Showing 12001 words to 14523 words out of 14523 words

Chapter 5 - Matar Habibi Book Complete By Lubna Sufyan -1.pdf

28 Jun 2025

5611

suke tareta bata ma bata lokacinta akansu, tunda ta
tabbata ba aurenta zasuyi ba. Baffa shine namiji na farko da yazo wajenta taji ya kwanta mata
har cikin ranta, duk kuwa da taso ace yafi haka kudi, saboda Mummy da ta tabbata Baffan ba
zaiyi mata ba, ya aka kare ma lokacin auren Jalila da Balarabe. Shisa Mummy ta tattara burinta
da fatanta kacokan akanta.

Aziza itace 'ya ta hudu a wajen Marigayi Malam Ayuba da matarshi Rahanatu. Shi din
Bafullatani ne dan asalin garin Adamawa. Neman kudi ya shigo da iyayensu garin Kano, da
kuma rabon suma din arzikinsu yana nan Kanon. Rahanatu kuma 'yar Dawakin tofa ce ta asalin
garin Kano. Haka iyayenta duka 'yan Kano ne. Ta taso cikin gidan yawa, mata hudu, su kuwa
yaran gidan sun bawa talatin baya. Haihuwa ake a gidansu da ta zama gasa, duk da mahaifinsu
ba mai karfi bane ba. Dan 'yana aiki ne a gidan sarki, da yana cikin masu gadi, da yake mutum
ne shi mai shisshigi da tusa kai, haka ya dinga shiga da fice har saida aka maidashi bangaren
kula da dawakai. Sannan wannan shisshigin nashi yasa yake samun alkhairi babu laifi tunda
gwani ne kwarai wajen koda duk wani ahali na gidan Sarkin.

Kusan a cikin yaran gidan, Rahanatu itace tafi kowa haske da manyan idanuwa, hakan yasa
mutane suke cewa tafi kowa kyau, da yake za'a iya cewa ta biyo halin mahaifinta, saita kara da
iyayi da kuma son ace wata ce, da ta kafa rigima da naci saida aka sakata a makarantar bokon
da har mazan gidan ba damuwa sukayi da ita ba. Ta kuwa rungumi fadin rai ta dorawa kanta,
duk inda zata zauna saita san yanda tayi ta fadi cewa ita jinin sarauta ce. Yaran unguwa da aka
taso tare kullum cikin gulmar wannan karya ta Rahane suke tunda mafadaciya ce ta gaske ba'a
isa ayi a gabanta ba. Ko Rahanen ma ta hana a kirata dashi sai Rahanatu.

Tana aji uku a sakandire ta hadu da Ayuba, dan gaye dai-dai da zamanin shi. Yana da shagon
saida kayan masarufi. Gashi Bafullatanin usul, fari sol dashi. Cikin kankanin lokaci akayi
bikinsu, yana kuma yi mata hidima har ya zarta karfinshi wani lokacin saboda yanda take da
son harkar karya. Dai-dai gwargwado tsaye yake kansu. Data nemi komawa makaranta bai
tauyeta ba, dakyar dai ta hada takardun sakandire, dole ta hakura, sabodq hidimar gida data
yara. Tana da cikinta na biyar ya rasu, bayan gajeriyar jinya. Wannan rasuwa ta kidima
Rahanatu, gashi daga shagon nan sai gidan daya bar musu. Yara kanana, tunda a lokacin
Khalifa ne kawai yake da shekaru goma, Anwar takwas, Jalila shida, sai Aziza uku, dan ta samu
tazarar shekaru 3 ne a wannan karin. Bayan ta haihu ta samu namiji sai aka mayar masa da
suna Ayuba suna kiranshi da Nur.

Sai ga takardun sunyi mata rana, shige-shigen mahaifinta da mutanen daya sani, sai gashi an
samar mata aikin rubuta kati a Asibitin Aminu Kano. Kuma bata zauna haka da aikin ba, duk
wata sana'a da zata kawo mata karin kudi bata sanya da ita. So take yaranta su haska sufi na

kowa a unguwar tasu, su samu ilimi tunda ita dai taga ranarshi. Rayuwar karyar dai data
dorawa kanta, Malam Ayuba kan nuna mata rashin jin dadin shi akan irin rayuwar lokacin da
yake da rai, tunda yanayi mata komai, bayason yanda dai idonta yake kan wasu a cikin
kawayenta, tana so ta taddosu ko ta zartasu. Yanzun da kasa ta rufe masa ido, ga aikin data
samu, sai abinda yayi gaba.

Cikin yaran nata biyar kuwa, Khalifa ne ya fita zakka. Ya samu karatu zuwa NCE, yana aikin
koyarwa, yanzun haka yana da mata da yaro daya. Ko kadan Khalifa bayason irin rayuwar da
Mummy kamar yanda suke kiranta takeyi, ta kuma dora kannenshi akai. Ga Anwar nan, yana
BUK a yanzun haka, saboda shi yace daman ba zai iya FCE ba, kusan yafi kowa jin kai a
cikinsu, saboda shine sak ya biyo mahaifinsu, yana daga cikin matasan da suka rungumi mining
din Pi lokacin da yazo, dan gani kasheni ne akan Pi, dan zaku iya raba jaha dashi idan kayi
kokarin rage masa burinshi akan Pi. Haka yayi sa'a yana cikin wanda aka budewa yin kyc da
wuri, saboda haka lokacin da aka fara bumburutun Pi saiya zamana ya samu kudin da bai taba
rike irinsu ba.

Khalifa ya bashi shawara ya samu sana'ar da zai dingayi, suka zauna sukayi magana sosai,
kuma Anwar ya nuna masa ya dauki shawarar, yana komawa gida, suka zauna da Mummy ya
fada mata kudurinshi na da yayi niyyar yayi musu gyara ne a gidan, sai ta rushe duk wani tsari
da Khalifa ya dorashi akai, sai gani yayi an dauko gyaran gida, gini ne na zamanin da, na kasa,
sai akayi masa shafen suminti, dan haka katanga akaja bayan an ware daki daya akayi masa
gyara na gaske, sai katangar ta raba wannan dakin da sauran gidan ba'a gyara ba, ya siyo
wannan katon gate din aka kakaba a gidan.

Sauran Pi din yace ba zai siyar ba zai jira a shiga kasuwa dashi ne, dan abinda yayi saura ya
fara saro gilasai, hulunan hana sallah da zobunan azurfa, daman yana dan taba siyar da
takalma, yana samun rufin asiri dai-dai gwargwado dan kuwa Anwar ya iya kasuwanci, karya ce
kawai takeyi masa cikas, tunda kudin maimakon yayi abinda ya kamata dasu sai a siyi turaruka
ko takalma designers. A wajen Anwar dama Jalila a yanzun, da aji kunya gara an kwana da
yunwa. Kawai wani hali da suke dashi su dukansu, suna son farin cikin Mummy, duk wani fata
nasu na yanda zasu gatanta ne, ko Jalila tayi niyyar yin auren kudi yanda Mummy take so, sai
ga Balarabe da suka fara wata irin soyayya mai tsayawa a rai duk kuwa da tarin talaucin shi.
Haka Mummy naji tana gani ta hakura akayi auren.

Shikuwa Auta Nur yanda duk akayi dashi haka yake binsu. Jalila a yanzun haka ta gama
diploma dinta anan Kano Poly, amman ita data samu mijin daya kwanta mata sam ba zatayi
wani karatu ba. Aure take so, tunda ta tasa tasan ma'anarshi, ko yaushe cike take da mafarkin
auren nan. Balle data kara samun babbar waya, tana cikin group din matan sirri na Facebook,
tana bibiyar manyan bloggers a manhajar Instagram, sai ta karajin tanason auren, babu kuma
abinda yafi burgeta irin ace yau ta mallaki kitchen dinta na kanta, tana dafa ma mijinta
abubuwan burgewa itama ta dauki hotonsu ta shiga wannan trend din da ake yayi na 'ga abinda
nake ciyar da mijina'.

Shisa duk shiriritarta, tunda Mummy tayi musu tsaye a bangaren boko dama Islamiyya, itace dai
sai taga dama take zuwa Islamiyar lokacin, bata wasa da addu'a akan aurenta. Dan bata
dagowa daga sujjada bata roki Allaah daya bata miji nagari ba, kuma tana da yakinin rokonta
Allaah Ya amsa ya jeho mata Baffa. Duk da karsashinta ya rage lokacin da taji yana da aure
harda yara uku, amman shi da kanshi Baffan ne ya kara mata karfin gwiwa, a bakinshi takejin
shi da Jamila aure ne akayi musu na hadi, yanzun a tare da son da takeyi masa, akwai tausayi
mai yawan gaske da yake bata. Ace matashi dan kwalisa kamarshi, ga rufin asiri yana dashi
dai-dai gwargwado amman baiyi sa'ar mata ba.

A goman karshen nan batayi wasa ba wajen addu'a, harda Mummy take hadawa idan Baffa
shine mijin nata, to abin ya kwantawa Mummy a rai. Tasan duk yanda zasu so juna da Baffa, in
dai Mummy bata karbe shi da budaddiyar zuciya ba, ba zataji dadin zaman yanda ya kamata
ba. Ai tana gani akan Jalila, duk wani abu da Balarabe zaiyiwa Jalila sai ta kushe, ko ita kuwa
ya bada aka kawowa haka zata karba tana kushe abin da Balaraben ma gabaki daya. Wani
zubin ma da kuka Jalila take barin gidan saboda kwarzabar Mummy akan auren nata. Shisa ba
zata taba wasa da addu'a ba ita kam, tunda tasan babu wanda zai tausaya mata sama da
Ubangijinta, to kuwa gara ta gurfana a gabanShi ta kai kukanta.

Yanzun a cikin kawayenta su shida, Aisha da Hassana duk sunyi aure, saura su hudu, ita, Mimi,
Nabila da kuma Maryam. Sunfi dasawa da Mimi saboda yanayin rayuwarsu yazo daya, suna da
son asan dasu a waje, gayu, dama karya, duk da ita Mimi suna da kudi, amman kudin nasu bai
kai yanda ita take zuzutawa ba. Maryam yanzun haka ansa ranarta, Nabila ma anyi gaisuwa,
shiya karawa Aziza jin kamar ta janyo Baffa yazo ayi magana tasan cewa da gaske yakeyi, yau
ma sunyi zasu hadu a gidan Hassana,ita, Mimi da kuma Nabila, tunda duk Hassana dince
takeyi musu dinki. Ta kware sosai, haka kuwa akayi, suna cikin hira ne, Mimi take basu labarin
saurayin da tayi Nawaf

"Nifa bawai baiyi mun bane ba, yanda yake isata da hirar matarshi da yaranshi shine abinda
yasa duk ya fice a raina, to tunda yana son matar tashi uwarme ya kawo shi wajena?"

Hassana tayi dariya

"Ke dai Allaah Ya shiryeki, ai wannan alama ce mai kyau, ba wai hirar matar tashi ba da yakeyi
miki, yanda yake nuna miki iyalanshi ma da muhimmanci a wajenshi, kema sai kiyi fatan idan
abin ya tabbata Allaah Yasa kiyi muhimmancin nan"

Kai Nabila take girgizawa

"Koma menene, karka kawomun maganar matarka, babu ruwana da ita, kazo muyi hira kan
abinda ya shafemu, nifa shisa sam bana son ma in kwasowa kaina mijin wata, duk yanda zakiyi
dashi sai an samu damuwa, wannan makirar matar tashi saita kawowa soyayyar taku wani
cikas din"

Aziza da take jinsu ce tace

"Bafa kowacce ba, wata ma bata da wannan muhimmancin a wajenshi, kinga kaman Habibi na,
wallahi har tausayi yake bani, saboda dama can shi ba auren soyayya sukayi ba, wata dusa ce
aka hadashi da ita, hakuri kawai yakeyi, shisa nake ta shiri, dan na tabbata kwace shi a
hannunta ba wahala zaiyi mun ba"
Wannan karin Nabila ce tayi dariyar harda kyakyatawa

"Wallahi karya yakeyi miki..."

Take fadi har lokacin tana dariya

"Wato zama yayi yana shirya miki drama ke kuma kika hau? Auren hadin shekara mai zuwa ma
kina iya ganinta da lodin shagamu, in babu kenan, ya mika mata ta karbe da hannu biyu, yazo
yana shirgaki"

Wannan karin su duka sukayi dariya banda Aziza da maganar ta bata mata rai sosai

"Meye kuma shagamu? Kefa Nabila kina da matsala"

Mimi tace

"Ciki mana, ba haka suke zuwa suna samun su Aziza suna shirga musu karya ba, yanzun daya
shiga gida zakiga ba zai sake waya dake ba sai gobe idan ya fito, makirin"

Fuska sosai Aziza ta sake daurewa

"To ni ba waya ba, wallahi har video call munyi dashi jiya da daddare, yana gidan nashi kuma
balle wata waya"

Hassana tayi mata wani kallo

"Video call da daddare? Ita matar tashi tana ina?"

Dan murmushi tayi

"Nace miki fa wata dusa ce yake aure, tana can tana baccin asara mana"

Aziza ta bata amsa sunayin dariya tare da Nabila, amman banda Hassana da fuskarta ke kara
hadewa waje daya

"Amman kinsan daga ke harshi baku kyauta mata ba, saboda abune da idan akayi miki shi ke

ba zakiji dadi ba"

Mima ce ta karbe zancen

"Babu wani rashin jin dadi, aina dauka shirga mun kawa yakeyi, in har yana video call da ita a
gida to da gaske waccen batama san ciwon kanta ba balle har tayi muhimmancin a wajen miji,
idan irin wannan wawayen matan ne to fa kwace miji a hannunsu ba zaiyi wuya ba, ke dai kawai
ki shiga da shirinki"
Ganin kome zata fada ba zasu taba fahimtarta ba,sai tayi shiru, amman ita tayi samari masu
mata, bama guda daya ba. Ita asalima bataso ka kwaso mata maganar matarka, sannan in dai
ka shiga gida, tasan lokacin komawarka gida yayi, koya zaka kirata ba zata amsa maka ba, da
yake da anyi isha'i in ba wani abu zatayi ba, kwanciya takeyi tai bacci, ba'a wannan chatting din
daren da ita sam. Tana kokarin kiyaye kin yin duk wani abu da ba zataso ayi mata ba a
matsayinta na mace to kar tayiwa wata macen.

Sai ta cigaba da fere doyar da takeyi tunda daman suna tsakar gidane

"Duk dani dai in ba kaddara ba auren mijin watan nan bai kwanta mun ba"

Aziza ta kalli Mimi

"Nifa na kasa gane wannan maganar ta mijin wata, waishi namijin inace don mace hudu aka
halicce shi? Sai wata ta kwakume tace ita kadai zata rayu dashi, ni wallahi babu wani mijin
wata, mijinmu dai"

Nan fa musu ya kaure tsakanin Mima da Aziza da kowa yaki fahimtar dan uwanshi, ganin abin
na neman zama rigima Nabila ta katse su da fadin

"Kuna da fadin, yanzun fa akayi azahar, kuna nema ku karar da dan energy din naku akan
gardamar da banga amfaninta ba, kowa ba sai ya auri wanda yayi masa ba"

Kafin su amsa Hassana tace

"Ni iskancin kawo mun dinki a kurarren lokaci ma nake so ku duka ku bari, nayi muku magana
kunqi jiko, to zaku sha mamaki wannan karin"

Su duka sai suka koma lallashinta, dan sun san Hassana, tsaf zata iya kin dinkawa ko da kuwa
tana da lokaci, gashi sun kasa sake wani wajen dinkin, bayan kwarewar da tayi, suna samun
rangwame saboda kawancen da yake tsakaninsu. Duk da haka Aziza da Nabila saida suka
sake zantawa akan Baffa da suka tashi tafiya tunda hanyar su daya ce, acan ma suka bar Mima
da yake ita bata da nisa da gidan Hassana din, unguwa dayace, layi biyu ne ya rabasu

A lokacin da Nabila take karawa Aziza kwarin gwiwar shiga gidan Baffa, da kuma karin dabarun
da zatayi amfani dasu ta kamashi a hannu, wasu dabaru da take hadawa da fatan bawai ta
kama Baffa kawai ba, a'a ta jijjige Jamila daga gidan gabaki daya ta rayu ita dashi su kadai.
Shikuma yana can shago ulcer din da bashi da ita na neman duk wata hanya da zasu kulla
zumunta...

********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login