Showing 6001 words to 9000 words out of 11892 words

Chapter 3 - GIDAN MATI BOOK COMPLETE (1-END) by D Young .pdf

D Young   

03 Apr 2025

1713

tsakar gidan, da
dai yaji kamar babu motsi ko daga ɗakunansu, ai sai ya yi wuf! Ya faɗa Makewayin.
Abule ta yi miƙa ba salati ba rufe baki, ta miƙe tana mai riƙe mararta sakamakon fitsarin da ya
rike mata ita. A hankali ta fito waje, ganin ba kowa ya sa ta tsugunna nan gefen kwatamin
tsakar gidan ta tsiyaya abinta, ta wawwatsa ruwa ba ko cuɗawa ta miƙe, za ta koma ɗaki ta jiyo
kamar kacaniya a Banɗaki, a zatonta Kajin maƙotane ke kacaniya, sanin da ta yi sunsha
faɗawa wawakeken masansu azo a yi ta hayaniya ya sa ta zari sanda da sauri ta yi makewayin.
Sai dai fa turus! Ta yi tana sakin wani razanannen Ihu ganin Mati zaune a dutse daga shi sai
gajeran wando, Amarya Timah kuma duƙe saitin hammatar Mati da wani ɗan ƙarfe a hannunta
tana ta kwasar gashin hammatar tana hura masa iska, shi kuma yana dariya gami da fadin
"Wai, ci gaba, daɗi wallah." A firgice Faɗi ta yada ɗan ƙarfen saboda yadda ihun Abule ya kiɗimata, Abule kuwa da ƙyar ta
jawo sauran numfashinta tana son daidai ta kanta, sai kuma ta ɗaga sanda ba tai wata-wata ba
ta saukewa Faɗi ita a kafaɗarta.
"Sai na nakasaki baƙar mujiya me salon karuwai kawai, dan Ubanki ce miki akai nan bariki ne
da zaki shiga wanka da Mijina, ko kuwa ce miki akai ni ɗin zan yarda."
Ta sake ɗagawa za ta rafka mata Mati ya riƙe sandan jiki na ɓari, "Karki kuma dukanta, zan fa
rama mata, ke Abule ki fa fita idona da wanann jahilcin na ki, baki san aikin lada ba ne take yi?
Ba na son sakarci fa." Ai sai ta yi baya tana kallon Mati sama da ƙasa, kafin kuma ta rangwaɗa
guɗa. "Ahl lalle Mati yanzu na san ka ɗauru tamau! a Minjaye, yanzu saboda wannan me zubin

botoramin kake cewa zaka dake ni, Ni Abu? Da ka ce aikin Lada na ga dai kwanana ya shiga
daga sanda aka kira assalatu."
"To na ji, yanzu dai wuce ki tafi haka ba zai ƙarawa faruwa ba."
"Bazan tafi ba, Ni fa idan ba jini na fidda mata ba bazan ji daidai ba."
"Haba Abu tawa, na ce kije dai, da daddare zaki ji saƙo."
Ta ɓallawa Faɗime harara dake dafe da kafaɗarta, ki sake gwadamana karuwanci gidan nan ki
gani, wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi, shegiya da wani idonki kamar tsaka ta saka kwai."
Af! Abu mai sauki, wai kura ta zo gidan Maharbi, idan karuwancin ne ki gwada naki mana mu
gani, ai wallahi babu wata me siffar Fanteka da ta isa ta hanani kula da Mijina. Aikin lada ne
yanzu na fara, wanann sandar kuma bashi kika ci." Faɗi ta faɗa tana murguda baki.
Sanin Mati ba zai barta ta sake taɓa Faɗi ba, ya sa ta juya ɗakinta takaici fal ranta.
** ** **
Tun bayan da akayi cacar baki tsakanin Abule da Fad'ime gidan ya k'ara kacamewa. Tsakanin
Abule da Nene sai ka rantse tun da can kansu a had'e yake tsabar amincin da suka k'ulla na
munafunci. Koda suna cikin habaice-habaicen su ne Fad'ime ta fito tsakar gidan nan za su ɓige
da shewa suna watsamata bak'ak'en magana a fak'aice. Ko kallon inda suke Fad'ime ba ta yi
balle su saka ran za ta tankamusu.
Ranar wata laraba wanda ya yi daidai da cikar Inna kwanaki goma sha shida a birni, Abule da
Nene suna zaune a gaban d'akin Abulen suna k'us-k'us tare da Shafa makwafciyarsu. Shafa ke
yi musu tallar magungunan gyara na mata kala-kala. Ta d'aga wani k'ullin gari tana fad'in.
"Kun ga wannan? Na rantse da daren farkona da jikan Lamid'o yana da masifar kyau. Ke
wannan da ku ke gani sunansa 'Saki Matar Uba'."
Nene da ke soshe-soshenta ta dubi Abule suka yi wata iriyar shewa gami da cafkewa.
"Inda ranka ka sha kallo! Yo Allah na tuba idan kura na magani ta yiwa kanta mana!" Fad'in
Abule.
"Atoh, taya ni gani! Wai Matar kwarto da tallar maganin mata." Nene ta cafke.
Jin haka ya sanya Shafa kallonsu a fusace kafin ta d'an kalli d'akin Fad'ime, ga dukkan alamu
batasan ma me suke yi ba. Ta maido dubanta gare su cike da borin kunya ta ce.
"Oho dai, gwara ni akan ku, haka za ku k'arata a borori."
Ta hau tattara komatsanta a sadda suka yo mata ca! kowannensu da bak'ar maganar da yake
yarfamata. A daidai nan kuma Faɗi ta fito daga ɗaki da gudu zuwa bakin makwararar tsakar
gida ta hau sheƙa amai kamar ba gobe.
Nene ta miƙe ido waje tana tafa hannu, yayin da Abule ta dafe kirji tana duban Faɗi dake duƙe.
"Duka-Duka yau kwana nawane da Auren ni Nene? Taya ni lissafi Abule.
Abule ta hau kasafta yatsun hannunta, sai kuma ta zare ido waje.
"Duka-duka kwana goma sha bakwai kenan, kar dai da ruɓaɓɓan kwai aka shigo?"
"Oh ni Nene, wannan wace irin haɗama ce haka, ranar farko da rabon ciki kamar marainiyar
Karya? Ke kuma maƙaryaciya kika cemin ba ai komai ba ranar jikin tagarsu kika kwana?"
Abule ta ɓalla mata harara, "tuna dai, ke kika cemin ranar da aka kawo ta jini take, koma dai
menene ni ban yarda da wannan Salon ba, ban taɓajin cikin dake bayyana kansa daidai da
lissafin zuwan Amarya ba. Sai dai idan da shi aka shi..." Nene ta yi Wuf! Ta rufemata baki jin
sallama kamar ta Inna. "Barta ta ƙarasa mana manyan Akuyoyi, ai na dade tsaye ina sauraronku, wanda ya gani dai shi

ya ji kunya wai kallon fitsarin makaho. Idan ba ku da kuke cikin ƙauye, haihuwar ƙauye, renon
ƙauye, auren ƙauye, ina na taɓa ganin ana laɓewa sabuwar Amarya? Kunyi asara wallahi Nene,
matsa ni na duba 'yar mutane, shashashai masu wankin kai da ruwan daddawa, idan ma da
cikin ta shigo sai me? Na ce sai ƙaƙa? Irin kune a jahannamar ma can ƙasan wailun kuke.
Sannu 'yarnan, sannu."
Inna ta k'arashe tana mai k'arasawa ga Fad'ime wacce aman ya d'an lafawa.
Gefe guda ta ajiye akwatin kayanta, ta yaye gyalenta ta dora saman akwatin kafin ta tattare
zaninta dinkin rafa siket. Ruwa ta zubo a buta gami da mik'omata.
"Tayani duba Abule, toh wallahi ba za ta saɓu ba bari Matin ya zo, ni ban yarda wannan cikin
nasa bane, ga dukkan alamu dai mutum da abinsa ya zo, ai daman ni nasan za'a rina, angama
yawon ta zubar an k'untso.."
"Ki ka k'ara magana a wajennan sai na nunamaki ni ce nan na isa da Mijinki don kuwa yana
zuwa zan sanya ya sallamaki ga tsohonki."
Nene ta yi d'if ta ja hannun Abule wacce ranta ke ƙuna suka fad'a d'aka. Shafa kuma da ke gefe
kunne waje, tayi saɗaɗa ta fice daga gidan.
"Mun shiga uku Abule, yanzu idan ta tabbata matarnan juna biyu gareta ya za mu yi?"
Fad'in Nene kenan yayinda gumi ke tsirfomata. Abule wacce ta rasa bakin magana tsabar bakin
ciki da tashin hankali, sai a lokacin ta iya bud'e bakinta ta ce.
"Hum, ni na rasa ma abin cewa wallahi."
Sallamar Mati ce a gidan ta katse su, suka yi shiru suna sauraron yanda Inna ke gayamasa
rashin lafiyar Fad'ime da kuma cewar Fad'imen na tunda ta zo ba ta ga Al'adarta ba.

Page

*GIDAN MATI*
BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Kamar wasa cikin Fad'ime ya tabbata, Inna har Asibitin K'auyen ta mik'a ta tare da Abule da
Nene wadanda suka tik'e akan sai sun bisu sun ji da kunnuwansu. Itama Innar ba ta yi gigin
hanasu ba don ta fi so su ji abinda zai hana su bacci.
Ranar kam sun riga su yin gaba, zagi da tsinuwa ba irin wanda Fad'ime da Inna basu sha ba.
Tun daga wannan lokacin kuma sai sabon tashin hankali da makirci ya k'ara ɓallewa a gidan.
Akwai ranar da Nene ta shigo da Kuliya cikin gidan, sanin cewa Faɗime ba ta so. Hakanan ta
lallaɓa ta d'ora mata ita bisa gadonta tana cikin barci. Allah ne ya tsare da kwallayenta na jere
basu zubo bisanta ba, saboda yadda ta dinga razana tana bige-bige a ɗakin. Ƙarshe dai Inna ta
cece ta da fitsari ya fiddo ta, ta juyo motsi ɓarin Faɗimen. Shi kuwa Mati yana can ya saki
gañɗa ɗakin Abule. Sai washegari ne Inna ta sanar masa, karshe dai ta yi maganin abin da
cewa duk wacce ta k'ara kawo wani Abu gidan ko da Ɓera ne, ko ta jefi Faɗime ko Mati da
bak'ar magana to a bakin aurenta. Da wannan aka samu bakinsu ya rufu suka koma rara gefe,
ƙarshe dai Nene ta tattara ta tafi wani ƙauye bikin kanwar kishiyar matar babanta.
Inna zaune gefen Fad'ime tana lalla6ata ta samu ta ci kwad'on Zogalen da ta had'amata, ita
kuwa Abule tana tankad'e Garin Tuwo tana wak'e-wak'en habaici. Fitowar Nene daga bayan
gida ya sanya suka bita da kallo. Tayi daurin k'irji da tsohon zanin da ta ci 'yanmatancinta da shi
duk a huje, k'asan duk ya rarake har idan ka zura hannu a 6uli guda zai ta6o mazaunanta.

Fatarnan kallo daya za ka yi mishi kasan akwai nakiyayyar d'aud'a da bai kammala fita ba,
jikinta kuwa babu alamar ya wanku. Sai kyalli takeyi da nason datti da hamami dake tashi.
"Ke jik'ar Maduga, wai wankan da ruwan Taɓo ki ka yi shi ne?" Cewar Inna.
Juyowa ta yi ta mata murmushi, sai kuma ta yi gaba tana murzo wata naɗaɗɗiyar dauɗa a
wuyanta.
"Ah'ah Nene magana fa nake miki." Fasa ɗaga labulen kabar ta ta yi ta juyo tana kallon Innar,
sai kuma ta haɗe mata hannuwa biyu tana roko alamun ta kyale ta.
"Uhm! Sabon salo, wai gemu a kafaɗa, halan da kika je bikin rashin magana kika koyo? To ai
gaba ta kai mu, tuntub'en me carbi" Inna ta faɗa tana riƙe hab'a.
Ganin haka ya sa Abule ture tankaɗen gefe, ta mike zuwa dakin Nene.
Da shigarta ta same ta tsaye tana jan Jagira a girarta me kama da ta Tunku. Ai sai ta yi turus!
Da mamaki tana ƙare mata kallo daga ƙasa zuwa sama. Ta sha Atamfa koriya fatau, da dinkin
rigarta irin na Lema, wani abin mamakin har kallabin irin na atamfar ne, ba wai wari da wari ba.
Kwalliya dai irin wacce ko da tana Amarya ba ta taɓa yinta ba. Sai ƙamshin man kadanya ke
tashi da ta mulkawa jikinta.
"Wannan kallon fa? Ban fa san irin kakannin ki ba?" Ta faɗa tana kaɗawa Abule hannu ganin
yarda ta ƙame.
"A'a mamaki kawai nake, tunanina ko dai ƙanwar Nene aka musaya mana.
"Uhm! Kibar mamaki, kawai nasihar da Innata tamin kan zaman duniya da ƙiyama nake ta
tunanowa yau."
"Anya kuwa Nene? Ke din ce kike tuna wanda ya mutu? Abokin kuka ai ba a ɓoyemasa
mutuwa. Ki faɗamin abinda ya faru dake kika saki makaman haka? Ko duk tsoron kar Innar Mati
ta kora ki gida ne?"
Ai sai ta gundumo ashar tana me ture ɗaurin kallabin da ta dade tana murd'ashi dan ya yi kyau
gefe. "Ni wallahi har kin ɓatamin rai, tsohuwar banzar can zan ji tsoro? To Talle Bodara ce ta ba
ni maganin Ɓari, sharuɗɗan cikar maganin shi ne ko daka Ni Uwar Miji za ta yi kar na sake na
tanka ta. Kin ganshi a bakin Masai ake barbaɗashi." Ta karashe gami da bankad'a k'asan katifarta, wani k'ulli ta fiddo a bak'ar leda ta nunamata.
Abule ta washe baki don tsabar farinciki. Ganin babu damar ihu ya sanya ta kaiwa Nene
runguma sai dai tun kan ta k'ara sa had'a jikinta da na ta ta yi baya da sauri tsabar tashin da
Nene ke yi kamar mai warin k'ashi.
"Dagaske ki ke yi?"
Nene ta ta6e bakinta.
"Ni idan na fad'i abu na fi son ki yarda, zan miki k'arya ne? Nan da ki ke ganina ba ta wasa bace
ba. Bari ki gani, wuyarta dai Fad'ime ta tsugunna saman Masai, ko kwad'o ne a cikinta sai ya
fad'o.
Jin haka suka saki shewa gami da cafkewa, sai kuma da sauri suka rufe baki.
"Um kinga bari na je kafin wannan Tsohowar karuwar birnin ta ankara."
Dariya Nene ta yi.
"Ai mukam Allah Ya had'amu da suruka."
Suka dara sannan Abule ta fice.
***
Shiru-shiru ciki zai zube anjima, gobe, bai zube ba. Ko ciwon kai Fad'ime ba ta yi ba ballantana

a kai ga ciki.
Ganin haka Abule ta yanke gwada ta ta sa'ar ko za'a dace. Nene ta ba ta goyon baya d'ari bisa
d'ari, da wannan ta shirya tafiyar kwana daya da sunan ziyartar jikar abokiyar kakarta.
Dawowarta akayi sa'a babu kowa sai Nene a gidan da ke faman zazzaga bala'i ta katanga tare
da Delu wai Akuyar Delun ta shigo ta cinyemata shanyar da ta yi ta k'anzo.
Ganin Abule ba k'aramin dadi ta ji ba, itace har da rungumarta tana tsalle, da ace akwai mutane
a gidan da sun sha mamaki.
Bayan sun k'ule a d'akin Abule ne ta hau bata labarin abinda ta samo.
"Ba k'aramar wuya na sha ba in fad'amaki. Ban ta6a rawar 'yan bori ba amma shege
la'antaccen bokannan sai da ya sanyani yi. Amma tunda kwalliya za ta biya kud'in sabulu da
sauk'i. Bari ki gani."
Ta ɓalle ɓarin zaninta ta fiddo k'ullin magani har biyu ta nunawa Nene.
"Ya ce na kwa6a lalle da garin na d'aurawa Inna a k'afa don rufe bakinta. Shi kuma wannan."
Ta nuna d'ayan,
"A had'a Lemon Zobarodo a sanyawa Fad'ime a ciki ta shanye."
Shiru ya biyo baya kafin Nene ta jinjina kai.
"Tabd'ijam! Aiki ja! Yanzu banda abinki ina mu ina iya haka? Ni kinga banda kwaɗa zobo da kuli
ba abinda na sani kansa, sai yau da na ji ana lemonsa, kema kuma na san duk sammak'al. Inna
kuwa ba ta yanda za ta amince waninmu ya d'auramata lalle. Ina mafita?"

Page 9

"Ke dadina dake jahilci kwarankwatsa dubu, haba ai ko karamin yaro ya san ruwa za a
shekama Zubo a zuba Sugar shi ke nan ya zama lemo, batun lalle kuma kin manta Inna da
shegen san fadanci kamar matar Bawan Sarki? Ai kawai kururuta mata kai zakiyi har ta sake ta
baki kafar ki kunsa. " Nene ta yi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta gintse fuska ganin Fad'ime
ta fito zuwa makewayi. "Shegiya kai da wata fuskarta kamar taunanniyar gyada, Allah Abule
yadda naki jinin Matar nan bank'i a cemin karta fito raye daga makewayin nan, ba ni zoban ki
gani duka gidan zan had'a idan ya so a na tan sai na juye maganin" Ta fad'a tana wartar ledar
zobon da Abule ta riga ta siyo. "A'A hankali dai Nene d'an kad'an ya ce a zuba saboda
karfinsa." Ta balla mata harara "Wallahi duka zan juye idan za a sha giya asha ta dubu Abule!"
Ta fad'a tana mai ficewa daga d'akin. Kai tsaye madafi tayi ta dauko kwanon sha ta juye zobon,
ta tuttulo ruwa daga tulu ta sheka bisansa ta zuba Sukari wadatacce ta juya. Nan da nan ta
kasafta na kowa, na Inna ta fara dauka dauka za ta kai mata, da shigarta kuwa ta tarar ta tana
gyangyadi dan haka ta aje ta juya za ta fita. " Na shige su ni Uwar Biyu, Nene me nake gani
haka?" ta juyo da sauri tana kallonta kafin kuma ta saki murmushi. "Zobo ne muka samu
tsaraba daga Abule, shi ne na hadamana lemo da shi na san ai kin sanshi a birni." Inna ta balla
mata harara tana turo kallabi goshi." To ke ina kika taba ganin anyi zobo ba a tace tikar ba?
Wannan zobo za mu sha ko roman zobo? Idan ba ku iya abu ba ku dinga tambayata mana, ni
nan da kuke gani na bayan zobo durinkis (DRINKS)har mangwar durinkis (MANGO DRINKS)
Na iya, dan haka ban san jahilci d'auki ki ta ce shi sai ki kawon. Sum-sum Nene ta fice jin Inna
ta koma yaren 'yan sama jannati. Sake gyarawa ta yi, tukun ta dauki na Fadime ta kai mata
daki, komawarta daki ke da wuya Mati ya sawo kai Gidan. Kai tsaye dakin Fadi ya yi yana doka

sallama, fasa kai dan karamin kwanon shan baki ta yi ta aje tana amsa masa da murmushi kafin
kuma ta mike tana kokarin zare masa zungureriyar hular da ke kansa. Ya shaki kamshinta da
yake so na Karkar dan haka ya washe baki "ALLAH Amarya son ki nake kamar na mutu" Ta yi
murmushi tana rangwada kwalelen kanta "A'A Maigidana mai ya kawo mutuwa kuma, muna
tare ai." "Hmm! Ba za ki gane ba ne, idan kina kusa da ni ji nake kamar numfashi...
KYYYATTT...FYYTTATAT... Ya dakata yana mai kakalo kaki, kafin kuma ya dunkulo majinar
yana mai furzo ta waje da ba ta dire ko'ina ba sai cikin kwananshan Fadime dake cike da zobo.
Ita da shi suka zubawa kwanon ido kafin kuma ta kwabe fuska. "Haba Maigida na sha ce maka
ka dainamin tofe-tofe a bangon daki ko kasa, wannan ko a kan titi ne ba abin so ba ne. Yanzu
kalli yadda ka haramtamin abinda tunda na gani yawuna ke tsinkewa. " Ki hakuri na mantane,
yanzu bari na karbo miki kasona sai ki sha." ya fada yana mai daukan kwanon ya fice. Bisa
randa ya tadda wani kwanon rufe da Fai-Fai Dan haka ya aje wancan ya dau wannan ya tafi.
Nene da ta shiga makewayi rage ciki tana fitowa tayo inda ta ajje zobanta, ganinsa bude ya
sata doka ashar "Ko wane shegen ya budemin oho, to idanma diba akai an sha wuta bal-bal
tunda nawa ne. Ta fada tana hararar dakin Inna, kafin kuma ta daga kwanon ta kwankwade tas!
Har kakin Mati. Minti biyar da sha cikinta ya yi wani irin juyi, jin kamar ruwa da wani wari na
binta ya sata lekawa abin da ta gani na binta ratata ya sata doka ihu tana dafe mazaunanta
"Wayyo ni Mati! Yoyon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login