Showing 1 words to 3000 words out of 14523 words
Chapter 1 - Matar Habibi Book Complete By Lubna Sufyan -1.pdf
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
1
(Free page)
Daya tashi zaune, saurarawa yayi, wai ko kunnuwanshi ne suke son yaudararshi, da gaske
sallame sallah ne yakeji
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ya furta yana janyo wayarshi, ya duba lokaci, karfe biyar da minti goma sha biyu, cikinshi yayi
karar daya tabbata ta yunwa ce tunda daren jiya ba wani abincin kirki yaci ba, sai kuma cikin
nashi ya sakeyin wani sauti, wannan karin na tashin hankali ne, ya kuwa diro daga kan gado
cikin hanzari yana bude kofar dakin shi ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin Jamila, ko
tunanin ya zurfafa ba zai iya tuno ranar da Jamila ta makara ba, in ba don ita ba ai da ya
tabbata makota sun sakashi a jerin mazan da ba'a gani a masallaci sallar asuba
"Jamilaa..."
Ya kira bayan ya tura kofar dakin nata, a kwance ya ganta kan darduma, jikinta sanye da hijabi
ruwan toka, ta dunkule jikinta waje daya, alamar da tayi sallah bacci ya dauketa a wajen,
karasawa yayi yana dan bubbugata hadi da sake kiran sunanta
"Jamilaa"
Motsawa tayi da sunan Allaah a bakinta, tayi hamma tana kokarin mikewa
"Lafiyarki kuwa yau?"
Karasa mikewa zaune tayi
"Sallah nayi fa, ina lazumi ashe bacci ya kwasheni ban sani ba"
Dan karamin tsaki Baffa yaja jin tana lafiya
"To kuwa yau babu kanta, dan wallahi mun makara"
Dauke da tashin hankalin da Jamila ta aro ta shimfida kan fuskarta tace
"Subhanallahi, makara kuma?"
Tana mika hannu ta dauko wayarta da take kan gado
"Wallahi kuwa..."
Bayan ta duba ta kalle shi tana fadin
"Kayya, baccin daya daukeni ne, kasan kuma ba alarm nake sakawa ba tunda na rigada na
saba tashi"
Kai Baffa ya dan dafe ya sauke hannun shi
"Allaah Ya kyauta, amman akwai damuwa, saboda ba wani abin kirki naci ba jiya, ga aikin da
yake gabana a shago yau, ni anya ma na tabayin dorere a rayuwata?"
Sai taji zuciyarta tayi mata wani iri, tausayin shi yana neman danneta, sai kwakwalwarta ta
dawo mata da maganar shi
"Nifa ba karamin taimako na kikeyi ba tunda kike tashina, badan ke ba ai in ta matar nan ne sai
dai inyi dorere..."
Gabaki daya dan tausayin sai taji ya murmushe
"Ai shikenan haka Allaah Ya nufa, sai ka samu kaje kayi sallah, lokaci na tafiya, bari in shiga
bayi..."
Ta karasa maganar tana mikewa, tana jin yanda yake binta da kallo, sai bayan ta shiga bayin
kuma tukunna taji karar budewa da rufewar kofar dakin nata, alamar ya fita. Ta danyi mintina
biyu kafin ta fito, saita cire hijabinta ta koma kusa da Nana da take ta bacci, har yanzun kirjinta
yayi mata nauyi. Tun da ta auri Baffa, bai taba gajiyawa wajen nuna sha'awarshi ta auren mace
fiye da guda daya ba, shisa ma ta sakawa ranta salama, duk kuwa da yanda take da zafin kishi.
Wani lokacin bayan tayi masa addu'ar karin yalwar arziki sai taji kamar ta koma tace Allaah
karya bashi da yawa, iya wanda zai ishesu hidimarsu batare da sun takura ba, amman banda
na karin aure.
Wata rana sai taba kanta dariya, lokacin daya fara gini, haka ya daukota akan mashin dinshi
yazo ya nuna mata, ta dinga kallon yanayin tsarin gidan cike da sha'awa, musamman da yake
fada mata za'a dora bene, saboda yanason yayi part biyu
"Aikuwa saman nake so"
Ba zata manta ba yayi dariya yace mata
"Idan kuma amarya zansa fa?"
Taji dirar maganar har tsakiyar kanta, amman saita dake ta amsa shi da
"Sai ta zauna a kasan, ni kuma ina sama, ai dai naci arzikin kasancewa uwargida da akasha
gwagwarmaya da ita a bani zabin inda nake so ko?"
Dariyar dai Baffa ya karayi batare da yace mata komai ba. Kuma lokacin daya kammala ginin
kasan, aka fitar da kafar benen akayi dakin da komai, sai suka tashi suka dawo, watanni takwas
kenan, yace mata a nutse yake so saman ma suna ciki ana ginawa, da duk karsashin
dawowarsu sabon gida, harma da kujerun da ya sake mata duk ya rage saboda tana tunanin
kowanne lokaci zai iya rakito aure, amman da taga ko bulo ba'a shigo dashi ba saita fara sakin
jiki. Amman gab da azumi ta fara kula da canzawarshi, shi mutum ne da inya shigo gida to
yakan ajiye wayarshi ne ya zauna ya biyewa yara suyita shiririta.
Kuma itama din akan zauna da ita a taba hirar, amman lokaci daya inya dawo, to yana manne
da waya yana dannawa, sai kayi masa magana nawa baiji ba, hankalinshi yana kan wayar, da
bata damu ba, saida ya fara tashi yana barin dakin in tana nan aka kirashi, tasan yanayin aikin
shi, yana mu'amala da mutane kala-kala, kuma ciki harda mata, sau nawa suke kiranshi a
waya, wata rana ma ba amsawa kawai yakeyi a gabanta ba, a lasifika yake sakawa yayi
maganarshi a nutse. Saita kara ganin wayar bawai da daddare bane kawai, har da asuba. Baffa
da ana idar da sallah zai shigo gida danya koma bacci, amman sai gari ya fara haske ma wani
zubin kafin ya shigo, ko inya shigo din ya wuce dakin shi ya turo harya murza mukulli.
Shi yasa Jamila sanin cewa wata tayi mata kutse cikin rayuwar miji, da ta ganshi rike da wayar
sai taji zuciyarta nayi mata zafi, babu abinda yake dawo mata sai lokacin da yake neman
aurenta, kalamanshi, yanda yake riritata kamar kwai, saita hasaso irin wannan riritar wata take
samu, wani abu daya jima da mutuwa a tsakaninta dashi, amman taji dadi saboda a lokacin
azumi na karatowa, tasawa ranta zata tsaya ta kara kyautata duk ibadunta a cikin watan, sai
tayi addu'a sosai. Kuma hakan ne ya faru, har a sujjadarta rokon Allaah takeyi daya saka mata
salama idan har Baffa nada rabon zama da wata matar bayan ita. Sai gashi ta fara samun sauki
"Allaah Kasa kar mijina ya juyamun baya, Allaah Kasa kar in taba wulakanta a idanuwanshi,
Allaah Kasa kar mutuncina ya zube a idanuwanshi, Allaah Kasa kar matar da zai auro ta cutar
dani koni in cutar da ita, Allaah Ka rabani da kishin da zai zame mun fitina koya hanani zaman
lafiya"
Haka take jerowa tana sake maimaitawa duk sallah, duk wani motsi ma da zatayi, tasan Baffa,
ko tace ta dauka ta gama sanin shi, shekaru bakwai ko tace takwas in za'a hada da lokacin da
yake nemanta, ko kadan bata taba hasaso zai kasance cikin irin mazan nan masu kushe
matansu a wajen 'yan matan da suke nema ba, tana can gurfane kullum tana addu'ar karta
wulakanta a idanuwanshi, batayi tunanin hadawa da addu'ar kar ta wulakanta ta sanadinshi ba
sam, tunda akwai wani wulakanci daya wuce ace mijin daya kamata ya kare maka mutuncinka
shine yake zubar maka dashi? Abin yayi mata zafi matuka, kuma inda ma ya tsaya iya abinda
tayi din da zaifi mata, sai gashi kirikiri ya yanko karya a cikin wata mai girma irin Ramadan
"Hmm..."
Ta furta a fili ko yanzun dinma, farkon aurensu ta dauka shine zai dinga tashinsu sallah, da yake
ta saba gidansu har kananun yara ma sai an tashe su da asuba, mazan haka Baba zai tattarasu
su wuce masallaci, to da lokaci yayi take bude ido, ko da bata sallah kuwa saita farka, tun
tanayin luf da ita tana jiranshi harta gane in dai ta biyewa Baffa to zata daina yin sallar asuba a
cikin lokacinta, saita tashe shi shima. Amman wai yau dadin soyayya yasa shi rufe ido yana
zabgawa budurwa karyar cewa wai indan itace da sai dai ya dingayin dorere, budurwar da sai
bayan ta tashe shi, yana zaune ma yana sahur zataji vibration din wayar alamar ta kirashi, ko
taji ringing din wayar idan ya manta bai sata a silent ba.
Shisa ta daukarwa kanta alkawari har azumin ya kare ta daina tashin shi, zata barshi da
budurwar tashi, duk da ba karamin danne zuciyarta tayi ba kafin ta iya kin tayar dashi din, tunda
ita ba sahur takeyi ba, sai dai tasha ruwa, da daddare take cika cikinta. Shikuma Baffa in an kira
sallah ya sha ruwa ya tafi masallaci, koya dawo sai dai ya dan sha kayan ruwa, baya iya sakin
jiki yaci abinci sai ya dawo daga tarawih. To jiyama daya dawo ta hada masa komai, sai waya ta
dauke masa hankali, lokaci zuwa lokaci zaiyi murmushi mai sauti, tun tana danne zuciyarta har
tace masa
"Abincinka yana hucewa fa, daka hakura ka gama ci saika danna wayar"
Cikin halin ko in kula yace mata
"Kwashe kawai, ba yunwa nakeji ba yau, naci anjima idan Allaah Ya kaimu"
Haka ta kwashe komai tanajin kamar ta fisge wayar ta kwala da kasa, balle da aka fara jera
masa kira ya kalleta yana fadin
"Akwai gajiya sosai a tare dani, ga kaina na dan yimun ciwo, inaso in samu bacci sosai yau"
Tasan a fakaice so yakeyi yace mata ba sai taje dakinshi ba, tunda yanaso ya sake yayi wayar
shi da budurwa, da wannan takaicin ta kwanta, shine ma abinda ya kara mata karfin gwiwar
komawa daki abinta bayan tayi brush tasha ruwa. Haka tayi nafilarta, tayi addu'o'inta, ta zauna
zuciyarta nata bugawa, tana kuma kasa kunne ko zata juyo motsin Baffa, amman shiru, har aka
kira sallah, saida tayi, tana zaune tana azkar din safe ta juyo takun tafiyarshi, tayi maza ta
kwanta ta jirashi, tana kuma aiwatar da diramar data shirya zatayi.
Tun tana tunane-tunane har bacci ya kwasheta, rigimar Nana ce ta tasheta wajen karfe takwas
da rabi, saita mike gabaki daya, tayi mata wanka, ta shiryata, tukunna ta hada mata shayi ta
zuba mata a kofinta ta bata, ta kama hannunta zuwa dakinsu Asaad, ta lekasu, bacci sukeyi
daga shi har Arif din. Idan akwai abinda take kara godewa Allaah akai shine yanda in dai babu
makaranta sukeyin baccin safe, tana yawanjin iyayen yara na korafin yanda suke tashi da
sanyin safiya idan babu makaranta, amman ita dai Allaah Ya duba mata. Ta gyara musu labulen
dakin, taja hannun Nana suka nufi kitchen, saida ta zaunar da ita akan kujera irin ta katakon
nan a cikin kitchen din tukunna ta hada wanke-wanke.
Ta gama tana goge wajen Baffa ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, fuskarshi fayau, yayi kyau
kamar ko da yaushe, zuwa yanzun kuma ta tabbata bawai a idanuwanta bane kawai Baffan
yake da kyau, tunda gashi nan ya haska a idanuwan wata ma
"Sannu da aiki"
Yace mata, ta amsa shi da
"Yawwa Babansu..."
Kamar yanda ta lakaba masa, shikuma ya kirata da
"Mamin yara"
In yanajin nishadi, gaisuwar safen da basuyi ba dazun ita tayi masa ya amsa a sanyaye yana
dorawa da
"Zan fita, saboda nasan aiki nacan ya cushe mana"
A jikin doguwar rigarta dinkin bubu ta kara goge hannuwanta da suke da danshi tana fitowa
daga kitchen din
"Allaah Ya tsare Ya bada sa'a"
Ta fadi tana rakashi har wajen mashin dinshi, ita ta bude masa gate tunda ba maigadi ne dasu
ba, saida ya fita ta mayar da gate din ta rufe, ta koma ciki.
*
Karfe shida da kwata tagama komai tunda ba wani abu mai wahala tayi ba, doya fa kwai ta
soya, tayi zobo, tana da sauran dafaffen nama, tayi miyar ganye, dan wannan tun safe ma tayi
ta, saita tuka tuwon shinkafa dai-dai cikinsu, kuma ita da wuri take fara aikinta koma meye zata
dafa kuwa, bataso ana shan ruwa tana kitchen sai dai bacin rana, sai su Asaad da Nana da
suke binta, Asaad nata yi mata surutunshi kan abinda batajin ta fahimta gabaki daya, wani
tsohon labarine akan yanda littafinshi ya bace a Islamiyya
Tana kwasar komai zuwa falo, Arif yana nan zaune akan kafet yana kallon MBC3, Baffa kuma
yana kan doguwar kujera a kwance kamar gawa, ko mintina goma baiyi da shigowa ba, sannu
da zuwan da tayi masa ma da kai ya amsa, daga shi har mashin din kamar zasu tuntsire,
idanuwan nan sun shige ciki, yayi zuru-zuru, ko dasu Nana suka dinga masa oyoyo ma dan
rikesu yayi kadan batare da yace komai ba
"Kuzo nan Babanku yau ya gaji, karku dame shi"
Sai suka kyale shi din kuwa
"Ka tashi an kusa kiran sallah"
Tace tana kokarin danne dariyar da take neman kwace mata
"Barni a kwancen nan, ki dai cikamun jug da koma menene kikayi mana na sha dan Allaah, ki
matsomun dashi kusa, ki kuma zubamun abinci, yau inaga a gida zanyi Magriba"
Saida dariya ta kwace mata, tun asali daman Baffa bashi da jumurin yunwa, dan azumi daga
Ramadan, sitta shawwal sai kuma na arfa yakeyi, bayansu baya karayin wani azumi
"Karka bada maza mana"
Cewar Jamila tana karayin dariya
"Ke ba zaki gane ba..."
Dakinta ta shige bayan tasa su Asaad da Nana sun zauna kusa da Arif, ta dauro alwala tukunna
ta fito, bata biyewa Baffa ba, ta samu kofi madaidaici, ta zuba masa zobo, sannan ta hada masa
doyar ma a plate. Ya kuwa tashi zaune yana karbar kofin
"Wai har yanzun ba'a kira ba?"
Kafin ta amsa sukaji kiran sallar kuwa, nan da nan ya kwankwade zobon hannun shi, jikinshi har
rawa yake lokacin daya sauke kofin ya dirarwa doyar
"Baba kaci a hankali, babu kyau cin abinci da sauri ko Mami?"
Asaad ya fadi
"Bari ka fara azumi tukunna Asaad"
Dariyar dai suka sake bawa Jamila, ta tashi ta tafi dan ta gabatar da sallar magriba yanda zatayi
buda bakin cikin natsuwa. Sanda ta dawo a kwance ta samu Baffa
"Kwanciya ka sakeyi?"
A hankali yace mata
"Cikina ke juyamun"
Wani abu na rashin jin dadi ya tsarga mata, cike da tausayawa take ta jera masa sannu, doyar
ma data dorawa buri saita kasa ci da yawa, ta dai zubawa yaran, zobo daman kowa na da robar
shi da take zuba musu saboda a kofi za'a iya zubarwa a sakata aiki. Itafa ba haka taso ba,
kawai dai taso ya dan sha wahala ne kadan, azumin ya gasa shi, bawai yayi ciwo ba. Sai gashi
sallar Magriba a gida yayita, ya samu ya lallaba Isha'i saboda Tarawih. Daya dawo yasa ta zuba
masa tuwo, saita tashi dansu Asaad da wuri suke kwanciya, kuma saita tsaya tana biya musu
addu'ar bacci suna maimaitawa duk da sun haddace, ta karayi musu wata tukunna, ta goya
Nana, dan itace take hirar dare wani lokacin
Sanda ta koma falon Baffa ta samu rike da wayarshi, da alama ranshi a bace yake, tana zama
yana mikewa ya nufi dakinshi, tana juyo yanda ya turo kofar garam kamar itace ta bata masa rai
"Allaah Ya kyauta..."
Jamila ta fadi, ta sauko Nana, ta janyo kulolin gabanta, a cikin kwanon da yaci tuwon ta zuba
itama, tana ci tana bawa Nana itama, suka gama ta sake goya Nana dan tanaso ta kimtsa
wajen kafin su kwanta. Kuma hasashenta ya zama gaskiya, ran Baffa a bace yake. Gabaki daya
yau tunda ya fita shago komai ya rincabe masa, ya samu yaran shagon nashi sunata aiki,
danma sun rufe karbar dinkin sallah tun saura sati biyu azumi, kuma shi yayiwa kanshi alkawari
tuntuni, duk runtsi ba zai dinga kwana a shago yana dinki ba. Suna cikin aikin aka dauke wuta,
tun jiya Gen dinsu yaketa wata qara, yau ma sai yaki tashi, daya kira Sani dan yazo ya duba
musu sai yace masa sunje wata gaisuwa baya ma cikin garin Kano, sai yammaci, zaizo ya duba
bayan shan ruwa, dan haka dole yayi abinda bayaso, aiki da keken dinki wanda bana wuta ba.
Zuwa la'asar duk ya zazzage dan abinda yayi saura a cikinshi, ga ciwon cinyoyi da yakeji duk
sun rike, kwata-kwata baima samu natsuwar danna waya ba, yama manta a silent ya sakata har
sai bayan ya dawo daha Tarawih din nan, sai abin ya fado masa, ya riga yasan dole zai sha
mita wajen Aziza. Yana duba wayar kuwa ya samu ta kirashi babu adadi, ga sakonni ta text da
WhatsApp ta bar masa har yana rasa ta inda zai fara karantasu, sai kawai ya fara da tura mata
da gajeran sako
"Ayimun hakuri Babe, yau abubuwane suka rincabemun a shago, wayar kuma tana silent. Nayi
missing dinki da yawa"
Saida ya tura ya fara bin nata sakonnin, sai kuma zuciyarshi ta buga daya tuna yau yayi mata
alkawarin zuwa yayi buda baki a wajenta, tun kwanaki biyar da suka wuce sukayi wannan
tsarin, ya tabbata ta shirya masa shagali, lokaci daya yaji ranshi ya baci, musamman ma da ta
dawo masa da sakon daya tura da
"Ka kusa? Inata jiranka tun dazun. Gashi har tara saura"
Yana shirin kiranta ne Jamila ta shigo, shisa ya tashi ya shiga dakinshi yana addu'ar Allaah
Yasa karta biyo bayanshi, yasan halinta da naci wani zubin
"Dan Allaah kiyi mun hakuri Aziza, dan Allaah..."
Yake fadi cikin magiya da kwantar da kai saboda yanda Aziza ta birkice masa, kamar ma kuka
takeyi
"Ni ba sai kaci anan ba, kazo ka dauka kawai dan bansan yanda zanyi da abubuwan nan dana
shirya maka ba"
Muryarshi ya karayin kasa da ita
"Na fada miki da zazzabi na dawo, yanzun