Showing 3001 words to 6000 words out of 9108 words
Chapter 2 - Dame Ake Ado Book 1 By Fauziyya D. Suleiman .pdf
shege dukanka yayi ko? Yagirgiza kai yana fadi a.a badukana yayiba riga babansu yasiyo masa
maihoton maradona zai dinga yin ado yanafina kyau nadaina zuwa filin kwalloma adaki
zandinga zamana jikin Ahmad yayi sanyi yakalli abokinsa yamika masa rigar yana fadin kada
kadaina zuwa don Allah garigar tawa kadinga Ado da ita yamika masa saidai tuni mahaifiyarsa
ta warce tana fadin Banza soko aibada riga ake ado ba kaga wannan tanuna rigar ana saidata
akasuwa da uba ake ado wanda shikuma ba.asaidashi akasuwa kasha kuriminka wata rana ko
rigar gwal da zinare yasanya yafita saiya tsani kanshi don baida rigar Ainihi ta mutunci
tawurgawa Ahmad rigar tanacigaba da fadin dauki tsiyarka kawuce shegen banza watarana
zakagane Abinda nake nufi hankalin yaran gabadaya yatashi duk basu fahimci komai azance
ba
yakwasa da gudu ganin tayi kansa da ice gadan gadan saida ta kaishi har babban soro sannan
takoma yanufi gidansu jikinsa sanyi kalau yana hawaye Ummansa tafito daga daki dazummar
dora girkh taci karo dashi zaune shiru gabanta yafadi don tasan yarone mai kazar kazar da
wasa tabbas bashida lfy takara dasauri tana kiran sunansa manya yaya na ganka anan zaune
shiru meke damunka yadaga kai yana kallonta idonsa yakada yayi jajir saita kuma rudewa tace
gayamini meyake damunka cikin shashshekar kuka yace innarsu musa ce takoroni don naje
nunama musa rigar da babanmu yace kisiyomana tayi ajiyar zuciya wato dai bazaka daina
shiga gidan nan ba kadaina kajiko yadagamata kai Alamar to sannan yace Amman idan musa
yakwalamini kira indan leka amman kada nashi dakinta ko? Abin yaso bata dariya wata irin
shakuwa ce tsakaninsa da musa wacce bazata iya rabasuba dan Allah ne yahadasu da
daddare suna barbaje atsakar gida suna cin abinci cikin tsakiyar hasken farin wata tuwone da
danyar kubewa wacce tasha kifi Ahmad yakai katuwar loma bakinsa yahidiye tadakyar yakalli
Ummansu tasu yana fadin Umman wai meye shege ne? Gabanta ya yanke yafadi matuka
tawaro idanu waje
........... Cike datashin hankali can kuma saitayi saurin dakewa takwantar da murya tace banace
kadaina tambaya irin wannanba Ahmad meye Amfanin wannan tambayar inace a makaranta
malaminku yace kudaina tambaya akan duk wani abu dabayada Amfani gabadaya duk tarude
jikinta har rawa yake ganin haka yasanya shima hankalinsa yatashi don baya son yabatawa
ummansa rai yace kiyi hkr umma nadaina daman innarsu musa ce naji kullum saitace mini
shege canake ma suna ne Ashe magana ce mara kyau ma takuma Rudewa tace kadaina
damuwa idan tace haka idan akace da mutum shege aiyayi wata gwaninta ne yayi dari.a yana
fadin natuna har kika hanasu cewa hakan ko? Tace yauwa yarona ashe kagane ka daina
damuwa idanta kuma cemaka kuma kada na kuma jin kalmar abankinka kada kuma ka tambaxi
wani ko malaminmu tunda kaga nagaya kako yace to umma bazan kuma tambayaba sannan
yacigaba dacin Abincinsa tayi wawiyar Ajiyar zuciya cike dafargaba saitaji duk Abinci yafita
daga kanta magabadaya tabbas dole mijinta yadauki mataki akan wannan abin idan bahakaba
saidai tabar gidan da yaranta dantayi Alkawarin har abada bazata gayawa Ahmad wayeshiba
saboda hakama tunyana dansheka ukku tadaina kaishi gidan rainon yara shugabar makarantar
ce kezuwa taganshi har gida har sanda tabar aikin agidan rainon yaran takanzo ganinsa saboda
tana masifar sonsa itama hartadinga danasanin barinsa agurinsu din gashi babu damar ta
amsheshi a lokacin dadaddare duk yaran sunyi bacci ta tashi maigidan nata wanda shima
haryafayin bacci yatashi cike da mamaki da fargaba don tun dayamma yaga ranta abace nakula
tunda maraice akwai wani Abu dakike boyemin to kinshiya fada kenan yanzu tafashe da kuka
tana fadin aidazun mabakin gaya maka haka kawai ba sai don gudun kada yaransu ji Abinda
zamu tattaunawa to wallah nagaji dazaman gidan nan na.amince kakamini haya da masifar da
ake shirin kunno mini saita kara fashewa da kuka batunyau ba nake sanarda kai irin azabar da
matar nan takeyiwa yaron nan Ahmad ba har Abin yakai nadaina sanarda kai toyau takai har
Lami kenunuwa Ahmad shi shege ne bazan yadda ba Allah wannan neman masifa ne dason
tozartani Hankalin mlm sulaiman yatashi yadinga fadin subhanallahi garin yaya hakan tafaru
tasan kuma doka ce nasanya agidan nan tunba yauba ko mijinta nace yafadi wannan maganar
zamuraba gari dashi
2⃣9⃣ DAME AKE ADO ....... ........... Dasassafe yatura yaran makanrata safe kamar yanda suka
saba duk Ranar Assabar da lahadi da babu boko saisu tafi daukar darasi amasallacin Unguwar
kaitsaye suka shiga gidan jibiril sunyi sa.a kuwa yaran gidan suma sunfice sai matar gidan
zaune akan tabarma suna ta hira suna jin sallamar su mlm suka daga kaida mamaki
dominsunsan baya shiga gidansu saita baci jibril yamike yana fadin A.a yayane sannu dazuwa
zauna mana yadaga hannu yana fadin ba wannan takawoni ba gargadi nashigo yiwa matarka
duk da nasan kasan duk abinda take aikatawa to wlh ahir dinta hawainiyarta takiyayi ramata
Lami ta dafe kirji tana fadin nikam nashiga ukku nazama shara komai aka kwaso sai ayaba mini
yanzu kuma nayi..... Rufemin baki marar kunya banza aikinfi kowa sani Abinda kikayi waike
danbakida mutunci harkike tsare yaron nan Ahmadu kina masa habaici dole duk saiyasan shiba
mune iyayensaba ko? Lailaha ilallahu nidin wlh sharri akemin yaushe nataba tareshi
nagayamasa wannan maganar kuma? Yakalli deeje yana cigaba dafadin gayamata duk abinda
tafadi tasan ya dawo kunnenmu deeje tamaimaita duk Abinda Ahmad yasanar da ita har
shegen datake cemasa sai lami tayi wuki wuki babu kuma bakin magana dontasan tafada
yanda kuma suka tsara sai take tunanin ko deejen taji nema
-------> DAME AKE ADO part 3.
3⃣0⃣ Malam sulaiman yace to yaya koharyanzu sharri ake miki eye? Mijinta ya amshe don Allah
yaya kayi hakuri kuskurene akasamu kuskuren gidanku nace kuskuren gidanku tun yaro nan
yana wata guda matarka ke cutar dashi yanzu kuma abin yanzu kuma abinda zata koma yi
kenan idan kinkwantar da hankalinki watarana zan sanarwa Ahmad wacece mahaifiyarsa kodon
yadinga yimata Addu.a ma amma sai sanda ya mallaki hankalin kanshi yatara iyali yasami
wadanda zasu debemasa kewar danginsa amman ayanzu banshirya sanardashiba don
banason hargitsa masa rayuwa yakasa karatu da.anfanar rayuwarsa idan kuma bazaki daina ba
zan saida gidan mukoma haya kowa ma yahuta don daki salwantarda rayuwa Ahmad gwara na
kare rayuwata ahaya har Abada kana jina yanuna jibirilu kaine mijinta banason jin
makamanciyar wannan magana a gidan don Allah yaya kayi hakuri wallahi tadaina insha Allah
baisaurareshiba yakalli deeje yace maza wuce mutafi duk sanda yakuma sanardake irin
wannan maganar datafito daga bakin Lami kisanar dani nikuma za.aga hukunci dazanyi wlh
suka wuce suka fice Lami tabisuda harara tanafadin aikin banza ko kunya bayaji mace
tasakoshi agaba yazo yana jaraba kaikuma takalli mijinta awulakance saiwani rawar jiki kake
kana bashi hkr yana kara kumbura to idan ancemasa shege shin karya akayi? Yanada uban
tsinanne dan mahaukaciya insha Allahu sainayi Ajalinsu aitsintacciyar mage bata mage yau
tundasafe gidan babu dadi gurin samarin gidan dasuka fara mallakar hankalinsu domin tunsafe
Ummansu batada lfy
A Iyakacin shekarun Ahmad sha ukku da sani shabiyar da Auwalu shabakwai rabi.u shabiyu
sunfahimci nakuda ce takeyi tunsafe yan uwan maman nasu mata keshige da fice anyi su tafi
makarntar boko sunkasa zuwa alokacin Auwalu yanada shekar karshe sani yana aji hudu
Ahmad yana aji daya hakama Rabi.u dayake kusan tard akemusu komai donsun tashi kamar
yanbiyu cankamar daga sama suka farajin kukan jariri suka mimmike a rude suna lekawa
amman sun kasa fita sunajiran Abasu izini saida aka kammala gyara uwar dajaririyata sannan
akwala musu kira har rige rigen fita sukeyi ganin Umman tasu tana zaune akan filo afalo kamar
ba ita ce tahaihu ba tayi kyau sai kamshin turaren wuta ketashi suna shiga ta washe baki cike
da farinciki tana dariya inna balkisu kanwar tace tace Albishirinku samarin umma Atare sukace
goro inna tayi dariya tanafadin yara saikunbani tunda nayi muku albishir yar budurwa da.aka
haifa muku wacce kuke marmari amakota sasuka saka ihu atare saida umma ta kwabesu
sannan suka natsu suka dinga amsar yarinyar suna kallo duk wanda ya.amsheta baison baiwa
dan uwansa saboda kyan yarinyar Ahmad kam kamar jira yake su fito yakwasa dagudu yayi
gurin Abokinsa musa yama manta shaf yana makaranta domin yanaimasa gorin kanne mata shi
guda biyu yake dasu Raliya yarsheka shidda da Amina yar shekara ukku kofada suke saiyayi
masa gori don haka yaga yashiga da ihunsa ko sallama babu yana fadin musa musa zokaga
kanwata nima yau Ummanmu tahaifa mana mace mekyau datafi yan gidanku..... Yatsaya turus
cike da tsoro sanda lami tafito daga daki tana muzurai kamar zata cinyeshi danye cikin tace
shege meyakawoka gidanmu tsinanne yatsaya jikinsa yana kyarma bakinsa yana rawa yace
daman..... Daman um Ummarmu ce tahaifi diya mace shine nazo nagayamasa takara
dokamasa tsawa kaitafican banza shege ummanku ko ko ummansu kana murna anhaifi mace
agidan wasu ko shashasha da baisan ko shi waye ba shege
3⃣2⃣ fice kabani guri kuma kaje kasanar da uwar rikon naka inci ubanka shege yajuya yafice
dasauri jikinsa yana rawa yana jujjuya maganganunta aransa yakasa fahimtar abinda take nufi
sukaci karo da musa azaure yakalleshh yana fadin Ashe ummanku tahaifi mace yanzu rabi.u
yake gayamin Awaje yadaure yayi yar dariya ainashiga nagayama banganka ba dokin
yarbudurwa yamantardashi Abinda innar musa tayi masa Ranar da hjy Amina tazo barka ranar
kwana biyar da haihuwa sanda zata tafi mlm sulaiman yashigo dakayan lambu masu yawan
gaske dayake sana.arshi kenan suyake saidawa kasuwar yankaba shagone dashi babba
yasamya akadibarmata mai yawa tace yabarshi yace saita tafi dashi saidai motar haya tazo
gidan domin motarta tana wurin gyara Ahmad yadaukar mata kayan yakaimata bakin titi suna
tafe suna hirar makarantarsu dasauran Abubuwa saiyace mata Anti daman inason Intambayeki
wani abu tatattara hankalinta agurinsa tace masa Uhum inajinka yagyara kayan dake kansa
yace wai meye shege da Uwar riko kuma? Hjy Amina taja wani wawan birki tatsaya cike
datashin hankali tace kai waye yake gayama wannan maganar badai ummar kaba ko ganin
tarude yanda ummansa tayi idan yasanar mata yasanya gabanshi faduwa dan Allah kada
kigayawa ummana zatamini fada daman Innarsu musa ce take gayamini kuma canake wani
abune mai Amfani shine nake tambaya tayi ajiyar zuciya don zatonta deeje kefada masa haka
tace lallai ta cika munafuka tunda take nuna batason kowa yanuna masa ba itace tahaifeshi ba
amman duk da haka har lokacin ranta abace yake ta daure tace Agaban ummarka take
gayamaka haka kuma yagirgiza kai yana fadin a.a saidai idan nashiga gidanta kuma ummana
ma tahanani shiga ranar suna yarinya taci suna Asma.u sunan da deeje kenacin idantahaifi
mace asanya mata saboda kaunarta ga mahaukaciya babar Ahmad tun washe garin suna
tafara kiranta da ma'u kwanakinsu goma da haihuwa Hjy Amina tayomusu Asubanci sundan
tsorata daganinta dasassafe amman ganin tanata wasa da dariya dayara yasanya suka fahimci
ba wani abu ne yafaruba saida yaran suka wuce makaranta sannan suka kule adaki aka kara
gaisawa suka nutsu sunajiran abinda ketafe da ita tagyara zama tace tabbas kunzama iyaye
nagari masu rikon Amana kuma kuncancanci kuyi rainon kowane irin da banzo amatsayin
shugabar gidan rainon yara ba domin nayi ritaya saidai nazo amatsayin inakaunarku dason
danku Ahmad inafatar idan nafadamuku dalilin dayasa nakeson amsarsa bazaku bata rankuba
tunda tafara magana suke kallonta jintazo wannan gaba yasanya deeje mikewa tana fadin tafdi
jam ai wlh bazai yiwu ba koshugaban kasa bai isa ya.amshi Ahmad ahannunaba clkin matukar
tashin hankali da kuka take maganar shikanshi malam din yakadu dayake namijine yasanya
yadanyi karfin hali
Yakwantar da kai yanafadin Adokar daukar yara agidan daman tanuna akwai wani lokaci da ake
karbar yaro daga iyayen rainonsa ba.asanar damuba ko kuma rainonmu kikaraina kinaganin
kinfimu iya raino hajiya takula dayanda suka shiga Rudu daman kuma tayi tunani haka zata faru
dantasan yanda suke matukar son yaron takwantarda murya tana fadin kufahimci kamar yadda
nasar da ku banzo da sunanan ma.aikaciya ba saidai yar uwa agurinku Ahmad bashida iyayen
dasuka fiku saidai inason na rikeshi nawani lokacine har zuwa sanda zai iya daukar kowacce
irin magana akwakwalwasa nasan kun san halin matar can Lami kumasha jin irin rigimar da
kuke yi da ita akan yaron to abinnata yakiyin sauki donhaka mezaihana kubani aronsa
haryagama Karatunsa na University insha Allah sannan nadawomuku dashi gabadaya suka
sauka daga kan fushin nasu dansunsan inda maganarta tasanya gaba donhaka sungano
magana tafimtar juna takawota mlm yace shin wani abune yafaru takwashe duk yanda sukayi
da Ahmad tasanar dasu sanda zai rakata tahau mota sai deeje tasanya kuka tana fadin Ahaf
ainasha gayawa mlm maganar nan matarnan batada mutunci wlh bazan yadda ba Hajiya kiyi
hakuri wlh bazan iya rabuwa da Ahmad ba sai inmutuwa ce tarabamu kifahimci Abinda nake
nufi Deeje bawai zankwacemiki Ahmad bane dawata manufa hjy Amina tafada da lallashi ganin
yanda duk Deejan tabirkice mata mlm ne ya raba gardamar dafadin ke hajiya kiyi hakuri dan wlh
rabamu da Ahmad babbar matsalane sannan hakan ma zai iya tona Asirin dakike son Rufewa
indai lami ce matsala to zanyi maganinta ayau ba sai gobe ba dakyar suka shawo kanta ta
amince zata barshi amman dole tace taza yiwa Lami kashedi da barazana don haka tare suka
shiga gidan Lami da ita lami tamike jiki yana rawa tashimfida musu tabarma dan Allah yayita
datsoron Hukuma tasan tsaf za.a iya daureta hajiya ce tafara magana cikin bacin rai kinfi kowa
sanin laifinki bawai rarrashinki nazo yi ko rokon kiba a.a umurni ne nake baki abinda kikayiwa
yaron nan yasarnar damu cikin rawar murya tace wai menayi mlm sulaiman ya yunkura da
bacin rai zaiyi magana hajiya Amina datakatar dashi takalli lami tana fadin Kinmance sanda
yashigo gayawa abonkinsa musa haihuwa abinda kikace to zakiyi bayani agaban hukuma tunda
tunaninki rashin mutunci saita mike tsaye Hankali jibirilu yatashi yamike dasauri yana fadin a.ah
hajiya baza.ayi hakaba tabbas tayi kuskure ayimata afuwa dan Allah yaya kasanya baki Lami
kuwa tuni tafashe dakuka tagigice mlm sulaiman yayi dariya aransa yana fadin fitsarar riyar
banza saida suka wanasu sannan tayadda tajanye sanarda hukumar yansanda wannan
tasanya tadaina kiran Ahmad da shege koda sunhadu ahanya bata kyarar sa saidan harara
kawai gabaki daya yaran sundauki soyayyar su sundora kan ma.u shekarunta biyar akasanxata
aprimary saidai kullum sai dai kullum sai anyi dambe da ita kamar dage yawanfadan dasukeyi
da raliya yasanya ummansu tayimasa kashedi akanta don kullum
Dan kullum Lami ahanyar kawo kara take tayita zage zage da gore gore kalala dole tasanya
yadaina kulasu Rayuwa yin Allah ayanzu haka Ahmad yana BUK takano inda yake karatunsa
akan computar science Sani kam diploma yayi anan FCE sai yayi sa.a yasamu yasamu aiki
awani kamfani maizaman kansa shikuwa Auwalu makarantar aiki tsafta yayi HND yabude
chemist anan jikin gidansu yakuma samu aiki a temprary rabi u kam yanbokone nahakika ma.u
kam ana aji daya a secondary school saikara firirita ake da iyayi da gwalli tafi kowa kokari a
ajinsu gaba daya kai harma acikin tsaran ajinta itace kedaukar na daya wannan yake karamata
soyuwa awurin yayyanta kafin ummansu ko babanta yayimata abu daya sunmata goma
dominshi idan yatashi saiya hada dasu Raliya danhaka tafisu komai Raliya datake ganin itace
budurwa dayadace tayi kwalliya sai taga ma.u tafita dawani yammaci lokacin ma.u tadawo hutu
domin makarantar kwana take tataso daga islamiyya tana rike da kur.ani tahango lariya taci
kwalliya tanufi shagon sisko wani dangayene a Unguwartasu da inmace kekulasu ake ganinta
mara kamunkai dan haka tanaganin Raliya tashiga shagon sisko jikinta yadauki rawa hankalinta
baikara tashiba saida taga saida ta hango sisko yadan leko yakalli gabas da yamma sannan
yaja kofar shagon nasa dasauri ya kulle tayi dum dum cike da tsoro da fargaba tayi hanyar
gidansu dasauri tasanarwa da yayyanta tayi sa.a ta tadda Ahmad da musa akofar gida zaune
suna hira jikinta yana rawa idonta nazubda hawaye tanufesu Ahmad ne ya farga da ita yakalleta
da mamaki yana fadin yadai ma.un baba lfy cikin rawar murya tace Raliya Raliya ce tashiga
dakin sisko suka mike atare arude suna fadin Raliya zomuje saidai wani Abin bakinciki sanda
suka isa kofar shagon suka hango cincirindon mutane ashe wani saurayi yaga sanda tashiga
darufe kofar da akayi ya gayyato wasu matasa aka balle kofar dakyar suka barta tadaura zani
suna mata ihu suka fito da ita tanufi hanyar gida tana kuka shikuwa sisko rufeshi sukayi da duka
Ahmad da musa suka isowurin cike da bacinrai tundaga nan suka zare belt dinsu suka fara
narkarta tana ihu tanufi gida da gudu Ahmad yarufamata baya shiko musa takaici ya isheshi
yaga garayaje yakoyawa sisko hankali tashiga gidansu dagudu tana ihu daga itasai daurin kirji
yankayanta data dauko duk tawatsar dan zafi duka yabita hargidan nasu yana dukanta tana ihu
lami tafito daga daki arude tana fadin meyene yake faruwa tatsaya turus ganin Ahmad nadukan
Raliya har cikin gida wata zuciya ta ciyota ta isa dasauri
3⃣5⃣ ta angajeshi tana fadin shege dan iska mediyata tayimaka dazaka biyota kana dukanta
tamike cike damamakin ganin diyar tata daga ita sai daurin kirjg Ahmad yamike yataso daga
cikin kwanikan wanke wanke data hankadashi yana karkade jikinsa ya isa kusa da ita yana
fadin inna wannan yarinyar yau ta tona asirin gidannan ta tozartamu ashagon sisko aka kamata
yara suka rakota suna mata ihu meyafi wannan takaici da tozarta sunan gidannan yakarasa
maganar da kunan rai Lami takalleshi cike da wani irin bakin ciki data kasa rikewa tace Ahayye
yaufa karin maganar hausawa tafito SHEGE YANA YI DAMAI ZINA don ankama Raliya
ashagon sisko zaka biyota kana mata wannan dukan kaine kafi cancanta da adaka ba Raliya ba
Shege irinka ne zaitonawa maiyin zina asiri cikin tada jijiyar wuya take magana musa dayashigo
bakomai ahannunsa ya isa cike da bacin rai dadamuwa ganin yanda Ahmad ya tsaya sororo
yana kallonta cike da madaukakin mamaki donshi sam baifahimci tana daurewa diyarta gindi ne
akan abin da ta.aikata musa ne yace haba inna baidace kidaurewa yarinyar nan gindiba har
kidinga ciwa Ahmad mutunci ba kai rufemin baki da.ace kai ko Auwalu ko sani suka kamo
yarimyar nan dawani banzan damuba tunda ku kowa yasan "ya"yan halak ne ba shegu ba
amman wannan yaron shege ne zai aibata diyar da akahaifa tahanyar Auren sunna ta Nuna
Ahmad gaba daya suka tsaya suna kallonta cike da fargaba tashin Hankali musa