Showing 6001 words to 9000 words out of 9108 words

Chapter 3 - Dame Ake Ado Book 1 By Fauziyya D. Suleiman .pdf

08 Jul 2025

843

yafara
magana cikin kaduwa da gigita inna kazafi baida kyau kada tunanin nemawa Raliya kariya
yasanya kifita daga haiyyacinki harkije ki fadi abinda baidaceba ninasan Ahmad dan gidan baffa
sulaiman ne kuma...... Kai tafi can toyau zanfasa kwan da.akajima ana kiwonsa yau zansanarda
kai abinda bakusaniba saunawa nake gayamuku kudaina damuwa dan Ahmad yafiku wani abu
kasha damuwa danyafika kokari kasha damuwa danyafika kaya nasha gayamaka duk dayafika
aikin banza ne tunda ku kunada abin ado wato uba shikuwa shege ne dan mahaukaciya wacce
ba.asan daga inda ta fitoba ........ Innalillahiwainna ilaihi rajuun lahaula walakuwati illah billah
muryan Ummansu Deeje ta ankardasu wacce ta shigon gidan gigice jiyo hayaniyar da akeyi
taleko taga abinda ke faruwa Ahmad kam mutuwar tsaye yayi yakasa motsawa daga inda yake
tabbas yasha tunanin maganganu Lami dake fada akansa Ummansa da Hjy Amina suna tauye
masa tunaninsa wannan ne yasanya hankalinsa ketashi aduk sanda sukaji ance masa shege
faduwar da Ummansa tayi jib dafasa ihun ma.u ne yadawo dashi cikin hayyacinsa
Yanufeta da gudu kamar yanda yaga musa yayi idonta yabirkice yajuye da alama banumfashi a
tattare da ita cikin karaji ma.u kefadin umma kada kimutu kibarmu dan Allah Umma kitashi
shikam gaba daya tunaninsa da basirar sa suntushe yakasa cewa komai sai hawaye da idonsa
keyi musa ne yamike dagudu yadebo ruwa abuta ya yayyafa mata amman abanza bata ko
motsi sai asannan ya iya bude baki yana fadin Umma kada kimutu kece Uwata maisona idan
kika mutu zankasance banida kowa kitashi Umma kici gaba darikeni a matsayanin danki na
cikinki kada ki mutu Umma na yana kuka da majina yake wannan magana musa ne yayi dabara
fita dagudu yanufi gurin Auwalu dake chemist wanda bai san wainar da ake toyawaba Lami kam
tayi tsuru tsuru tsaye da fargabar da tashin hankalin abinda zaije yazo Raliya kam sai sharbar
kuka take yi cike da takaici da dana sani Auwalu yashigo aguje hannunsa rike da fanfon auna
jini ya isa gurin mahaifiyar tasa yahada bakinsa danata yafara bata taimakon gaggawa da ake
kira da mouth to mouth yatallafo kanta cikin ikon Allah saiga numfashin nata yadawo tabude
idonta dasauri saita mike zaune kamar ba itace tasuma ba yanzu takamo Ahmad tana fadin
karya take nice nahaifeka ba mahaukaciya ba ranar dana haifeka ne tazo nan gidan katambayi
malam kaji ainasha gayamaka Lami makaryaciyace tana kuka take maganar shima Ahmad
kuka yakeyi Auwalu da baisan abinda ke faruwa ba yamike cike da mamaki yana fadin wai
meye yafaru me yasameki Umma? Arude yake maganar saita mike cikin karfin hali tana fadin
babu komai kuzo muje gida banason kara kallon fuskar Azzalumar matarnan tanuna Lami da
hannunta Ahmad yarirriketa dakafarsa suka nufi gidansu harlokacin musa Ahmad da ma.u kuka
suke Lami ji take yi kamar maganar tadawo tamaidata cikin ta donbatasan abinda zaibiyo baya
ba amman saboda tsabar taurin rai saida taga sunfice eh gaskiya ce nafada sai dai Akasheni

wallahi haka kawai shege zaitonawa diyata Asiri yanda yatona m
ini asiri nima natona masa
3⃣7⃣ koda suka iso gidan abin datake maimaitawa kenan Auwalu yace Umma mema tacene?
Meyafaru ne? Cikin kuka tace Azzalumace Lami waicewa tayi Ahmad shege ne bayan nice
nahaifeshi da cikina cewa tayi dan mahaukaciyane bayan gashi dana ne ranar dana haifeshi
ranar mahaukaciya tazo nan gidan bari kuganima na dauko muku takaddar dazaku san danane
saita mike jiki yana rawa takama lalube saidai abinda batasaniba shaidar datake son kare ta
itace zata kara sanyawa abin yafito fili tunda duk mutumin dayakasance danka dakahaifa
aibabu bukatar wata shaidar takarda arubuce gashi ita batasan abinda akarubuta na yarjejeniya
bace baiwar Allah saida tafito dakayan wata tsohuwar adaka sannan takwakulo wata takarda
acan kasan jikinta yana rawa tamikama Ahmad tana fadin karanta kagani karya takeyi nice
babarka ya.amsa yafara karantawa bawani abu Acikiba illah yarjejeni sun amsheshi zasu
rikeshi kuma duma duplicate ce aka basu da.alamu original din tana can inda suka basu shi
kukansa yakuma karuwa hankalinsa yakuma tashi tabbas ba sune iyayensa ba Auwalu ya
warce takardar yafara karantowa yakalli mahaifiyar tasu datausayi datashin hankali rashin ilimi
datayine yasanya batasan Abinda takardar takunsa ba data sani data kara boye takardar cikin
sheshshekar kuka yake fadin Umma wannan takardar tana nuna yarjejeniya dakukayi ne
asanda zaku amshi wani yaro nasan ba Ahmad bane mantawa kikayi kika fito da ita sai
asannan tagano wautar datayi amman taji dadin yanda Auwalu din yakawo mata mafita dasauri
tace ahaf namanta wannan ajiya ce akabani bari nazakulo wancan bani na adana wannan din
kafin masu ita suzo nema ta.amsa dasauri tanufi akwatin tana cigaba dalalube tsanananin
tausayin dasoyaryar Ummansu tashigeshi yakula da idan baiyi wani abuba zata iya rasa
hankalinta ko wani yashigeta yanufeta inda take tazakulo kaya daga cikin tsohuwar adakar
yadafa bayanta yana kokarin kwantar mata da hankali yace Umma kidaina lalube nifa nasan
kece mahaifiyata bakece kikasha gayamin innarsu musa karya ne da ita ba tayaya zanyadda
damaganarta dake ba uwataba ce ba saikin nunamini watarana dakuma saiwani yayi mini gori
acikin layin nan kishare maganarta ki kwanta ki huta tana son bata miki raine don ankamo
diyarta dakin sisko suna iskanci tadago cike da matsananci farinciki tana fadin haba ainasan
saboda mugunta take son rabani dakai tahadda samaka wani ciwon dazan rasaka bakayadda
da abinda taceba kenan? Yadaga mata kai yana kokarin kakalo murmushi wannan yasanya
tadan sami sassauci aranta daga wannan karon anyita takare ko ita ko lami dole dayan yabar
gidan dakyar ta iya kyalesu suka tafi masallaci bada farali gani take yi kamar daga can bazata
koma ganin Ahmad dinta ba saidai shi yana sallah yana kuka ransa yayi baki ashe shi yanata
barankadama da homa ashe shi shege ne bashida kowa aduniya shin wacece mahaifiyarsa
datayi shegensa koda yake ance mahaukaciya ce to waye mara imani dayayi mata ciki har
kawo shi duniya
3⃣8⃣ tana ina ita mahaukaciyar ta warkene kohar yanzu tana cikin haukan? Yakasa natsuwa daga
masallaci yalallaba yafice yayi gabas yana ta tafiya baisan inda zaidosaba Anshirya cin abinci
yanda aka saba amman babu Ahmad tun Ummansu nasanya rai zaishigo har tafara karaya
bacin rai datake kokarin boyewa yafara yabaiyana tadinga sanyawa ana nemansa sam tahana
kowa cin Abinci nan malam yashigo cike da taikaci yana fadin wai Ahmad yaro ne dazaki sanya
ayi ta wani nemansa saika ce wanda zaibata kinsa dai bazai wuce yana gidan yaron Abokinsa
Abdullahi ba cikin sheshshekar kuka basan abinda nasaniba tabbas idan Ahmad bai bata ba to

zaigudu kuwa saita fashe dakuka cikin mamaki yakd kallonta hasken wutar lantarki da.aka kawo
yanafadin wace irin magana kike yi khadijatu kamar wacce tayi gamo memukayi masa da zai
gujemu cikin kuka tace yau Lami tasanar da Ahmad shi shege ne tasanar da shi banice
nahaifeshi ba tagayamasa shidan mahaukaciyane baniba... Kuka take yi sosai kamar wata
karamar yarinya malam yamike cikin tashin hankali yana fadin mekikeson sanar dani khadija
inanilillahi wainna ilaihi rajuun yanzu ina Ahmadu bari nanemoshi... Baijira yi jin abinda zatace
ba ya fice sani da salisu da rabi.u ne agurin sunkuma riga sun fahimci abinda ake anufi saidai
harkarfen dayan dare babu Ahmad babu labarinsa hankalin kowa yatashi sanda malam
sulaiman yashigo gidan Umma Deeje tamike tana fadin yaya dai malam kungan shi yagirgiza
kai cike da damuwa mai tsanani takuma wurga masa tambaya hargidansu Abdullahi mlm kunje
munje taredashi muke ta nemansa ma yanzu haka nabarsu shida Auwalu suna ta bin gidajen
Abokanansu Akanme zaku wahalarda kanku wanda yabata ake nema bawanda yagudu ba
Ahmad bazaije inda zaku ganshi ba abinda najima ina nusar da kai kenan wlh Lami
bamasoyiyar mu bace ko Ahmadu yadawo ko baidawoba nagama zama a gidannan yanda
Ahmad yatafi haka nima zatasalwantar min yarana tana magana tana kuka ya hasala matuka
gaya yama rasa hukunci dazaiyanke sai kawai yamike cikin fushi yanufi gidansu Lami
Yanashiga yakama kwada sallama kamar zaitsaga gidan dafarko sunyi shuru adaki don lami
tagayamasa tabargazar dayayi duk da lika abin asharri yayiwa diyarta ammam duk da haka
mijin nata yabata rashin gaskiya don yana tsoron abin da zaije yazo can dai sai ga mlm jibiril
yabayyana cike da tsoro mlm sulaiman yagalla masu harara yana fadin Barkanku Ahmad
yagudu yabace mana yarabu da mu saidai kusani jibril yanda Ahmad yarabu damu tokaima
karabu da komai nawa kashirya kayanka agobe zansanya gidan kasuwa tunda dai zamanmu
tare baida Amfani sai haddasa masifa nima nahakura dazaman gidan gabadaya hankalin jibril
yatashi idan yarabu dan uwansa inazaisoma rayuwarsa waye zai iyaciga dabashi taimakon
dayake bashi tabbas shikansa yanzu lami ta isheshi yabi dan uwansa yana bashi hakuri amman
ina tuni yafice yadawo tsakar gidan yayi duru duru cike da tashim hankali saiyafada dakin
dasauri yatadda lami zaune tayi wuki wuki tana zare ido yana shiga tafara magana ka kwantar
da hankalinka malam indai akan gidane muje mukama haya tunda ai....... Rufemin baki
munafuka sau nawa nake cemiki kicire hannunki daga kan maganar yaran nan yaji koshi waye
aduniya amman saida kika fadamasa to tsaya kiji banida wani gata dayawuce na Allah da dan
uwana daya daukoni daga cikin wahala yanemo mini aurenki yaci gaba da dawainiya dani
kisani idan na bar nan banida wurin zuwa don haka kedai da kika janyowa kanki kece zakibar
gidan dolenki kuwa takalleshi damamaki matuka tana fadin malam akanfadin gaskiya kake
wannan furucin kinga banja dagon zance dakeba kiwuce kawai nasakeki yana kaiwa nan ya fice
daga dakin .......4⃣0⃣ Lami tafashe da kuka tana fadin na shiga ukku yanzu akan dan shege har
akasane natsani wannan yaro daman nasan zuwanshi gidannan Annoba ce kuma harzuwa
yanzu banyi nadamar fadin cewar shi shege neba dawannan tadinga sambatu tana kuka
Sunwayi gari cikin tashin hankali kam tun Asuba tabar gidan saboda yanda jibril ketayimata
kwakwazo hankalin yayanta yatashi matuka musamman Raliya da Amina musa kam yanajin
ciwo sakin mahaifiyar tasa Amman yanajin takaicin Abinda ta.aikata gaba daya gidan angaza
karyawa kowa yanacikin damuwa ma'u kam kuka takeyi tana fadin danasani dabangayawa
yaya Ahmad abinda raliya keyiba duk da deeje tana cikin tashin hankali hakan baihanata
rarrashin diyar tata ba tunda suka dawo daga masallaci jibril yatare malam yana kara bashi hkr

dasanar dashi hukunci daya yanke tun dare jiya malam sulaiman yakalli dan uwansa cike da
tashin hankali yace subhanallahi meya sanya ka.aikata haka nima bacin raine yasanya fadin
abinda nafada kayi hakuri da abinda nayimaka dankai dan uwa nane jinina daban isa
nasakakaba Dejee kam bataji ko dar da mutuwar auren lamiba tunda tarasa danta komaima
yafaru wajen misalin karfe goma sai Hajiya Amina ta iso akidime don yan dubo Ahmad sun iso
hargidanta duk yanda deeje kekorin taddanne zuciyarta saida ta fashe dakuka ganin hjy Amina
tana fadin yagudu hjy bamusa inda yashigaba danasani munbakishi ina zankai hakkin yaron
nan tadafa kafadarta cikin kwantar da murya take fadin kidaina wannan maganar deeje ko ina
yake aibazaiwuce kaddararshi ba Nakuma tabbata duk inda Ahmad yake zaidawo inda kuke
muyi Addu.a kalaman hjy ne suka dan kwantar mata da hankali tace kuma adaina zuwa
nemansa zaidawo dakanshi tasoyin maganin lami saidai tasamu lbr sakin da.akayimata
kwanaki ukku suka cika cikin tashin hankali abincin kirki babu maici agidan Ranar kwana na
hudu datafiyar tasa ma.u tadawo daga kai markaden gero na kokon da yamma sakaliya tana
tafe tarera wakokinta tahangoshi tafe da kayansa tunna ranar dayatafi yarame yayi duhu dakyar
yake tafiya kamar me ciwon kafa batasan sanda ta watsar da robar markadan ta falla gida
dagudu tana fadin Umma gayaya Ahmad umman dake tukin tuwo tafito da.azama jikinta sai
kyarma yake harzaninta yana neman faduwa darawar baki tace A ina kikanshi gashinan
zaishigo gidannan yashigo gidan dasallama
4⃣1⃣ yatsaya turus cikeda farin ciki ganin ummansa itama tsayawa tayi turus tana kallonshi kuma
kome tatuna saita nufeshi da sauri ta wanka masa mari sai kuma tafashe dakuka tajuya gida da
sauri ma.u dake tsaye ta zuba masa ido wanda ya ciko da kwalla shima idon ya zubamata yana
hawaye shida kansa yasan abin da yayi bai kyauta ba cikin kuka tace yaya Ahmad mai yasanya
ka gudu ka barmu Umma ta daina bacci tadaina cin Abinci baba yadaina fita kasuwa yaya
Auwalu yadaina zama a chemist sani yadaina zuwa kasuwa ni idan akaturani makaranta bana
zuwa sai intafi nemanka ranar har gwammaja naje dakafuna nemanka memukayimaka kagudu
kabarmu yakamo yarinyar maicike dawayo ya rungume yana kuka yafadin ba gudowa nayiba
tafiya nayi nasamu natsuwar zuciya ta saidai bansamuba zama daku shine nutsuwar zuciyata
yamike hannunta suka nufi cikin gida saidai duk yanda yaso yayi wa Umma magana taki
sauraronsa tayi fishi dashi maitsanani wanda yakara tada masa hankali Malam sulaiman
yagyara zama yana fadin tabbas hjy Amina tayi gaskiya tace mini Ahmad bazai iyabarinmuba
munyi masa rikon dako mahaifiyarsa ce tadawo duniya bazatayimasa irinsa ba saidai nayi
mamaki dakabarmu Ahmad shinkanaganin kayimana adalci yadukar dakai cikin kuka yake fadin
kuyafemin baba tabbas nasan na.aikata muku laifi mai girma wani irin tausayi yakama malam
mai tsanani shikadai yasan Abinda yakeji Azuciyar sa game da yaron
4⃣2⃣ kwanaki sunja ga Lami tun tana ganin abin kamar wasa har karamar magana tazama babba
domin sam mlm jibril yaki zuwa biko sai abin yazamomasa kamar gaba takaishi domin daga
gidan yayansa yayansa akefitomasa da girki maidadi wanda yafi namatar sa Su raliya kam
kullum saita saci jiki ta tafi gurin uwarta suyita ta kitsa mugunta dadai lami ta kula abin bana
wasa baneba hankalinta yafara tashi ga wahalar gidan tafara damunta da yunwa don haka
tafara bin kan mahaifinta
DAME AKE ADO PART 4

Saidai mlm jibril yace bashi za.aba hankuriba yayansa za.aje abaiwa idan yahakura shikenan

dan bawan Allah baiyi kasa agwiwaba yanufi gurin mlm sulaiman din darajar tsohon tasanya
yace shikenan komai yawuce amman sujawa Lami kunne matuka domin bazasu kuma yadda
da irin wannan rashin tarbiya ba haka tsohon yatafi yana godiya haka aka tarkato Lami aka
dawo da ita su Raliya tamkar sallah shi kuwa mlm jibril sai cika yake domin wahala takuma
dawo masa sabuwa dal yanayin Rayuwar Ahmad tasanya gaba daya yadukufa kan karatunsa
bashida lokacin komai sai karatu idan kaga yana dariya yana cikin gidan donka da Ummansa ta
damu ahaka har suka shiga aji hudu Ummi sada itace yariyar data dafe masa tun farkon
shigowar su take bibbiyarsa dafarko dasigar koyon karatu tashige shi har shakuwa tashiga
tsakaninsu ahankali tajuya soyayya kusan kowa yasan halin da ake ciki cikin dakinsa ma katon
hoton tane kyakykyawa ce fara da ita duk da bata cika tsayiba Ummi ce kadai kesanyashi
farinciki idan yana cikin damuwa yana son Ummi matuka musamman yanda iyayanta suka
daukeshi kamar su suka haifeshi yana tsaye adaki yana kallon hotonshi na ranar dasuka
kammala karatu yana sanye da kaya wadanda digiri yan uwansa sun baibayeshi cike da farin
ciki ga hajiya Amina agefe dakuma babansa ga ma'u nan anyimata kwalliya yana matukar son
hoton arayuwarsa domin yasanshi dangata ne lokuta dadama kalmar shege tafado masa
yatuna wannan matsayin dayake kai yakuma tuno yanda yan uwansa da iyayensa kesonshi sai
yaji zuciyarsa tayi wasai baitaba kukan rashin dangiba sakamakonsa yayi kyau matuka har an
turashi jahar taraba bautar kasa hankalin Ummi gabadaya yatashi domin batason yayi nisa da
ita aganinta shekara tayi yawa saida yadinga tausarta dasu ishak sannan tahakura itakam tayi
sa.a batayi nisa ba jigawa akaturata amman bakincikin rabuwa damasoyinta yaraunana
farincikinta kwanci tashi kamar yaune shekara guda sai gashi haryadawo umma tayi murna
matuka hajiya Amina kamar itace tayo sabon digiri sai murna take yi da Alfari ta amshi
takardunsa daniyar tanemasa aiki saidai abin yaci tura domin samun aiki agarin saika shirya
daga karshe dai tasamomishi aiki n gidan wani mai dasuke mutunci da maigidanta da maigidan
man kwarai dagaske Alhaji nura kwangila yayi murna kwarai da samu don babu abinda yake
buri illah yafara cin gashin kansa yataimakawa iyayensa kamar yanda suka yimasa duk sanda
yatuno iri dawainiyar dasukayi dashi saiyaji son su yakuma cika ranshi Lami tayi tagama
tsakaninta dashi saikallo sai harara domin tunbayan dawowarta gidan tashiga taitayinta saidai
samun aikin nasa yatsaya aranta matuka domin cikin kankani lokaci komai nasa yasauya
yakuma yama dan gayu cikin lokaci kankani yasayi babur dinsa irin wanda samarin zamani ke
yayi tsutsun soyayya ...
4⃣4⃣ ba umma ba hatta mlm yadaina kukan babu domin Auwalu da sani da Ahmad sun isheshi
kowa akwai abinda yaware yake siya awata don ma dai Auwalu yatattago Aure amman duk da
haka yana iyakacin kokarinsa ko kishin yanda rayuwar gidan ke gudana Lami batayi nata sanya
yayanta suzama mutane nagari idan kafidda musa saishegen kishin tsiya da kyashi Raliya kam
likkafa taci gaba tazama gogaggiyar yarduniya domin duk tayi billicin tayi fari tas kamar gauta
ga tara samari kala kala akofar gidan tun yayyen suna fada har sun gaji sun watsar domin lami
ke dauremata gindi tace anayiwa hassada dakyashi cikin wannan sati aka kai kayan Auren
Ahmad gidansu ummi saidai mahaifinta yatsaida lokacin biki gabadaya wata hudu wannan abin
yafi yiwa Ahmad da ummi dadi domin sunkagu sumallaki junansu Abba da umma kuwa sunyi
farinciki da hakan Ahmad kam yadage hada kayan Aure sai Alokacin yagano kokarin da Auwalu
yayi dominshi har gini mayayi koda yake tuni yazama cikakken ma.aikaci yana da albashi me
kyau shi kam haya zaikama dole amman gaskiya ba zai kama hayar karamin gida ba domin

yasan Umminsa yar gayuce gwara ya kama gidan da zaiburgeta saura wata daya biki yagama
hada kayan lefensa yayi kokari matuka domin saida yayi akwatuna hudu sanda yakawowa su
umma kaya sun cika mamakin kokarinsa daganan yafara kokarin nemo gida da kudin haya
dama babansa ya sauke masa sadaki domin tun sanda za.akai kayan lefe yabada dubu ashirin
na sadaki biki yarage sauran sati biyu yasami gidan sa makyau acan Unguwar gaida mai
dakuna madaidata guda ukku da kichen da bandaki dangin Ummi harsunzo sun gani sunyaba
komai gabadaya gidan ansanya masa wuta yaimasa fenti maikyau saidai abinda yafi damunsa
da za.ayi bikinsa ma.u bataman domin suna gab dafara jarabawa tunsauran kwana goma biki
yafara rabao iv nabiki yabaiwa Ummi nata anshirya shagali daidai na takala ma'u kam harkuka
tayi amakaranta domin tana lissafin bikin yayanta yazo saura sati guda biki da magriba Umma
tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login