Showing 9001 words to 12000 words out of 14523 words
Chapter 4 - Matar Habibi Book Complete By Lubna Sufyan -1.pdf
10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da
kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
4
(Free page)
Adai-daita na ajiyeta, ta dauki katon kwandon data hada komai a ciki, don da taga almajiri ma
shi zata ba ya dauka ya tsallakar mata dashi saita bashi ko Naira dari ne sadaka. Kwandon yayi
mata nauyi, haka ta kinkima saboda wani mai mota daya gansu a tsaye, mata su wajen biyar
saiya daga musu kafa suka samu suka tsallaka, sai nishi takeyi, ta ajiye kwandon a kasa dan ta
numfasa. Ta godewa Allaah da tabarwa Rufaida har Nana. Da yake ba kwiya gareta ba, su
Asaad na dauke mata hankali ta samu ta silalo, ai da taji a jikinta da daukar wannan kwandon.
Yanda Baffa yace ba zai dawo da wurin nan ba, sai kaga har goma ta wuce ma kafin ya shiga
gida, tasan yana son shan ruwan shayi wani zubin, saita hada masa shi yasha kayan kamshi.
Shisa kwandon ya kara nauyi.
Kamar ance ta juya, ta hangi Baffa yana daukar mashin dinshi, sai dai ba kayan daya fita dasu
bane a jikin nashi, yadi ne yanzun, kuma daga inda take taga yayi kyau duk kuwa da bai saka
hula ba. Babu yanda za'ayi ta ware baki ta kwala masa kira, bata kuma fito da wayarta ba.
Hakan yasa ta dauki kwandon, nauyin shi na hanata sauri yanda ya kamata, sai dai kafin ma ta
karasa Baffan ya haye mashin dinshi yayi gaba, tunda baya ya bata ya fice ta dayan bangaren
shisa bai ganta ba
"To ko dai gida zai koma?"
Wata zuciyar ta raya mata, sai tayi tunanin ta karasa shagon taji. Haka kuwa akayi, Abbati ne ya
fara ganinta tunda yana bakin kofar shagon a tsaye da kankana a hannunshi
"Maman Asaad"
Ya fadi yana dorawa da gaisheta a daburce
"Naganshi ya fita ma yanzun, kar dai gida ya koma, yace mun zaku dade yau a shago saboda
akwai ayyuka"
Sai Baffa ya juya yana kallon Isma'il cikin neman dauki, dan shi karya bata cikin dabi'unshi, ko
da kuwa ta kare kaice, kalamai ma gabaki daya basa yawaita a bakinshi.
"A'a um...yaje ya dawo ne"
Cewar Isma'il shima sarkin maganar yau da alama ya rasa ta cewa, kuma hakan nada nasaba
da yanda Jamila takeyi musu kwarjini. Macece da nagartarta take shimfide akan fuskarta.
Yanayinsu, da kuma yadin jikin Baffa ta hada waje daya a cikin kanta, kwakwalwarta ta dai-daita
mata lissafin. Shisa ya kirata yau kenan? Shisa yayi mata kirki? Saboda zaije zance wajen AZ
dinshi kenan, acan zaiyi buda baki kome? Ita tana can tana kitimillin hada masa, banda ruwa da
dabino bata saka komai a cikinta ba tanata sauri ta fito, ashe tana da rabon ta cika cikin nata taf
da bakin ciki.
"Na bar yara a makota, ga kayan buda baki nan, bari in wuce"
Saboda jikinsu a sanyaye yake su duka, kamar sune suka saka Baffa tafiya zance a ranar yau,
sai suka kasa wani yunkuri har Jamila ta juya, ta tare napep, zuciyarta na wani irin tafasa.
Numfashi kawai take maidawa har suka isa, dari biyar din data bashi ma ca tayi ya rike canjin ta
wuce ta shiga gidan Rufaida, taji dadin samunta ta tayar da sallah dan kwata-kwata bata son
wani dogon surutu, ta sabi Nana tana riketa a hannu ta cewa su Asaad
"Ku taso mu tafi"
Bata san ko muryarta bace ko yanayin fuskarta yasa duk suka shiga hankalinsu. Tana zuwa
kofar gida kuwa ta samu Yayarta Yasmin da take tsaye tana danna waya
"Yanzun nake shirin juyawa dan nagaji da kwankwasa kofa..."
Murmushin karfin hali Jamila tayi
"Kai su Maman Danjuma babu hakuri"
Yasmin din tayi dariya. Tun haihuwar Yasmin ta biyu, ta kwallafa rai akan idan namiji ne za'a
saka sunan mahaifinta Abubakar, har shafa cikin take tana fadin Assadiqu kamar yanda take da
niyyar kiranshi, ta shiga watan haihuwarta, Kanin mijinta ya rasu, kawai tana haihuwa da yayi
masa huduba, bata kawowa ranta ba Abubakar din ya saka ba, sai ranar suna taji ana
"Ashe yaro sunan margayi yaci, Allaah Sarki Ya'u"
Ta tabbata da ba'a zaune take ba sai jiri ya tikata da kasa, ita tun yana da rai ma ba shiri sukeyi
ba, duk da ance babu kyau tado da halayen mamaci musamman wanda ba nagartattu ba, shi
kam mutum ne mai tsugudidi, sannan ya saka mata ido ainun, duk wani husumi da zai taso
tsakaninta da dangin mijin nata in aka bibiya shi ya kitsa zancen. Kamar mace haka yake da
gutsiri tsoma. Da yake kuwa ranar Juma'a ne ta haihu, saita fara kiran yaron da Danjuma, wani
suna da mijin nata da dangin shi suka tsana saboda sunce akan meye zata boye sunan yaro,
shima mijin da yayi magana sai tace masa
"Ni da nayi dakon wata shida, nayi nishin nakuda ai ayi mun alfarmar kiran yaro da sunan daya
kwantamun ko? Tunda ban hana kowa ya kirashi da sunan da aka rada masa ba"
Haka dole ya hakura ya kyaleta, tunda yasan hali, jan maganar kamar neman zunguro sama da
kara ne tunda har batace masa ta tafasa ba akan sauyin sunan da aka samu. Tun daga lokacin
ta tashi daga Adda Yamin a wajen kannenta ta koma Maman Danjuma, tun suna kiran sunan da
zolaya har yanzun kusan kowa ma haka yake kiranta dashi. Gidan Jamila ta bude suka shiga,
su Arif suka gaishe da ita
"Mu karasa ciki mana"
Kai Yasmin ta girgiza
"Keni ba zama zanyi ba, Yaya Babangida ne ya hadani da aiki, ga sakonki nan"
Cewar Yasmin tana mika mata ledar data shigo da ita, kafin ta fara kokarin sauke jakar
kafadarta, sai ga wuta sun kawo, daman fitilar caji ce da take dorawa sama, ita ta haske tsakar
gida, saita wuce daki da yara ta kunna musu tv ta dawo, Nana ce kawai ta makale taki sauka.
Kudi ne Yasmin ta mika mata, tasa hannu ta karba
"Kudin dinkin kine yace a baki"
Haka kawai sai taji hawaye ya balle mata, wani irin rauni ya mamaye ta
"Jamila, ikon Allaah, meya faru kuma?"
Da sauri tasa hannu ta goge hawayen, kawai tana hasaso tarin kauna da hadin kan da suke
dashi, yanda ta fahimci ba sai iyayenka nada kudi bane kake kasancewa dangata, ita kam 'yar
gata ce, sun taso cikin tarin kulawa, yanzun gashi aure ya rabota da gidan nasu, ya kuma
sakata yunwar wannan kulawar. Tunda in ba yunwarta da takeyi ba, wayar kasa da mintina biyu
da sukayi da Baffa itace fa tasa ta son faranta masa
"Wai menene? Kinsan banason wannan shirmen banzar naki"
Yasmin tayi maganar cikin fada, amman zaka iya tsintar damuwa a kasan muryarta. Saboda
tasan halin Jamila, abinda zaisaka hawayenta zuba ba karami bane ba, akwai kujerun roba
guda hudu, wata cikin wata daga can gefe, Yasmin ta karasa ta dauko guda daya, duk da batayi
niyyar zama ba
"Kiyi mun magana tunda dai ai baki da wanda suka fimu"
Numfashi Jamila taja tana saukewa
"Baffa ne"
Ta fadi, Yasmin ta kalleta tana jiran karin bayani
"Zance ya tafi"
Sai Yasmin din taja wani dogon tsaki
"Shine kike shararar hawaye sai kace wanda ya nakadawa duka, to in ba daukar kafa ba ke ina
ruwanki da zancen shi?"
Wasu hawayen suka ciko idon Jamila
"Adda bafa dan ya tafi zancen bane ba, kayan buda baki na shirya masa na tafi na kai saboda
yace mun zai dade bai dawo ba, na samu ya tafi wajenta"
Kureta da ido Yasmin tayi
"Da yace miki zai dade sai yace kiyi abinci ki kwashi kafa ki kai masa?"
Ta girgiza kai
"Shegiyar kankanba ce irin taki kenan"
Tayi shiru
"Ke yanzun waye yace miki anayi wa maza wannan kankanbar? Ai kina budurwa ne kafin ya
sameki, shine zaki burgeshi da irin wannan iyayin, amman yanzun tunda ba sakaki yayi ba gara
ki rufawa kanki asiri, in ba kina neman ciwon zuciya bane ba"
Fada sosai Yasmin tayi mata kafin ta dora da lallami, ta nuna mata duk taji, ta kuma lallasu,
haka sukayi sallama, ta rakata tana dawowa. Ta duba ledar, lace ne mai kyan gaske sai atamfa
kala biyu, sai kuma shadda da tasan ta Baffa ce. Da yake Yaya Babangidan yanzun kasuwa
nayi dashi, kuma shi din mutum ne mai son hidimtawa dangi, babu ruwanshi da kana dashi,
inya tashi zaiyi maka, su matan har mazajensu yake hadawa. Ta tattara duka ta shige dakinta
dasu ta adana. Kamar yanda Yasmin ta fada mata ne, ita ta kai kanta, babu wanda ya aiketa.
Amman ta kasa daina jin takaicin wai saboda yana so yaje zance ne yau yayi mata kirki.
Tana da hakuri, amman tasan idan bata rama wannan abin da Baffa yayi mata ba, zata jima
dashi a rai. Ta samu tayi sallar isha'i da asham, ta dan zuba abinci kadan taci, tazo ta dauki su
Asaad da sukayi bacci a falo ta kaisu dakinsu, tana tashin kowanne yayi fitsari, tukunna tayi
musu addu'a, Nana da take goye a bayanta itama tayi bacci, taje ta kwantar da ita. Taji ana
kwankwasa gida, wani abu ya taso mata, haka ta sauka taje ta bude masa, ta kuma danne
zuciyarta tayi masa sannu da zuwa
"Kece da sannu ai Mamin yara, ya naji gidan tsit, ko har sunyi bacci"
Data kalle shi, yanda yadin yayi masa kyau bai hanata ganin bakin shi ba, sai takejin kamar
dariyar da yakeyi mata dinma duk ta yaudara ce yau. Shikuma ganin irin kallon da takeyi masa
yasa shi saurin cewa
"Kinganni da yadi ko? Hmm, kwata na fada, Allaah Ya taimaka Isma'il ya dinka mun wannan
yadin, na samu na canza, kayan na can ma shago na manta dasu"
Baffa ya karasa maganar yana gyarawa mashin dinshi zama
"Da mashin din ka fada kwatar?"
Jamila ta tsinci kanta da tambayarshi duk kuwa da shiru taso yi
"A'a fa"
Ya fada da sauri
"Da naje azahar ne"
Sai wani guntun murmushin takaici mai sauti ya kwace mata hadi da mamakin yanzun ne Baffa
ya koyi shararo karya haka, ko kuma tunda can ne itace dai bata maida hankali ba.
"Allaah Ya kara tsarewa"
Ta furta tana wucewa ta shige daki, bata kuma tsaya ko ina ba sai dakinta, ta haye gado, tana
shirin kwanciya ne Baffa ya turo kofa, ta daga kai ta kalle shi
"Abinci na Mamin yara, bakiji yanda cikina yake daurewa ba"
Zuciyarta tayi wani tsallen murna a cikin kirjinta, ta danyi 'yar dariya
"Yau kuma zolayar taka ce ta motsa, wanne abincin kuma Babansu? Banda wanda nasan yau
har makotanku a shago sai sun samu rabonsu"
Ya dan diririce yana juya maganarta, yana juya maganarta, sai yayi dariya shima duk da kuwa
bai gane me take nufi ba
"Ni dai a dawomun da robobin dana zuba zobo dan Allaah"
Jamila ta fadi, zuciyar Baffa ta buga, kar dai abinci ta aika musu dashi shago?
"Bari dai insa wayata caji"
Yace mata yana ficewa daga dakin, zuwa yayi yasa wayar tashi a caji, ya kunnata, ya dan
zauna a wajen yana jira ta gama kawowa, sai ga sakonni, na Aziza, sai kuma Isma'il, da hanzari
ya fara bude na Isma'il din
"Inata kiran wayarka a kashe, yanzun Madam tabar shagon nan, ta kawo mana kayan buda
baki, amman dai munce mata kaje ka dawo"
A fili ya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Bayan ya karanta sakon, a yanda yasan Jamila, ya tabbata abinci ne niqi-niqi takai, kuma anan
gida din wanda zata bari ba mai yawa bane ba, tunanin karyar da zaiyi mata ya samu ko da
taliya ce ta dafa masa yakeyi, saboda da gaske yunwa yakeji. Haka ya bar wayar batare daya
ko bude sakonnin Aziza ba, ya sake komawa dakin Jamila ya ganta tana duba drawer din gefen
gado
"Me ake nema?"
Batare data dago ba tace masa
"Paracetamol zan hadiya, kaina ke ciwo"
Ya danyi jim
"Sannu, kuma da zuwa nayi ince a zubamun abinda aka rage, kinsan yan shagon nan,
musamman Isma'il, shiya fita da plate yan shagon Rahusa suka ganshi, nan suka tattaro suka
zo, dan abinda nacin ba mai yawa bane ba, anayi asham duk ya zazzage"
Sai lokacin ta kalle shi, amman ya kasa hada ido da ita
"Aikuwa babu wani abu sai abincin Sahur dinka, shisa na zuba muku shi da yawa daman, ko da
baku kadai zakuci ba, kuma da yake banma zaci yanzun zaka dawo ba"
Yayi shiru, itama tayi shiru
"Bani shi inci kawai yanzun din, da sauran biredi? Ko shayine sai in sha anjima din"
Ta jinjina masa kai, tana mikewa, acan kitchen din ta zuba masa a filet, ta samu dan karamin
kwano ta zuba masa miyar, tana dan saka masa kifin kadan, duk kuwa da yawan da yake dashi
a cikin miyar, ta daukar masa pure water da kofi, a falo ta same shi zaune, ta ajiye masa komai
a gabanshi
"Ko dan zobon bai rage ba Jamila?"
Tayi 'yar dariya
"Ai kam dai bai rage ba, mun shanye ni da yaranka"
Ya kalli shinkafar
"Bari inje in samu maganin nan in sha in kwanta ko zan samu bacci"
Da sauri Baffa yace
"Kisa alarm dan Allaah karmu sake makara"
Ta jinjina masa kai kawai tana wucewa batare data amsa ba, haka ya tashi da shinkafar tas,
miyar tayi masa dadi, ya dinga cancana dan kifin da yake ciki kamar karya kare. Ya sha ruwan
yaje ya kwanta, sai lokacin ya dauki wayar shi yana kiran Aziza. Hira sukayi sosai, harda video
call din da yayi mata alkawari, duk da bai bari video call din yayi nisa ba, ko dan dare ne, gashi
ba hijabi ta saka ba, duk da baya ganin komai banda wuyanta sai kuma gashin kanta da yake
kwance luf har akan goshinta,hular data saka ta dan zame baya. Gashi duk ta narke sai
shagwaba takeyi masa, yaji ya fara susucewa, kuma tunda watan azumi ne, yasan bashi da
halin labewa bayan shaidan.
Haka yayi mata sallama yace zai kwanta, kuma kwanciyar yayi, amman cikinshi daya murda ne
ya saka shi tashi babu shiri yayi bandaki, wasa-wasa kafin karfe biyun dare ya shiga bayi yafi
sau takwas, danma Allaah Ya taimake shi cikinshi bai fara ciwo ba, da yazo ya kwanta dai sai
yaji jikinshi yayi laushi matuka, kamar duk yinin ranar baici komai ba, yasan dole ya lallaba
Jamila anjima ko indomie ce ta dafa masa ta soya masa kwai kamar guda biyar yayi sahur
dashi, dakyar ya samu bacci yanata mafarkin abinci
Abinda Baffa bai sani ba shine Jamila bata kwanta da niyyar tashin shi ba...
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da
kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
5
(Last Free page)
Kudin da Baffa ya bata ta kirga bayan tafiyarshi, saita tabe baki, saboda ta raina dubu goma,
kamar yanda ta raina kayan sallar da yayi mata, musamman lace din. Ko Mummy da ta ganshi
saida tace
"Wannan lace din ai karami ne Aziza, ba zai wuce dubu sha biyar ba"
Aikuwa dansu tabbatar haka ta dauki hoton shi ta turawa kawarta da take siyar da kaya tana
tambayarta, ita a wajenta ma dubu sha uku da dari biyar ne
"Inya baki wasu kudin a hankali saiki tarasu ki hada ki dauki babban shi"
Haka Mummy ta bata shawara. Jaka da takalmin dai sunyi mata kyau sosai. Taji sanyi da ba da
Baffa kadai ta dogara ba, sauran samarinta sunyi mata hidima kamar yanda suka saba. Kawai
matsalar zuciyarta ce, itace ta narke akan Baffa, saboda tana tunanin fata da kuma bakin
Mummy ne yake binta, ita take yawan fadar
"Kefa ba matar kananan yara bace ba, In Shaa Allaahu ke din matar babban mutum ce"
Manyan mutanen ne suke binta kuwa, masu kudi, dattijai da suka kusan haifarta dama wanda
suka haifi kamarta sau babu adadi. Tana son rayuwar hutu da jin dadi, amman fa auren tsoho
bai taba burgeta ba komin kudinshi. Duk kuwa yanda take ganin jin dadi shimfide a fuskar
Mummy din idan sun hidimta mata, wani zubin ko don Mummy ta huta sai taji kamar ta duba
wanda suka fi dama-dama a cikin maneman nata, a lokacin ne kuma ta gane da yawansu ba
auren bane ya kawosu. Alhaji Sadisu ne kawai yayi mata maganar aure da kanshi, shikuwa
matanshi uku a yanda ya fada mata, uwargidanshi ta rasu, da ita yake so ya cike ta hudu.
Shikuwa ko bai fada ba ta tabbata ya ba saba'in baya. Ba tajin tarin dukiyar shi zasu lullube
mata shekarun shi. Samarin kuma da