Showing 3001 words to 6000 words out of 11892 words
naki mai warin hammatan wanzamai, da kyar idan kin
chanja wannan tsohon zanin gadon wanda na gama yayinsa tun jegon mijinki. Ba wa abokiyar
zamanki akwatin na ga na ta kamun ludayinta." Ai sai Abule ta kece da dariya, kallon banzan da Inna ta watsamata ne ya sanya ta nutsuwa.
Nene ta cika ta yi tam! Yau ita Inna za ta ci wa fuska akan Abule? Lallai ya dace ta zage
damtse.
Tana numfarfashi ta zauna, Inna ta dubeta sannan ta k'ara duban Mati.
"Wai ni Mati wacece me juna biyun a matanka?"
Mati ya hau washe baki.
"Ai duka biyun ne."
Inna ta kwalalo idanu cike da mamaki tana duban Nene, karshe ta sauke idanunta akan Abule
da ta zauna tana wani sussunne kai ita a dole kunya. Sai kuma ta hau tafa hannuwa da shewa.
Farin ciki ya cika su don a zatonsu ta yarda suna da cikin. Sai dai ga Inna kuwa sam zuciyarta
ba ta amince Nene na da ciki ba, shekaru nawa da aka yi ta rad'e-rad'in ba ta da mahaifa, ai
kuma ta saka ayar tambaya. Dabara ta zo wa Inna.
"Yau na ga abin al'ajabi, to ai shikenan, zama ya kamani a k'auyen nan duk da ba na so, amma
zan zauna har na ga 'ya'yanka Mati."
Hanjin cikin Nene da Abule ya kad'a sai dai kowaccensu ta yi fuska. Mati kuwa wani dad'i ne ya
mamaye zuciyarsa ganin burinsa ya kusa cika.
Abule ke da girki ita ta shiga hidima da Inna, Nene kuwa d'akinta ta fad'a tana tunanin mafita
nan gaba.
*** *** ***
Bayan kwanaki hud'u da zuwan Inna ana zaman lafiya kowacce ta ciki na ciki. Karshe kuma sai
Mati ya tsuro da wuni a d'akin Abule wai hira da Inna, haka za ta yi ta tsinkayo dariyarsu.
Da abin ya isheta ta shirya ta nufi gidan 'Yar Magaji don neman mafita. Tana isa ta
zayyanemata komai, 'Yar Magaji ta buga uban tsaki.
"Ke ce ai ki ka yi sake da ba ki mallake Mati tun fari ba, yanzu da komai zai zo ma ki da sauk'i."
Jin haka Nene ta gyara zama.
"To yanzu ya za'ayi."
'Yar Magaji ta d'an yi jim, sai kuma ta saki dariya ta mik'e ta fad'a d'aka. Can sai ta dawo d'auke
da k'ulli ta mik'amata. Nene ta hau jujjuyawa.
"Na menene?"
'Yar Magaji ta d'an murza hanci tsabar warin da bakin Nene yake yi kamar na 'yan ga ruwa.
"Kinga wannan, k'asar k'ark'ashin gadon ma'auratan da suka tsufa tare ne suna soyayya,
matuk'ar kin yi turare da shi na kwanaki uku Mati ya kusanceki to an gama."
Nene ta girgiza kai.
"Matsalar mun fi wata biyar bai nemeni ba, ni kinsan na tsani a maisheni jaka."
Wani kallo 'Yar Magaji ta yi mata sai kuma suka kwashe da dariya 'Yar Magaji na kauda kai.
"Dad'ina da ke ba dai warin baki ba."
Nene ta muskuta tana shafa bakin.
"Um to ya na iya da abinda ya fi k'arfin wuta?"
Ta6e baki 'Yar Magaji ta yi.
"Ke ki ka so, ni yanzu dai kinsan ina jiran kaso na, makira ai ina shigowa daman na ga
yanayinki na gane makircinne ya motsa."
Nene ta dara.
Suka gama k'ulle-k'ullensu dai Nene ta koma gida da zummar soma gabatar da aiki.
Page 5
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Inna ta d'aga hanci sama taja iska, sai kuma ta furzar ta baki tana hararar kwanukan da Nene ta
aje gabanta.
"Uhm ni wai da mushe kikai miyar ne Nene?"
"Me kika gani Inna?" Nene ta fad'a tana so sa kai.
"A'a gani nayi tunda kika doso gurinnan ya cika da tsami da k'arni tamkar wacce ke aiki a kwata
ko mutuware."
'Ai fa, komai na yi ban burge ba, to ai sai dai ki mutu, aikin na Mati ne, mallaka kuma tawa ce,
sai shegen kinibibi da wani bakinta kamar na ba'kar Akuya...' Ta faɗa da gunguni
"Me kike cewa ne?"
"A'a cewa na yi Binta Sudan ne na balbala a jikina saboda kiji ƙamshin."
"Ko kuma Binta Maliya ba? To wanann dai ƙarni yake sai a sake lale, ki kwashe kwanukan nan
daga gabana, anjima zansa Mati ya karbomin Abincin daga gidan Larai."
"Uhm gaba ta kaini, dama ke na tsamewa kai da ƙafar kazar." Ta faɗa da 'kun'kuni tana tattara
kwanukan.
"Baki ji ba" Inna ta fad'a
"Ina ji Inna" Ta fad'a tana gabda barin d'akin.
"Idan gyaran zaki yi ki fara gyara can cikin, shi ne ko da kinsa turaren zamu ji dadinsa, amman
wanann in gayamiki gaskiya yau sai an turaramin dakin nan da miski zan iya zamansa. Yanzu
haka sai na sha kanwa sabida kumburin ciki."
"To masharranciya." Nene ta fadi a hankali tana barin d'akin a fusace.
Abule dake maƙe a gefe tana sauraro ta k'yak'yace da dariya tana juyawa Nene mazaunai.
Nene ta yi kwafa tana gyaɗa kai, kafin kuma ta yi dakinta tana mai sauke kaba.
Gab da Maghriba Abule na tsakar gida tayi ɗaurin kirji, da zabira a hannunta tana tsifar kai. Can
daga k'ofa kuma Nene ce zaune tana gyaran Tafasa tana yi tana sakin habaici a waƙe.
"Munafuncin dodo dai mai shi yakan ci, yau ba jumma'a ba idi ba, ba kuma kwanan mutum ba
ya d'au niyyar wanka harda tazar kai na asara." Nene ta faɗi da karfi tana hararar Abule."
"Oh ni Abu? Lalle idan ta karewa kare barin haushi yake ya koma tunkuyi, na ga dai abin rabo
ne auran Mace da ciki. Ki gwada naki salon mana mu gani, ai wani asirin baya ci da turaren
hayaki sai an had'a da yan dabaru."
"Uban wa ke asiri da turare?" Nene ta faɗi a fusace tana ture fai-fain tafasa gefe."
"A'a ai kinji matsalarki baki cin ribar magana, yanzu mene na sakin na maguzawa a wannan
hirar? Ni kinga wucewata yin abinda zai fisshe Ni. Ta faɗa tana mai sunkutar bokitinta ta fada
Makewayi.
Nene ta ciji yatsa tana mai tura baki gaba, sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan da
Abule ke d'orawa saman yar katangar bandakin ta langa-langa. Abin mamaki harda wani tsohon
dankwalin wata atamfarta me fanteka da mati ya sa mata tun a toshi. Har dai ta juya zata wuce,
sai kuma dai ta sake juyowa tana kallon katangar zuciyarta na kiyastamata abinda Abule ke yi
da kaya haka. Nan fa idanuwanta suka sake sauka kan wata tsummar rigar Mati da tun yana
Saurayi ta sanshi da ita. Wani makirin murmushi ta saki da ta gama hasaso abinda take zato. Ai
sai tayi gun 'yar katangar a hankali ta janye kayan bata bar mata komai ba sai zanin da zata
yane jikinta.
Da sauri tayi ɗaki gurin Inna dake gyangyadin shaiɗan na gabda Maghriba. Itama Innan sai da
ta firgita na ganin yarda Nene ta fad'o Mata ba ko gafara dai.
"Lafiya Nene kika katsemin barci haka dan rashin mutunta Uwar Miji?"
"Bari dai Inna, ai abinda na gani yau idan ban sanar miki ba na cika ma-ci Amana, na rantse
miki da izifi sittin Abule cikin zani gare ta. Idan baki yarda da batunnan ba biyoni kofar
Makewayin ki gani."
Inna ta watsa mata wani kallo she'ke'ke, sai kuma ta mi'ke tana tura d'aurin kallabinta gaba."
"Muje na gani." Ta fad'a tana yin gaba.
Abule da ta gama jika-jikan ta mi'ke za ta mai da zannuwanta ta d'aure yanda ta saba, ai sai ta
tarar babu, ta d'auka ko baya suka faɗa dan haka ta fito a sad'ad'e tana Addu'ar Allah ya kau da
idon Nene har ta kwashe. Sai dai fa turus! Ta yi ganin Inna da Nene tsaye tana sakar mata
dariyar Mugunta. Jiki na tsuma ta sunkuyar da kanta 'kasa. "Shegiya guntuwa me bakin hali, abinda ban zaci gare ki ba sai gashi ya tabbata gunki. Uwar
wa ta koyamiki wanann kinibibin ko dan ganin yar uwarki na da cikin? Inna ta faɗi tana mai kai
mata rankwashi a jikakken kanta.
"A'a Inna lafiya kike bugurmin Abule" Mati ya faɗa da shigowarsa kenan.
"Zaka rama mata ne? Sha-sha-sha kawai, Matarka na cikin Zani dan sakarci ka kasa gane wa."
Ya kwalalo ido yana dubanta, sai kuma ya hau sosa kai yana noƙewa.
"A'a Inna ya za ai na sani, abinda rabon da ayi abu tun watan shekaran jiya.
Ai sai Inna ta hau tafa hannu da Sallallami.
"Haka Auren ya mayarmin kai Mati sai abinda Mace take so?Mene amfanin auren idan ba za ka
taki mace tamkar gona ba? Ya kinan baƙar Munafuka sai kin faɗimin abinda kike bawa dana da
har kike juyashi haka ko kuma ki tafi gidan Ubanki wallahi."
Ta faɗa tana jawo gashin Abule. Da sauri Mati ya shiga tsakani yana faɗin "Sakarta Inna."
Da dai Abule ta fito daga hannun Inna ai sai tayi kan Nene dake ta sheka dariya a fusace tana
faɗin " Bazan fita Ni kaɗai ba sai da ke bakar mujiya muga naki cikin mana in gaske ne." Ta kai
mata wawura.
Nene ta kankame jikinta tana ture Abule, ta ɗaga hannu zatai naushi, Abule tayi nasarar
bankare hannun ta kuwa gatsa mata cizo a hammata da dazunnan ta barbadawa hammatar
toka dan ta rage tsami, ai kuwa bata ɗaga bakinta gurin nan ba sai da ta cisge gashin
hammatar Nene har jini yayi tsartuwa. Nene ta saki ihu tana dafe hammatarta. Abule kuwa ta yi wuf! Ta fisgo zanin Nene sai ga tullin
tsummokara ɗaure a ciki. Wani abin mamakin har da wani koren Gajeran Wandon Mati da ya
gaje shi tun gurin ƙaninsa yasha doyin jakai da warin fitsari, da Mati ya shafe shekara yana
nemansa, yau sai gashi a cikin Nene ɗaure...
Page 6
Inna ta hau tafa hannuwa tana salati iyakar k'arfinta, kan ka ce me magulmatan makwaftansu
sun hau lek'e cike da al'ajabi.
"Yau na ga abinda ya fi karfina ni Uwar biyu! Kai! Kai! Wallahi ba za ta sa6u ba, Mati!"
Ta juya ga Mati wanda zufa ke ta karyomasa, gabadaya ya susuce, daman ita Abule ya san
k'arya ce ta shukamasa musamman da ya ji tana maidawa Delu irin tuggun da ta shirya na iska,
ita kuwa Nene bai ta6a kawowa k'arya ta ke ba, a zatonsa idan Abule ta ɓata rawarta da tsalle
to yana da mafaka a wajen Nene. Sai dai ashe dukkansu taron na ayya ne. "Eh dole ka rasa bakin magana mana! To wallahi ba za ta sa6u ba! Ko ka k'ara aure ko kuma ka
saki kowace shegiya ta koma akurkin ubanta. Za6i ya rage naka, yanzu na ke son amsata."
Inna ta k'arashe tana gyara zaman siket dinta na buje. Nene da Abule suka shiga tashin
hankali, kada fa su yi biyu babu.
"Kai nake sauraro ka tsayamin k'erere kamar liman ya manta Fatiha."
Mati ya saci kallon Matansa, to da ya rasa tafkekiyar gonar Inna da kuma gida ai ya gwammace
ya k'ara auren ya samu haihuwa.
Ya mai da idanunsa kan Innarsa.
"Shikenan, ki nemo min mata."
Ai sai Inna ta rangad'a gud'a.
"Ayyiriririii! Haba ko kaifa, yanzu na tabbatar da cewa kai jini na ne. Sai ka shirya don kuwa
yanzu za ka yi aure."
"To amma..."
"Amma me? Inna ta katseshi tana harararsa.
"A'a wai dama gani na yi su biyun ma mangalar jakai na biyu bata iya rikesu da ita, shi ne nake
tunanin kar ta ukun ta shigo kuma idan ina cin abinci sau biyar a rana na dawo sau uku."
"To batunu ƙiyama sarkin ci, in ce dai gidan nan nawa ne?"
"Naki ne har ni d'inma." Ya faɗa yana dukar da kai.
"To tunda ni zan ma auren mene na tunani? Idan ta ciyarwa kake zan ƙarama akuya da rago ka
kiwa ta. Ina ce dai shi ke nan?" Ta waigo ɓarin da su Abule ke tsaye.
"Ku kuma sai ku shirya don kuwa falleliyar budurwa zan samar masa, ba irinku zawarcin titi ba."
Bak'in ciki ya turnuk'e Nene da Abule. Musamman Nene da ta tabbatar bata kai na ta matancin
ba, amman dai ai ita ce ta fari, kuma ma ta toshe yanda ba za a gane ba, don haka ta karkata
baki.
"Allah na tuba ko dubu zai auro ba kamar ni a zuciyarsa, ni ce dai Nenen Mati, kaf k'auyennan
an shai da soyayyarmu."
Inna ta bankamata harara kawai ta wuce d'aki. Shi ma Mati da saurinsa ya fita ya hau jakinsa ya
fice. Abule ce ta saki shewa.
"Aikin banza wai bille a d'uwawu, duk dai abinki bai sanya an fasa auroni ba, dad'in abin ma ba
abinda bansani ba. Ina ce da sa hannun aljanu da 'yan bori a aurenki da shi ko?"
Nene ta fusata, za ta kai mata bugu tuni Abule ta nufi d'aki, ta mai da dubanta ga masu lek'e.
"An yi asara munafukai da tsakar rana babu ko kunya!"
Babu wacce ta tankamata acikinsu, ta gama haukanta ta fad'a d'akinta.
BAYAN WATA BIYU
Ta faru ta k'are, duk wani shiri da gyare-gyaren da ya dace a yi na zuwan Amaryar Mati an
kammala, amaryar ba wata bace illah Faɗime d'iya ga aminiyar Inna, Ladidi. Daidai da lefe Inna
ce ta koma birni tare da Ladidi suka haɗo. Abu kamar wasa dai aka sanya biki sati biyu, duk irin
borin Nene da Abule bai sa an fasa ba, ganin babu Sarki sai Allah ya sanya suka hak'ura.
An kawo Amarya lafiya lau da gud'a da komai, cikin 'yan rakiyarta har da Shafa da Delu.
Kwanan Amarya d'aya a gidan Inna ta tattara ta koma birni da zummar sai nan da sati biyu za ta
k'ara lek'owa.
Nene na zaune ta tsefe kitsonta wanda ya kusa shekara yayin da Abule ke kwance saman
tabarmar kaba tana jifanta da wak'e-wak'en habaici tana ramawa suka tsinci muryar Mati da
Amaryarsa suna shek'a uwar dariya, suka dubi juna da sauri kamar wadanda aka mintsila suka
nufi k'ofar d'akin nata har suna bangaje juna, ƙarshe dai suka nutsu suna lek'esu. Amarya Faɗi ke kwance saman cinyar Mati, shi kuma yana yagar tsire yana sa mata a baki
suna hirarsu cike da nishad'i. Nene ta dafe kirjinta gami da had'iyar yawu. Ba ta jira komai ba ta
yi wuf ta shige ganin haka Abule ta ja baya tana mai rike ƙugu.
"Kan uban can! Wato Mati dama amanarmu ku ke ci? To wallahi ba za ta sa6u ba! Sai dai ayi
raba daidai!"
Za ta d'auke ledar naman Faɗime ta cafke hannunta ta mik'e tsaye.
Baki Nene ta saki ganin shigarta.
"Riga da wando a gidan nan? Jakar Uba! Mati karuwar birni Innar ta auromaka ashe banda
labari?"
Harara Mati ya sakarmata bai ce komai ba don wani sa'in yana shakkarta. Faɗi ta kauda fuska
gami da murgud'a bakinta da ya sha jan baki.
"Ke Malama don Allah ki bar nan wallahi warinki na tayarmin da zuciya. Ga dukkan alamu dai
ko wankan tsarki ba kya yi."
Ta saki hannunta.
"Kuma wallahi ki ka k'ara ta6a ledar nan sai na miki ihun mahaukaciya. Ce miki akai Ni
haɗamammiya ce irinki? Ga naku kason can a gefe dan bazan yarda Miji na ya tashi da
shanyayyen ɓarin jiki ba ranar gobe ƙiyama."
Nene ta hau tafa hannu da shewa.
"Hehehe! Yau nake ganin bariki a gidan nan, ashe kuwa yau wata za ta bi tsohon najadu
barzahu. Idan kin fasa kirana mahaukaciya ba ki cika d'iyar Ladidi mai siyar da kayan maye ba!"
Fad'in haka keda wuya, ta kai hannu za ta d'auki ledar, Faɗime ta damk'i gashinta ta mai da ta
baya, tayi taga-taga za ta fadi k'afar Mati dake ƙasa ya miƙe ta kwashe ta sai gata Tim! A ƙasa
tayi zaman 'yan bori.
Faɗi ta juya da Mini-minin idanuwanta ta dubi Mati "Sannu Maigida bata dai jima ciwo ba ko?"
Mati ya washe baki ya ce "Faɗi Amarya ina gabanki ai bana jin ciwo."
Ta yi masa far! Da ido ta ce, "Mai gidana na sha ce maka Timah zaka dinga kirana yarda
kawuna na birni ke faɗi.
Taɓɗijam! "Yau na ga sabon salo wai tafiya bariki da Uwa" Cewar Abule daga bakin ƙofa.
Amarya ta waigo ga Nene dake baje ƙasa tana cije baki, "Ke kuma ki ci gaba da shiga shirgi na,
wallahi da ruwan sanyi zan dafaki dan ban iya dambe tsakar gida ba, balle na haifawar
maigidana talauci, ku da kuka saba kuje can ku ƙarata, ga tsiyarku nan." Ta faɗa tana tura musu
kasonsu na tsire.
Page 7
"Maigidana Randar Zuciyata, Idan ka fita kaje shagon Bakari Mai Ashana ka ce a baka Makilin
da Burushi." Mati ya washe baki yana kallon kwalelen kanta da yasha zanen shuku yana ta
ƙamshin Karkar.
"Wani sabon Abinci ne muka samu Amarya Timah?"
Ta yi far! Da ido "a'a kai dai jeka kawo za ka ga abinda zan maka da shi."
"To shi ke nan, bari na yi wanka sai na fita na siyomiki, kinsan tunda na sameki bana iya fita
banyi wanka ba.
Ta yi murmushi "Yauwa kama tunamin abinda na ce zan nuna maka rannan, muje Makewayin
na maka kaga sai na cuɗamaka baya ma."
Ta faɗa tana jawo hannunsa su fita. Fisgewa ya yi yana nuna mata waje da baki, sai kuma a
hankali ya ce "Ki rufan asiri safiya ce fa? Kinsan su Nene sun tashi kar ya zama abinda zan
kasa cin abinci yau."
"Haba Maigida Ni wallahi kanamin irin wannan sai in dinga ganinka ragon maza, ranar kwana
nane fa, kuma baka shiga haƙƙin kowa ba dan ka shiga Makewayi da ni, Matarka ce ni, ba ta
aro ba, ko ta titi, kuma ko su ka shiga Makewayi da su ba abinda zai dameni tunda na san aikin
lada ne. Ya zare ido yana dubanta "Da gaske aikin lada ne?"
"Kwarai kuwa, ai zaman Aure indai ba cuta lada gare shi."
"Au to muje, amman dan Allah saɗaf-saɗaf bana so Nene ko Abule su tsinkayi motsi na.
"To shi ke nan muje" Ta faɗa tana me yin gaba. Ruwa ta tuttula daga tulu a ɗan kwatashin
wankan na su, ta sunkutu ta yi Banɗakin da shi, shi kuma Mati ya hau kewaye