Showing 1 words to 3000 words out of 37712 words

Chapter 1 - 'DAN HALAK Book Complete (By ummu maher)miss green.pdf

08 Jul 2025

1873

[7/1, 11:52 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)🍃: *_�D'AN HALAK�_*

*_UMMU MAHER(MRS GREEN)🍃_*

~Wattpad~
Rabiatu333

~Arewabooks~
Rabiattu0444

1
_Destiny_
Around 5:pm

..........da mugun sauri ya d'ago yana kallon Salima sannan ya ce"yanzu Salima ni kike kira da
d'an shege"?.

Ta wani juya idonta sannan ta ce" eh na fad'a idan k'arya ne ka musa mana"?.

Ya k'ara kallonta akaro na biyu, yaji tamkar zai bugeta saboda bak'in ciki yana da muguwar
zuciya Idan ya ce zai yi magana zai iya shak'eta ta mutu, yayi saurin rintse idonsa sannan ya
ce" get out of my side".
  Ya fad'i hakan tamkar zai bugeta, ai kuwa ta firgita ta fita da saurin gaske saboda tsoronsa
takeji da gaske saboda Haidar namiji ne guda acikin maza.

   Go ahead ya bawa direbansa, nan da nan yaja motarsa sukayi gaba yana jin wani irin suya
aransa tamkar zai mutu, kiran sunan Allah ya ke Amma shi kad'ai yasan masifar da ya ke ciki
zuciyarsa sai k'una take hannunsa d'aya yana kan xuciyarsa har sukazo dai dai wata plaza
tamfatsetsiya.
Ya dakatar da direbansa ya tsaya, da sauri direban ya fito domin bud'e masa ya dakatar dashi
da Sauri ya fito ya bud'e da kansa yana wani juya kyakkyawan eyes d'insa Wanda kallo d'aya
za kayi masa ka gane yana cikin matsala, domin sun kad'a sunyi jawur jijiyoyin kansa sun tashi
sunyi rud'u rud'u kallo d'aya zai baka tausayi ayanayin da ya ke ciki.
  'HAIDAR SHOPRITE'

Ya rintse idonsa yana jin wani irin mugun haushin tarin dukiyar da Allah yayi masa gashi bata
amfanesa wajen samun macen da zai aura ba haryanzu duk don saboda wani rufaffan sirri
Wanda fad'arsa ma bai da wani amfani, a iya k'iyasinsa ya nemi aure ya kai sau goma, sai Abu
yayi nisa sai ya lalace saboda wannan bak'in dalilin Wanda baki ba zai iya furtawa ba.
Ya goge kwallar da ta zubo masa, ya fara tafiya cikin yanayin tafiyarsa me kama da tafiyar

hawainiya.

Aminu direbansa yayi magana afili ya ce" Allah sarki bawan Allah, haka kai kuma Allah ya tsara
maka ga kud'i ga kyau ga ilimi Amma sai Allah ya yi maka wannan babbar jarabta ta rashin
samun matar aure Wanda ko nasaba d'aya ka had'a acikin hud'un nan zaka samu matar aure,
Amma sai gashi duk basa wani amfani awajen matan.
Tunda ya shigo kowa ya fara kai gaisuwa wajen babban oga Boss Haidar, sunan da suke fad'a
masa kenan saboda yanayinsa na rashin son yin magana da kuma iya had'e girar sama da ta
k'asa.

Tuni ya isa babban ofishin babban me kula masa da wannan babbar plazar.

Azaune ya samesa yana ta aikin ciccike wasu takaddu da Sanya hannu aciki, yana ganinsa ya
saki fara yana ce wa" Boss wallahi yanzu Ina aikin nan amma tunaninka nake, saboda akwai
wasu kaya da suka shigo tun jiya kuma kai nake jira ka sanya Han......"

Saurin dakatar dashi yayi, yana me zama ad'aya daga cikin manyan tamfatsa tamfatsan
manyan kujerun da suke k'unshe cikin ofishin Wanda sanyin A/c ma kad'ai ya isa ka tabbatar
abin na manya ne.

Hammud ya ce" Boss da damuwa kan fuskarsa fa? Ko dai Salima ce"?.

Ya furzar da numfashi sannan ya nisa ya ce" triple ayau na tabbatar da abinda mutane suke
fad'a akaina, da duk gani nake zancan banza ne da shirme Ashe gaskiya ne domin masu iya
magana sunce wak'a abakin me ita tafi dad'i, domin alokacin da ake fad'ar wannan mummunar
maganar akaina d'auka nake babu mak'iyina irinsa, Amma ayanzu na gane masoyana ne su,
tunda masu son abin hannuna basa iya fad'amin gaskiya sai dai suyimin shiru suna d'aukata
shasha, domin yau Salima ta fad'a mini ba zata aureni ba tunda ba nida Uba duk ranar Dana
nemo waye ubana inzo in aureta ita kuma ashirye take".

Hammud yayi shiru, yaji k'irjinsa yayi masa wani mugun nauyi ko kusa baya San ganin amininsa
cikin matsala Amma ya zamar masa dole awannan karon yayi wani Abu domin ceto abokinsa
daga halaka.

Ya nisa ya ce" Boss inason ka Sanya aranka wannan itace k'addararka, Kuma baka isa ka 
goge taba domin kuwa daman can an rubutashi alauhul mahfuz kaga babu wani bawan daya
isa ya goge sa, yin hak'uri shi ne mafita Amma ka daina sanya damuwa sannan inason ka nutsu
ka koma wajen Ammi ka k'ara tambayarta waye mahaifinka? Watak'ila awannan gab'ar asamu
cigaba".

Ya d'an ja numfashi me fasali, sannan ya ce" kana ganin zan iya zuwa in sameta awannan
gab'ar? Ka manta abinda yake tsakanina da ita ahalin yanzu? Rabon da mu had'u yau wata

hud'u kenan, nak'i zuwa Inda take tun bayan da nak'i karb'ar labarin da ta bani akaina, domin
kuwa gani nake tamkar ba haka bane Idan kuwa hakane me ya hanata sanarmin tunda can"?.

"Duk wannan ba dabara bace Boss ba'a yiwa iyaye haka fa? Musamman ma Uwa, lallab'a
lamarinta ake asannu domin gudun b'acin ransu tun sanda ka fad'amin na ce kaje ka bata
hak'uri shi ne ka k'i? Ai Idan zaka yiwa wani zafin ranka bai kamata ka yiwa Ammi ba, tasha gori
da habaici da zagi tun daga samuwarka har zuwa yanzu bata tab'a jin dad'in rayuwarta ba,
kuma duk akanka haba Boss ka dinga sassauta zuciyarka domin gudun fad'awa halaka, kuma
yin aure a irin wannan halin naka, domin su mata sunfi son namiji me sauk'in zuciya da nuna
kulawa akoda yaushe, sai kaga mace ta sakar maka dukkanin abinda ya shafi rayuwarta harma
da abinda baka tab'a tunani ba".

Ya gamsu da abinda ya ce, ammanfa wannan zafin zuciyar tashi baisan yadda zai yi dashi ba,
domin kuwa haka Allah ya yisa awani lokacin ma Idan ransa ya b'aci sai yaji tamkar zai yi hauka
saboda tsabar k'uncin abinda ya keji.

Hammud ya ce" akwai k'anwata Zahra, tana nan makarantar ABU Zaria ina ganin me zai hana
Idan ta dawo ka neme ta? Tunda yarinya ce me hankali na kuma yarda da hankalinta da
nutsuwarta".

Ya d'anyi jim, sannan ya ce" uhum Allah ya kaimu ni zan wuce maganar saka hannu kuma na
bar maka wuk'a da nama duk abinda kayi dai dai ne".

Suna tafiya suna d'an tab'a hira har yazo bakin motarsa, Hammud ya koma ya cigaba da
ayyukansa yana me jin tausayin amininsa aransa domin kuwa Haidar mutum ne me matuk'ar
buk'ata Amma kuma Sam baisan Neman mata ba, sai dai ya gama ciwonsa ya bari babu
Wanda ya sani Wanda ayanzu haka ya ke Neman Haifar masa matsala babba.
$$$$$$$

......wani irin kuka nake yi, Wanda kana ganinsa kasan kuka ne na wacce ta gaji da duniya, sai
zarya nake daga cikin asibitin zuwa waje hankalina duk amatuk'ar tashe ina tunanin halin da
mahaifiyata take ciki, na samu wani d'an benci na zauna ina ta rusa kukana, mutane sai kallona
suke wasu su tsaya su tambayeni lafiya? Wasu kuma suyi wucewarsu matsalata ce ba
matsalarsu ba.

Na dad'e acikin wannan halin sannan na garzayo na dawo cikin asibitin, na lek'a d'akin y'an
haihuwa na hangota can sai kiran sunan Allah take, na kwalla mata kira cikin tashin hankali.

   "Umma! Umma!!".

Da sauri wata nurse tayo kaina tana yimin masifa, tana hargagi wai uban me Nazo yi?.

Jikina duk asanyaye na bar wajen, ina tafiya duk jikina amatuk'ar sanyaye na zauna ina tunanin
halin rayuwa.

K'annena 8 ne, ni ce babbar y'ar mamanmu inada shekara 18 yanzu aduniya, mahaifina Sam
bai damu da rayuwarmu ba sai ta matarsa wacce ta zamar masa y'ar lele, kuma bata tab'a
haihuwa ba ta sanya rayuwarmu agaba da tsangwama da cin mutunci, mahaifiyarmu ba tada
damar ko yin tari agidan sai ta tambayi ba'asin wannan tarin na ta, baki d'aya ayanzu ta had'a
tsanar kowa agidan ta d'oramin wai duk mugun halin uwata na kwashe sa, duk hak'urina sai
danaso tanka mata Amma mahaifiyata sai ta hanani.
ko yau dana kawo mahaifiyata asibiti dana je na faÉ—a masa ce min yayi ai dama ta saba
haihuwar gida kaza uwar Æ´aÆ´a, shi baida kuÉ—i saboda haka duk ma yadda zamuyi muje muyi
idan taji haushi ta daina haihuwar, wannan maganar tashi ta ƙarshe ta sanyani acikin
wani hali, na fashe da kuka saboda bansan yadda zanyi wajen kai ta asibitin ba domin ba muda
ko ƙwandala haka muka tashi gashi dama aikatau mahaifiyata takeyi kuma ba a bata kuɗin
watanta ba ni kuma kullum tallan shinkafa da wake nake É—auka da safe da yamma, dashi muke
rufawa kanmu asiri ni da ƙanwata Amira ita tana ɗaukar nata da rana, wannan yasa mahaifinmu
ƙara buɗa ƙafafuwa yake cin karensa babu babbaka domin kuwa sisinsa bata shigo mana,
saboda wannan sana'ar tun dama ba wani abun kirki yake bayarwa ba naira É—ari biyar yakw
bata
acewarsa tun safe har yamma, haka zamu ƙwaɗa garij ƙwaƙi idan mukasha ma lokaci ɗaya
shikkenan, kuma kada kuce mahaifinmu zaune gari banza ne a'a shi ma'aikacin gwamnati ne
sannan yana da gidan biredi ƙato shi da ƙaninsa wanda bayan an raba musu gado suka buɗe
Gidan biredin tunda su biyu kacal iyayensu suka haifa Æ´an asalin garin shanono ne.
wannan albashin nasa kaf na matarsa ne sai abinda tayi niyya take sammasa mudai wannan
matar Allah ya isa bata goge mana baƙin cikinta domin kuwa kullum sai munyi mata amma ko
ajikinta, domin dama mutane masu aikata rashin mutunci sunfi daÉ—ewa agidan duniya.sam
bana ganin mahaifina da daraja ko wani mutunci sau da dama ko amajalissarsu na gansa bana
ko kallonsa, saboda da tsanarsa na taso agidan duniya bansan me yasa ya tsani mahaifiyata
ba? Ko da yake nasan wani al'amarin sabida tana yaean haihuwa shiyasa ya tsane ta wai taƙi
yin tsarim iyali, shiyasa ko kaÉ—an bana ganin girmansa domin da ba'a haihuwa da shi kansa
ba'a haifesa ba.

Ina cikin wannan tunanin likitar ta fito ta ce" ke! mahaifiyarki ta haihu Æ´an biyu duk maza, kije
gida kuxo da Æ´an uwanki ku biya kuÉ—i ku É—auketa".
Jikina har ɓari yake domin in isa gare ta, likitar ta dakatar dani da ce wa" wa yace ki shiga? Ko
gama gyarata ba'ayi ba kije dai can gida ki faÉ—a musu kafin nan an gama komi".
da hazama na runtuma                   da gudu saboda inason isa gida domin in ɗan siyar da wasu
abubuwan in kawo, nasan dai abinda take nufi kuɗi ne ba wani abu ba.                                       
      https://chat.whatsapp.com/LcnDvlFNqL0Enq7llnpAVe                                               


                                          UMMU MAHER CE
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)🍃: *_�D'AN HALAK�_*

MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)🍃_*

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚_*

~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159

*Danna wanna link ɗin kai tsaye xaka samu 3k daga tsarin palmpay amma waɗanda basu taɓa
buÉ—ewa ba, kisa lambar wayarki zai kai ki inda zaki É—akko application É—insu, idan baki gane ba
ki tuntuɓe ni ta lambata 07068606171*
Hey, I use the PalmPay app for free transfers and to get cashback on every transaction. Use my
link or my code "SUQD6653" to join and get ₦1000 welcome bonus.
https://link.palmpay.com/34vPB

2
_________sauri-sauri nake har ina É—an haÉ—awa da gudu, har Allah yasa na samu damar isowa
gida tafiyar danayi daga asibiti zuwa gida za tayi ta awa É—aya idan a daidaita ne tafiyar minti
talatin ne.
Tun daga nesa na hango mahaifina, riƙe da kaya niƙi niƙi kusan ledoji manya viva guda uku sai
nishi yake kamar wanda ya É—akko ingarmar dutse.
Nayi saurin matsar da idona daga barin kallonsa, domin arayuwata ayanzu babu abinda na
tsana sama da mahaifina, idan na gansa maimakon naji irin daÉ—in nan da Æ´aÆ´a sukeji da
rahama daga kallon iyayensu a'a ni sai dai naji kamar na bindigesa, ban tsaya ba na kuwa
wucewa ta abina zuciyata tana saƙamin in tsaya ko gaisuwa inyi amma na kasa domin kuwa
Allah ya sani bazan iya hakan ba, Umma tasha yimin faÉ—a akan kada na kuskura fushin
mahaifina ya tabbata akaina, domin bazan taɓa samun abinda nake so arayuwa ba kuma bazan
samu albarka ba, saboda haka sai na canja shawara na dawo da baya har na isa kusa dashi na
ce" sannu Baba bari in É—aukar maka kaya...."
A'i tun kafin in ƙarasa yayi saurin dakatar dani, gamida ce wa" yanzu kika hangoni, marar
albarka da zaki taho? ina tun daga titi kika hangoni, amma tsabar gulma sai da na kusa shiga
gida zaki ce zaki tayani? Ko da yake idan bakiyi ba ai baki yo halin Rabi uwarki ba, mace sai iya
gulma da kinibibi da son haÉ—a mutum da Æ´an uwansa, ni dai ko mayu ne ku keda uwarki baku
isa ku cinyeni ba, masu yawom tsiya tasi no gareji kuyi nan kuyi nan tun jiya kuka fita sai yanzu
ne ke kika yi tunanin dawowa gida, tinkiya uwar tamɓele".

Wani irin malulun baƙin cikine ya tokare ni, na kasa haɗiye wani irin wahalallan yawu saboda
tsabar jin zafin furucinsa "tinkiya uwar tamɓele". wannan maganar tashi ta ƙarshe ta sanya jikina
yin la'asar, domin ban taɓa tunanin wannan ranar zata zo da mahaifiba zai dinga jifana da
waɗannan miyagun kalaman ba, raina in yayi dubu ya ɓaci wato shi bai damu da tambayata
inda ma naje ba? abinda kawai ya damesa shi ne zagi da aibata mu, abu É—aya na yarda dashi
shi ne bazan yiwa matarsa biyayya ba domin kuwa duk wani halin da muka shiga ahalin yanzu

ita ce ummul aba'asin haÉ—a wani abun, domin kuwa ada ba haka mahaifinmu yake mana ba
tana zuwa ta buɗe masa ido da zuga, kullum cikin wulaƙantamu yake da aibatamu idan tashi tw
ciwo shi cikin dare sai ki gansa aɗakinmu yazo wajen Ummanmu, ya lallaɓata su tafi ɗakinsa
yana rarrashinta tamkar ba shi ba, ya gama ci mata mutunci atsakar gida an jima kuma yazo ya
ce zai lallaɓata, ita kuwa Kande tana can tana sharɓar barcin asara domin kuwa bata sanin me
ke faruwa? sai dai taga Umma da ciki ta haihu, wannan abu yana baƙanta mata rai sosai
saboda ita ko ɓatan wata bata taɓa yi ba.
na goge busasshen hawayena na shiga cikin harabar gidanmu.

ina shiga na wuce ɗakinmu, tsakar gidan babu kowa kuma banji hayaniyar ƙannena na ba, ina
shiga na hangosu atakure agefe ɗaya suna ta jan numfashi suna shasheƙar kuka, da sauri na
ƙarasa gabansu jikina har yana kyarma saboda sam banason in gansu cikin wani hali, nima sai
naji duka hankalina ya tashi na ƙaraso da sauri na rungumosu duk yawansu, ai kuwa duk suka
maƙalƙaleni suna kuka na rintse idanuwana saboda nasan ƙwanan zancan ba zai wuce Baba
kande ba, domin ta tsani buÉ—e ido taga waÉ—annan yaran gashi Umma kusan gwarnai take kafin
ta yaye take ƙara samun ciki, gashi mu 9 yanzu mun zama mu 11 cif cif tunda ga ƴan biyu nan.

"Anti ya jikin Umma"?.

cewar Amir, ƙanina ɗan shekara 12 me bin Ummi ita kuma tana da 15, sai Amira me shekara 17
ni kuma 18 da rabi sai sauran ƙannenmu dama ni ce babba.
na shafa kan Amir na ce" da sauƙi Amir ta haihu ma, ƴan biyu duk maza masu kama da kai da
walid".
Ai tuni suka sanya ihu suna dariya da murna suna ce wa "Umma ta haihu! Umma ta haihu!!".
Tuni suka firfito har ƙaramarmu Anisa me shekara 2 tana tsalle ganin ƴan uwanta ma suna yi,
na bisu ina kira amma ina har sun fice waje domin faɗawa maƙota nayi nasarar kamo Anisa na
riƙe domin ita tayi ƙanƙanta bana bari ta fita, kullum tana goye abayana.
Amira ce ta shigo da murnarta ta ce" kai ai har naji daÉ—i Anti, wallahi tun jiya bamu runtsa ba
ashe Umma ta haihu? yanzu Amir yake faÉ—amin".
Tuni Ummi tayi gaba, tana turo baki ta ce" ni wallahi banji daÉ—i ba ace kullum Umma ba tada aiki
sai haihuwa,kuma idan ma ta haihun ko kaza ba a yanka mata balle taci ragon suna, shi ne za'a
zo ana wani yaÉ—awa ta haihu".
Amira ta É—ala mata duka ta ce"shegiya me zuciya irin ta Babanmu, yau da Baba kande ce ta
haifeki da na ce kinyi gad........."

"uwarku ma ai mugun halin gare ta, shegiyar yarinya me zuciyar rashin mutunci wacce bata san
annabi ya faku ba".
ta É—aga labule.
"malam fito kaji zagin ala tsinen da wannan marar albarka take mini, fito ka tsitstsinewa shegiya
Æ´ar gadon Fulani masu mugun hali".
Ai kafin ta rufe baki har Babanmi ya fito, yayo kan Amira da gudu tayi ƙofar gida Ummi me baƙar
zuciya ta tsaya awajen ko nan da can bata je ba, domin ita Allah yayo ta da shegen taurin kai
ga faɗa da son wulaƙanta mutane tamkar ƴar Baba kande.

Ni kuwa ɗakinmu na shige, ina saƙawa da warwarewa ga Anisa a hannuna har ta fara barci da
alama yunwa takeji.
ya gama faÉ—ansa da tsine tsinensa ya koma É—aki, kamar baban É—aki domin kullum yana É—aka
sai ka rasa me suke tattaunawa shi kuma ba sana'a yake ba daÉ—inta ma yana aikin gwamnati
duk wata zai amshi albashi, amma yadda kasan baya samu dama shi duk É—an albashi ya saba
haka, duk sanda ya dawo daga aikiin ya shige É—aki to sai dai sallah amma ko majalisa bai fiya
zuwa ba, idan kuwa kaga ya fita to matar son nasa bata gari ne.

Amira ta shigo ta sameni na haÉ—a uban gumi, taÉ—an kalleni afakaice ta ce" yanzu Anti ya
Umman? nasan dai kun tafi babu ko biyar to yanzu ya za'ayi asamu kuÉ—in sallamo Umma daga
asibitin"?.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login