Showing 1 words to 3000 words out of 32509 words

Chapter 1 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf

27 Apr 2025

2140

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
[2/18, 10:36 AM] +234 703 962 5239: 25/10, 5:10PM
♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡

GARGADI:banyarda wani ko Wata yajuya min min wannan kirkirarren labari nawa ba,banyi Dan
wani ko Dan Wata ba,sunayen da garuruwa naciki da nasa dukdan su nishadantar dame
karatune banyin dancin fuskaba saboda haka kada ajuyamin wani sashe ko wani bangare
naciki batare da izinina ba inhar hakan tafaru NAJA ALLAH YA ISA!!!! ..♡..♡..♡
STORY AND WRITTEN BY:
HALEEMA G KHALEEL

0⃣1⃣

Cikin sauri-sauri take tafiya kada lecturer insu yarigata shiga, sabida dokarshi ce inyarigaka
shiga tom sede katara next,time.
Dauke take da lab-cout da sch bag inta dressing inta wanda kusan kullum shine shiganta, gown
ne eather Material, Atamfa, ko Ready made kiran Bahrain Oman, ko Kuwait.
Yanxunma Gown ce jikinta Sea,green tayane kanta da peach colour veil. Kannan yasha
Top-knot. Setashin sanyin kamshi take, wanda bazaka tantance wana irin perfumes take using
ba.
Akan kwanan dazata sadata da Biology Lab insu tagansu sunata K'us-K'us i. Tai saurin fadin "
````LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN```."

Inda sabo tasaba dahakan dasuke mata koyaya zata hadu dasu sesunyi magananta. That Y!
tabama "Innansu labari tace mata tai ta addua duk wani mai nufinta da sharri, in sha Allah baze
tasiri a kantaba.
Musamman yadda bata shiga abinda bishafeta tun a farkon zuwansu sch in, duk abinda
baruwanta bata minding buissnes inta akai. Hasalima bata fiya maganaba bakowa take
kulawaba. Hakan yasa dayawa dakacin mates innasu suke ganin girman kai gareta especially
Shema da Zuzu. Tun farin karatunsu suke shigemata datagan ba karatunne gabansuba yasa ta

ajesu a Side. Hakan yasa suke takun saqa dasu.. A bakin kofan Lab in tatsaya tasaka lab-court
inta tana zura Tag inta agaban rigan taji anbangajeta.

Tag in yai gefe tai taga2 zata fad'i tai saurin dafa jikin block in. Ko ba a gayamataba tasan
bazasu wuce Shema da Zuzuba.

Daukan Tag inta tai tasa tashige Lab in batareda ta dubi kowaye yamata hakaba. Tareda
qudurcewa a ranta matuk'ar yau aka had'asu Group daya a Practical in bazata shigaba sede
yakoreta.

Yanadaka gefe yagan duk abinda yafaru yaji tak'ara birgeshi matuk'a shima yarufamasu
baya yashiga Lab in anata hayaniya seda practical teacher in yaxo kowa yanutsu. Yai dividing
insu Group Group. Allah yataimata group insu daban2, su biyu mata daka ita se Jidda ja'o. Aka
fara practical in Tissue Respiration. Tanata hadamasu Apparatus tazo aje ruwa kawai tazubama
USMAN BELLO GALADIMA ajikinshi. Gashi dama yabi yasa mata idanu duk abinda take
idansa nakanta tun shigowanta dasafe.....

To suwaye wadannan??
Kutara kusha labari

IN DEDICATION TO MY ANEE AND MISS XOXO......

ANISA_DIDI�
[2/18, 10:37 AM] +234 703 962 5239: 26/10, 9:30AM
♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡
Na
Haleema G Khaleel

Godiya ga Allah. Godiya agareki ANTY AZIZA I GOMBE{```UMMYASMEEN```} Allah yabar
k'auna❤

0⃣2⃣

A haka har suka kammala practical innasu duk da ita atakure take yadda yaketa satar
kallanta.. Kiran Attendance malamin yayi kowa yai ficewarsa. Har suka kammala darusan
ranar.

Agajiye liss tada gida kayanta kawai ta ajiye tashiga band'aki, wanka tai tareda d'auro Alwala.
Shiryawa tai tanufi d'akin Innarsu.
Zaune tasami Innar tana ta gyaran kayan K'annanta, gefanta kuma Ahmad(deedat) dan,autansu
yanata rikici Inna tahanashi fita. sannu da gida inna tafada cikeda ladabi, Innan ta amsa fuska
sake. To Rigimau miye kuma? NAJA'ATU tafad'a tareda janyoshi jikinta. Meya faru da d'an
Inna? Tace masa tana shafa kansa, alamun rarrashi. Ba Innace tahanani futaba, yafad'a tareda

rufe idansa waishi yayi fushi.

Haba Deedat banda abunka ai Inna tayi dai-dai datak'i bari ka futa bakaga Magriba takusaba.
Kuma ba asan Yawo, yahakuri kaji wataran zamuje unguwa muma ko? Damurna ya amsa yace
ah! Har gidansu Anwar zaki kaini muhau lilo ko? Yafara tsalle yana murna yasaki ransa kaman
bashiba.
Murmushi tai k'asa-k'asa takallo Innar tasu da itama Deedat in yasata dariya. Naja'atu tace Inna
gara shima Deedat asashi a Makaranta tunda ankusa d'iban sababbin D'alibai. Wannan surutun
da san yawan nasa duk ya ragesu.

Ajiyar zuciya Innar tayi hmmm! Yayar,Salim kenan. Domin Innar bata fa'dar sunanta itace
'yarta tafari. Su zauna si hirama seda Najar ta dage. Dan ita Innarsu Al-kunya gareta irin na
iyayen daa. Kuma inbatai da itaba dawa zatayi tinda Rayuwar tazama Naka sai naka. Dadin
zama sai bare inji Hausawa. Innar tace Allah yakaimu muga yadda za'ayi. Domin Rayuwar gidannan tana bani tsoro. Hakuri
zamu kara Inna, wataran sai labari Naja'atu tace tana mai share hawayenta.

Mutara domin jin gundarin labarin!!!


Didi_Aneesa�
[2/18, 10:37 AM] +234 703 962 5239: 28/10, 5:07PM
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*.....♡
Na
*Haleema G Khaleel*

Godiya sosai *ummyasmeen*. Allah bar kauna❤

WAIWAYE:

0⃣3⃣

Alh,Abdul mu'iz Auwal Getso shine Mahaifinsu Asalinsa 'yan Getso ne dake Gwarzo, su uku
mahaifiyarsu Iya Rakiya tahaifa Baba,Barira seshi Abdul Mu'iz da k'aninsa Muhammadu.

Dakanan kuma Allah yakar6i abarsa, hakan yasa mahaifinsu k'arin aure. Ya auri Baba Asabe.
Har itama tahaifi nata 'ya'yan su biyar hudu mata d'aya Namiji Azeema, Furera, Saudat,
Kareema sekuma Umar autansu..
Rayuwa sukai cikeda k'aunar junansu, suntaso duka kansu a had'e. Baba Asabe takula
dasu dukansu. Bata yadda wani zaije gidan yaga Alamun ba ita tahaifesuba. Sunsami tarbiya
da karatun addini dana zamani dai-dai misali. Har yasamu yashiga F.C.E Bichi ita kuma Barira
aka mata Aure.. Haka har lokacin da kowannensu yai aure. " Ta dalilin cigaba da karatunsa

yamaidahi Birni". Yafara kasuwanci. "Tinda 6angararen dayake kenan".

Yana zaune a unguwar 'Dorayi,Babba. Ba laifi yayi Aure-Aure.
"Hajiya Aina'u itace matarsa ta lalle. Tanada 'ya'ya biyar. Tarasu awurin haihuwarta ta k'arshe.
Matarsa ta biyu kuwa. ```Auren,zuminci```, akaimasu da ita wato Mama-Lubabatu itama
'ya'yanta takwas dashi.
Dakanan ya Auri Momy Lami da Goggo Safiya. Goggo Safiya itama 'ya'ya takwas ta haifa.

Tarasu yai su duka "yasanar masu zai 'kara Aure". Bakowo bace kuma face, Ummu-Salma.
K'anwa gawani abokin cinikayyarsa dake Gusau. "Wadda itace Innarsu Naja'atu".
Jin hakan bak'aramin Tayarwa da Momy Lami hankali yaiba. Ta tada K'ayar baya. "Hakan
kuwa yai sanadiyar barinta gidan.

Inna Salma itace matar daya auro ta 'karshe kuma yake Matuk'ar santa da tausayinta. "Domin
tasha wahala agurin mutan gidan dama 'ya'yansa mata manya dasuke ganin Sa'arsu aka auro."
Kuma tanama kansha.
Danma tana Hak'uri da kawar dakai gameda abubuwa da dama.
**********
Wannan kenan!!!

*Didi_Aneesa*�
[2/18, 10:40 AM] +234 703 962 5239: 29/10, 12:30PM
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*....♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

0⃣4⃣

Banafsha itace Babbar 'ya agidan, Allah yayita mai Larurar, Kurmanta dakabaya ma ta,rasu.
Daka ita sai Habiba, se yaya Lawan shine babban namiji kuma 'da na uku duk 'ya'yan hajiya
Aina'u ne takuma haihuwar Adam inda A haihuwar Kausar ta rasu. Se rik'onta yakoma gurin
Mama Luba. Itama 'ya'yanta takwas. Dina, Fadil, Bahijja, Fahad, Haris, Labiba, Rumaisa da
Habibu.

Momy Hadiza kuwa 'ya'yanta hudu: Bilkisu, Afiya, Fa'iza se Musa su kadai tahaifa tabar gidan.
Inda Goggo Safiya takeda Takwas itama: Hafiz, Idrisa, Mabruka, Madina Bilal, Dauda, Nasir da
Juwaira.

. Inna Salma, Mahaifiyar su Naja'atu. Tun lokacin datazo gidan, Dina da Habiba sunga Sa'arsu
mahaifinsu ya auro suke taya Iyayensu Kishi. Bak'aramin wuya tasha agurinsuba. Gashi bata
haihu da wuriba sedaka baya. "Bayan anmasu Aure har Dina tahaihu" da shekara biyu sannan
Inna Salma tahaifi tagwaye, Isma'il da Ibrahim. Sannanne haihuwa ta bud'e mata akai-akai.

"Ta haifi Naja'atu dak'annanta Kamal, Samiha, Fawad , Salim da Autansu kuma Autan gidan,
wato Ahmad(Deedat)".

Duka 'ya'yan gidan su 32 ne biyu sun mutu.
Naja'atu itace 'ya ta Ashirin da biyar Agidan. Duka in an ha'da da kannanta tara dana sauran
d'akin dakuma wadda suke Uwa daya Uba 'daya.
"Alh Abdul-Mu'iz yakasance mai yalwatawa iyalansa komi dayake ahakkun Uba shiyakeyi.
Makaranta mekyau da tarbiya gwargwadan iyawarsa " Lokacin dayake kan samunsa. "Tinkamin
karayan arziki tasameshi.

Watarana Inna suka tashi Samiha bata da lafiya, ciwan ido dakyar aka wanke, mata da ruwan
'dumi yabud'u.
"Ga Alh, bashida kudi"
Sukarasa yazasiyi,
Ita ba sana'a ba.

dakyar Hafiz d'an Goggo Safiya yasamo mata 'dari hu'du. "Dominshi yana tausayamata" kuma
jininsu ya had'u. "Tamaidashi tamkar ita ta haifeshi ita dama bame zafi ba".
Sau dayawama inyasamo 'yan ku'di wurin sana'arsa yakan raba biyi yabata, duk abinda
yasameshi kuwa na dad'i ko akasin haka zai gaya mata tabashi shawarwari. Kuma yaga fa'idan
hakan.

Hausawa sukace ```Abinda babba ya hango, yaro ko yahau Dala baze ganoba.```


*Aneesa_didi*�
Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:40 AM] +234 703 962 5239: 30/10, 4:17PM
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

0⃣5⃣

Da d'ari-hudu da hamsin, tahad'a suka tafi Asibitin, Murtala dake cikin gari,
Dukda haka bak'aramar tafiya tashaba, duk dan tarage kudim motan.
Aka duba Samihan aka bata magani. Sunsha wiya kafin sudawo.

Da dawowarta tatarar da abin mamaki. "K'aninta Sa'ud yazo daka Gusau" . Da farincikinta
tatareshi. Dukda bata da wani abu dazata bashi. Koba komi ```Shinfidar fuska.... Tafi ta
tabarma```.

Balle d'an uwanta dasuke ciki d'aya dashi.

Sannu da zuwa sukaima juna. Yakarb'i katin asibitin, segani tai yafuta.
Tare dasu Isma'il suka shigo, yasiyo mata magungunan da madara me sanyi.
Bayan ya huta yaci yasha.
Yacikasu da tsaraba da Mahaifiyarta tahad'o yakamata, kwana2 yai yacikasu da
shatara ta Arzik'i. Yakoma Gusau.

Haka rayuwa taita tafiya, Inna nacigaba da fuskantar k'alubalen rayuwar gidan iri-iri, da
dad'i ba dad'i. Tana cigaba da hak'uri. Sabida 'ya'yanta " sune k'ananu agidan, kuma sune abun
a tausaya musu. Naja'atu da yarinta, tin bata fuskantar abunda akema Mahaifiyarsu harta fara
ganewa. Dukda tataso cikin gidan yawa.
Allah beyita mai hayaniyaba, asalima batada yawan magana. Hakan datakeyi yasa wasu daka
cikin yayyunta mata kecemata "Munafuka. Sumimi kasam. Kawai saidai tai murmushi. Inta
gayawa Innarsu tace mata tayi hakuri, 'yan uwantanw." Wataran zasu dena.

*bayan shekara5*
*Cigaban-labari*
Naja'atu yarinyace mai sanyin hali. Duk wasu haleyenta nak'warai tasamosu daka Innarsu.
Kyakyawace sosai, farin dangin babansu kawai ta d'akko, hatta yatsunta da sirantarta, na
Innane asalinsu fulanin Gusau ne. Akwai dukiyar fulanin. Sedai batada tsayi sosai.
Tashare siraren hawayenta. Tana tunanin wannan rayuwa. Wani abubuwanma sabida
ganin idon Babannasu ake bari. To inaga yafad'i yamutu! Yazasiyi?
Taja nannauyar ajiyar zuciya. Hmmm!!

*Didi_Aneesa*�
Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:41 AM] +234 703 962 5239: 31/10, 5:15PM
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*♡
*Na*
*Haleema G khaleel*

0⃣6⃣-1⃣0⃣

Ranar takama lahadi. Bata da sch, bayan ta kammala gyaran dakin Innar tasu, tashare tai
moping, se tashin k'amshi dakin yake bakace sunada masu fitsarin-kwanceba.
Babban floor ne se dakuna guda biyu da band'aki. Da k'aramin kitchen agefe. Inna da
Samiha da ita, a d'aki daya, "d'aya kuma kananun k'annanta mazane su3 ne aciki.

K'a'idar Alh ce dazarar yaro namiji yakai shekara 10 -12 za a maidaka waje boys quaters, haka
duk sauran d'akunan matan gidan yake. Dukda akwai babban Kitchen, wadda takeda girki ita
zatai azubama kowane 6angare.

Misalin 10am Hantsi yad'aga, tayi wankanta tanata tashin k'amshi, gefanta ☕ruwan-bunune, da

wainar gero taji k'uli�. Tagama karin safenta, tahau yin tsifa. Tawanke kan, ta gyarashi. Dan
dama ita ba ma'abociyan san kitso bace, duk da yawan gashin datake dashi.

Kitchen tashiga. Dan taya Innarsu had'a abincin Rana. " Tuwan dawa, da miyar d'anyar kub'ewa
taji busashshen kifi. sukayi. Suka kammala. Takaima kowana d'aki nasu. Sannan takimtsa gurin.
Dakomawarta d'aki sallah tai, ta d'an shingid'a, Nannauyan bacci yai gaba da ita. K'arar
wayanta ne yata data. Hafsa Hussain ce, 'yar ajinsu a islamiyya.
"Salamu Alaikum ukty"
Daka d'aya 6angaren Hafsa ta amsa, suka gaisa hafsa tak'ara mata tunida Aikin da aka
basu cikin littafin ``` *Durusulluggatul arabiyya* ```domin tayi kada tazo a hukuntata cikin wanda
basiba. Tad'anyi mata bayani darasun dayadda zatayi. "Sukai sallama. Sesun hadu a
islamiyyan. Duk da bakullum take zuwa ba. Amma tana kiyaye kowane abu dazesa a
hukuntata.
Sauri tai tad'akko jakanta, tafara yin aikin, tai iya wanda tagane, sauran kuma in sunje
Islamiyyan kan akar6a takarasa.

Wanka tafarama Salim shi kuma Kamal yai nasa suka shirya seda suka jira Samiha ita ma
tashirya sannan
Naja'atu tasasu agaba sukama Inna sallama 3:30 suka tafi a hanyar islamiyyan, suka hadu da
Fawad yayi futu-futu da alama daka fillin ball suke. Salim yace" yaya,Fawad yau bazaka
makarantaba? "Ganin kallan da Naja'atu kemasa ya hau sosa k'eya. Yanzun zan shiryo nataho.
Yafiye maka de tafad'a. Danshi tin yana yaro inda abinda yafi tsana to ace yatafi makaranta. Tin
ana dukansa har akagaji aka basshi. Kunsandw maza dak'in makaranta.
Musamman Islamiyya. Sukai gaba suka barshi karya sasu latti.

Bayan an idar da Sallah, kowa yai Ajinsu.
A Ajin su Naja'atu maza sun zauna matan ko suna tsaye basu sami Tabarma ba, gashi
indai Malam yariga yashigo sede su zauna ak'asa.
Yadda kua sukeji da gayu,(miss u gayu-gayu). Nafisa tatashi sarkin tsiwa� aiko tama
mazan tatas hadda fad'in basa kishinsu. "Su sunsamo abun zama amma su ko oho. Wani dan
ajin Sanusi yaita bata hak'uri. Yafita yasamo masu.
Hannun Naja'atu taja dukda ita bame yawan maganabace, se ma abum yabata dariya
ganin anja Hafsa,Sady da Nafisa hassan. Aji-Aji sukai tabi, Har suka gano Tabarmassu.
Aikan ansha jaraba kafin su kar6o. Wata Fiddausi a ajin ta tashi tanata sirfa masifa, sega
Malaminsu Malam,Farouk, yakirasu shima yahau nasa waisu sun had'e kai farare, se rashinji
sukai. Nafisa kuwa ta Cuno baki�(mom heena).
Yace "kuma karna k'ara ganinku haka batare da kunsa bak'a acikinkuba. Amsawa sukai
yace kowa yakoma Ajinsu.

Nafisa sarkin mita kuwa tai tayi d'ayan Nafisa da Sady natayata. Sukuwa Hafsa da Najah
sede si murmushi.
Akasa tabarma kowa yazauna. Suka kara jerewa su biyar a layi. Ita Naja'atu sarkin tsoro
k'ok'arin chanja waje take aikua Nafisa tajawota hartana k'okarin fad'uwa abinka da ba k'iba.

Muraja'ar Al-qur'an akafara. Hakan yasa kowa ya nutsu.
Sukai karatunsu suka gama. Har aka kammala karatun. Malamin Arabiyya yaxo ya
ansa Aikinsa dukda bata gamaba, haka tabayar..
"K'arar K'ararrawace ta ankarar dasu. Sunata surutu. Sukai addu'a kowa yatafi.
Abakin get in Makaranta ta tsaya jiransu Samiha, suka rankaya sukai hanyar gida. "Kamal
bazaka tafi a hankali ba! "Kullum kai kenan kaita gudu ahanya sekace yaro. Bakaganin ko Salim
baya abunda kake."

Bata ankaraba sejitai Kiiiiiiiy. Mota tai gaba da Kamal...
Waiyoo yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login