Showing 12001 words to 15000 words out of 32509 words

Chapter 5 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf

27 Apr 2025

2144



"Ah mana kobakisan inada Mata ba? Kishiryama gidan mai mata zaki"😉

Reply in dabata sake maidawaba, dama wannan yanada mata amma baigaya mata ba? Yanzu
yazatai, gashi tarigada ta amsa a wurin Baba, da fasawa zatai, dan ita bata marmarin auren mai
mata, kodan irin wuyar da Innarsu tasha, dukda bata yadda sanshi takeba.

Anya kuwa Naja'atu?
Kodai kinyi gamo? Kihine dai kawai😂!!!


Sory 4 late post
So many isues nakeda.
Afuwa plss makaranta ina k'aunarku duka. Allah bar zuminci.


*Aneesa_didi*🍼🍉�
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: 13/11, 12:20PM Didi
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*


*31-32*

Ta dad'e tana mamaki, har sarkin iya sata yasaceta daka inda take.

Jin shirun yai yawa bata damai da reply ba, shikad'ai yaita dariya abinsa. "Nafara gano lagonki
Queen of my Heart". Seda yai salloli da Addu'oinsa sannan yakwanta, da tunanin Naja'atu.
Abaya idan akace zaiso wata macen bayan Bilkisu bazai ta6a yadda ba, amma yanzu
gashi daga had'uwarsu da ita komai ya chanja, yanzu yafahimci Soyayyar, duk zaman dasukai
abubuwan dayakeji dangane da ita Tausayine, yanzune soyayya tai masa *Dabaibayi* taimasa
kamun da saiya had'a da Addu'a, karta sashi a mawuyacin hali.
Jitai kaman ana magana akanta, tafarka da addu'a a bakinta, Innarsu tagani cikin yanayi, tayi
k'ok'arin tashi amma takasa koda motsa k'afarta, Naja'atu tace "Inna miyasameki? Lafiyar Allah
muka kwanta".
"Kamamin Naja kikaini band'aki" tayi mamakin jin Innar ta ambaci sunanta yau. Da
taikamakon Allah tataimaka takaita band'aki, har alwala tai tadawo da ita kan sallaya tazaunar
da ita, alwalan itama ta d'auro, taita nafilfili tana kai kukanta gun Rabbi da nemawa Innarsu

Afuwa.
Har aka kira assalatu, Innar daka zaune tai sallar, itama tai *Raka'atanul-Fajir*, ta d'ora da
Sallar asuba.
Zamatai tanata zikiri, har gari yafara haske, data duba taga Inna tasamu bacci, tashitai
tahau kintsa d'akin nasu, tasa Kamal, Salim sukai wanka taiwa Deedat, itama tayi, Samiha
kuma duk tahad'a musu kayan karin safe, Inna tafarka tagaduk shinrya, suka gaidata tareda
yajiki, addu'a tamusu sosai sannan suka tafi. 6angaren sauran mutan gidan suka biya, suka gaidasu tareda sanarmusu halin da Innar
ke ciki, sabida halin rayuwa. Naja tace da Maman danAllah in Iya tazo tasa tataimakawa innan
kafin sudawa. Suka tafi makaranta.


Wunin ranar haka tayi sukuku, dandai kawai makarantar suna zangon k'arshene, bataso tasake
dawowa inta tafi kawai tatafi, wani sashen na zuciyarta tatuno yanda suka k'are da Usman
adaren jiya. Jitai ma komi yafuta akanta, taita Allah Allah atasi.

Sunagama lectures in ranar ko Sallahr, la'asar bata tsaya tayiba tatafi gida, seda ta duba Innar
hankalinta yad'an kwanta, sallah tai sannan tataimakawa Innar tai wanka tareda Alwala.
Tashafeta damai tasamata kaya, abincima dak'yar taci kad'an.
Homework suke koya musu Fawad da Samiha, itakuma tana harhad'a musu kayan
wanki da Unifoam insu,
Inna tana daga d'aki, tari yasark'eta, yitake ba k'ak'k'autawa, dagudu duk sukayo wurinta,
me mik'o ruwa nayi masu sannu nayi, Naja dak'yar ta d'agota tanata hawaye, Fawad fita yai da
sauri yaje ya fad'awa Babansu yanatareda Idrisa Dauda da Hafiz, atare duk suka shigo d'akin,
shigowar Ibrahim kenan, yada daka wurin shirye-shiryen tafiya makarantarsu, Isma'il kuma
bayanan.

Sukai ta mata sannu, abin kaman k'arashi ake, ganin haka yasa Alh yace akaita asibiti.
Asibitin Nasarawa aka kaita ```Emergency``` Dr,Badariyya itakeda duty a lokacin, aka
kwantar da ita Drip tafara samata, tai mata 'yan tambayoyi, tarubuta magunguna da allura asiyo
mata.

Ya,Hafiz da Ibrahim ne sukaje ```Pharmacy``` suka siyo magungunan da alluran aka bawa Inna
maganin, allurar kuma akasa cikin drip in.

Abu kamar wasa jikin Inna yak'ara tsanani, dole aka bata gado. Naja ce ke kwana, dasafe kuma
Isma'il da Ibrahim su wuni, tunda basu tafi Makarantar ba sukuma sauran k'annannasu sede
akasu jefi-jefi saboda Makaranta.
Haka ta had'a da zuwa Makaranta da zaryar asibiti, tsawon sati biyu Ummin tama da
Anty Husna saida Kawu Sa'ud yakawosu suka dubata..


*Bayan Wata d'aya*

Hankalinsu yakwanta ganin Innar tasamu lafiya, duk nacin da Usman keyi akan tayadda yazo
taki, seda aka sallamosu sannan ta amince yazo harma yaduba Innar. Haka kuwa akayi, ranar
batada Sch. Bayan la'asar yazo, suka gaisa da Alh, sannan tafito.

Akan bench suka zauna dasuka gaisane yake tambayarta miyasa take wahalar dashi haka?
Hmmm tace "ni bana wahalar dakai miyasa kace haka?".
Hakane mana kowayanki nakira kullum akashe,
Kasande bana zama asalima bana cikin nutsuwa tinda kaga haka, se a 'yan kwanakinnan
nasamu kaina. Amma kayi hkr,
Wane mutum ai "Amarya bata lefi kota mari uwargida".
Rufamin asiri "Bata marabane",.
Sukai tahira abinsu, tafahimci sauk'in hali gareshi, anan yagaya mata ainahin waneneshi,
tsokanar ta yake amma yata6a Aure sede matar ta mutu yazo haihuwa ita da abinda kecikinta.
Zam baki labarinta bayanzuba amma. Taimasa jaje, yashiga yaduba Innan, itama asannan
taganshi. Yamusu sallama yatafi. Itama tacigaba da harkokinta.



Mutara danjin cigaban labarin.


*Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: [14/11, 3:41PM] Didi
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA......* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*33-34*

*Bayan wata biyar*
Takammala makarantar ```school of science``` cikin nasara, cikin lokacin sunyi shak'uwa
sosai da Usman Galadima, duk rashin magana irin tata saida yai nasarar koyamata hira,
musammanma dashi. Soyayya suke cike da aminci bege da k'aunar juna.


Dawowar yayansu, Bilal d'an Goggo Safiya daga karatu, a k'asar Ethopia inda ya had'a degree
insa nabiyu, a 6angaren Agric, hakan yasa 'yan gidan suka shirya masa walima.
Tunda safe wasu daga cikin 'ya'yan gidan suka fara zuwa, anata harhad'a abubuwan
dazasuyi.

Niyyarta a ranar taje gidansu Hafsa taga kayan lefanta. Amma walimar da aka shirya dole
tahak'ura, badan tasoba. Har d'a da jika suka had'u gidan yacika mashaAllah, kowa ya hallara

sede wanda basa gari.

Yammacin ranar bayan gama Walimar, Rumaisa yayarsu tasa Naja takai 'ya'yanta mata kitso
su biyu, shiga d'aki tayi kamar taafashe da kuka. Ganin haka yasa Inna tambayarta "Allah Inna
ni banasan shiga gidan Yawa.

Gashi yaya Rumaisa tace nakai Aisha da Nana, "kiyi hak'uri kikaisu.

"Haka tasasu agaba suka tafi, inta kaisu seta dawo in angama musu ta d'akkosu.

Gidan Yawa gidane dake cikin Unguwarsu, gidane dake d'auke da sassa daban-daban kowane
6angare da irin Sana'ar dasuke, wasu daga cikin mutan gidan kuma Bak'in ciki da hassada
taimusu katutu.
Basa k'aunar subud'e idanu suga wani yafisu, inda wasu kuma suke Rayuwa dabasu da
mai fad'a musu suji.
Sale d'ane agidan, yazo yace yanasan Bahijja, ita kuwa tai masa tatas gani shikansa baida
wata cikakkiyar tarbiya, daya takura mata ma tahadashi da mazan gidansu sukai mai magana
anyi d'auki badad'i bakad'anba, Dalilin dayasa suke cewa 'yan gidan su Naja'atu masu
girmankai, dad'i da k'arin basa Auren talaka sai mai kud'i.
Yanzunma badan tasoba tashiga gidan kaisu kitson, tinda ayanzu channe kad'ai zata kaisu
susami kitson.

Seda tai wuce-wucen hanya da lunguna duk acikin gidan, kanta kai 6angaren Magajiya mai
kitso, dasallamarta tashiga sashen, ganin Magajiyar tai cikin shirin fita unguwa.

"Ah ah! Yau kune a gidan namu? Inji mai kitson

"Gaisawa sukai, Naja tace "bazasu samu kitson ba kenan naga fita zaki?

"Bakomai se ai musu ai tafad'i. "Masamu na karin safe.

"To angode inji Naja'atu ta mik'a mata kud'i da man kitson, tace zata dawo in angama ta
d'aukesu.

"To shikenan sekin dawo.

Tin shigowarta suke ta munafincinta, sam bata kula dasuba, se yanzu dazata tafi, taga se
harararta wani Rabi'u yake, itadai tawucesu batace komaiba se Addu'a data karanto acikin
ranta.

Gidansu Hafsa kawai tashiga, bata koma gidaba, suka bud'e dandalin hira ta shantake acan.

Yaya Rumaisa kuwa ganin magriba takusa basu dawoba, ta Aika Bahijja taganosu, dazuwanta
angama musu kitson, suka taho.

"Innalillahi Hafsy se anjima nabar yara gurin kitso, gashi magriba taka kai kin rik'eni, hmmm
kinga natafi, tarakata sukai sallama.

Gidan Yawa takoma, yawanci basa nan, gidan yayi shiru, tanata sauri, tawuce lungunan ganin
bakowa gurin sekukan tumakai da kaji.

"Jitai an janyota had'e da toshe mata baki, kici-kicin tak'wace take amma takasa, ga ba halin
ihuu an rufemata baki.
Shikuwa lalubar yadda zai yaye hijabin jikinta yake.
Ihu take tana k'arawa amma babu maijinta balle aka mata agaji, yadda aka rufe mata baki


😳Waiyo Naja'atu lovers!!


© *Aneesa_Didi*
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: [15/11, 5:30PM Didi]
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*35-36*

Tsam yarungumeta a jilinka, yana sauke ajiyar zuciya, Rik'o yamata bata yadda za ai tak'wace,
kyakkyawan motsi kasawa tai, ambaton Allah kawai take azuciyarta yakamata d'auki.

Kici-kicin yadda zata k'wace jikinta take. Wani k'arfi taji yazo mata, Gwiwar hannunta tasa
tabugamai a fuska.

"Beyi aune ba yaji bugu a idansa, ihu yake yana k'arawa ganin haka yasata gudu bata tsaya ko
ina ba sai d'akin Inna.
Kan meye wannan mutan gida duk sun firfito, ganinsa sukai rik'e da ido yanata zunduma
ihu, seda yayansu Sale yazo yajanyeshi.

Kallo duk mutan falon suka bita dashi wasu daka cikin yayunta dabasu gama tafiyaba, ganin
tashigo ba sallama kuma se kuka take, toilet tai saurin shigewa dankada ma su tambayeta
abinda yafaru.

"Kuka take kamar an aikomata da sak'on mutuwa, ganin abin nata bana k'are bane yasa Inna
tashi tabarta, hannun Innar ta rik'e tacigaba da kukan, ganin haka Innar takoma tazauna,

lallashinta takomayi hartai shiru, asannan tagayawa Innar komenene.

"Hankalinta ba k'aramin tashi yaiba, dajin abunda yafaru abinka da mahaifiya 6oye tata
damuwar tai tareda lallashin, Naja'atun tayi mata nasiha mai ratsa jiki. Kwantawa takoma tayi
tanata juyayin abun cikin ranta.

"Cikin kwanakin da suka biyo baya, zancen tsiyayewar Idon Saminu duk yabaza unguwa,
Naja'atu kamdamuwace fall aranta, duk tabi tarame abinci ma dak'yar takeci. Ko bacci take
arazane zata tashi, ganin yanayin nata yasa Inna tasa akaitamata addu'a da zamzam tanasha,
hartafara dawowa nutsuwarta, niyarta takoma Islamiyya, amma ita kanta fitar baso take ba.
Zaune take tana karanta novel mai suna *'Yar Baba*tanata nishad'i abinta, k'arar wayarta taji
Inna ta mik'omata, ganin Usman ne, cikin raha tace "yau antuna mu kenan"

"Hmmm yaja gauron numfashi yace "hakanema? Ke kin tunani ko saud'aya, gara nima za amin
uzuri, tinda karatu yarufeni.

"To amun afuwa banji dad'i bane kwana biyu.

"Subhanallah! Miyasami ```Q```ueen of my ```H```eart? No wonder jikina yaban, kinsan yanzu
kominmu d'aya. Kifito kawai kekad'ai nakesan gani, shiyasa daka dawowata ko 'yan gidan bamu
ida gaisawaba nataho gurim Zuciyata.

Hmmm cike da kunya kaman yanaganinta, dukni kad'ai? Banganeba yaushe kadawo? Tace
tana zaro ido alamun mamaki.

"Kifito zakigan, inba so kike nashigo cikin gidanba, kinsan nine d'angidan kekuwa haya kike.

"K'yalk'yalewa tai da daria " kai ya Usee" tunda cikin raha take yasata fad'in haka,


"Baki yaddaba kenan to natafi, dama Mama tanatamin tsiya, nazo kuma kinmin haka Nagode.

"Laaah! Afuwa DanAllah, Ina zuwa takashe wayan. Tareda mik'ewa. Band'aki tai saurin fad'awa,
Inna ko tahau fad'in, " Badai wanka zakiba, mutum yayo tattaki yazo amma sekin 6atamasa
lokaci.

Murmushi yai tareda shafa kwantaccen gashin bakinsa. Yasamu Bench daka gefe yazauna,
kamin tafito.


Afuwa plss makaranta,
Kutaya mu addua plss Allah yabama Uncle lafiya.!!!

© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: {21/11, 2:00PM, Didi}
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*37-38*

Da hanzarinta tafito daka toilet in, fuskarta fayau Hijabi kawai tasa tafita.
Tun kafin ta k'araso murmushinsa yake mata maraba, ganin yayunta sun shigo gidan
kunya kaman k'asa tabud'e tashige.

"Tasowa Usman yayi sukai Musaba ha da yayunnata. Itama tagaidasu tawuce.

"Nesa dashi tazauna bayan taimasa sallama.
"Ai nazata bazaki futo ba, yace.
"Hmm to ai kaine nasan ko zolayata kakiyi.
"Au hakane ma abun?
To yahak'uri ai gani. Fatan kazo lafiya?

"Lafia lau, Queen, nasameku lafiya, yasu Innata dakowa na family?

"Alhamdulillah kowa sunane lafiya ya,mutan gida? Ina yaya Yusra?

"Kowa lpy tunda kika ganni, Ah tace mun kuna waya ai. Amma kink'ki yadda ku gaisa da Mama,
gashi ita Sis Yusy har waya kukeyi.
"Sunkuyi dakai tayi tana wasa da abun Hijab inta. K'arfin hali kawai tai tace "to zangaidata
amma ba yanzuba, nasan yanxu saika kirata" Kede wannan kunyar naki keda zaki zama matar
d'anta inhmm!

"Hmm! To ai *kunya adon 'ya mace* (littafin My Feedo-Deedo). Hakane kinyi gaskiya shiyasa
kike k'ara shiga raina Najata.
"Harma nazama takan? Tafad'a tana karamar dariya.

"Dariya ma kike to ai kinkusa zama, yad'an sha mur tareda fad'in "Naja'atu yau nazo da
magana, dukda nasan anrigada anyi abaya, amma yanzun za akuma jaddadata.

"Ganin datai yadan sha mur seta tattara duk nutsuwatta tana sauraransa, tinda taji ya ambaci

sunanta tasan muhimmin abu zai fad'a.

"Naja'atu yakira sunanta akaro na biyu, AURE nakeso, kinga niba yaro bane, lokaci yayi tinda
nakusa kammala komai gameda karatuna course in da aka turamuma miyi saura wata uku
mugama. To sonake dana dawo lokacin ayi Auran, koya kikace?

"Nannauyan numfashi taja, tace "wannan maganar ai ba a hannuna takeba. Wurin manyana
zaka, su zasusan abinyi.

"Nasan da haka ai, amincewarki kawai nake nema. Inkin yarda sai ak'arasa magana. Ad'aura
aure kinzama tawa.

"Kasa cemasa komai tayi ta duk'ar da kanta tareda cewa "Allah yatabbatar da alkairy yashige
gaba. Amma kuma.
Ameen. Amma kuma me? Kifada kinji bazan cutarda keba kome kikeso ki fad'a kunyarnan
arik'a rage ta kaman ba mijinkiba yace yana darawa.

"Bawani abu bane, cigaba da karatuna kawai dama zance.
Indai dan wannanne karki damu, karatu sekince ya isheki, keda zaki aure likitan mata,
kinga sekina tayani nima ko nadubaki kidubani, batare da wani yagane miki miji ko angane min
mata ba.

"Dariyar da take 6oyewa saida tafito fili, wayarshi yazaro yashiga d'aukanta a hoto, bak'aramin
kyau tamaiba jiyai kamar yajawota k'irjinsa koya samu sassaucin da azazzalar da zuciyarsa keyi
akanta. Yai k'ura mata ido yana kallan kyakykyawar zagayayyar fuskarta. Komai kamar ita ta
za6awa kanta. Ganin abin nasa nayau yasa tace masa inyaje gida yagaida su Mama da K'annanta.

"Kawai dai kice korata kike, kingaji dani be ida rufe bakiba sega su Fawad sundawo daka
Islamiyya, Salim da gudunsa yazo hannu yabashi suka gaisa, sauranma duk suka gaidashi
suka wuce gida.

"Aranta taji dad'in dawowarsu, koba komai yanzu zetafi dan yau ta fuskanci da zolaya yazo
mata.
Shima Usman ganin dawowarsu yatabbatar mai da lokaci yaja. Badan yasoba yai mata
sallama, had'e da mik'a mata k'aramin buhun bagco daukeda Plantain, Kwakwan-manja,
Kwakwa da Agushi. Mamaki tai tayi tace Haba danAllah kai kana Student hadda wani tsaraba,
kaida za abama amma kaine mai kawowa? Cikin shagwa6ar data zamemata jiki hadda turo dan
bakinta.(Maryam Speaker�)
Usman kuwa galala yai yana kallanta, bak'i su dauwama a hakaba. Lallai Allah yasoshi daya
had'ashi da kalan matar dayakeso, wadda komi tahad'a, "Sokike mukwana anan naga Alama,?
Danai me kajika tace, toshikenan zanwa Mama waya nace 'Yarta ta rik'eni.

"Nidai baruwana ban rik'eba, angode wannan kayan dukmu kad'ai. Allah yasaka da alkairi.
kiran sallar magriba dole yasa sukai sallama, yana mai jaddada mata da kadata kashe wayanta.

"Murmushi kawai tamasa tashige gida shima yatafi.

"To bayan Sallar magriba sannan taiwa Inna bayanin kayan takarkasa tabawa kowa nasa,
gudun k'ananun magana irin ta mutan gidan.

Afuwa plss makaranta.

© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: [24/11/16, 6:22PM] Didin Anee�
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*39-40*

Cikin watannin da suka biyo baya Soyayya sike kaman yacinyeta yakeji, dama ita kunyarsa
datake matuk'ar ji yake hanata maida masa da martanin irin zafafan kalaman dayake gaya
mata.
Saranar biki akai nanda sati shida.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login