Showing 33001 words to 36000 words out of 37712 words

Chapter 12 - 'DAN HALAK Book Complete (By ummu maher)miss green.pdf

08 Jul 2025

1876

su?.
Ɗakin cike yake da ƴan taro, Omer sai zagaye ɗakin yake yana hawaye mai sosai zuciya, ganin
wannan hawayen ya ƙara sanya jikin kowa yin sanyi ya murza idonsa wanda yake yi masa
matuƙar nauyi ya ce" tabbas a yau muna cikin alhini, tabbas Ifkam ya rusa mana dukkanin abin
da muka rufe, domin yana ganin shi ne babba kuma shi ɗin ba wanda zamu iya taɓawa bane
wallahi tallahi ba don shi bane da wani ne da sai inda ƙarfin takubban mu suka ƙare, tsabar
tozarta wai kamar Ƴata Nurata wai ita ce za a haɗata da Nurrr yaron da har yanzu bai daina
shirme da shiririta, kullum cikin yawon ƙasa-ƙasa yake yana neman ƴar iskar da zai shaƙata da
ita, saboda shi ba a yo shi da mutunci ba sannan mu nan duk bai ɗaukemu da mutunci ba, hatta
shi sarkin ba wai yana ganin mutunci shi bane amma shi ne za a jajibo shi a haɗa shi da ƴata"?.

Abu Nurrr ya yi saurin ce wa "kai Omer ka iya bakinki, akan mi za ka dinga zagin ɗana? Yaron
da ko a yanzu bai haura shekara 30 ba shi ne ake yiwa irin wannan zagin ɗibar albarkar?

Domin kawai son kai, ita ɗiyar ta ka wani irin iskanci ne ba ta yi? Ko an faɗa maka bamu sani ba
ne? To har da boka tunfafiya tana lalatar ta dashi, wanda ya kasance ƙazami kuma faƙiri sai ni
za a dinga zaginmu saboda bamu kai ka kuɗi ba, to idan ma domin kuɗi ne ai har yanzu baka
kai shi Sarkin ba duk da ana haɗawa dana sat..."
Wata irin shaƙa Omer ya kaiwa Abu Nurrr sannan wajen ya kaure da bala'i, mai makon abarsu
suyi faɗansu faɗan mutun biyu sai ya zama faɗan mutane sa yawa waje ya hau sowa, abin ka
da ɗakunan gidan sarauta manya-manya sai ga shi an jiyo faɗansu tun a babban masarauta
idan ka kasa kunne za ka ji.

babu shiri aka buga busar giwa, nan da nan suka ja munafukan bakunansu suka yi shiru domin
sun tabbatar suka bari aka ƙara buga wannan sarewar to fa kashinsu ya bushe, duk da haka
basu daina aikawa juna mugayen kallo ba saboda Ƙabilar Turam akwaisu da taurin kan tsiya
yadda kasan mutanen farko, ga su da mugun yawa domin iya su gidan masarauta za a haɗa
gari biyar awaje ɗaya kuma ba ƙaramin gari ba a a babban gari wanda yake ji da tumbatsar
mutane.


ƘASAR NIM

Babbar ƙasa ce mai tafe da mutane da dama, sannan idan ka gansu saboda kyau sai ka ɗauka
su ne da kansu suka ƙera kyawunsu ba manya ba yara, gasu da kyawun halitta yadda kasan
larabawa haka suke sai dai har sun fisu ma fari da haske su ɗin mutane ne masu yare da al'adu
da dama, suna wani yare wanda ake kira YIMAN yaren kamar larabci yake amma ba larabci
bane, sannan suna yin yare da dama a garin har yaren da baka tunanin ji ba sai ka ji shi a
ƙasar, kusan mutanen duniya da dama suna zuwa ƙasar domin yawan buɗe idanuwa domin
Allah ya yi musu kyawun gine gine, kyawun furanni,shuke-shuke albarkatun gona. Sannan suna
da dukiya sosai ba kaɗan ba idan nace ba kaɗan ba ina nufin sosai ɗin nan. Ta yadda ko da za
suyi shekara malala gashin tunkiya suna raba kuɗa ɗe ba zasu ƙare ba, domin kullum arziƙinsu
gaba yaje ba baya ba saboda Allah ya sani suna cinikayya da haɗakar dukiyoyi da ƙasashen
africa dama na yamman duka, shi yasa sam ko asara idan ta hau su basa damuwa domin suna
da bila adadin ɗinsu a bayan ƙasa.


Wannan rigimar da aka fara sarki yasa aka buga ƙahon giwa ya yi ne saboda kawo ƙarshen
tarzoma, domin shi da kanshi ba magana zai yi musu ba saboda sam ba ya son surutu ko
hayaniya a tsakanin mutanen shi, ya fi son ya yi musu shiru yaga iya gudun ruwansu saboda
sai suyi fin wata ma ba tare da sun sanya idanuwansu akan sarki ba, suna gida ɗaya mai sassa
daban-daban kuma duniya daban tunda kowa ba ya ganin kowa tsakanin inda suke, da inda
sarki yake a ƙalla ana samun tafiya mai nisan gaske wacce idan a ƙafa za kaje sai ka yi tafiyar
awa ɗaya.

*HMM KA DA KUGA LABARI YA JUYA, TI BAI JUYA BA YANA NAN DAI AKAN ƊAN HALAK
ƊIN SHI KU DAI KU CIGABA DA BIYO NI*




_HUMAIRAH_


Babu mutanen da ba a aikawa Babanmu ba, akan mu koma gidan shi ya yi haƙuri, amma ya
murzawa udanuwanshi kwalli ya ce sam ba zamu koma mishi ba, idan munga dama mu shiga
duniya ma amma shi ba shi ne ya haifemu ba, tunda mu ba zamu zauna lafiya ba.

Wannan maganar da ya yi ta ƙara tunzura zuciyoyinmu, musamman ma su Ameera Umma ma
taji haushin furucin sosai.

Muna zaune a tafkeken tsakar gidansu Umma, ni Ummi, Ameera, Anti Salamatu, Matan
gidansu. Duk hira ake akan Iyan Salame wato mahaifiyarsu Umma wacce take ƙasar larabawa
shekaru goma kenen amma har yanzu ba ta dawo ba taje aiki. A nan ne ma ake ƙara
tattaunawa kan matsalarmu, Anisa ce ta shigo tana kuka wato ƙaramar ƙanwarmu, idanuwanta
sun yi jawur ga ƙafafunta babu takalmi, raina ya yi mugun ɓaci idanuwana suka kawo ruwa
domin duka-duka shekarar Anisa uku, amma mahaifinmu ya yi tsallen baɗake ya ce ba za a
ɗaukar mishi ƴa ba, domin kada mu koya mata mugun hali irin na mu da uwar mu. Ni daman
nasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya domin ni nasan Baba ba zai iya kula da ƙannen
mu ba balle kuma Anisa da take yarinya ƙarama, ga hantarar Baba kande da dukan da take
musu.

Da gudu ta rungume ni tana ce wa"Yaya unwa ina ji, cicina ciwo ake mini".

Sosai na fara hawaye na ce"Sannu baby Anisa zo ki ci abinci". Na ɗakko sauran gadin kwakin
da muka sha na fara ba ta tana ci, hannu baka hannu ƙwarya tamkar dai za ta haɗa da ƙwanon
saboda gunwa. Kowa ya dinga kallon yarinyar cike da tausayi, tana gamawa na ɗebo mata
ruwa tasha na ɗora ta akan cinyata ina shafa kwantaccen gashinta mai kyau da sulɓi, dama ga
Anisa da son jiki sai ta ƙara shigewa jikina na fara tambayarta? "Baby Ani tun yaushe rabon ki
da abinci"?.

"Yaya tun da chafe da Baba kande a bamu ɗumamen tuwo".

Da sauri Ameera ta ce" tun da safe Ani? Yanzu fa la'asar ake kira? Inna lillahi wa inna ilaihi
raji'un".
Muka saki kuka, amma banda Umma domin tabbas abin ya girgizata shi yasa ma ta kasa
magana saboda baƙin ciki.

muna zaune matan gida suna ta zagin Babanmu da matarshi da ta gama mallake shi, sai kuma
wani tashin hankalin ya riskemu domin kuwa Anisa ce ta fara wani irin amai tamkar za ta
amayar da kayan cikinta, ga bakinta sai kumfa yake...

*KEMA HAKA KI KE ZAUNE BA KIDA SANA'A? KO KUWA KINA YI SAMU NE BAKYA YI? KO
KUWA KINA CIKIN MATA MASU ƘIWA?*

TO KU BUƊE KUNNUWAN KU DA KYAU, SANNAN KU SANI SANA'A ITA CE JIGON
RAYUWA MUSAMMAN MU MATA, UMMU MAHER TA SHIRYA TSAF WAJEN KOYA MUKU
WAƊANSU SANA'O'I KAMAR

*BEAD WORK*��
*GRAPHICS*✍
*MAGUNGUNA NA MU NA MATA*
*RIBOMS NA YARA DANA MANYA*‍♀️‍♀️

IDAN KIN SHIRYA KOYON DUKKANIN WAƊAN NAN SANA'O'IN KI YI MIN MAGANA TA NO
ƊINA KAMAR HAKA;
07068606171



*$IFKAM*
*$HUMAIRA*
*$AMEERA*
*$UMMA*

*SHARE*
*COMMENTS MY FANS*
*CHART NO CALL 07068606171*
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN):
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx


*_�ƊAN HALAK�_*

MALLAKAR
*UMMU MAHER(MISS GREEN)*


_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_

_AREWABOOK_
https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159

_WATTPAD_
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info

Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargabayar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi
adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan
hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..


30k weekly parking 300k

1)Haj Maryam✅

2)Ada umar/hafsat yahya✅

3)Usman

4) barrister hauwa'u

5)shafa bello/baby daura

6)

7)

8)


9)


10)
Akama slotd

https://chat.whatsapp.com/HAkm8rINu8a0ouQsRmuDuL

19



________Hankalinmu ya yi ƙololuwar tashi, tun ma ba kamar ni ba domin kuwa kowa yasan
yadda nake son Anisa tamkar ƴar dana haifa a cikina. Umma sai kuka take tana kiran sunan
Anisa amma tamkar dai an shuka dusa saboda ko motsi ba ta yi, cike da tashin hankali muka yi
waje neman ɗan sahu muka yi sa'a wani ya kawo wasu maƙotanmu, da gudu muka sanyata a
ciki Umma ma ta shigo muka wuce asibiti, sosai muke kuka Umma ce ma me ƙarfin halin tofa
mata addu'ah tana shafa kanta tana ɗan siririn hawaye mai tafe da abubuwa da yawa.

Ƙaddara da tsautsayi tamkar abu ɗaya ne a fassare sai dai a baki harufan suna da banbanci,
domin ita dai ta tabbatar ƙaddara ce ta sanyata afkawa kogin maganaɗisun auren mahaifin
yaranta, domin ko kusa ba ta ma sanya shi a sahun manemanta ba, saboda ba shi take so ba
amma da ƙaddara ta zaɓa mata shi tasan tabbas da babu yadda za a yi ta zaɓe shi a matsayin
mijinta, domin ko a lokacin da ta aure shi kowa tofa albarkacin bakin shi ya dinga yi, musamman
ma masu cewa wai ita matar manya ce duk da ba shi da mugun hali kamar yanzu, tunda ada
can baya in har ta ce yana mata wani abu tabbas ta yi mishi ƙarya, zuwan Baba Kande ne ya
canja komi rayuwar su ta zamo tamkar rayuwar ƴan bariki, sannan baya shakkar dukanta a
gaban yaransa duk domin matar shi.


*WACECE BABA KANDE?*


Baba kande dai ƴar asalin garin Jos ce, sannan babu wanda bai san mecece sana'ar ta ba ƴar
bariki ce me siyar da taba da wiwi, aƙalla aurenta ya kai shida tun ana ƙirga mata aka daina
saboda aurenta na biyu ne ma ta kai shekara ɗaya amma duka aurenta ba ta kai ko cikakkun
wata biyu take tafiya, kuma duka babu wanda ta taɓa haihuwa dashi domin a cewarta ba ta zo
duniya domin haihuwa ba ta zo ne domin hutawa. Saboda haka Allah ya ɗora mata son
mahaifinsu Humairah tun wani zuwa da ya yi Jos, ta liƙe mishi tun yana guje mata har Allah
yasa ya faɗa komanta, tunda ta asirce shi baki ɗaya ya zama bawanta babu abin da yake haɗa
shi da yaran shi sai zagi da hantara. Bayan ya aure ta shi kenan bata ƙara fitowa ba da zummar
bazawara, har yau da take da kusan shekara 5 a gidan shi.



Mu koma labarinmu.

Sosai take shan jiki, domin ko kafin mu zo asibitin ba ta numfashi ko kaɗan hankalinmu ya ƙara
tashi sosai, da ƙyar likitoci suka amsheta domin sun ce tana cikin koma sosai, wato tana cikin
matsanancin hali muna ji muna gani aka shigar da ita emergency(ɗakin gaggawa).

Muka tsaya a reception muna kuka har Umma ta gaji da kukan mu ta ce" wai shin bawa yana
iya canja ƙaddarar shi ne? Shin idan Allah ya so ɗaukar rayuwar ta za ku hana ne? Bakwa mata
addu'ah sai kuka? Haba ku dinga yawan kiran 'LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI
KUNTU MINAZZALIMIN, yawan kiran wannan addu'ar yana cire dukkanin bawa musulmi acikin
wani hali, saboda haka kuyi ta kiran wannan addu'ar komi tsanani akwai sauƙi da yardar Allah".


Tuni bakunanmu suka fara wannan addu'ar, muna cikin wannan halin ne wani dr ya fito kai
tsaye ya yo inda muke, jikinmu duk a sanyaye sai da ya fara kallonmu a nutse sannan ya ce" ku
ne ƴan uwan yarinyar nan ko? Da sauri muka amsa, ya cigaba da magana "muna so ku sanya
hannu da gaggawa za a mata tiyata ne domin fitar da gubar da ta sha a cikinta, sannan za ku
biya kuɗin tiyatar naira dubu ɗari".

Salati muka sanya mu dukanmu, tashin hankalinmu a fili muka fara kuka a wannan lokacin har
da Umma a masu kukan, likitan ya ce" ba kuka za ku yi ba ku nutsu kuyi abin da na ce idan ba
haka ba zaku iya rasa ta baki ɗaya".

Ni ce na fara magana ina kuka" likita ayi mata aikin duk inda kuɗi yake zamu nemo shi don
Allah ayi mata". Na saki kuka mai ƙarfi, gami da haɗe hannayena waje guda alamar ya taimaka
su yi mata.

Ganin hakan ya ce" A a, bama aiki sai an fara biya kuyi haƙuri dai ku bubbuga ku kawo mu
samu mu ceto rayuwarta". Da sauri Ameerah ta ce" likita wallahi ko kaɗan bamu da wannan
kuɗaɗen ko kusa, ko dubu biyar bamu da ita balle dubu ɗari ni na tabbatar akan kuɗin nan sai
dai yarinyar nan ta mutu".
A kiɗime ya kalle ta sannan ya ce" shin ba ku da mahaifi ne? A iya sanina mahaifi shi ne jagaba
akan dukkanin lalurorin iyalin shi, saboda haka ku kira shi ku faɗa mishi".

Babu musu na danna lambar wayarshi a wayar Umma, wacce Anty Salamatu ta bata domin ta
dinga jinta tunda ita ta koma gidanta yanzu.

Bugu ɗaya ya ɗaga, da sauri na gaishe shi. Na faɗa mishi duk halin da muke ciki.

Saurin kashe wayar na yi, domin kuwa iya tashin hankali ina cikin shi domin maganar da ya
faɗa min ba wacce ya kamata kowa ya jita bane domin girmanta ya girmama har ya gagari
dutsen dala, ɗaukar maganar sai an naɗa gammo ɗari ba tare da an iya ɗauka ba.

_HAIDAR_

Kallon Mimi ya yi yana ce wa" ki fita a idona fa? Ni ba sa an wasan ki bane akan mi za ki dinga
ce min ango?".

Mimi ta ƙunshe dariyarta tana ce wa"Sorry ya Haidar". Bai ƙara tanka mata ba ya zauna jiran
Ammi da Alhaji.

A hankali suka fara saukowa a tare, Haidar yaji wani irin abu me masifar zafi ya sauko mishi a
cikin zuciyar shi, tunda ya taso Allah bai taɓa ɗora mishi son wannan bawan Allahn ba, domin
kuwa shi kaɗai ya barwa kanshi sanin abin da yasa ya tsane shi har haka, sam bai iya tsana ba
idan ya so abu a farko abu mai wahala ne ya ƙi shi, idan kuma ya ƙi abu a farko to a ƙarshe ma
yana matuƙar wahala ya so shi, ya kasa gane wacce kalar tsana ma yake yi wa wannan bawan
Allahn, shi dai yasan tabbas tsana ce wacce har ka mutu kana yiwa mai shi.

Alhaji da fara'ar shi ya ce" A a Haidar ango, sannunka da zuwa".

Ya faɗi hakan da maɗaukakiyar fara'a. Haidar ya ɗan kawar da kai tamkar dai ba zai mishi
magana ba, sai kuma ya tuna da alƙawarin da ya yiwa Ammi na gaida mijinta a duk lokacin da
suka haɗu.

A ɗan basarwa ya ce"sannu da fitowa". Ammi ta yi saurin kallon shi alamar wannan gaisuwar da
ya yi ba ta yi mata ba, yasan sarai dama ba za ta so gaisuwar ba amma saboda son tabbatar
mata har yanzu fa wannan tsanar tana nan a cikin ran shi.

Alhaji ya amsa yana fara'a ya ce" Haidar ɗazu mun yi magana da Amminka akan gidan da za ka
zauna, to ga mukullin sabon gidana mr part huɗu wanda na kammalashi kwanan nan, kuma ya
kasance mallakin ka har abada domin da sunan ka aka gina shi".

Haidar haushi ya kama shi, tamkar dai zai saki kuka saki kuka domin shi dai ko kaɗan ya tsani
shisshigin da wannan bawan Allahn yake mishi, ce mishi ya yi bai da kuɗin da zai sai gida ko
mi? A iya sanin shi ya mallaki gidajen da ƙirga su ma tamkar ɓata baki ne saboda zunzurutun
yawansu, cikinsu kuwa har da waɗanda shi da kanshi alhajin bai isa ya gina su ba.

bai gama tunanin ba yaji Alhaji yana ce wa" sannan na ware maka kuɗi kimanin naira biliyon
biyar, domin ka yi hidimar biki sannan na ɗauki nauyin yi maka laife yanzu haka ma na bawa
ƙanwata tana can dubai".

Cike da matsanancin haushin abin da ya yi mishi ya ce" na gode".

Daga haka bai ƙara magana ba, ya tashi gami da sanya hannuwan shi duka guda biyu a cikin
aljihun shi sannan ya miƙe tsaye ya yi musu sallama. Ammi ta kira sunan shi da sauri, ya juyo
yana mata kallon kar ki yi min haka. Cike da isa irin ta ɗa da mahaifi ta ce" amma Haidar kana
da hankali kuwa? Kai bakasan ayi maka abin alheri ka yi godiya mai yawa ba? Shi ne ka yi
mishi wannan banzar godiyar ka tafi? Allah wadai da lamarinka wallahi".

Da sauri Mashal ya dakatar da ita wajen ce wa" ahir ɗin ki Habibty, kada ki ƙara faɗawa ɗanki
mummunar magana sabili da wani abu ya haɗa ku, kuma ma me ya yi ne? Godiya fa ya yi min
so kike sai ya dafa ƙafafuna sannan za ki tabbatar da cewar ya yi mini godiya? Kada ki sake
Allah wadai da shi kin ji?.

Cike da matsanan cin haushin ɗan nata ta amsa mishi da to, Shi kuwa Haidar rintse idon shi ya
yi sannan ya fice baki ɗaya daga gidan, yau bai taho da direban shi ba dama kuma bai fiya
fitowa da bodyguard ba idan zai je gidan Ammin shi ba, Yadda ya tsani mutuwar shi haka ya
tsani mijin mahaifiyar shi har baya son tunawa da mugun ƙullin da ya haddasa mishi a arayuwa
wanda har yanzu bai fita daga cikin shi ba.


Kiran Khausar ya dinga shigowa akai-akai, sosai yaji tamkar zai fasa wayar saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login