muka fyauɗe ka sai ka dangana da Gyatumarka" Yaji
murya na gargaɗinsa kamar ta Kuyangar Kutare.
Turus! Yayi ƙafafuwansa na rawa kafin kuma ya zube ƙasa yana kallon yarda Abule ke naɗewa
bakinta na dilalar yawu.
"Kiyi haƙuri Abule wallahi bansan kina da larura ba."
Ya faɗa kamar zai fashe da kuka.
Taja majina.
"Kai! Ka iya bakinka, wanann ba lalura ba ce, kai ne ka kira mu da kanka da kake taɓa mana
Goɗiya kana sa ta kuka."
Ta faɗa tana zare manyan jajayen idanuwanta.
"Ƙarya take min bantaɓa sa ta kuka ba, Nene shaida."
"Munafuki menene wannan a aljihunka na hagu?"
"Fa..fa ...fara ce."
"To wa ka siyo wa?"
"Abule mana, ita ce Amarya ta da bana iya motsi sai da ita."
"To bawa waccar ta kawo farar nan gabanmu, gargaɗin ƙarshe kuma ka kuskura ka ƙara kawo
ko Dusa ce ba ka haɗa da Goɗiyarmu ba sai mun musanya mata yaron cikin da take ɗauke
dashi da Kadangare."
"Ban..ban..gane ba..."
"Au! Dan fitsara ma baka San Goɗiyarmu na da cikin ka ba?"
"Na sani, ku yi hakuri. Ke Nene miƙa musu Farar mana."
Ya faɗa yana jefa mata kullin ledar dake ta kyallin mai .
Abule ta kalla idonta kamar zai faɗo dan tsoro, gani take kamar bakinta ma ya koma gefe, dan
haka ta Yi baya cikin hawaye.
"Ba zan iya ba Mati."
"To kuwa zan fita na barki da su, ki miƙa musu ko za su tafi."
Ya faɗa da tsawa.
A ɗarare ta miƙa ledar gaban Abule dake naɗe, a guje ta juya zuwa ɗakin ta ta lafe bayan kaba
tana hangen su.
Ƙatuwar Hamma Abule ta saki, kafin kuma ta ɓingere gefe maƙale da ledar farar ta. Akwai
alamun Borin ya sauka.
*** **** ***
Page 4
Assalamu Alaikum mutan gidan." Fad'in 'yar doguwar dattijuwar kuma tsamurmura mai
sharɓa-sharɓan tsagu a gefen bakinta, bak'a ce wuluk kamar d'anta Mati. Mati ne a gaba d'auke
da k'aramar akwatin kayanta, ita kuwa tana biye da shi a baya.
Abule ta soma fitowa daga d'aki sai Nene daga band'aki suka saki baki suna kallonta.
'Ikon Allah, wai na kwance ya fad'i.' Cewar Abule kenan a k'asan ranta ganin shigar da surukar
ta su ta yi, wata k'aramar Atamfa Super ce ajikinta an mata dinkin riga da siket sai wani babban
mayafi da ta yafa a kafad'a ba rufin kai ba. Fuskarnan ta sha farar hoda, ba'a gane wa
sakamakon bakin fatarta da ya ciza saidai kuma kana gani ka rantse yanayin hunturu ne wanda
ya yi sanadin da fatar fuskar nata ya bushe ya yi furu-furu, ga uban jan janbaki da ta lafta a
le66anta masu tudu.
A hankali Nene ta maida dubanta ga Abule, akayi sa'a itama ta kalleta sai kuma suka sauke
ajiyar zuciya kafin kowaccensu ta shiga rububin tarbarta da amsa sallamarta.
"Waalaikumussalam, lale maraba." Fad'in Nene kenan ta karasa bakinta a washe ta kar6i
akwatin Inna, caraf itama Abule ta sanya hannu da zummar kwacewa ta kai nata d'akin.
"A'a menene haka? Yaushe akayi daren kuma da har ace gari ya waye? Malama sakarmin."
Cewar Nene ta na k'ara jogana akwatin a jikinta.
Dole Abule ta saki tana harararta ta karasa wajen Inna cike da kissa ta ce.
"Maraba Inna."
Inna ta hau k'arewa Abule kallo, eh kam ta yarda da rahoton da Aminiyarta Ladidi ta kai mata
game da Amarya d'an nata. Ta tabbatar mata tafi Nene tsafta kuma ta ga alama. Sai dai kuma
ta kasa fahimtar me ya ja Mati ga aurenta? Wannan abu a dunk'ule haka?
"Yauwa sannunki kema."
Ta fad'i tana mai k'arasawa ta zauna a saman tabarmar da aka shimfid'a. Nene za ta yi ciki da
kayanta ta yi saurin dakatar da ita.
"A'a 'yarnan dakata."
Zani na kuncewa tana sake d'aurawa ta karkata k'ugu ta tsaya gami da dire akwatin tana jan
majina.
"Na'am, to."
Inna ta yamutse fuska.
"Ai kuma sai dai wannan karon ki hak'ura don a d'akin ita 'yar uwarta ki zan sauka. Na gayamaki
bana son kwana kan wannan gadon