Showing 24001 words to 27000 words out of 32509 words
Chapter 9 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf
rabuwa sukai. Itada zuwa kuma se ikon
Rabba. Danma zuriyar data shiga tsakaninsu in Allah yaraya abinda zata haifa.
Har sukaje gida bata k'ara cewa k'alaba, dasukaje gidan nema bayan anfito da ita daga motar
wasu daga cikin 'yan Mazan gidan dasuka tarar a harabar gidan suka k'ara yimata ta'aziyya. Da
hawaye tashiga gida. D'akin Innar aka gyara mata bayan gadon dake d'akin, k'atuwar katifa
baban yasaimata aka samata daka gefe daduk sauran kayanta aka shirya mata, kwanciya tai
tanata maida numfashi. Tafad'a duniyar tunani har bacci yai awon gaba da ita.
Zamanta agidan tun bayan dawowarta bayabo ba fallasa. Duk abinda takeso dai-dai
gwargwado tanasamu. Matan gidan sunanan da halinsu, danma bakasafai take fita ba daga
zuwa Asibiti dashima tafi zuwa dadare, se d'an atisayen datake zagaya cikin gidan. Ahaka har
cikinta yashiga wata tara. Haihuwa yau ko gobe. Inna duk tatanadi kayan jego da ake buk'ata
gamai haihuwa tashirya. Hatta kayan mai jegon duk tashirya sejiran Allah yasauketa lafiya.
Zuwa lokacin Usman yayi kwana Arba'in harda d'oriya da rasuwa.
Sosai take kewarsa, danma Inna tayi namijin k'ok'ari wajen hanata zuzzurfar tunani. Data fara
zatai tabata hak'uri da nasiha harta samu tasaki jikinta. Maman Usman ma tana yawon zuwa
dubata banda aiken datake mata. Haka itama Yaya Yusra tana tafe da abubuwan arzik'i duk
dan ragewa Naja'atun damuwa da kewar babban rashin datayi.
Afuwa makaranta ankusa k'arka'arewa da yardar Allah.
© *Didi_Sady*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*76-80*
""Tun suna saran haihuwarta har EDD haihuwar yazo yawuce, ba abinda kedaminta se
kumburin dajikinta yake gawani haske da d'ashewa daduk jikinta yayi.
Wata safiya suka nufi Asibiti da ita dan tun cikin dare take abu guda, dak'yar ta iya Sallah
asuba. Dan itama Sallar azaune take tunda cikinta yatsufa. Abincin da Inna takawo mata taga
bata bud'a komaiba. Tana kishingid'e sefitar da numfashi take da k'yar duk tahad'a gumi. Inna ta
tallafota tareda jinginata ajikin garun d'akin "Inna Bayana ciwo" Naja tafad'a dak'yar.
"Subhanallah! Badai abinne yazoba? Ina zuwa" Innar tafad'a tafita daka d'akin.
D'akin Mama Luba Uwargida tashiga tasanar mata "ko zatazo takai Naja'atun Asibiti tunda itace
babba agidan. Bud'ar bakin Mama Luba secatai "Ita gaskiya bazata iya futaba dan bak'i zatai,
yanzuma zaman jiransu take suna hanya." Inna mai sauk'in kai takuma cewa "dama dan kada
abin yazama laifi shiyasa tazo tagaya mata dan abata girmanta na babba agidan... bata idasa
rufe bakiba Mama Luba tace "kinga dan Allah banasan hayaniya kinzo kin gayamin tunda nace
bazaniba a hak'ura mana". Sum-sum Innar tafita tana Addu'ar Allah yanuna mata ranarda
mutan gidan zasu shirya.
To yadda sukai da Mama Luba haka sukai da d'aya matar gidan wato Goggo Safiya ita
cewa tai ma "Unguwa zataje taje takaita mana su innasune wasuke nema yakai musu. Ranar
Inna ranta ya6aci sosai, dandai kawai batada dangi agarin za'ana yimata haka. Samiha tanemo
a waya, suka rufewasu Fawad d'akin insun dawo tunda kowa zai iyaima kansa komai dama
Deedat takeji inyada yaga batanan.
A Napep suka tafi Asibitin ko Alh bata sanarwaba. To duk zaman awannin dasukai Naja'atu bata
haihuba aranar. K'arshema dawowa gida sukai wajen Maghriba da aka tabbatar musu da cewa
"ba haihuwar ceba. Haka Naja taita fama saida taikwana biyar ahaka.
Zuwan da Maman Usman tayine suka yanke amaidata Asibiti.kar aje asamu matsala da
abincikin ko ita uwar. Da wannan shawarar sukai amfani. Motar da Maman tazo da ita suka
kaira Asibitin. Basu nemi kowaba dan ita kanta Maman d'an zuwan datake gidan tafahimci irin
zaman dasuke agidan. Dandai su Naja'atun da Mahaifiyarsu sun maida komai ba komaiba sam
abin baya damunsu dan dole wataran zasu dena ko duniya tabasu darasi. Lallai hausawa sunyi
gaskiya dasukace *"DUTSEN CIKIN RUWA..BAISAN ANA RANA BA"*. Asibitin Nagari Hospital
& meternity sukaje dan tun dawowarta Kano nan take zuwa.
Tun rana da aka kaita Asibitin Naja'atu take abu guda Nak'uda sosai take likitan dake Dutyn
Ranar yana kanta har dare lokacin tashinsa yai. Zuwa daren duk k'arfinta yabi yak'are Mama sai
mulmula mata bayanta take. Dr nafeesa datake dutyn daren tana zuwa lavour room d'in taga
yadda Naja'atun tayi cikin yabi yarairaye yai k'asa iya galabaita tayi bata haihuba. Kayan aiki
aka had'a mata da taimakon wash Nurses suka shirya Naja'atun Dr Nafeesan dakanta taturata
zuwa ```Theater room``` Emergency C.S zatai mata takadda tabasu sukai singning akai ciki da
ita.
Inna Addu'a take ta mata. Suna zaune jugun-jugun. Jiran tsammani har goma da rabi na
dare. Dr Nafeesa kuwa suna kan Naja'atu itada Dr Moses da sauran nurses. Baby boy akafara
cirowa sannan aka ciro 'yan mata guda biyu d'ayardai andenneta sosai acikin. Yara kamar
mahaifinsu duk aka gyaresu sede wadda aka ciro ta k'arshen ita sam batai kuka ba. Dr nafeesa
da Dr Moses suka rik'o 'ya'yan tareda wata Nurses suka kawasu Inna yaran. Se farinciki Mama
cema tai k'arfin halin cewa Ina Maman tasu bata gama maganarba aka turota akan gado zuwa
d'akin hutu aka shigaddasu duka da ragowar kayanta.
Yaran annad'esu a showel harsu uku, Maman Usman kuka tasa sosai da ganin yaran, yau ga
jinin Usman alokacin da Usman yabar duniya. Batareda hayaniya ba sukaita d'aukan yaran
sud'au wannan su ajiya sud'au wancan. Maman Usman kuwa ga hawaye ga dariya duk
afuskarta. Waya tasa tana tai musu Hotuna jitake kamar tamaidasu ciki sekace yanzu akafara
haifa mata Jikoki. Inna har tausayinta taji.
Se wajajen shabiyu suka bar asibitin akabar Inna da Samiha. Cikin daren yaran sekuka
suke mace d'aya da namijin, d'ayar ko motsawa batai ba. Zam-zam Inna tasa dabino aciki taita
basu suna sha, se jijjigasu suke seda sukai bacci suma suka runtsa dukansu.
Da Asbah bayan sun idar da Sallah Dr Nafeesa tashigo dubasu dan dawuri zata wuce. Anan
Inna taimata complaining kan d'ayar babyn sam batai Kukaba ko motsi bataiba. D'agata Dr tayi
tak'ara jijjigata amma shiru overall d'in Jikinta tayaye duka tad'an d'ala mata, nanma shiru,
tak'ara jijjigata ba alamun numfashi tace "I think so dama itace ak'arshe kuma biyun sundanneta
dakuma galabaitar da mahaifiyarsu tayi yataka muhimmiyar rawa. Batazo da rai ba." Atafi da ita
gida abunne. Allah yaraya sauran yabada masu albarka. "Haihuwar farine ko? Dr Nafi tafad'a
tana kallan Inna tareda mik'a mata Jaririyar. Tai musu sallama tatafi idan incharge na safe
sunzo zasu duba Naja'atun may b kafunnan ta farfad'o.
Karfe 7 nasafe Maman Usman tazo hae har Yaya Yusra, lokacin sukaita bugawa dangi nakusa
dana nesa waya. Suna sanar musu da haihuwar. Mik'o mata Matacciyar Jaririyar Inna tayi tace
"wannan bata da rai kutafi da ita gida a bunneta". Allah sarki Mama tace "Allaj yai bame shan
wuyar duniya bace." Can Sharad'an suka tafi da ita aka binneta inda aka kai mahaifinsu.
Lokacin dasuka dawo har Alh dasu Sadiq a sannan Naja'atu ta farfad'o. Likitan daya karb'i
dutyn safen shiyazo dubata yace "kar abari tai jijjinan motsi sosai, espcly kafarta sannan subata
ruwa ko abinci mai ruwa-ruwa, banda abu mai k'ayau. Yafaffad'a musu duk irin abubuwan daza
ai mata dawanda bazataiba. Dataimakon wata Nurse tai brush, aka bata shayi sannan suka gyarata. 'Ya'yan data
haifa aka ajiye mata kusada ita sunsha wanka sai k'amshin turaren jarirai suke. Tana daka
kwance 'ya'yan duk agabanta, kallansu taitayi cike da k'auna, wata soyayyar yaran taji tanabin
kafofi da jinin jikinta. "Kamarsu d'aya dashi ko Yaya Yusra? Naja tace da Muryatta dabata gama
warwarewaba, k'wallace tabiyo bayan maganar tata, itama Yaya Yusran sun bata tausayi sosai
taji itama kamar tasa kukan, dandai kadata k'ara bata k'arfin gwiwar yin kukan yasata danne
zuciyarta. Anan suka sanarmata uku tahaifa sedai d'ayar batazo da raiba. Zaro idanu tayi tace
"duk acikina, lallai Iyayenmu sunsha d'awainiya damu. Kuma dole miyi Biyayya agaresu
tahanyar dabata sa6awa mahalicci ba muddin munaso mu wanye lafiya a duniya. Alllah yasaka
musu da d'umbin Alkairu yabiyasu da babban rabo. Allah yak'ara bamu ikon cigaba da faranta
musu dayi musu biyayya bisa turbar Islama. Itakuma Allah yamata rahma yakyautata namu
k'arshen. Duk mutan d'akin suka amsa da Ameen.
Kwanansu biyar a Asibitin mai jego tawarware sosai, har tana shayarda yaran. Namijin mai
hak'uri, macen kuwa rikici gareta. Danna Inna da Samiha basu gajiya da d'awainiya dasu ko
kuka suke tana bacci ba kasafai suka fiya tashintaba. Inna takance "batta tai bacci tad'an samu
hutu, ita kada'i tasan gumurzun datasha daga rainnan ciki har haihuwarsu." Dukda dai kowace
mace da kalan nata abubuwan.
© *Didi_Sady*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*81-85*
_Afuwa Makaranta wannan labari. Bajan rai bane kunsan d'an adam ajizi ne. Abubua sunyi
yawa. Kwana biyu kuma banida lpy. Ga bukukuwa da aketayi a fam. In sha Allah before Jan
2017, zan kammala. Nagode da k'aunarku gareni aduk inda kuke._
~~~Aran kwana bakwai da haihuwar aka sallamesu da rana. Duk wani kud'i da aka kashe tun
farkon zuwansu Asibitin Baban Usman ne yabiya, dan cewa yai "Haryanzu da nauyinta akansu,
dan haka duk abinda ake buk'ata yace "Agayamasa" Mama kuwa suka 6alle bakin aljihu akai
komai cikin mutunci da girmamawa. Bare dasukaga anhaifar musu Tagwaye. Kayan barka sosai suka siya ranar dasuka koma
aka bisu da tukwici dak'yar suka kar6a. Acewarsu "Ai yiwa kaine anriga anzama d'aya.
Ranar suna kuwa bawani taro akai ba. Rad'in suna akai aka sawa Namijin sunan Usman
itakuma macen aka samata Asma'ul Husna. Samiha tasa musu Hassan da Husna. 'Yan barka
sukai tazuwa 'yan uwa da abokan arzik'i. Kayan barka iri-iri suka samu, wasuma sa shekara
suna amfani dashi.
Mejego tayi k'alau da ita. Dan jego mai kyau ake mata har sukai wata biyu. Yaran sunyi 6ul-6ul
dasu, kamarsu da mahaifinsu se dad'a baiyana take. Ita kanta Naja'atun kamar ba ita ta haifesu
ba, dan gyara sosai Inna da taimakon k'anwarta Aunty Husna sukai mata. Irin zugudan nan
dayawan masu ciki keyi bayan haihuwa, basu bari tayiba. Tayi k'alau da ita. Sedai idan takalli yaran nata takanji tausayinsu natashi dazasi basuda
mahaifi. Tak'udurce aranta bazata ta6a bari siyi Maraiciba.
Duk yadda zatai takare Mutuncinsu zatai wanda bai kaucewa shari'a ba. Kuma ga
kakannunsu da dangin mahaifinsu dasuke sansu da ji da k'aunarsu.
*BAYAN SHEKARA HUD'U*
Hangota nai cikin _Nagarta Shoping Complex_ d'auke da basket a hannunta. Deedat nagani
yak'ara girma rik'e da hannun wasu yara masu kyau dabazasufi shekara uku da rabi ba. Mace
da Namiji, kalan kayansu iri d'aya, sedai Bambanci na Mace da Namiji. Macen anmata kalba
datasha Bead se reto suke ajikinta. Tsayawa tai wurin kayan k'amshin gida tanata duba irin wanda takeso. Domin ita
ma'abociyar k'amshi tundaka najiki zuwa na d'aki hakama kyawawan 'yan biyun 'ya'yanta
Hassan sa Husna.
Naja'atu kenan matashiyar Bazawara, datun bayan rasuwar Mijinta bata sakeyin wani auren ba.
Asalima catai ita tagama, seda mahaifanta suka tsaya tsayin daka da Addu'a da rok'on Allah
tasaki ranta tadawo da walwalarta daduk wata mu'amala harta koma Makaranta da D.E daga
level2 tafara har take shekarar k'arshe a course in ```Nursing and Nursing science```. Jitake zata iya Aure ayanzu, kowaye yazo muddin yanada d'abi'a da mu'amala ta k'warai,
kuma yakwanta mata tayi Na'am dashi da wanna tasamu tarufe bakin Iyayen nata. Ganin ana
shirye-shiryen Auren Samiha da sauran k'annanta Mata, amma ita shiru.
K'wace hannunsa Hassan yayi, daga hannun Deedat ganin Husna tayi gurin toys dandama
tafishi wayo. Da gudunta nayara tayi gurin toys tagano 'yar tsana, Bangazar mutumin dataine
yasata tsayawa. (Sanadií ½í¸»)
Agogon daya d'aukane samfurin ```Dior``` yafad'i daka hannunsa har saida Glass in ya tsage.
"Ya salam! Ya furta da _Husky voice_ insa mai amo. Irin yawan dayasha yana neman ```Wrist
watch``` in besamuba se anan gashi yanzu kuma abinda yafaru ko biyan kud'inshi baiyiba, cikin
jin haushi da takaici afuskarsa yad'ago zai mata masifar wata irin matace dabata tafiya a
hankali? Tajamai wannan d'anyen aikin. Batasan irin wuyar dayasha yana abu guda naneman
brand na Agogonba.
'Yar k'aramar yarinya kyakyawa idanuwansa sukai tozali dasu.
Husna kam ganin yasha mur bashiri takama kunnuwanta tai kalar tausayi tace "Am sory Uncle"
ai saurayin besan sanda ya murmusaba yaji yarinyar ta burgeshi sosai. Inama 'yar sace, tunano
yadda Mahaifiyarsa babu abinda takeso irin yayi Aure, har matakaiga samun zuri'a.
Shafa kanta yai yace mata "Be careful kinji Babyta next time kirik'a tafiya a nutse karkije
kima wani irin tawa yadakeki, bama haka ba kada kiji ciwo kinji." D'aga kanta tayi alamun taji
tace "Thank you Uncle" Matashin saurayin yace "Oya give me five" yabata hannunsa suka tafa
sunata dariya.
Hassan ganin ba a daki Husna ba, sunata dariya, shima yataho yana dariya dabaisan akan me
ake ba.
Da mamaki afuskarsa yake kallansu duka. Mik'amai hannu Hassan yayi da nufin su gaisa.
Saurayin kuwa yakama d'an hannun Hassan suka gaisa. Tsugunawa yai dai-dai tsayinsu yace
"U are identical 2wins?" Saboda tsananin kamanninsu yayi yawa. Yakuma fad'in "Am i right?"
Yana cigaba da kallansu.
Husna da surutu takuwa hau zuboshi "Mamynmu tace mu Triplet ne amma d'ayar tamutu ita
bamugantaba.
Dariya yahauyi sosai daya jima baiyi irin taba. Yace "Shikenan nikam nayi new friends yau,
amma bansan sunankuba."
Husna takuma cafe maganar tace "Mu 2wins in Mamynmune yanzu amma sunannu ni
tanuna kanta sunana Husna Usman Bello Galadima, shukuma Hassan sunanshi Usman Usmab
Bello Galadima, sunan Babanmu aka samai shine ake cemasa Hassan. Amma har yanzu
Abban bai dawoba Mamy tace "Yayi tafiya inda ba a dawowa. Shiyasa bayanan.
Kuma mu kullum baya d'aukomu a school, sukuwa su Farouk Abbansune yake zuwa
d'aukansu." Tafad'a tareda kama hannun Hassan. Shima yace "Se Mamynmu ko Uncle."
Sunbashi tausayi sosai, yafahimci komai wato Mahaifinsu yarasu basuda wayo ko ba a
haifesuba.
Kama hannayensu yai duka yace "Tare dawa kukazo gurin nan?
Hassan yace "Da Mamy da Ya Deedat. Batasan munzo nanba dan tace mudena surutu inba
Alkairi mutum zai fad'a ba yai shiru. Har Rok'o dayawoma tace. Ana sace mutum inyaje yawo
inda baisaniba yadena ganin kowa har Mamanshi." Ko Husn Yafad'a yana kallan Husna.
Surutun kuwa sukai tamasa yanata record dan sun birgeshi. hadda tambayarsu to in aka
saceku yazakuyi. Zaro ido sukai suduka. Husna datafi wayo tace "semu kira Mamynmu awaya
ko Uncle Isma'il da Ibrahim."
Yace "To tayaya zaku kira?" Digit tahau fad'omasa yanata mamaki.
Jiyai sunkuma shiga ransa, kamar yatafi dasu tunda duk yaji details insu har Adress in gidansu
dana kakanninsu. Suka gayamai yaran masu d'ankaren surutu kamar sunci Kabarai. Ga wayo.
Kuma ai shima 'ya'yansane. Tunda hausawa sunce *D'a nakowane*
Tinanin dayai idan yatafi dasu Mahaifiyarsu yazatai dan ko ina take bazataji dad'i ba. Toma
haka ake daka ganin Sarkin Fawa sai Miya tai zak'i Koshi bazaiso amai haka ba. Dankuwa sai
inda k'arfinsa yak'are.
Yace musu "Shi sunansa Uncle mai zane, daga yanzu yazama Uncle insu shima. Sukuma sun
zama Friend d'insa. Suka tafa dukansu. Sunata mumma, yama manta da batun Agogonsa.
Zagaye sukai tayi, yasai musu toys da chocolate, wafer,biscuit dayawa. Aikam yasha
godiya gurinsu.
Sukaje aka biya kud'in. Har waje yarakosu, kaya taganosu dasu nik'i-nik'i. Ita Husna ma jan
kayan take.
Nemansu take tayi har suka futo zasu shiga mota. Cogewa tai tana kallansu se muzurai
suke.
© *Aneesa_Didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*86-90*
~~~Yaran sunsan in Mamyn tasu tai shiru, tana kallansu sunyi laifi kenan.
Tun basu fahimtaba, har suka gane me shirunta kenufi, dukansu suka saki kayan
hannunsu suka kama kunnuwa atare sukace "Afuwa Mamy" ganin tayi shiru batace komaiba
suka k'ara langa6ar dakai, kalar tausayi sukai sosai.
Shigewa mota tai kamar zatatafi basu, da gudunsu suka taho har Hassan yakusa kifewa,
"kayanfa wakuka barwa" Mamyn tasu tace, tana kuma kallansu, tasha mur. Suma d'if sukayi
suka sunkuyar dakai.
Bud'e motar tai atsawace tace "Kushige mutafi, zakusan kunje yawo daga zuwa daku
harda rok'o, punishment zaku kwana kunayi, Abincima bazakucuba tunda bakujin magana.
Ai bata k'arasa maganganunta ba suka shige motar dasauri suna kuka dukansu jin hukuncin
daza amusu.
Duk abinda