Showing 21001 words to 24000 words out of 32509 words

Chapter 8 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf

27 Apr 2025

2143

yahad'ashi inda yadace kaman zasi tafiya.

~~~~~~~~~~~~~
Akwana atashi lokaci yaita tafiya wasu daka cikin dangi sun zazzo mata. Harsu Samiha Ya
Hafiz yakasu ranar kuwa tasha surutu kaman karsu rabu. Inna taita aiko mata da rubutu da
magungunar gargajiya dan ance mata tafara kumburi. Har cikinta yai wata 8 kaman yanzu zata
haihu dole wasu abubuwan dakansa yake mata.

Tafiyar gaggawace tataso mai badan yasoba zaitafi yabatta tunda dama yakusa maidata gida
danta haihu acan. Yanemi alfarma gurinsu Maman benua da Mijinta kan suna kula masa da ita
badad'ewa zaiba danma dole ne tafiyar dabazaiba.

Dararranar kaman bazai bartaba tabashi farin ciki bakad'anba, jiyake kaman sukad'ai ne
masoyan da suka rage adoran duniya. Seda yamata wanka shima yayi suka hau hira
yanamaijin kama kada yatafi batareda Queen intasaba. Seda ta lallasheshi sosai da kalamai
masu kwantar da hankali dasa nutsuwa. Tausa yahau yimata yana lailaya bayanta har tahau
bacci yai musu addua shima yakwanta.


Safiyar Alkairy!!!


Waiyo team Naja afuwa plsss. Makaranta abun se hak'uri. Allah de yak'aremu da lafiya. Nagode
sosai didi tana sanku duk inda kuke.


© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*61-65*


Safiyar juma'ar dazasi tafiyar, dawuri yatashi, shara yafarayi yagyara gidan hadda kunna turare
a burner.
Ruwan tea yad'ora yahau ferara Irish, yafara suya yana 6arar plantain. Yasoyawa kansa
k'wai daban dan ita tunda tasamu ciki bakasafai take cinsaba. Yana cikin wanke kayan dasuka
6aci tashigo kitchen d'in ashagwa6ance tace "kai Habibi kullum saikai ta kwashe ladan" da
murmushi a fuskarshi yace "Yo ai kema kullum cikin samun lada kike, farantamin dakikema lada
kike samu, ballantanama cikin dake jikinki Allah kad'ai yasan ladan da kike samu. Allah dai
yarabaku lafiya. Yau ace ga 'ya'yana Jinina kuma Queen itace ta haifamin wana irin farinciki
zanyi. Allah de yanuna mana lokacin darai da lafiya. "Ameen" tace takarasa gyaran kitchen d'in.

"Wanka yafarayi yataimaka mata itama tayi, suka shirya sunata soyayya abinsu. Har sukai
Break-fast yakuma gyara gurin, duk saboda tausayinta dayakeji. Jiyake kamar kada yatafi ba
ita.
Kaya kala uku tahad'a mai tafiyar kwana biyu zasiyi a k'aramar bus in makaranta zasu tafi
awannan karan. Likitoci su biyar aka za6a zasuje workshop a jami'ar kano se driver dazai
tuk'asu.

"Kamar bazasu rabuba k'arfe 9 yakaita gidan Maman Benua kada zaman kad'aici ya dameta.
Haka sukai sallama tanata musu Addu'uan samun nasara da sauka lafiya, k'arfe 10 nasafe suka
d'auki hanyar Kano.
Maman benua da Karamci, dukda ba Musulmai bane amma Kafiran Amanane, tun
farkon zuwansu tafahimci hakan. Yanzuma cemata tai "tadena girki zatana aiko mata dashi,
dandai cikinta ita kad'ai bazai gagaraba musammanma yadda tai nauyi komai dakyar takeyinsa.
Ranar agidan tawuni se kusan La'asar takoma tareda Stepme 'yar Maman Benua da tatayata
zama. Kallo takunna mata tashiga d'aki fes-fes dashi se k'amshi yake rigar Usmance a kan
gadon ta d'auka ta rungumeta sosai ajikinta tana wasu maganganu dagaji nayabone. Sallah tai
tahau had'a kayan duk daya bari kowanne a inda yadace tasakashi.
Falon tadawo suka cigaba da kallan dukda ita rabi kallo rabi tana gwada kiran wayar Usman
datak'i shiga.

~~~~~~~~~~~~~

Tunda su Usman suka d'au hanya basu tsayaba se awani k'auye sukai sallar jumu'a, tafiya suka
cigaba dayi. Usman yanata kiran Queen d'insa da 'yan gida amma yakasa samu. Tun suna hira
jefi-jefi har kowa yai shiru, se karatu da suka kunna masubi nayi masu danna waya nayi. A
Kaduna garin gwamna suka k'ara tsayawa basu wani dad'e ba suka cigaba da tafiya har suka
shigo kano.
Tsautsayi daba a samasa rana/lokaci sunata sharara gudu daidai kwanar Waratu mai Tifa
yafito dagudu shima yai kansu motar su Usman tai gefe se cikin ruwan dake kasan kwaltar,
dukda duhun dagari yai mutane sun d'an taru sunata Salati da neman agaji abakin ruwan, motar
kuwa tashige cikin ruwa sai gefanta kad'an ake gani.
"Motar wata Ma'aikata ce sukazo wucewa ganin mutane a tsaitsaye sun fara taruwa yasasu
parking, dasaurinsu suk'a k'arasa bakin ruwan. Mutanen dake gurin sunyi iya bakin k'ok'arinsu
suga sunfito dasu amma badama dole aka nemo fire service, suka ciro motar datacika lumtsum
da ruwa. Ganin rubutun dake jikin motar suka tabbatar daga doguwar tafiya suke. A Ambulance
aka d'au su Usman daba wanda yake motsi acilkinsu, motar kuma akajata da jan way. Cikin gari
akai dasu General hospital ala kaisu A&E ba ai wani dogon bayaniba aka kar6esu danbasu
taimakon gaggawa. Tunda sunji bayanin suwaye kuma daka inda suke.


"Mama Mahaifiyarsu Usman tunda yamata waya kafin su taso yasanar mata zaizo gida ayau
Abinci iri-iri taimasa yaza6i duk wanda yakeso. Jin shiru-shiru har bayan Isha baizoba wayarsa
kuma tanata kira shiru.
Naja'atu takira bayan sun gaisa take tambayarta Usman ko yakirata sun sauka? Takasa
samunsa awaya. Naja'atu jitake kamar ta rusa ihu dan ita har batasan iya adadin kiran data
maiba muryarta araunane tace, itama tinda yatafi wayarsa tak'i shiga, lallashinta Maman tayi
sukai hangin wayar.
"Kiran wayar Samihane yasa takuma motsawa tanata tsokanarta jin Yayar tata tai shiru

bakamar yadda takewa samiha ba, tasha jinin jikinta, "Lafiya Maman biyu? Samihan tace tana
k'ara rik'e wayar "Alhamdulillah kawai tace suka gaisa tabawa Innar wayan jin Muryarta
k'asa-k'asa Innar tad'anji ba dad'i tace "Yayar Salim ko bakida lafiya ne? Kuka tasawa Innar
tagaya mata "wayan Ya Usman taketa kira bata shiga dan suntaho kanon, batasaniba kowani
abun yasamesu.
Hak'uri Innar tashiga bata ko matsalar network ne tabari zuwa jimawa tasake gwadawa
zata sameshi, seda taji alamum tasamu nutsuwa Innar taitamata Addu'a sukai sallama
kowannensu da irin sak'ar zucin dayake.

"Ad'aya 6angaren kuma a Asibiti duk wani abu dayakamata ai musu anyi Amma mutum biyune
suka farfad'o ansamo numfashinsu daka Driver sewani Dr Hashir suma ba a hayyacinsuba.
Suka cigaba da duba sauran. Ganin haka yasa suka kira Vc University aka sanarmusu.
Dolensu suka kira Guadians d'in duk wanda akai tafiyar dasu. Mahaifin Usman suna tsaka
dacin abinci dare wajen k'arfe Tara nadare sak'on yariskesu. Bak'aramin tashin hankali suka
samu kansu acikiba dajin labarin. Abincin da basu gama ciba kenan suka tafi General Hospital
sauk'in abunma agarine.
"Ward d'in da aka kaisu Usman suka nufa. Usman gashinan akwance kamar ai magana yatashi
yai wani fayau dashi. Kukan da Mama tasane Alh yarik'ota bashiri sukai waje alokacin
yasanarwa da 'yan gidansu Naja'atu. Adaren wasu sukazo har Inna k'annan Usman ba abin
suke se kuka manyan nata Lallashinsu. Anan kuma tunanin kowa yakoma kam Naja'atu baiwar
Allah idan taji yazatayi ga tsohon ciki. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda sukaji
Inna tahau fad'a.


© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*66-70*

""Nannauyan numfashi Abban su Usman ya sauke, wajen 12na dare suka bar Asibitin. Baban
su Naja'atu da Abbansu Usman sun tattauna sosai da Likitocin inda suka sanar musu da tashin
Usman se wani ikon Allah.
Washegarin ranar tun bayan asuba Abban suka koma Asibitin ko Maman bai yarda taje
alokacinba sha'anin mata saisu. Tin kafin Likitan yagamai masa bayani ganin Usma d'in a
lullu6e yatabbatar da zarginsa yazama gaskiya, wasu zafafan hawaye yaji suna bin fuskarsa,
"Allah sarki Usman Ubangiji yaimaka Rahmarsa yaro mai biyayya da girmama nasama dashi.
Allah yasa Mutuwa tazama Rigar hutu agareka." Addu'a sosai yai masa yashare hawayen
dasuka zubomai. Duk wani ciki-cike yayi dan abashi gawar Usman d'in gida. Tun a Asibitin yaja
gefe yana buga waya duk wanda yakamata yasani.
Kiran V.C in Jami'ar da suka aiko su Usman d'in Worlkshop wanda akan hanyarsu suka

sami Accident. Tun awayar yafara masa Ta'aziya dan tun cikin daren sak'on mutuwar wasu
daga cikin D'alibansu kuma Likitoci ya riskesu. Anan Abban yanemesu su sako Matar Usman
ajirgi akata Kanon sabida cikin dake jikinta, zatai kumburi intai zaman mota tunda tafiyace ba
kad'an ba. Yace "bakomai za ai hakan dayardar Allah" suka aje wayan. Kafin 8 nasafe sunda
gida Mutane har sun fara zuwa dole aka maida Jana'izar 11 nasafe. Musamman sabida Naja'atu
itama tai masa addu'a dafatan samun dacewa da tafiyar. Mama kuwa saida Abban yad'aureta
da jijiyoyin jikinta kada tai kururuwa. Duk da haka suma tai da aka shigo da gawar Usman d'in.

"Naja'atu kuwa V.C in suna gama waya da Abban Usman tingari baigama haskeba suka nufi
Staff Quaters in, tareda matarsa Yarabawane amma Musulmai ne, matar tabashi shawaran su
nemi taimakon Naibours insu. Baban Benua shiya bud'e k'ofan ganin V.C dakansa yasashi
rusunawa suka gaisa cikin yaren Yoroba bayani sukad'an masa yataso Maman Benua si musu
taimako seda tafito yadda bazasi musu kwarwa ba V.C yasanar musu Dr Usman Mak'ocinsu
dawasu likitoci da aka turasu Workshop sun sami Accident, har wasu sun rasa rayukansu. V.C
yace "Gidan Usman d'in zasu rakasu" Maman Benua kuwa k'ara tasa tareda d'ora hannu akai
tafara "Oh my Goodnees woo!" Dak'yar matar V.C tabata baki tai shiru. "Matar za a tura injishi,
ance ciki gareta suje ahad'a mata kayanta duka za aturata kanon a Jirgi.
Naja'atu tana daka kwance tunda tai sallah takasa rintsawa tunane-tunane kawai take da
sak'ar zuci, wayarta kuwa har tamutu sabida neman wayan Usman batareda tasameshi ba.
Jin bugu yasata tashi dak'yar seda tatsaya taja numfashi had'e da zumbula Hijabi kan faffad'ar
rigar baccinta har k'asa, tanufi k'ofar.

"Bak'armin tausayamata sukaiba ganin idanunta duk sun zuge, tunaninsu tasan abinda yafaru
"Am so sory" shine abinda sukee cemata, itadai basu guri tai suka shige ganin harda
Mak'otanfa. V.C yai mata bayanin abinda yakasu batai musu musuba, suka shiga tattara mata
kayayyakinta. Maman Benua da Lokaci-lokaci take share hawaye a wayance karta k'ara birkita
Naja'atun, suka tattaramata duk kayansu itada matar V.C. dukda haka seda Maman Benua
tahad'a mata kakkauran shayi wanda dak'yar Naja'atun ta iya sha. Sukai musu sallama.

"Dawani captain Oba V.C yahad"ata dan basu samu jirgin dazaije Kano awannan safiyarba se
Abuja inda acan sukesa ran samun mezuwa Kano kafindai Ranar ta bud'e. Akasai mata ticket
Kayanta duk aka shi cikin jirgin. K'arfe takwas nasafe sukai Abuja.
A canma bayan 'yar hada-hadar dasukai Allah yataimaka dakwai jirgi mai zuwa Kano
daga abuja ticket aka kuma siya mata kafin 11nasafen sun isa Kano. Babansu dakansa yazo
d'aukarta shida yayunta biyu da Samiha. Dalabinta take k'ok'arin tsugunawa tagaidasu Baban
yai saurin dakatar da ita. Idanun Samiha taga sunyi ja sosai, bade wanda yace mata komai
sukasa duk akwatunanta amotar suka tafi Baban nasu yana k'ara tausaya mata. Ganin k'atotan
cikin dake jikinta duk abinda keciki yazama *Maraya* yanzu kuma taje tatarar da Mummunan
labari. Da dabara yashare hawayen daya zubo mai batareda wani yaganiba.

Naja'atu kuwa ganin sunyi hanyar sharad'an tunaninta ko gida zaikaita, zuciyarta tai wani bugu
ganin ciccirindon mutane tun daka farkon layin, har suka zo gidan Mama. Jitai duk wani k'wari
datake dashi ya salu6e motsi ma dak'yar takeyi kanta tahau tambayar meke faruwa anan?

Dukda haka takuma kumburi akan nada
Kasa fitowa tai daka motar dole Samiha da Baban suka fito da ita takunma dak'yar take, tunanin
Mijinta yahauyi da Usman ne seya had'ata da jikinsa, ya tallafota yanayi yana mata sannu
cikeda kulawa suje duk inda zasu. Toko ina yake daba'azo d'aukarta dashiba? Cikin gidan suka
nufa, nanma ganitai mutane dayawa dangin su Usman Mata da Maza yawanci duk sun zubo
mata idanu. Ahankali tafurta Mamace tarasu? Jikintane yahau rawa. Baban su kuwa tak'ofar
gaba suka shigar da ita falon Abbansu Usman da mutane da dama a falon wasu daga ciki sunci
kuka Yusra yayar Usman tana ganinta takuma sa kuka. Jitai wasu nafad'in "Mutuwa mai yankan
k'auna kinga matarsa da tsohon ciki, jitai cikinnata yawani hautsuna har tana naman
durk'ushewa.

"Agaban gawar Usman d'in aka ajeta. Kwance yake amik'e anmasa sutura nannad'e da Likafani
ankuma yafa zani akai. Idanuwanta takai kan mutanen falon kowa taga yananan har Innarsu
cikin jimami da taraddadi y
Suke, to bataga Mijinnataba. Hannu takai tana shafar jikin zanin da aka lullu6e gawar Usman
dashi
"Kiyi Hak'uri Naja'atu *Kullu nafsin za'iqatul maut/ kowane rai seya d'and'ana zafin
mutuwa*.kowana lokaci takan iya riskarmu to Allah daya fimu sanshi yakar6i abunsa.
"USMAN NE NE KO BABA? Abinda ta iya fad'i kenan dayawa agurin sunji tausayinta. Dan
bakasafai zakaji ta ambaci *Usman* d'inba. Gaba d'aya iyayen suka matso kusa da ita suna
banbaki da nasiha "tayi hak'uri da tawalkali wataran kowa in lokacinsa yayi seya amsa kiran
Ubangijinsa. Karki tumami dan *Annabi S.A.W yace "Basa tare damu, #Masu marin fuskokinsu, #Da masu yaga Aljihunansu,
#Da masu D'aga murya suna kira irin Na Jahiliyya. Ayayinda akai Mutuwa. @bukhari da muslim
ne suka rawaito.*

"Kiyi masa addu'a zaitafi gidansa nagaskiya muma wataren mune haka" Inji Maman Usman
tana dafo bayan Najar.
"Allah yai masa rahama yakyautata namu zuwan" abinda ta iya furtawa kenan. Dukkansu
sunaji suna gani musamman Naja'atu da jinta take kamar kara cikimma tanemeshi tarasa haka
aka fita da Usman d'in akai mai Sallah suk tafi kaishi zuwa kushewa.


Semuce Allah yajik'an Muslim Umma. Ameen.!!

@Team naja'atu kuzo mujewa Naja ta'aziyya gsky
#sharar hawaye!!!



© *Didi_sady*🍼🍉�
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*

*Haleema G Khaleel*

*71-75*

""Tunda aka fita dashi ta d'ora idanuwanta kan k'ofar, gani take kamar a mafarki. Lallai Rayuwa
batada tabbas, yanzu kake Mutum yanzu zaka iya zama Gawa. Shiyasa ake so kazamto mai
aikata Alkairi arayuwa kazauna da mutane lafiya yadda kobayan ranka Kyakykyawar Shaida
zata rik'a binka. *Hak'ik'a duk Mutumin daya manta Allah to tabbas yana tareda Shaid'an*. Allah
Yai mana muwafak'a. Ameen.
Haka tazama kamar Mutum Mutumi, tana kafe aguri d'aya kamar gunki. Motsi ma
kasawa tayi bare Kukan dataga dayawan mutan gurin nayi, wani irin d'imuwa tasamu kanta
aciki, bugun da zuciyarta tayi hasseda taji Motsin abunda ke cikinta, kuka takeso tayi kota
samu raguwar Nauyin da K'irjinta.
Cikin kwanakin Naja'atu tazama komai sede aimata ko magana bayinta tacikaba. Abinci se anyi
kamar anayi zataci shima kad'an. Tabi tarafke tayi wani bak'i se k'atotan ciki dake jikinta.
Damuwace sosai tattare da ita. Agidan su Usman d'in take kwana.
D'akin Maman suke kwana itada k'anwar Maman Yaya Yusra da 'ya'yanta se autar
Maman. Bacci ma sede 6arawo ya d'auketa duk tabi tad'ashe tazama wata iri da ita.

Daren ranar da Usman yai kwana uku darasuwa, Naja tana kwance dare yatsala tunanin
rayuwar ta take harta gangaro kan zamantakewarsu da Usman cikin Aminci, Yarda, K'auna,
Kulawa da Soyayyar junansu. Lokaci d'aya Allah yad'aukeshi daga cikinsu badan baya
sanshiba, tatuno yadda yake san cikin jikinta tunkafin tahaifo shi irin burin daya d'ora akan abin
dayake cikinnata. Kuka tasaka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tin tanayi a 6oye har
shashshek'arta tafito fili, Yaya Yusra dabata jima da komawa bacci ba, taji alamun kukanta
tashitai tareda kunna fitilar wayarta tahaska kan gadon , jijjigar dataga jikin Naja'atun nayine
yatabbatar mata da ita keyin kukan, gadon tanufa itama kamar jira take tasa nata kukan har
Mama tashigo d'akin ganin suna kuka zuciyarta tak'ara tsinkewa, bata hanasu kukanba
musamman Naja'atu dasukeso tayi kota samu ragin damuwar datake ciki.
Batasan sanda itama hawaye yakecemata ba har wani nabin wani. Maman tai dauriya tai
shiru Yaya Yusran ma, ita kuwa Naja'atu seda tai mai isarta Mama tatasheta tareda jingina ta
ajikin pillow Ruwa tabata tasha sannan suka hau lallashi da nasiha tareda bata Misalai iri-iri na
Rayuwa itadai jinsu kawai take.
Cikin kwana bakwai darasuwar, sunsha bak'i daga 6angare daban-daban dayawa kuma sun
mata ta'aziyya. Har 'yan gidansu dukda irin zaman doya da manjan dasuke. Zuwa lokacin ta
kuma rama ba kad'an ba. Zagayayyar fuskarta tayi fayau da ita. Danna Inna kullum saitayi mata
tofi cikin zam-zam tanasha, Addu'oi dadama take mata banda wanda tabata takeyi. Taga kuwa
fa'idar hakan dan damuwar datake ciki taragu sosai. Tafauwalawa Ubangiji duk lamuran
rayuwarta shiyasan miyake nufi dayai mata haka.

Bata kuma rikicewa ba seda aka kawo kayan Usman ranar dayacika kwana takwas darasuwa,

taga abubuwansa dayawa komai yananan shid'in ne babu yatafi inda ba'a dawowa. Aranarma
tasha kuka wanda har zazza6i yasaukar mata.
Kwananta goma gidansu Usman d'in. Alh Abdul-Mu'iz mahaifin su Naja'atu dakansa
yanemi takoma gida dukda anriga anzama d'aya nanma gidane. Ganin irin damuwar dake
tattare da ita, bayan hakama komai sai anmata. Hakan yasa sukace "zasu tafi da ita gida.
Mama kuwa sotai abarta agurinsu har ta haihu. Kayanta duka aka kaimata gida tasha kuka
harsu 'yan gidanma haka tatafi tana ganin kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login