Showing 36001 words to 37712 words out of 37712 words
Chapter 13 - 'DAN HALAK Book Complete (By ummu maher)miss green.pdf
haushi
domin kuwa a rayuwar shi baya son ko tunawa da ita, musamman da ta zama ƴar aminin
Mashal abokin cin mushin sa.
_LULU_
"Hajiya don Allah ki taimakeni ki shige min gaba wajen son na auri yaya Haidar, wallahi ina
tsananin son shi da ƙaunar shi wallahi idan har ban aure shi ba bansan inda zan sanya kaina
b"...
Wani irin mugun mari Hajiya babba ta gaura mata, sannan ta fara magana tana huci ta ce" Allah
ina roƙonka ka sa mafarki nake, yaron da ba ɗan halak ba shi kike so"?.
*$HUMAIRA*
*$AMEERA*
*$ANISA*
*$UMMA*
*$HAIDAR*
*$MASHAL*
*$AMMI*
*$MIMI*
*$LULU*
*$HAJIYA BABBA*
SHARE
COMMENTS
CHART NO WHATSAPP
MRS GREEN CE
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_ƊAN HALAK_*
MALLAKAR
*UMMU MAHER(MISS GREEN)*
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
_AREWABOOK_
https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
_WATTPAD_
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info
Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargabayar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi
adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan
hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..
30k weekly parking 300k
1)Haj Maryam✅
2)Ada umar/hafsat yahya✅
3)Usman
4) barrister hauwa'u
5)shafa bello/baby daura
6)
7)
8)
9)
10)
Akama slotd
https://chat.whatsapp.com/HAkm8rINu8a0ouQsRmuDuL
20
______Ganin jikina ya yi sanyi ta ce"uhum dama wahalar da kanki ki ke amma ni nasan waye
mahaifinku, ku kuɗi suna bin shi ba zai bayar ba domin kuwa ba don ku yake neman shi ba".
Tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, tabbas da ɗaci da ciwo ace uban
ƴaƴanka ya maida ƙuntata maka shi ne abu mafi soyuwa a wajen shi.
Likita ya fuskancemu sosai, duk da ban faɗa mishi ba amma ya fahimci duk abin da yake
faruwa amma wasiƙar fuska tana ga zuciya, idan kaga wani yana dariya to halin da zuciyar shi
take ciki ne hakazalika idan kaga mutum yana kuka to tabbas zuciyar shi ma ba daɗi in har ba
kukan farin ciki bane.
Cike da tausayawa ya ce"babu damuwa ni na ɗauki nauyin yi mata aiki, Allah ya bata lafiya". Ya
shige gaba ba tare da ya juyo ba. Kukan farin ciki muka fara yi, Umma tabi bayan shi tana mishi
godiya kawai ya ɗaga mata hannu alamar ba komi.
Muna zaune kusan awa biyu, sai ga likitan ya nufo inda muke fuskar shi babu annuri, dukkanmu
muka tsira mishi idanuwa tamkar masu gano wani abu a idanun na shi, mun kuwa hango ɗin
domin kuwa kana ganin shi kasan yana cikin damuwa sosai.
Maganar da ya fara faɗa mana yasa na saki wata irin ƙara tamkar wacce iyayenta duka biyu
suka mutu.
_HAIDAR_
Suna zaune da Hammud Ammi ta kira, jikin shi a sanyaye ya ɗauki wayar domin yasan dole sai
ta kira.
"Haidar anya kuwa kana son gamawa da duniya lafiya? Shin meye laifin wanda yace yana son
ka? Shin ya dace abin da kake yi wa Alhaji? Duk irin abubuwan da ya yi maka tun kana yaro sai
yanzu ne za ka bijire mishi? Saboda ka kawo kai ko? Saboda a yanzu ya alkinta maka dukiyar
ka ya baka ita shi ne zaka saka mishi da irin haka? To bari kaji ni ba wani abu bane a wajena in
sallamawa duniya kai baki ɗaya, in yadda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda kuma aure ne ko
kana so ko baka so sai an yi shi, fitinannan yaro kawai mtsss"!. Ta saki me ƙara, Haidar yaji
ranshi ya sosu sosai wato ma tafi son mijinta akan shi? Wato duk irin abubuwan da ya faru acan
baya ita ɗin ba ta ga hakan ba? Duk irin rashin mutuncin da ya yi musu bata gani ba? Tabbas
akwai lauje a cikin naɗi, domin idan ba asiri ya yiwa Amminshi ba ya tabbatar bai kai ta manta
irin abubuwan da ya yi mata ba har ma dashi ɗanta, shi kanshi abin da yasa yake ɗaga mishi
bai wuce Mimi ƙanwar shi ba, ƴar shi ta cikin shi babu yadda zai yi dashi shi yasa ma yake ɗaga
mishi ƙafa, amma da ace wani ne ya aikata mummunan aiki irin wannan to tabbas da tuni ya
datse duk wata alaƙa dashi.
Hanmud ya tsura mishi ido, ganin shi cikin damuwa yasa bai tanka mishi ba ya kyale shi, idan
ya gama tunanin sai ya yi mishi magana domin yasan halin shi yi mai magana zai iya janyo
musu rigima.
Ko da ya fara tunanin baisan lokacin da barci ya sure shi ba, Hammud yana ta kallon shi yana
dariya domin idan shi za a yiwa auren gata irin haka shi ko a jikin shi, amma duk ya wani bi ya
ɗaga hankalin shi.
Wani farin mutum ya gani, a zaune cikin wata inuwa gwanin ban sha'awa ga wasu irin kurayen
furanni masu kyau da sheƙi, yana ta yiwa Haidar murmushi yana so yazo wajen Haidar amma
ya kasa, domin kuwa wani ƙaton rafi ne a tsakiyarsu shi ne abin da ya hana dukkaninsu
ƙarasawa amma dukkansu a zaƙe suke domin son ƙarasawa wajen junansu.
Haidar ya hango wani ƙaton kwale-kwale wanda yake a kusa dashi, da sauri ya ƙarasa ya shige
ciki yana murna domin bai san waccen mutumin ba amma Allah ta'Ala ya ɗora mishi son shi
sosai fiye da son da yake yiwa kanshi.
Sauri-sauri yake ya ƙarasa, ai kuwa cikin ikon Allah sai ga shi a kusa da shi nan da nan ya fito
da zummar zuwa wajen shi, cike da tsoro da firgici ya dinga kallon fuskar da ta tsaya a
gabanshi, wajen tare mishi ƙarasawa kusa da wannan mutumin da yake son zuwa, wannan
fuskar har ya mutu ba zai taɓa mantawa da ita ba wannan fuskar ita ce fuska mafi kyawu wacce
ya taɓa ganinta sau ɗaya tak kuma bai yi sa'ar ƙara ganinta ba, wannan fuskar ya daɗe da
mafarkin sake ganinta.
Firgigit ya tashi, yana waiwaye tamkar wanda ke son hango wata halitta a cikin ɗakin...
_TASLEM_
Marin da Hajiyarta ta wanke ta dashi bai sanya bakinta mutuwa ba, ta fara magana tana
kuka"Hajiya ko zaki kasheni na dawo bazan daina son Yaya Haidar ba, son shi a jinin jikina
yake ya zamanto tamkar shi ne komi na rayuwa ta, ina son shi tamkar yadda uwa take son
yaranta Hajiya a son shi banƙi in mutu ba, auren shi kuwa shi ne babban burina a rayuwa".
Tana gama faɗar hakan ta fita da sauri tana haɗa ƙafa, domin sauri take ta cimma ɗaki saboda
yadda take muradin yin kuka ba tare da wani ko wata ya hana ta ba.
takaici da baƙin ciki tamkar zai kashe Hajiya babba, ji take kamar ta shaƙe Tasleem ta huta da
baƙin ciki, ga shi akaf yaranta tafi son Tasleem bata haɗa son ta dana kowa saboda ita kaɗai ce
ƴa tilo ga Alhaji Mashal.
hum, ni ummu maher na ce idan baka mutu ba za ka yi kallo, yanzu ace yara kusan 7 amma
mutum ɗaya ce ƴarsa? ikon Allah to me ya janyo hakan? Uhum wannan wani sirri ne me girma
jin shi sai nan gaba.
Da sauri Tasleem ta fice, domin ba ta son kowa yaga fitar ta ayau ɗinnan za ta fasa kwai kowa
ma ya sani, domin ba zata zuba ido mahaifiyarta ta hanata samun muradin ranta Haidar ba, ta
rasa wacce irin ƙiyayya ce a tsakanin Haidar da Hajiya, domin ita dai tun tasowarta take ganin
irin mummunar ƙiyayyar da Hajiya ke yiwa Haidar, acan baya ko kaɗan bata ji tana son Haidar
ba shi yasa ma take taya Hajiyarta ƙin Haidar ɗin, amma tunda ta gane tana ƙaunar shi sai ta
daina ƙin shi sai ma wata sassanyar ƙaunar shi wacce ke barazanar huda zuciyarta.
Jin fitar ta a mota ya sanya Hajiya fitowa da sauri, gate man ɗin dake baƙin ƙofa ta tambaya,
suka sanar mata eh ita ce ta fita a mota. Sosai gabanta ya faɗi domin kuwa taji lokacin da ta fita
a mota.
Da gudu ta ɗakko wayarta, ta dinga kiranta amma baturiyar waya ta sanar mata wayar tana a
kashe, zuciyarta ta hau harbawa tana zillo tasan halin Tasleem da baƙar zuciya, in har ta ce
tana son abu to tabbas tana son shi da gaba ɗaya zuciyarta, kuma za ta iya komi saboda abin
da take so, idan ta tsani mutum kuwa ko duk duniya zasu taru to tabbas ba za su zamar wa
mutum gata ba.
Babu irin neman da ba ta yiwa Tasleem ba, amma sam bata ganta ba hankali a tashe ta dawo
gida, sai dai tana shigowa taja tunga saboda ganin motar asibiti a gidansu ga shi ko ina ya yi
jina-jina, ai bata san lokacin da ta buga wani ihu ba ta faɗi ƙasa sumammiya.
_HANAN_
Durƙushe take gaban shi, Yaya Jummai sai kyafta mata ido take ma'ana ta fara magana.
"Boka ni Sunana Hanan, Allah ya jarabce ni da son wani bawan Allah saurayin ƙawata, kafin shi
na so wani kamar me sai ya yaudare ni da kaina nake mishi hidima domin ya so ni amma ya
gudu, yanzu ma tsoro nake kada wannan ya suɓuce domin kuwa gab ake da ɗaura mishi
aure..."
*TIRRR ƘA SHI*
Me Hanan take nufi ne da Haidar? Sannan waye ya mutu a gidan Mashal? Sannan wani sirri ne
da Tasleem take ɓoyewa? Wani sirri ne Haidar shima yake ɓoyewa? Wa ya gani a mafarkin sa?
Sannan me ya faru a asibiti da fuskokin su Humaira suka canja?.
Wannan amsoshin na ku duk sai a littafi na 2, wanda zai zama na kuɗi ne complete ɗin shi 1k
ne wanda zai kasance har da littafi na 3.
Idan kin tashi jin dukkanin amsoshin ki na cikin littafin ƊAN HALAK ki tura kuɗin ki ta wannan
Account ɗin.
2212328303
RABIATU BASHIR
ZENITH BANK.
MRS GREEN CE
SHARE
COMMENTS
CHART NO CALL
07068606171.