Showing 9001 words to 11892 words out of 11892 words
Kashi ya kamani.
Page 10
Ihun Nene ya janyo hankalin mutan gidan, gaba daya suka fito har da Abule wacce ta
gwaggwa6e a d'aka tana kwa6a lallen. Kan kace me tuni Delu ta gyara zamanta jikin garu tana
lek'e, itama Shafa ba'a barta a baya ba wajen ganewa idonta. Mati a rude ya nufeta.
"Nene, lafi..."
Kii! Ya ja burki sakamakon wari da k'arar sakin tusa da ya bugi kunnuwa da hancinsa. Inna ta
sanya salati.
"Me zan gani haka Nene? Wane irin shashanci ne haka ki wuce Makewayi mana" Nene dake ta
kokarin danne mazaunanta da hannu ta daddage ta ja numfashi sama tana mai hade jikinta dan
ta tsayar da gudawar, ganin kamar an kara kunnu ta ya sa ta sakin wani wawan ihun "Wallahi
ba ta tsayawa, na shiga uku ruwan jikina zai k'are. Kai Mati! Kai mati zan mutu, za ta zuƙen jini"
Ai sai ta zabura ta danna a guje zuwa karshen gidan abu na yoyo. Mati ya yi sauri ya bita ganin
ta zube gun, "Nene, nene, jin shiru ya sa shi toshe hanci yana jijjagata, sai kuma ya dago a
tsorace yana duban Inna.
"Kamar fa ba ta numfashi Inna" "kai kauce nan, wane irin ba ta numfashi matsa ni ka ga na ba
ta fastu aidi (First Aid)shashasha ko dabarun lafiya baka iya ba dake kanka ya cika da gashin
jakai." "Um Inna yanzu dai bata ba'a ake ba ki duba ta kiga ni Aradun Allah Inna ba ta motsi"
Inna ta dan na masa harara, sai kuma ta hau karewa Nene dake yashe kallo, ganin har yanzu
Abun na tuttulowa daga jikinta ya sa ta kallo Mati "Tunda dai kai ne Mijinta matso kusa daidai
bakinta ka lalubo harshenta ka gantsara mata cizo, shi ne zai sa ta farfadowa yanzu" Mati ya
kalli Inna da ta kauda kai gefe tana jijjiga kafa kamar ba ita ta fadi wannan zance ba, ya waiga
ga Abule dake matsar kwalla, ya dora idonsa kan su Delu dake bisa katanga, ai sai ya hau
girgiza kai yana mai sharce gumi "Bazan iya ba! Kwarankwatsa dubu Inna wannan zalunci ne,
ya zan ciji marar lafiya. Kuma sannan wannan ai Yahudanci ne." ai sai inna ta zabga salati tana
mai fashewa da kuka Mati ya ce mata Azzaluma, kafin kuma ta share hawayen tana mai watsa
ma masa dakuwa "To ka tsaya jahilci Nenen ta mutu, numfashin mutum na daukewa da minti
goma idan bai samu taimakon gaggawa ba yake mutuwa" Jin haka ya sa Mati yin wurin Nene da sauri yana lalumar bakinta. Da dai ya zakulo harshen ai
sai ya gatsashi da karfi. Baya ya yi yana ganin Nene ta yi wani irin cilla kafa. Tana fadi a hankali
" Na mutu Mati" cikin magagi. Abule ta ƙara sautin kukanta "Inna dan Allah mu kai ta gun kula
da lafiyan da kika kai Faɗime kwanaki" Mati ya kalle ta, sai kuma ya yi waje da sauri. Ba
daɗewa sai ga shi da mai Baro. Abule ta taya shi kama Nene aka dora ta bisansa. Suka
ɗunguma Asibitin ƙauye.
Bayan dube-duben da likitan ya yi sakamako ya fita. Nene dai banda Maleria ba abinda ke
damunta. Likita duk tambayoyin da ya yi sun tabbata ba abinda ta ci na ɓata ciki tunda dai
abincinsu guda ne. Dan haka ya daura ma karin ruwa ya rubutawa Mati O.R.S da Napkin na
manya aje a siyo mata. Ta kuma dinga daura napkin din duk bayan sa'a biyu. Karshe ya
sallemusu da cewar su je Binni a duba ta da kyau shi kam iya na sa ke nan. Da komawarsu
gida Abule ta yi wuf! Ta fada ɗakin Nene tana sakayo kaba. Kallonta take cike da tausayi ganin
harta tsotse rana guda.
"Ni Nene anya ba maganin fadi kika sha ba? Na ganta sumul fa" Nene dake ji da yoyon
kashinta ta mike a hankali jiki na rawa" Shi ne wlh a randa na tadda shi a bude na sha, na
shiga musanyamin ta yi bakar muguwa wayyo ni. Mene makarin ki taimake ni Abule" Abule ta
dafe kirji ido warwaje "Lalle dara ta ci gida Nene! Makarin da wuya Nene, ba za mu iya ba, sai
kuma rushe da kuka."
Nene ta yi ruf da ciki tana numfarfashi.
"Ki fad'amin Abule, ko menene shi zan iya."
Jin haka Abule ta fyace majina ta soma magana.
Page 11
Abule ta yi k'asa-k'asa da murya.
"Makarin shine a jik'a wandon kwarto a shanye."
Nene ta zabura tayi zaman 'yan bori wanda ya yi daidai da sullu6owar tusa ta mai k'ara. Abule
ta toshe hancinta, a hankali Nene ta numfasa har da lumshe idanu don ba k'aramin sassauci ta
samu a cikinta ba.
"Na shiga uku, yanzu ina zan ga kwar... Af! Fad'uwa ta zo daidai da zama ai Abule, yo bana
manta ashe muna da su a kurkusa ba? Ga Basharin Shafa?"
Abule wacce itama shaf ta mance da batun Jik'an Lamid'on ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin
zuciyarta wasai, babban abinda ya sanyamata damuwa da lamarin ba komai bane sai na tsoron
kada ya kasance Nene bata warke ba ta tonamata asiri mutan gari su zageta. Ta daki cinyarta
tana mai washe rinannun hak'oranta. "Kai Allah mungode maka, ai ni dinma kaf tunanina bai je nan ba. Ko jiya da daddare ya
haurawa Kulu Gurguwa."
Suka saki shewa don Nene har ta hango warakarta a sauk'ak'e.
"Kai Allah Ya k'arowa Bashari ilimin kwartanci, wannan ai gaba ta kaini. Ashe kwarto da
ranarsa. (Kun ji jahilci!)"
Dariya suka k'ara kwashewa da ita.
A yammacin ranar Shafa na durkushe a gaban murhu tana kokarin iza wuta ta tsinkayi sallamar
Nene da Abule. Da mamaki ta dubesu kafin ta mike. Abule ta ci burki anan tana k'arewa gidan
Shafar kallo domin rabonsu da shiga gidan har sun mance. Daga can gefen garu ta hangi jerin
manyan duwatsu wanda ta taimakonsa ne Shafa ke k'arewa cikin gidansu kallo. Ta6e baki ta yi
gami da bin sahun Nene da har ta shige rumfar Shafar ba tare da ko neman izni ba.
Shafa za ta yi magana Abule ta hanata ta hanyar rik'o hannunta tanamata alamar ta yi shiru
gami da yi mata nuni da gidansu, nan take ta fahimci ba su kaunar Fad'ime da Inna su san da
zuwansu. Ta gyara zaman d'aure kirjinta suka shige ciki.
Nene ta washe baki.
"Shafa Shafa, Shafar Bashari, uwargida ran gida! Kin tare gaba kin tare baya, turmin tsakar gida
sha lugude!"
"Wannan haka yake." Fad'in Abule tana gyada kai kamar k'adangaruwa.
Shafa ta yamutsa fuska tana kallonsu d'ai-d'ai.
"Halan dai Nene acan asibitin har allurar mahaukata suka manta suka yi maki?"
Nene ta hau daure fuska za ta kwa6omata mai zafi ganin haka yasa Abule saurin tarewa.
"Kai Shafa, dad'ina da ke zolaya. Nene ai taki ce, banda abinki ai makwafci ance ya fi dan uwa,
a baya ma rashin fahimta ne."
Dariya Shafa tayi gami da tafa hannuwa. Nene da Abule suka dubi juna, dakyar dai suka shawo
kanta ta yarda zata sauraresu.
Nene ce ta soma magana bayan ta gyara zaman nafkin dinta.
"Ki taimakeni Shafa ki bani aron wandon Bashari."
Shafa ta fiddo idanu gami da dafe k'irji.
"Yau naga ta kaina! Nene me zakiyi da wandon Basharina? Anya Nene ba ki samu matsalar
kwakwalwa ba? Au to na fahimta, wato dai duk matattarar kwararar gudawar da aka sanyamaki
bai isheki ba sai kin had'a da wandon Basharina? To mine amfanin na Mati?"
Nene ta share zufa tana girgiza kai. Abule ta cafke zancan.
"Kinga Shafa duk ba haka bane, wannan maganar da za mu yi sirri ce, don Allah ki rufamana
asiri."
Shafa ta dan zubamasu idanu na 'yan dak'ik'u kafin ta gyada kai don ba za ta bari gulmarnan ta
wuce ta ba.
"Ina jin ku."
Abule ta zayyanemata duk abinda ya faru da kuma makarin asirin.
Shafa ta saki shewa har da tafa hannuwa.
"Yau abin namu ne! Oh ni matar na Lamid'o!"
Saida ta basu wuya Nene harda matsar kwalla sannan ta amince da sharad'in Nenen za ta
kyautarmata da tunkiyarta da take kiwo. Ba musu Nene ta aminta daganan ta mik'e ta fita zuwa
d'akin kwanansu ta hau lalube.
Jimawa kad'an sai ga ta rik'e da wani tsohon wandon Bashari da ya gada gun Lamid'o ta
mik'amata.
"Gashinan, kuma kada ya kai gobe a wajenki, ko ta katanga ki jehomin."
Nene ta hau godiya kafin kuma cikin lallami ta ce.
"Ki taimakamin Shafa, ki bani sabon d'inki mana."
"Cab! Ai idan kinga Bashari ya yi sabon dinki to mutuwa akayi a danginsa don haka ban
bayarwa, idan ba kwa so ku k'ara gaba."
Ta k'ara he tana girgiza k'afa gami da jefamusu tafin hannunta.
"A'a me ya yi zafi? Mu je Abule hakan ma ya wadatar" " To karki manta dai ki jefon ta katanga."
Da komawarsu kuwa Abule ta tarkata lallen ta watsar Masai, shi zaman duniya dama rabo ne,
idan ba ka da shi kuwa za ka zo ne a banza ka koma a wofi. Tuna hakan ya sa ta nutsuwa ta
ma fita daga batun Fadi. To haka ma ga Nene sai wayar gari akai aka ganta sumul tamkar mai
bugun Iska. Itama ta mai da rayuwarta shiru ta hanyar aro nutsuwar dole. Daga bisa ni ta kulla
Amintaka da Shafa ba ma ta zaman gidan balle ta zubda hali. Bayan watanni, ranar wata laraba
wanda ya yi daidai da kwanan Inna guda a birni ta je hado kayan haihuwar fadi. Faɗimen ta
tashi da nakuda. Gidan daga Abule sai Nene dake shirin fita.
Ta gyara zaman yafenta tana mai sauke kabar shiga d'akinta. Ta juyo gami da duban Abule, za
ta yi magana kenan suka ji nishi da salatin Fad'ime. Cikin hanzari suka dubi juna.
"kinji abinda na ji?" Abule ta ya tsina fuska" na ji mana kila abinne ya zo." "To ya za ai ko mu
dubu yar magaji... " Abule ta ƴi saurin rufe mata baki. "Ke gafara, kinmanta yanda ta musanya
miki magani? To yaune ranar ramuwa dan haka maza kwaɓe gyalen nan ki dauka surfe mu yi
yanzu dan karma makota su jiyo bayan awa guda ma lekata." Da sauri Nene ta aje gyalen ta
juye hatsinta a turmi suka hau dukansa ba ka jin karan komi sai tunkwal-tunkwal.
Fadime cikin azaba haka ta rarrafo bakin kofarta tana kiransu amman suka yi biriss da ita. Har
sai da suka bar jin muryarta tukun suka zubda taɓaren suna ma su nufarta. Ganin ruwa gefenta
ya sa Nene zare ido "Ke abu ai fayar ta fashe."
Abule ta karasa itama tana lek'e-lek'e, a karshe suka kinkimi Fad'ime suka maidata ciki. Haka
suka kar6i haihuwar santalelan d'anta suka yanke cibi. Nene dake rike da jaririn wanda bai bar
komai na Mati ba, katon kan Fad'ime ya yo. Ta yiwa Abule ido kafin ta fice zuwa d'akinta rike da
jaririn wanda ta cusawa yatsanta a bakinsa gudun kada sautin kukansa ya ankarar da
gulmammun makwaftansu.
Abule ta dubi Fad'ime wacce ba k'aramin k'aruwa ta samu ba wajen haihuwa sai murk'ususu ta
ke da alamar dai akwai abinda ke damunta. A hankali ta sulale ta bi bayan Nene. Idanu ta ware
a tsorace ganin Nene na kokarin sanya jaririn cikin kwali.
"Nene! Bakya tsoron asirinmu ya tonu?"
Nene ta harareta.
"Kinsan iyakar tsawon lokacin da na dauka ina ajiyar kwalinnan? Ai bazan bari damarnan ta
kufcemin ba, yau dan kwal ubannan sai kwanan daji."
Kafin Abule ta ce wani abu suka tsinkayi sallamar Mati.
A razane suka dubi juna har Nene batasan sadda ta cire yatsanta daga bakin jinjirin ba ai kuwa
ya canyara kuka.
"Lafiya Fad'i? Kin haihu ne?"
Mati dake jefowa Fad'insa tambayoyi ya tsaya gami da saurin bin inda ya jiyo kukan jaririn.
Duk kokarinsu na kada ya fahimci shirunsu saida ya gane. Nan ya hau salallami, wani wawan
tsalle da ya doka sai gashinan gaban Nene, ya kwasheta da mari kafin ya fiddo jaririn daga
kwali.
"Ka gantanan, yasin ba hannuna ciki! Yanzu na shigo daga makwafta ina.." Fad'in Abule
yayinda Mati ya katseta da sauri.
"Dalla can rufemin baki kema bakar munafuka! Wato kun yi shirin kashemin mata da d'a ko?"
Sautin karar Fad'ime ya kid'imashi, a guje ya fice zuwa d'akinta.
Kan kace me Shafa da Delu sun shigo domin tun kukan jaririn na farko sun tsinkaya saidai ba
su k'ara ji ba sai yanzun da Mati ke balbalin fad'a. Lek'owarsu suka san abinda ke faruwa suka
bazamo cikin gidan.
Su ya bari a wajen Fad'ime yayinda ya fice nemo abin hawa don mik'a Fad'ime asibiti.
Delu na gyara jaririn tana zubamusu habaici Shafa na tayata. Su kam kowacce na d'akinta sun
k'unshe gaba daya a tsorace suke da abinda zai biyo baya.
"Shegen, ashe d'agamin k'afa kawai ya ke." Fad'in Nene a k'asa-k'asa tana shafa kuncinta.
Mati na dawowa aka wuce kai Fad'ime ga likita bayan ya kora Nene da Abule gidajensu da
shika (saki) d'ai-d'ai.
Page 12
BAYAN WATA GOMA
Rayuwa mika a gidansu Mati, abubuwa da yawa sun faru ciki harda dawowarsu Nene bayan
sunyi Bikon Mati sau kusan goma. Wanda Nene sai da ta koma yini a gona gun Mati tsaban son
ta koma dakinta. A rana sai tai wanka sau hudu ko biyar. Goge hakora kuwa masu sai da
gawayin ƙauyen sai da suka shaidata, haka ma masu Gishiri. Saboda tsabar tsafta sai da ta
koma yawo da tsumma tana goge kafarta idan tai kura. Wannan fa duk shawarar ƙawarta Shafa
ce. To haka ma ga Abule itama sosai ta nutsu dan har dan abin kwalama take kaima Mati gona.
Musamman ma Kundun Kaza da ta san yana so. Karshe dai ya mai dasu. A daren Inna ta
tarasu da ta ta nasihar ta nunamusu laifinta ne tare da neman gafararsu.
"Haba Inna, ta ina kika zama mai laifi? Mu keda laifi mu yakamata mu nemi gafara."
Fad'in Nene kenan tana mai k'arashewa da sheshshek'a.
Fuskar Inna cike da damuwa ta girgiza kai bayan ta k'aremusu kallo gaba daya har Matin tana
mai shafa kan jikanta Atiku dake saman cinyarta, ya sha billensa a goshi an rambad'amasa
kwalli yayinda fuskar ke ta kyallin mai. Ta cigaba da magana.
"Um um Nene, bari fad'in haka, maganar nan haka take. Abule da bakinta ta sanarmin
musabbin wannan rashin jituwar a sadda take zuwa yawon biko, nayi kuskuren ware wani kaso
na dukiyata da zummar bawa jikan Matina na farko, kai kuma Mati bai kyautu ace kai da kake
Maigida ba kana nuna halin k'aranta, Abule ta sanarmin da irin yanda ka sanyata k'aryar ciki
wanda tun daga ranar zaman lafiya ya k'ara k'aranci a gidanka. To yanzu wannan sai ya zama
izna gareka, matuk'ar kana son had'in kan iyalanka kada ka k'ara wannan gangancin. Nima a
karshe ina neman gafarar..."
Da sauri duk suka tari numfashinta kowa na kara neman gafararta, Nene da ke tashin k'amshin
turaren matan arewa ta rungumo kafadar Abule dayan kuma ta rungumo Fad'ime wacce
farinciki ya cika don har zuciyarta bata son fad'ace-fad'ace, washe bakinta ta yi wanda ya sha
durji da gawayi ta ce. "Yanzu mun zama tsintsiya mad'aurinmu d'aya. Daga gareni Nenen Mati babu abinda zai k'ara
fitowa daga wurina."
Farinciki ya cikasu babu ma ya Mati wanda har aiken kiss ya yi musu ta iska bayan ya fakaici
idon Inna, suka tuntsire da dariya kuwa.
Cikin iko na Ubangiji kuwa tun daga ranar babu hayaniyar da ta k'ara tada hankula a GIDAN
MATI, Nene a matsayinta na babba ta ja girmanta da sauran mutuncinta da ya rage, hakanan
Fad'ime tana binsu sau da k'afa, saida ya zamana rainon Tanimu ya koma ga Nene, kai kace
itace ta haifeshi. Fad'ime me kawaici kuwa ta d'auke kanta daga Atiku, muddin ba nono zai sha
ba to fa babu abinda k had'asu sai kwanciyar bacci. Bangaren Mati shima kuma daidai
gwargwado yana kokarin yin adalci tsakankaninsu. Wannan ya kwantarwa Inna hankali.
SAUYIN RAYUWA
Gida ne wanda ya sha filasta madaidaici, tsakar gidan an shafeshi da sumunti. Dakuna ne jeras
har hud'u sai falo babba guda daya wanda daidai talakan k'auye ya tsaru.
Nene ce ta fito daga d'akin dake jikin na maigidannasu tare da Atiku da kanwarsa Sa'a, ta
cakare cikin atamfa mai kalar ruwan masara, tana kokarin rufe k'ofar d'akinnata bayan ta saki
hannun Atiku ta ce.
"Wai mutanennan kuna so dai dare ya yi mana ba mu tafi gidan bikinnan ba ko? Abule!
Kanwata!!"
Kusan a tare suka amsa gami da fitowa daga d'akunansu sanye cikin atamfa irinnata. Abule
rik'e da d'iyarta da Allah Ya bata wacce ko wata shida bata cika ba a duniya yayinda Fad'ime ke
goyon yaronta na uku Sallau don Nene kam Allah bai bata ba.
Nene ta washe baki.
"Inye, cakarewa. To ai ni har kun fini kyau."
Suka dara.
"Wane mu?"
Fad'in Abule da ke saita zaninta. Suka rufe ko'ina suka jera gidan Delu wacce ke aurar da
yanmatanta uku.
Kowa a gidan bikin ya yaba da shigarsu, Shafa ita kanta ta yi kyau tamkar ba ita ba, cikin
hukuncin Allah mijinta Bashari ya shiryu ya daina kwartanci, hakanan Delu itama mijinta ya
daina dukanta tun watarana da diyarsu Bushira (wacce duk cikin yaran ya fi kaunarta saboda
nutsuwarta) ta gwada d'aga hannu da zummar ramawa uwarsu, wannan abu ya dagamasa
hankali ainun karshe dai ya saduda bayan limamin garin ya shiga lamarin ya mishi nasiha.
TAMMAT BI HAMDULLAH