Showing 1 words to 3000 words out of 9108 words

Chapter 1 - Dame Ake Ado Book 1 By Fauziyya D. Suleiman .pdf

08 Jul 2025

840




DAME AKE ADO part (1)
1⃣Mahaukaciya yarmacukule mahaukaciya tasaci zare dandazon yaran da suka zagaye
mahaukaciyar ke ihu suna fada yaukam adurkushe take tana kuka tarike cikinta sabanin
canbaya da idan suna wannan wakar take rawa eyehuuh eyehuuh kuka takeyi yau babu rawa
suka kakama fada suna ihu malam sulaiman dayake dosowa tundaga nesa yacika yacika
dataikaicin yanda yaran unguwar suka takurawa matar dababu wanda yasan daga indatake
kawai an wayi garine anganta a unguwar yadauko tsumagiya yayi kansu yafara dukansu sai
suka watse sunaci gaba da ihu dawakarsu filin yazama sai ita kadai harlokacin tana durkushe
tana kuka
2⃣ya isa gurinta yana fadin baiwar Allah tashi kitafi abinki kinjiko wayyo Allah cikina mutuwa
zanyi maganar datafito daga bakin mahaukaciyar kenan wacce tasanyashi kara kallonta da
mamaki dan tsawon wata tara dayasan matar baitabajin tayi maganaba saiyau kuma abin
dayabashi mamaki baiwuce jin maganar tata yau irin tamutumin dayasan ciwonkasa baceba
kafin yakai gacewa wani abu yakuma jin tace wayyo Allah zanmutu saiyaga jini yanazubowa ta
karkashinta dasauri yace subhanallahi haihuwa ce zakiyi dandama tanada ciki wanda akezargin
wanine yayimata akan bolar datake kwana tabayan gidan malam sulaiman din baiyi wata
wataba yakamota dasaurinsa danjin kamar tana nishi ga yaran basu bar gurinba sai ihu suke
tayi yaciccibeta yakaita soron gidansa dake jikin bolar ya tura kyaure
3⃣soron yanufi cikin gida dasauri yana kwalawa matarsa kira Deeje Deeje sukaci karo tana
tahowa dasauri takalleshi lfy malam zomuje mahaukaciyar nan dake kwana akan bolar nan
tajikin gidan nance babu lfy ina tunanin nakuda cetakeyi subhanallah muje mlm tafada atsorace
sanda suka karasa soron tabbas nakudace takeyi bari nadauko zannuwa kirawo Lami acikin
gidansu mama yanufi gidansu Lami wacce yakasance soro guda akeshiga cikin gidan matar
kanin malam dince yafara sallama daga bakinkofar da zata sadaka da gida nasu

3⃣soron yanufi cikin gida dasauri yana kwalawa matarsa kira Deeje Deeje sukaci karo tana
tahowa dasauri takalleshi lfy malam zomuje mahaukaciyar nan dake kwana akan bolar nan
tajikin gidan nance babu lfy ina tunanin nakuda cetakeyi subhanallah muje mlm tafada atsorace
sanda suka karasa soron tabbas nakudace takeyi bari nadauko zannuwa kirawo Lami acikin
gidansu mama yanufi gidansu Lami wacce yakasance soro guda akeshiga cikin gidan matar
kanin malam dince yafara sallama daga bakinkofar da zata sadaka da gida nasu

5⃣Allah zaitaimakeshi mlm din yafada cike da matsananciyar damuwa ko ajikinta wai antsikari
kakkausa sai ma cewa tayi gaskiya saidai kayi hkr amman bazan iyatabataba abinda akace
wurinda akahaifi shege ka taka kaida arziki har abada nidazakuji ta tawa ma aidakunfita daga
soron gidanmu kada tashafamana talauci karabuda ita malam kaje kasamo mota akai matar
nan asibiti zubar jini tayi yawa tafi don Allah kada ta mutu malam din yayi duru duru sannan
yafice dasauri yajanyo kofar lami tayi tsaki takoma cikin gidanta tana cigaba da fadin Allah
daiyakawo mlm wlh waje za.ayi da ita bazata goga mana talauci ba daman kulum anata fama
sai anfita asamu dakyar ita dai Deeje kamo mahaukaciyar tayi dake tafadin wayyo cikina

mutuwa zanyi
6⃣deeje tace kinga daina cewa wayyo kama salati ringa kiran sunan Allah Aikuwa cikin ikon Allah
mahaukaciyar takama kiran sunan Allah dakarfi deeje tana rike da ita tadinga wani irin wani irin
nishi saiga katon da deeje tace insha Allah sauraki mahaifa daure kiyi nishi kozata fado takama
yin nishi da karfinta deeje tafara fadin subhanallahi ahankali zakiyi Amman ina yitakeyi da iyakar
karfinta sai deeje takula ba ita takeyin numfashinba daga Allah ne kawai saigigice ta rude ganin
mahaifar tafado jinin kuma yana bulbula kamar fanfo dakyar ta iya janyo yaron tayanke masa
cibiya jin yana ihu daidai lokacin mlm sulaiman yaturo kofar yana fadin deeje gamai motar nan
kota haihu ne cikin kuka take fadin shigo mlm shigo kaga halinda take ciki yaturo kofar yashigo
kallo daya yayimata

7⃣hankalinsa ya dugunzuma yakama cewa da deejan kamota muje Asibiti deejan nakokarin
kamata sai dai mahaukaciyar tariko hannunta tana fadin mutuwa zanyi kada kukaini asibiti
kuwahala sunana Asma.u haki yakamata deeje takuma rudewa tana fadin innalillahi kifadi
gidanku wacece ke maimakon ta iya cewa wani abu sai kalmar farko da deeje ta ambata ta
innalillahi wainna ilaihi rajuun raiyayi halinsa talangabe anan hankalinsa deeje da mlm yayi
matukar tashi deeje tafashe dakuka tanafadin mlm munshiga ukku hankalin mlm sulaiman
yatashi jikinsa yaduki rawa duk yarudema yarasa abinyi deeje ce tace mlm kasanar da jama.ar
unguwa sukawo mana
8⃣ dauki Allah yasani niyyar taimako mukayi mlm yanafadin dole saimun sanar da hukuma
kulada yaron da gawar bari na je nadawo kafin takara cewa wani abu yabazama yafice
tatsugunna tana kallon yaron daketa wutsil wutsil cikin zani kyakkyawa gwanin bansha.awa son
yaron yafara shigarta Lami taleko tana fadin yaya tahaihu ne tayi turus cike da tsoro tana kallon
mahaukaciyar saita dafe kirji tanaci gaba da fadin badai tamutuba deeje wane bala.i kuke shirin
kawomuna wlh babu ruwanmu takoma dabaya deeje tadaga kai tana harararta ranta abace
amman tagaza cewa komai don takaici
9⃣tana nan zaune tsawon minti arba.in tajiyo karar jiniya tamike jikinta yana bari jin datake bata
taba shiga police station ba amma yau ga motar police harkofar gidansu tana nansaiga mlm
sunshigo dayan sanda ukku kowanne dauke da bindiga daya dagacikin su yakalli mlm sulaiman
yana fadi mlm katabbata abinda kafada shine gaskiyar magana wlh babu kari ko ragi Allah yana
kallona mlm yafadi dasauri har lokacin hankalinsa tashe dansanda yagirgiza kai yana fadin duk
dahaka zamu tafi dakai da matarka danzamuyimaku wasu tambayoyi deeje tawaro ido tana
fadin nashiga ukku don Allah yallabai kayimini rai wlh bantaba shiga irin wannan
1⃣0⃣motarba yakatseta kada kidamu hjy bawani abu zamuyikiba tambayoyi kawai zaku amsa jiyo
karar zuwan motar yankwana kwana suka kuma rudewa haka nan akasanya mahaukaciya
deeje rungume dayaron suka fice daga gidan cikin rakiyar yansanda Lami tana labe tana
lekensu ta kofa tana dariya tana ganin sun fice tafara fadin Allah yakara maganinku masu
neman suna kenan banda haka daga ganin mahaukaciya tana nakuda har wani kinkimota
kukawo kamar kukukafi ubankowa imani koda yake ai neman sunane kuma kunsamu
tamurguda hannu ta tafa acinya tana juya idanuwa sanda suka fice jama.ar unguwar sun fito
cirko cirko ana kallonsu kowa da abinda yake fada mlm jibrin yashigo gida fakan fakan cike da
tashin hankali yana kwalama matarshi kira Lami Lami
1⃣1⃣DAME AKE ADO ......Tafito daga daki dasaurinta tanafadin mlm lfy wannan irin kiran kamar

zaka tsagan dodon kunne yakalleta cike datashin hankali yace jinayi ance yansanda sunzo
gidanmu sunyasheku gabadaya Anyi police station daku wai antsinci gawa agidan tarike kugu
tana kada kafa A.a bakarya bane gaskiyane saidai ba.abaka lbr dai dai ba andaitafi dayaya da
deeja dansu suka debo ruwan dafakansu kamar yaya kinanufin yanzu shi yayan da deeje suna
can wurin yansanda? Dagaske kenan Ansami gawar kaibakacin ribar zance wlh katsaya
nagayamaka yanda Abin yafaru mana
1⃣2⃣DAME AKE ADO Baikoma tankawaba hartasanar dashi duk Abinda yafaru tadora dacewar
danhaka nibaganin laifin yansanda wlh sunyi daidai kokai yayakagani? Yadansaki rai yana fadin
nasha gayawa yaya wannan halin nasa watarana saiyaja masa masifa gashinan kuwa mutum
yace kofada yaga anayi saiya raba can yaje yakarata idan naga abin yayi tsananani naje
nasarwa da Abokinsa mlm Habu bani ruwa nasha nakoma kasuwa yakarasa magana yana haki
1⃣3⃣DAME AKE ADO Malam sulaimai da deeje suna zaune agaban tebur din DPO kusan
awannisu shidda kenan apolice station din DPO yadaga kai yakallesu shikenan malam tamutu
kada kadaina taimako domin ladanka yana gun Allah yanzu zaku wuce dayaron gobe zamu turo
wasu jami.an namu zasu amsheshi amikashi gidan marayu Allah yasaka da Alkhairi Ran mlm
yayi fari yamike daidai lokacin damatar tasa ta mike itama tana fadin babu damuwa ranka
yadade dahaka sukabar ofis din deeje tana rungume da yaron suna isa gida deeje tadora
amurhu tawanke yaron tas wanda yayi kuka haryagaji malam yasamo zam zam da 1⃣4⃣ DAME
AKE ADO ...Dadabino akabashi yasha sannan ya kuma yasiyo madara irin tagari akajika masa
da ruwan zafi yasha saigashi yakama bacci Auwalu da sani diyoyin deeje sai murna suke wai
ansiyo musu yaro akasuwa sun sami kani mahaifiyar tasu dariya kawai take musu tana
rungume dayaron dayake kuma shiga ranta duk bugun dakika mlm yadawo daga masallaci
yataddata rungume dashi yayi dariya yana fadin Deeje uwa kenan ki ajiye dannan koyafijin
dadin yin bacci tayi dariya tana kwantarda shi agado tace wlh mlm jinyaron nake kamar nice
nahaifeshi yayi dariya yana zama sallamar malam jibrila daga bakin kofa takatse musu hirar
tasu mlm sulaman yatashi dasauri ya leka yana fadin jibrilu yaya akayi ne? ​ Free Mode​
See
DAME AKE ADO part2.
Jibrila yagyara tsayuwar sannan yace wani lbr nakeji yanzu gurin Lami danadawo wai ankaiku
police station amman yaya ka kasa aikawa agayamani ai da na biku naji abinda yafaru yayi dan
yake yana fadi gani nayi ba wata babbar bace ba shiyasanya ban Aiki maka ba amman yanzu
komai yawuce da izinin Allah to Aishikenan Allah yakiyaye gaba amman dai yaya karage halin
nan naka watarana zai iya janyo maka adaureka mlm sulaiman yayi murmushi yana fadin kayya
duk Abinda da Allah yakaddarowa bawa babu makawa saiya sameshi Amman kuma dai yaya
ance gidan da aka haifi shege masifu suna sauka acikinsa yanzu baka gudun abinda zaije yazo
madaukakin mamaki yaziyarci mlm sulaiman yadinga kallonsa baki bude da ................. Dakyar
yadaure yace A wanne hadisin ko ayar kaci karo da wannan batu Ya kama sosa keya na rashin
madafa yasan halin yaya nasa sarai zai iya yimasa wankin babban bargo dan haka ya wuce
dasauri yana fadin aishikenan Allah dai yasa ruwan sama yawanke mana daudar yabishi
dakallo har yakule sannan yaja tsaki cike da taikici yakoma ...Dasafe tun Asuba Deeje tadora
ruwan wanka ta wanke yaron tas tasanya masa kayan jarirai mlm yashigo tana rungume dashi
tana bashi madara a filinboti ya kama kuwa yata zuka yakalleta tana dariya yace tomasu amsar
yaron sun iso kishirya muwuce akaishi tadaga kai takalleshi nandanan hankalinta yatashi yakula

dahakan danhaka yayi sauri yadauke kansa yafice GIDAN RAINON YARA Ankammala duk
rubuce rubuce da dakaura hotuna harda na gawar Asma.u mahaukaciya mlm da deeje zaune
gaban shugabar gidan tana tana musu godiya takirawo wata cikin ma.aikata data amshi yaron
wanda harlokaci deeje take kankame dashi dan angama bincike ta goyeshi abaya ma.aikaciyar
jinyar tayi tsaye kikam tana jiran deeje takwanto yaron amman taki mlm sulaiman yadan
zungureta yana fadin kwantoshi mana deeje sai tamanne kafada suka zubamata ido da mamaki
sai kawai tafashe muru dakuka mamaki yacika kowa agurin shugabar gidan takasa magana
tana kallon ikon Allah koda yake takula dayanayin deeje tunda suka shigo bakuma yaune tafara
ganin irin hakaba saidai amatsayinsu na.ama aikata bazusuturawa mutum da baisanya kansa
ba dangudun azabtarda yaron nidai dan Allah Abarmini yaron nan tunda kunada su dayawa
mlm sulaiman yadibeta damamaki Allah yasani abinda keransa kenan amman kuma baisaniba
ko anayin hakan ba shugabar Hjy Amina tayi dan murmurshi gami da komawa takwanta jikin
kujerarta tana fadin daina kuka malama deeje zamu iya barmiki yaron nan saidai akwai wasu
sharudda da zamu gidayamiki 1⃣9⃣ wlh nayadda da duk sharadin da zaku gindayamani takatse
shugabar cikin hanzari Atake anan shugabar tagindaya musu sharadin amsar yaron suka
amince harda sanya hannu a rubuce sunrabu da shugabar akan duk wata guda zasu dinga
kawo yaron anaganinshi da haka sukayi sallama cike da jin dadi suna tafe ahanya deeje takara
kankame yaron tna dariya kai mlm da.ankwace yaron nan dasainayi jinya yaron dashi rai yake
wlh yayi dariya yana fadin ke kam da baki taba haihuwa ba da anshiga ukku kin kankame yaro
kamar zaki maidashi ciki to barka da mlm wane suna zakasanya masa kuwa Ta tambaya
Aubakiji sunandana fadi gurin cike takaddunba koda yake lokacin kin rude aitinjiya da daddare
nayi masa huduba da AHMAD 2⃣0⃣ idan Allah yakaimu ranar sunansa ta zagayo sai ayanka
hakika ayi radin sunan A masallaci gurin shayawar ne dai nake tunani yanda za.ayi tunda kina
dauke da cikin wata ukku bamu sani ba ko zaiyiwu kishayar da shi amman dai matambayi
malaman Asibiti tayi ajiyar zuciya kuma kaga na shekara ukku rabona da haihuwa sai dai mu
shayarda shi madara siyo madarar shanu yakama ka kenan kullum tana dariya to yaya na iya
tunda Allah yabani da haka suka isa gida cike da nishadi lami tana jiyo sallamarsu takwasa da
gudu tana lekowa sam basu kula da itaba tarike haba cike da mamaki ganin sun dawo dayaron
abayan Deeje dan haka takuma tabbatarwa har cikin gidan taleka taga sunata shigowa dakayan
arziki wanda hjy Amina tahado su da shi tayi musu Alkawarin zata dinga zuwa tana dubashi 2⃣1⃣
don Ta amshi Adireshinsu duk da sunce zasu dinga kaishi din sanda jibril yadawo yatadda Lami
a cunkushe ya tambayeta abinda ya faru saita fitittike tana fadin sai dai azabi daya azaman
gidan nan ko ni ko shegen yaron can sunfa dawo dashi dayaya zamu yadda murayu da shegen
a gida yagyara tsayuwa yana kankance ido don Allah kada ki gaya mini zancen banza inace da
safe suka tafi da shi kina nufin sun kuma dawowa dashi tagalla masa harara to zanmaka
karyane ka shiga gidan nasu kagani mana kuma da alama da shirin zama ya dawo don
nagansu da siyayyar kayan jarirai kala kala ya shuri takalmi cikin bacin rai yayi gidan yayan
nasa ko sallama babu suna tsakar gida azaune deeje tanayiwa Ahmad gashin cibiya
2⃣2⃣ Malam sulaiman yadaga kai ya kalleshi da mamaki yana fadin lfy dai jibrilu kashigo babu ko
sallama yasamu guri yazauna yana muzurai ramsa abace yace kayi hkr yaya rainane abace
nashafa.a jinayi ance wai kadawo dashegen yaron nan me kuma yadawo yi? Ransa yabaci
amman yadanne yace ba shege yakeba sunanshi Ahmad kuma yawuce wai tunda hargashi nan
kana gani ana masa gashin cibiya haba yaya wanne irin tonon siline saikace baka taba

haihuwaba idan karin ya'ya kakeso basaikaje kadauki nawaba ko kuma kaje kauye kadauko
wasu ba Amman saika bige da dauko shege nagayamaka kada kakuma kiransa da shege
kajiko kuma naki daukar naka dan ko kuma nakauye shidin dainakeso idan kuma kaine sama
dani sainaji marar kunyar banza ..........2⃣3⃣ irin naka duk wani abu dazaka aikata na Alkhairi
saiyazamana kaidashi kake gaba wannan yaron kasan iyakacin baiwar da Allah yayimasa to
tsaya nagayamaka daga yau yashiga cikin 'ya'yana zan kuma rubuta wasiyya ko bayan na mutu
araba dukiyata kashi shidda Abashi kaso daya don Allah baihalasta Wani yagaji wani bane ba
danace yagajeni jibrilu yayi shiru cike da takaici don yasan halin yayan nasa akwai fada idan
kataboshi danhaka yamike sumi sumi yang fadin Aishike nan nidaman inaguje maka illar da
akace zama da shege yana kawowa ne inji ubanwa aihar yau kakasa kawo mini hadisi ko ayar
datace hakan nakuma gayamaka kadaina Ambaton dana Ahmad dashege kajiko yakarasa
ficewa yana gunguni babu yanda zaiyi
2⃣4⃣ malam sulaiman yacigaba dafada sokon yaro sai mace ta huroka kazo kana yiwa mutane
fiffika daga ganinka wannan bara.ayinka bane ba matarce taroshi shakiyiya kawai deeje
takwantar da murya tana fadin karabudashi Lami kam saidai Ayimata Addu.a matar da yaran
gidan bata bariba balle wannan mudai Allah yarayamana shi cikin Albarka yakoma gida cikin
borin kunya yatadda lami tsaye tana jiransa yana shiga tatareshi yaya kukayi dashi? Yasamu
guri yazauna yana dafe kunci yayi tsaki yana fadin bakiji yanda yabalbaleni dafadaba kamar
wani ubana harfa cewa yayi bazairike dana kona wani dangi sai wannan shegen ke har doka
yakafa min waina kiransa dashege ma tayamutsa fuska tana fadin maganinka kenan mara
zuciya saunawa nake gayamaka kadaure kayi gidan kanka muhuta da mulkin mallaka dan
wannan dakin biyun dayabamu ke rudinsa dayasanan kana da iko agidan aida baiyimaka haba
saikayitayi kada ka mallaki nakanka kayita zaman karoro 2⃣5⃣ Ahmad yataso yaro maicike
dakwarjini da hikima da basira wanda kowa ke kauna. Duk inda yazauna zakaga ana sonsa
iyayensa suna nuna masa gata kullum yana cikin yan uwansa suje islamiyya da dare kuma
suzauna kofar gida saida rake ko mangwaro saidai tunda yatashi ya kula da tsangwama da
kyarar da Lami da mijinta ke masa ga wani suna dasuke yawaita kiransa dashi shege amman
yakula har sauran yayyansa da kanne Lami bata kauna saidai sanda yayi shekaru ukku yagano
azabarta ko ahanya suka hadu saita rankwasheshi musane abokinsa a gidan kuma sa.ansa
tasu tazo daya sauda yakanbishi gidansu wasa kamar yanda shima yake biyoshi amman duk
sanda yabishi saita azabtar da shi har wuta ta tabawatsomasa wata rana kuwa ta kulle
abandaki wai wuni guda mamanshi na nema har kuka tafarayi tadinga zagaye unguwa sai gab
da magriba ta hankodoshi yasha kuka majina damiyau lokacin yanada shekaru biyar sanda
mamansa tagansa tarungumeshi tanafadin
2⃣6⃣ Ahmad dina inakashiga kaida nasanka bakada yawo cikin muryan kuka yake fadamta
innarsu musa ce takulle ni abandaki wai saina shaki kashi namutu narasa abinda nayimata ta
tsaneni Ummata kigayawa baba yasake mana gida mana tausayin yaron yakamata tasha bala.i
da Lami akan yaron tun yana da wata ukku da Auwalu yashiga dashi tashaka masa ruwan
kumfa ahanci har kusan dambe sukayi tundaga tadaina baiwa kowa danta ga tirtsetsen cikin
haka zata goya abinta haryayi shekara ukku saita ajiye kaninsa Rabi.u tasungumeshi abaya
don haka rigimar tayi sauki yanzu kuwa yawuce goyo duk irin tsakanin mlm dayimusu takiji
hakanan dai rayuwa taci gaba da gudana cikin wahala da azabar Lami shidai jibiril baya
dukansa Amman baya ko kallonsa don yace masa baffa saiya dokamasa harara yau ummansa

tadawo awo abakin Asibiti saita siyowa kowa kayan sanyi da mlm yabata sallahu duk tashi tafi
kyau don hoton dan bal din nanne maradona daman shi yana da son bal don haka yasuri tashi
yayi waje da gudu kai tsaye gidan jibril yashiga yana kwalawa abokinsa musa kira musa yafito
daga daki aguje mahaifiyarsa na kwalamasa kira Amman baitsayaba saida yadangana datsakar
gida inda Abokinsa Ahmad ketsaye cikin farin ciki da dariya Ahmad ke daga masa rigar yana
fadin kalli yaro babanmu ne yabaiwa umma kudi tasiyowomuna kalli harda maradona ajiki
shugaban yan kwallo duk randa zamuje filin bal da ita zani kaikuwa bakada ita musa yatsaya
turus cike da takaici saiya saki kuka mahaifiyarsa tafito daga daki dasaurinta tana fadin tsinanne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login