Showing 1 words to 3000 words out of 61349 words
Chapter 1 - Halysaah Book Complete By Khaleesat Haydar -1.pdf
[20/05, 11:37 pm] +234 813 644 0264: *If you should come across this post plss say a prayer for
my late father, Allah ya sabunta masa rahama, ya gafarta masa da duk musulman da suka riga
mu gidan gaskiya, Allah ya kyautata makwancinsu gaba daya, ya sa mutuwa hutu ce a garesu,
Allah ya yafe masu kurakurrensu, Allah ya bamu guzurin tar da su*
**All thanks to Allah S.W.T for the chance and privilege to commence this new book, yanda
muka fara lafiya Allah ya sa mu idar lafiya*
_Hmm ga fa Halysaah, Allah ka bani ikon delivering babu cece ku ce_
*This first page goes to all the members of Mayraah Conversation, i love and appreciate you
all*
✨✨HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍
1....
Tsaye take ta jingina da trunk din bishiya a wani babban garden dake dauke da shukoki iri iri da
suka kawata wajen, tsuntsaye sai shawagi suke a garden din happily making a chirping sound
as the sun set slowly, the view was so beautiful and breathe taking, duk da yanda ta kafe view
din da ido gaba daya hankalinta baya gun, she was just staring at the setting sun
absentmindedly, tayi nisa cikin tunanin da take, daga gefenta wata ma'aikaciyar asibiti ce in her
mid 40, likitar ta dafa ta tana kallonta cikin kwantar da murya tace "Magariba ya gabato mu je
kiyi alwala ko" Kallon likitar kawai take babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda take cewa
ba, sai ga hawaye ya fara taruwa idonta tana sauke numfashi a hankali, likitar ta kama
hannunta ta jawota jikinta calmly tace "C'mon sweet heart, are you breaking ur promise
already?" ta kwantar da kanta jikin likitan hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, likitan ta lumshe
ido tana patting dinta duk jikinta a sanyaye, a tare suka juya jin footstep a garden din, ya tsaya
daga inda yake bai karaso ba yana kallonsu, likitan ta fara gaishesa cikin girmamawa, zame
jikinta tayi daga na likitan ta juya masa baya alamar ko ganinsa bata son yi hawaye na zuba
idonta, ji take kamar numfashinta zai dauke kamar ko da yaushe, ta fashe da matsanancin kuka
ta dafe trunk din bishiyar dake gefenta, ko amsa gaisuwan likitar bai yi ba ya juya ya fice daga
garden din, da sauri likitan ta kamota ganin faduwa zata yi, ta fara kokarin zaunar da ita akan
lallausan carpet dake shimfide wajen trying to calm her down tace "Haba kanwata, me yasa
baza ki cika min alkawarin da kika daukar min ba?" Muryarta na rawa tace "Kiyi hakuri bazan
iya ba wallahi" Rungumeta likitan tayi tana bubbuga bayanta a hankali wani mugun tausayinta
na shigarta, tayi attending to different cases in her career as a medical Doctor amma babu
wanda ya taɓa daga mata hankali ya tsaya mata a rai irin na baiwar Allahn nan, she wish she
can take away her pains, she wish she can make her happy once more, she wish she can make
her forget the past and face the present, a hankali likitar tace "Halysaah...." khaleesat ta daga
rinannun idonta tana kallon likitan, likitan tace "Kiyi hakuri Halysaah, kiyi hakuri" Khaleesat ta
sauke idonta bata ce komai ba, likitan ta daga ta tana rike da hannunta suka bar garden din
zuwa babban compound din gidan.
Few years back!
"Talk to Abdul about it, nasan bazai taɓa yarda da haka ba, and he will definitely find a way out
for u immediately..." Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallon kawarta Safiyyah,
kamar bazata ce komai ba sai kuma ta sauke idonta a hankali tace "That will be another huge
burden Safiyyah, u know how expensive apartment can be in this state, gida da akwai tsada
sosai, kuma na fa ce maki ni bazan sake tambayarsa komai ba, ko kuma ince yayi min wani
abu...." Safiyyah tace "Cabdi, to in ba ki tambayesa ba kina da wanda zaki tambaya? Balle ma
kinsan halinsa lokaci daya tsaf zai juya situation din nan against you, i think gwara kawai ki
sanar masa yafi maki kwanciyar hankali" Khaleesat tayi shiru tana nazarin abinda Safiyyah ta
ce, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai tace "It's fine Safiyyah, ba sai na gaya masa
ba i will cope in sha Allah, after all we have just a year and a half to go" Safiyyah na kallonta ta
kamo hannunta tace "Ko zaki dawo wajena sai in gaya masu kawata zata zo ta ɗan zauna da
mu zuwa wani ɗan lokaci?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Let not inconvenience them Safiyyah,
kar ki damu kawai, i will sort my self out...." Safiyyah tace "No, i will talk to Ya Musty about ur
current situation khaly, nasan bazai ce a'a ba, matarsa ce dai gagarumar er iska, and do i even
care? Ba ki ma san me take min ba yanxu a gidan, duk dare bata girki da ni sai dai in nemi
abinda zan ci tunda kinsan Ya Musty night shift yake, ni kuma dama kin san i prefer junk food,
kawai sai in hada cornflakes in sha abu na" Khaleesat tayi murmushi tace "Shine kike son in bi
ki zuwa gidan a haka ko? You are very funny" Safiyya ta juya ido tace "So what? Naga ai ba
kanta zaki zauna ba in kin dawo gidan, Yaya Mustyn nan fa is my cousin brother ko kin manta
ne? Saboda haka ko taki ko ta so dole in zauna a gidan har in gama karatuna, very wicked and
self centered woman, wallahi kar ki wani damu in dai nayi ma Ya Musty magana kawai ki dauko
kayanki ki dawo gidan ko zuwa gobe ne...." Khaleesat tace "Aa gaskiya don't even start that
Safiyyah, i will cope with my present situation with time, nasan zan saba gradually, beside it's
something that is normal kawai dai ni ce nake damun kai na saboda addinina da culture dina da
dai wasu abubuwan da baza a rasa ba, any way... it's fine Safiyyah" Tana fadin haka ta kalli
wayarta dake hannunta jin shigowar notification, tace "I think my Lyft is here Sophie, sai gobe in
Allah ya kai mu" Safiyya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk then, take care of ur self, i will stroll
home too" a haka suka rabu, Khaleesat ta nufi Lyft din da tayi ordering zai maida ta gida.
Khaleesat na kitchen wajen karfe goma na dare ta gama girka Noodles da zata ci for dinner
kenan taji alamar an bude kofar parlor, a hankali ta karasa juye Indomie dinta a plate ta dau fork
ta saka sannan ta wanke pot din ta ajiye, ta bude fridge ta dau bottle water ta fita daga kitchen
din, hanyar dakinta ta nufa direct, dai dai corridor aka bude kofar wani room that is just few
steps away from her own room, ko kallon direction din bata yarda tayi ba tana kokarin bude
kofar dakinta taji ance "Hi, good evening, we didn't get to meet when i was here in the morning I
guess you've already left for school then, you can call me Jay, and i am ur new House mate, I
moved in this morning...." Sai a sannan Khaleesat ta juya ta kallesa amma bata ce komai ba, ya
gyada mata kai yace "Jay" babu yabo babu fallasa tace "I see" Ganin zata shige daki yace "A
minute pls" Ta juya ta sake kallonsa da wani expression, a takaice yace "Ke bahaushiya ce?" Ta
ɗan hade rai tace "I don't know what u are talking about" Yace "Oh ohk, i am asking for a
permission..." Ita dai kallonsa kawai take, Ya gyara tsayuwarsa yace "As u can see it's late
already now, can i use some of ur portable water and Beverages before i get mine tomorrow if
you don't mind?" Khaleesat ta dauke kanta a takaice tace "Ohk" Yace "Alright" Daga haka ta
shige dakinta ta kulle kofar ta saka key, ko da ta gama cin Indomie din bata ji zata iya bude kofa
ta fita kai plate din kitchen ba, daga karshe kawai ta bar shi a wajen bayan ta shiga bandaki ta
wanke bakinta ta dauro alwala ta fito ta zauna edge din gadon dakin ta dau wayarta, Miss calls
din Abdul ta gani har biyu wanda yayi mata tun karfe shidda, ta sauke ajiyar zuciya tana duba
agogon wayarta dake nuna mata karfe goma da kusan rabi, meanwhile karfe kusan biyar kenan
na asuba agogon Nigeria, bude WhatsApp dinta tayi ta dubasa taga yana online, hakan yasa ta
masa WhatsApp call, yana dagawa tayi kasa da murya ta gaishesa a hankali, Bai amsa ba yace
"Yanzu kika ga kirana?" Ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kayi hakuri, yanzu naga kiran
wallahi" Yace "You mean tun daxu wayarki baya gun ki kenan?" Tace "Not really, tun dai da na
dawo schl nake karatu, in few months time zamu fara exams" Yace "I see, shi ne yasa kika ga
ban yi deserving lokacin ki ba don zaku fara exams, ta yaya ma wayarki zai yi ring ki ce baki
sani ba in ba rainin hankali ba?" Rasa abinda zata ce masa tayi, don wayar a silent yake kuma
ya hanata barin waya a silent on several occasions, to avoid further issues sai bata ce masa
wayar a silent yake ba, a hankali tace "Kayi hakuri, wallahi ba haka bane, i am sorry..." Yace
"Sorry for ur self, malama so nake ki gaya min kina ina har wayarki rang twice baki ji ba? ur
lectures today terminated by 4pm Baltimore time, so ina kika je daga nan?" Ta rufe ido ta bude
don ta fara gajiya da tuhumar tasa, After few seconds ta marairaice tace "Ina parlor ne ina
karatu, wayar kuma na daki" Yace "Kin fara zaman parlor kenan, when did that start? House
mate din taki ta dena shigowa da saurayinta ne gidan?" sai da gaban Khaleesat ya fadi, A
hankali tace "Bata nan, taje LA jiya" Yace "Sau uku kenan ina kiranki a satin nan baki dagawa
sai sanda kika ga dama ki biyoni, that nonsense shouldn't repeat it self again, a kanki aka fara
karatu ko ni zaki gaya ma karatun Exams?" Shiru Khaleesat tayi lkci daya hawaye ya cika
idonta, a ɗan fusace yace "Baki ji na ne?" Cikin sanyin murya tace "Naji, kayi hakuri hakan
bazai sake faruwa ba in sha Allah" Yace "Good, you can go to bed" Tana goge hawayen da yaki
tsaya mata tace "Nagode, sai da safe" Shi ya katse call din ta ajiye wayarta gefen gadon ta dora
kanta a pillow hawaye na zuba idonta, after a while ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta
dawo ta kashe wutan dakin tayi addu'an bacci ta kwanta.... Washegari Friday da wuri Khaleesat
suka gama lectures dinsu, suna zaune a exact spot din jiya ita da Safiyyah dake waya, sosai
Khaleesat tayi nisa tunanin da take har bata san sanda Safiyyah ta gama waya ba, dafa
kafadarta da Safiyyah tayi ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, Safiyyah tace "What is
wrong Khaleesat, ina ta magana baki ma san ina yi ba, tunanin me kike haka?" Khaleesat ta
ɗan kirkiri murmushi tace "Kawai ina kewar Ummanmu ne da siblings dina" Safiyyah ta girgiza
kai tace "Ban yarda ba, there is definitely something that is bothering you" Khaleesat ta kauda
zancen tace "Ke da George ne ke waya ko?" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Pls gobe
weekend ki shirya mu tafi Virginia Leesat, George is throwing a party for his birthday tomorrow,
kuma za mu je Beach, don Allah kar ki ce a'a, we need to take a break and rest our brain, ba ko
da yaushe karatu ba kamar mu muka kawo boko duniya...." Khaleesat dake ta kallonta tace "Ke
yanzu sai ki kama hanyar Virginia Safiyyah??" Safiyyah ta hade girar sama da ta kasa tace "To
menene, it's just a 4 hours ride from Maryland, kamar fa ace daga kaduna zuwa kano shi ma in
mota bai yi gudu ba, pls for once ki zama social mana Khaleesat, ke baki gajiya da zama guri
daya ne a kasar nan? Baki gajiya da karatu? ranan Monday fa za mu dawo in sha Allah, kuma
babu wanda zai san mun je wani Virginia, dama Ya Mustapha na riga na gama plan din abinda
zan ce masa, ke da ba ma ki da wanda zai sa maki ido kike mis using opportunities haka, da
mun koma Nigeria fa shikenan, tafiyar nan maza ne hade da mata" Khaleesat ta girgiza kai tace
"Lallai... Ni dai ina baki shawara kar ki je Safiyyah" Safiyyah tace "Bana ma son shawaran,
abinda mu goma za mu je" Khaleesat tace "Toh Allah ya tsare hanya ya dawo da ku lafiya"
Safiyyah ta mata wani kallo tace "Baza ki je ba kenan dai?" Ba tare da Khaleesat ta kalleta ba
tace "Kema kin san bazan je ba ai" Safiyyah tace "Ke kika sani, mu dai za mu je wallahi"
Safiyyah na kai wa nan ta mike tace "Sai ran Monday" Khaleesat na kallonta a hankali tace "Wai
tafiya za ki yi? Da sauran time fa Safiyyah" Safiyyah tace "Aa toh me za mu zauna yi a schl
bamu da aji? Yau kuma kece ke cewa da sauran time duk son ki da komawa gida da wuri? Ikon
Allah" Khaleesat ta kasa cewa komai, ita har ranta take jin ta tsani gidan nata yanzu, she no
longer see the home as her comfort zone, and she don't think she can cope staying together
with an Hausa Guy under same roof, da ma bature ne ko kadan bazata damu ba kamar yanda
ta damu yanxu, har ta taho school bata hadu da sabon Housemate din nata ba da safe,
Safiyyah ta ɗan buda ido ta koma ta zauna tace "Ohh now i remember, wai saboda new House
mate dinki? To wai ke meye damuwarki ne da shi? Yayi harkan gabansa kiyi naki ne fa a gidan,
ko magana in baki son ya maki you just call the cops a maki iyaka da shi, just dial 911 and
that's all, balle nasan kilan da kyar aka kukuta masa ya taho makaranta kasar nan to kuwa ina
zai tsaya bata lkcnsa akan abinda ba shi ya kawo sa ba, don dai in wani Shege ne shi bazai
zauna a shared apartment ba a USA, kuma 'ya yan masu kudin nan sun fi iskanci su kuwa
talakawa abinda ya kawo su kawai suke yi, kiyi ta kanki kawai shi ma yayi ta kansa, kar kiyi
mamaki ta scholarship ya zo kasar ma" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta
kyabe baki tace "Tashi mu je gidan, ni banda Ya Musty bazai yarda ba da ba sai in tattaro in
dawo gidan naki ba mu zauna kawai" Khaleesat ta marairaice tace "Plss ki sake masa magana
ko zai bar ki mana, ai sanda ya hanaki kinga bamu dade da fara makarantar ba" Safiyyah tace
"Kar ma ki bata bakinki mutumin nan bazai yarda ba, tashi mu je in raka ki, in House mate din
ma yaga kina wani yin abu a tsorace renaki zai yi wallahi, yi zaki yi kamar kema er gari ce kawai
sai ki ga ya fara shakkar ki a gidan" Khaleesat ta mike tace "Kar fa muje kiyi ta Hausa, just
pretend we are not Hausa" Safiyyah tayi dariya tace "Kece dai is not Hausa, ni kam Bahaushiya
ce cikakkiya kuwa" A haka dai suka bar makarantar suka nufi gidan da Khaleesat take....
Khaleesat ta bude handbag dinta ta ciro makulli ta bude kofar shiga gidan suka shiga parlor
Safiyyah na biye da ita a baya, Safiyyah na gyada kai jin wani kamshi da parlon yake tace "Da
alama bai dade da fita ba ma" Khaleesat dai bin parlon take da kallo ganin duk reading
materials dinsa ne saman kujera ya tula a kai, Safiyyah tace "Kinga don Allah ki saki ranki ki ci
gaba da harkokin ki Khaleesat, a Maryland fa kike a Amurka ba Kano Nigeria ba, ki dinga abu
irin na wayayyu mana pls" Wani kallo Khaleesat tayi mata ta ajiye handbag dinta tace "Ance
maki in bature ne ko wani yare ni zan damu, kawai my issue here is about him being a Hausa
Guy, har fa tambayata yayi jiya ko ni bahaushiya ce" Safiyyah tace "Ohh kun ma yi magana
kenan...." Khaleesat tace "Ni ban kulasa ba kuma ban nuna masa ni Bahaushiya bace, i will just
pretend i am from Morocco" Safiyyah ta dinga dariya har da saukowa daga kan kujera tace
"Gashi kuwa an ma fi saninsu da fararen mata kyawawa na ajin karshe, tsaf zai yarda daga can
kike, kinga da larabci ya zauna daram a bakinki sai kiyi ta zabga larabci nasan ba lallai yana ji
ba, daga haka zai kama kansa yayi zaton ke balarabiyar gaske ce... sai ma Abdul yaji kuna gida
daya da Bahaushe kilan Baltimore yayi maku kadan wallahi, shi sa nace ki gaya masa kika ki"
Khaleesat ta ajiye jakarta bata sake kallon Safiyyah dake ta dariya ba tayi wucewarta kitchen
tana tunanin me zata dafa masu dama ko breakfast bata yi ba ta fita daga gidan, tsaye tayi
kitchen din tana kallon cartons din bottle water kusan bakwai wanda duk yafi tsada a state din,
sai kuma ta juya ta kalli beverages masu yawa da ya ajiye kan cabinet, ta karasa cikin kitchen
din ta bude babban fridge zata dau kwai da za ta dafa masu Noodles, kallon fridge din ta dinga
yi ganinsa fully stocked with everything, tun daga tsadaddun drinks kala kala, fresh milk,
varieties of fruits, with many eggs, muryar Safiyyah taji a bayanta tace "Kai kai kai, shi ya zuba
abubuwan nan a fridge Leesah?" Khaleesat ta juya ta kalleta looking speechless, can dai ta dau
eggs din da zata dauka ta kulle fridge din ta tafi inda foodstuffs