Showing 27001 words to 30000 words out of 37712 words
Chapter 10 - 'DAN HALAK Book Complete (By ummu maher)miss green.pdf
santa, sai kuwa ya gimtse fuskarsa lokaci ɗaya saboda ganinmu tare da ya yi. Ganin hakan
yasa Hajiya ƙarama ta fuskanci aƙwai wani lamari, amma bata nuna ko a fuska ta gane abinda
ya ke nufi ba, domin ance labarin zuciya a tambayi fuska.
Baba kande ta ɗakko mata kujera da sauri, ta samu waje ta zauna tana yiwa Baba kande
kallon tsaf domin aɗan lokaci kaɗan ta fuskanci wacece ita, domin ayanayin mutum da
mu'amalarsa kana gane komi, na farko taga sauyin fuska sosai alokacin da Baba kande taga ta
shigo da yaran, sai taga ta haɗe fuska tamau tana wani muzurai tamkar dai za ta kawo hannu
ne.
Bayan sun gaisa Hjy Ƙarama ta ce" dama waɗannan yaran na rako gida, amma ashe ba nan
gidan bane domin alamu sun nuna ba nan ne gidansu ba, domin da nanne gidansu zanga kun
nuna damuwarku da alhinin abin da ya same su na ƙaddara".
Da sauri Baba ya kallemu, sai kuma ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya magantu da ce wa" eh
tabbas nanne gidansu sai dai sam basa daga cikin yarana, musamman waccan munafukar".
Ya nuna ni da manuniyarsa, yana me dalla mini harara wasu zafafan hawaye suka shiga
ƙwaranyo mini na sanya gefen yalolon mayafina ina sharewa, tabbas an shiga tsakanina da
mahaifina tsakani me doguwar wutsiya tamkar wutsiyar raƙumi, domin ni ɗinnan yarinya ce ƴar
gatan gaske wajen mahaifinta, da yaji kuka na gwara yana zaune ka taƙarƙare ka maresa,
domin yana sona sosai kasancewa ta me sunan mahaifiyarsa kuma ƴarsa tilo daya fara samu
aduniya, kafin yasa kowanne ɗansa ni ya fara sani aduniya saboda haka duk wata ƙaunar da
zai yiwa ɗansa to bari na ne, domin ni da kaina na shaida kuma na tabbatar ni ƴar lelen babanta
ce kuma shalelensa maganin kukansa, tun ranar daya auri Baba kande har zuwa rana me kama
ta yau Babana bai taɓa buɗe baki yayi min addu'ar samun cigaba ba, ko kallona baya sonyi
saboda wai ni ba nida kunya ina yiwa matarsa rashin kunya, ni kuwa indai akan a taɓa Umma
ne inyi shiru a cutar min da ita shiyasa bana jurar rarrasar zuciyata wajen yin shiru idan har an
taɓa ta ɗin, musamman Baba kande sam bana mata uzuri ko kaɗan idan har ta taɓa Umma na
bana shiru, har ta kai ta kawo yau agabana Baba Kande za ta zagi Umma na amna ban isa ko
ɗaga kai nayi ba, saboda furucin Baba akan fushin Baba kande akaina, tun lokacin da ta faɗa
na faɗa kuma yaji saboda haka sai yayi min babban baki akan in har na yarda na ƙara faɗa
mata magana akan mahaifiyata Allah ya isa bai yafe mini ba, saboda haka tun daga nan nasha
jinin jikina na daina yiwa kai na ingiza me kantu ruwa na daina kula ta sam, in dai ba abin yaci
tura ba.
Ina cikin wannan tunanin naji Hajiya ƙarama ta baje kolin sallallami tana ce wa" ya
subhanalillahi, me ya kawo maganar cire su daga cikin yaranka? su fa ƴaƴa rahama ne sannan
ubangijin daya bamu su kiwo ya bamu bawai namu ne ba, duk abinda yayi zafi maganinsa
Allah".
Da sauri Baba kande ta ari bakinsa taci masa albasa ta ce" haba ke kuwa baiwar Allah, ina
ruwanki da wannan batu wannan ai tsakanin uba da yaransa ba a shiga ko da kuwa ita ce ta
tsugunna ta haife su".
Baba ya yi saurin gyaɗa kansa, alamar gamsuwa da maganar ta. Amira tayi karaf ta ce" mijin ta
ce ko kafin ta ce".
ta faɗi hakan ba tare da ta kalli kowa ba.
Baba ya kawo mata mazga domin babu wanda baiji abinda ta ce ba, ni kuwa gabana ya tashi
sosai domin ko giyar wake nasha bazan faɗa ubana ya faɗa ba, domin duk abinda kake nema
na duniyar nan banza ne indai babu albarka iyaye, saboda haka tun kafin Baba ya kai mata
duka ni nayi saurin wanke ta da mari ina shirin ƙara mata Hajiya ƙarama tayi saurin ce wa"
haba ke kuwa Amira me yayi zafi haka?, maza zauna kuyi haƙuri dukkanku amma inaso ki sani
duk lalacewar uba ko uwa to fa ba a canjawa tuwo suna".
Baba sai ciccika yake yana yi mana wani wulaƙantaccen kallo irin wanda ya ke wa Ummanmu
aduk sanda ta yi masa wani laifi ko matar sonsa Baba kande.
¢¢¢¢¢¢
_HANAN_
Cike da razani Hanan ta ce" whats me kike ce Saleema? aure Haidar ɗin zai yi? Dalili dame
za'a masa auren dole abarsa mana ya auri wacce ya ke so?".
Kuka kawai Saleema take, domin tasan sarai son da take wa Haidar in har bata aure sa ba
komi zai iya faruwa da rayuwarta, tunda take bata taɓa son wani ɗa namiji ba sai Haidar, shi ne
na farko kuma shi ne na ƙarshe domin ta tabbatar ba zata ƙara samun wanda ya kama ƙafarsa
ba ballantana ya kaisa, shi ne bugun zuciyarta shi ne komi na ta shi ta baiwa yardata domin duk
macen da ta samu miji kamar Haidar to ta samu rabin jin daɗin duniya.
Hanan kuwa jin zuciyarta take tamkar za ta tarwatse, domin ita a ganinta kaf duniya ma babu
wata macen da ta kai ta son Haidar ciki kuwa harda uwar da ta kawosa duniya domin ita gani
take ma babu maƙiyyarsa irin mahaifiyarsa, domin ita aganinta da tana sonsa da baza tayi
masa auren dole ba.
Ko kula Saleema ba ta yi ba, tayi saurin ɗaukar ƴar ƙaramar handbag ɗinta ta fice daga ɗakin
tana tafiya ko kallon gabanta bata yi har tazo inda take son tsayawa wato parking space, ta
waiwaya bata ga kowa ba sai wasu fadawan sarki acan daga jikin wata kyakkyawar baranda
kewaye da filawa masu matuƙar kyau da ɗaukar ido domin baby ƙarya gidansu Saleema gida
ne babba sannan gashi gida na sarauta ga kuɗi.
Ta dannawa Antinta kira, sai da tayi kira har sau biyu sannan ta ɗaga ai kuwa ko gaishe ta
batayi ba ta fara faɗa mata maganganu masu zafi akan zuwan da sukayi wajen boka kuma
gashi babu abinda zuwan ya haifar.
"Hanan yanzu ni kike faɗawa magana kan wannan yaron?".
"Eh na faɗa ɗin, ƙarya nayi aikin da akayi ya kamasa ne? ai kinga an cuce ni an ƙwacemin ƴan
kuɗaɗena".
"Au ke yanzu ba kiji abin da boka ya faɗa bane? Cewa ya yi irinsu asiri bai fiya kama su ba,
amma muci gaba da yin abin da za a samu hankalinsa ya karkata kanki, amma saboda ba kida
kunya kike faɗar wannan maganar".
"Yanzu dai sai in bari har sai yayi aure, wa ta ta rigani shiga gidan kafin ni na shiga ko? To ta
Allah ba taki ba Allah ni zan fara shiga gidan idan ma baƙin ciki kike ki dena".
Ƙit! ta kashe wayarta tama wani irin mugun tsaki, dama ta barta da ta gwada basirarta ta kissa
da kisisina har Allah yasa hankalinsa ya karkata agare ta, amma yanzu ma baza ta yi wasa da
damar ta ba za ta baje kolin basirarta.
Ta koma cikin gidan ta nuna ita masoyiyar Saleema ce, wajen rarrashinta da nuna mata ai dole
ma sai ta auri Haidar domin babu namijin daya dace da aurenta sai Haidar, ƴar sarki jikan
sarakai kuma gimbiya..............
$HUMAIRA
$AMIRA
$UMMI
$HAJIYA ƘARAMA
$HAJIYA BABBA
$BABA KANDE
$SALEEMA
$HANAN.
*MISS GREEN CE*
07068606171
CALL NO CHART
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_ƊAN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
~*Wattpad*~
D'AN HALAK
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info
MAHER'S COLLECTION
https://chat.whatsapp.com/C3tsX4CqiEp939DhYvJ3SZ
*MY CHANNEL LINKS*
DOMIN SAMUN DAƊAƊAN LITTAFAINA.
https://whatsapp.com/channel/0029VaEuTqi17En0eYizXq3d
*KEMA HAKA KI KE ZAUNE BA KIDA SANA'A? KO KUWA KINA YI SAMU NE BAKYA YI? KO
KUWA KINA CIKIN MATA MASU ƘIWA?*
TO KU BUƊE KUNNUWAN KU DA KYAU, SANNAN KU SANI SANA'A ITA CE JIGON
RAYUWA MUSAMMAN MU MATA, UMMU MAHER TA SHIRYA TSAF WAJEN KOYA MUKU
WAƊANSU SANA'O'I KAMAR
*BEAD WORK*
*GRAPHICS*✍
*MAGUNGUNA NA MU NA MATA*
*RIBOMS NA YARA DANA MANYA*♀️♀️
IDAN KIN SHIRYA KOYON DUKKANIN WAƊAN NAN SANA'O'IN KI YI MIN MAGANA TA NO
ƊINA KAMAR HAKA;
07068606171
14
*_HAIDAR_*
Wani irin ciwon kai ne ya turniƙesa, computer ɗin daya ɗauka domin yin aiki ya ajjeta can
gefe, ransa amatuƙar jagule yana tunanin abubuwa da dama musamman kan wannan auren da
za'a masa wanda bai shiryawa hakan ba, jin jikinsa yake tamkar ba nashi ba. ko da ya rasa
yadda zai yi ya ɗauki wayarsa ya kira amininsa Hammud domin ya faɗa masa halin da yake ciki
ko Allah zaisa ya samu sassauci.
Bugu ɗaya ya ɗaga yana tsokanarsa da ce wa" a'ah kaga manyan mutane kira ɗaya ninkin
kuɗi biyu Allah dai ya.
Bai kulasa ba, daman kuma Hammud yasan ba lallai ne ya magantu ba saboda haka ya ce"
kaga malam riƙe son kuɗinka agefe ba wata ƙwangila da zaka samu, wata magana ce na kira
ka muyi amma inason ka bani shawarar daya kamata".
ya ɗan ja fasali, sannan ya ce" uhum ina jinka Horror".
baiyi niyyar sakin dariya ba, amma saboda kiran sunansa da yayi ahaka yasa ya ɗan dara
sannan ya ce" Ammi ke son yimin auren dole, kuma wallahi ni ban shiryawa hakan ba, sai dai
inason ka sani wallahi bana son wannan auren sam domin ni ayanzu haka auren ma ya fice min
azuciya, gwara inyi zamana kawai domin aƙwai mutane da dama da sukayi rayuwarsu ba tare
da kowa ba, kuma suka mutu cikin aminci".
sai daya gama maganarsa tsaf, sannan Hammud ya ce" banƙi ta bakinka ba Terro amma
gaskiyar magana abinda Ammi tayi shi ne dai dai, haba Haidar shekararka nawa aduniya?
ayanzu haka fa kana da kusan shekara 35 aduniya idan baka kai ba to kaɗanne, amma ace
baxa ka yiwa kanka faɗa ba? Ammi ta sanya maka ido ne kawai, amma ganin baza kayi abinda
ranta yake so ba yasa ta nema maka mafita, sannan kai da kanka kasan rashin lafiyarka aure
shi ne maganinta, amma madadin ka samowa kanka mafita da maganin damuwa me ɗorewa
sai kuma kayi watsi da hakan? gaskiyar magana kabi umarnin Ammi, amma idan har kace zaka
bijire mata ka zauna babu mata gaskiya har abadan ba zaku taɓa shiryawa da Ammi ba".
"Hammud ba wai naƙi ta taku bane, a wannan rayuwar da muke ciki mafi yawanci mata suna
aure ne saboda kuɗi, ba wai don suyi aure saboda samun aljannah ba, suna yi ne saboda
muradin kansu da kuma wani ɓoyayyan sirri na son shagalin rayuwa, kuma ita kanta matar
bakasan wacce iriya ba shin ƴar gidan tarbiyya ce ko akasin haka? shin me son abun duniya ce
ko akasin haka? sanin gaibu sai Allah".
"haka ne, amma duk da haka ka sanya yaƙinin zakayi aure ne ba don komi ba sai don son
sunnar annabi, sannan kayi domin mahaifiyarka kai yanzu awajenta kake neman aljannah ba
wajen matarka ba, saboda haka ka bita sau da ƙafa azauna lafiya".
shiru ya ɗanyi alamar tunani, sannan ya ce" uhum zanyi yadda kace amma Hammud sai na
dinga ganin kamar ba Ammi ce ta haifeni ba, domin tunda na taso ko jana ajiki batayi kamar
yadda take jan Baby ajikinta, ko ƴan aikin gidanta tana matuƙar ɗaukarsu da muhimmanci fiye
dani ma duk da nasan aƙwai wasu abubuwan da suka sanyata haka, ciki kuwa har dani na
kasance ɗan fari kasancewarta Bafulatana to dole asamesu da kunya, amma abin yana shafata
sosai bayan rashin uba har da rashin uba akusa dani".
Hammud ya gane me yake nufi, amma saboda bayason ya sanya abokinsa cikin damuwa sai
ya ce" Ammi tana sonka Haidar, domin babu wata uwa da zata ƙi ɗan ta, saboda wani dalili
hakan ma zai faru? tasha wahalar ɗaukar cikinka rani, zafi, inuwa, haka har ka girma ka mallaki
hankalinka, to duk idan bata sonka wallahi baza tayi maka su ba, domin idan bakason mutum
fita kake daga rayuwarsa amma ita Ammi kullum burinta ta janyo ka ajiki, shawarata gare ka
kayi haƙuri komai zai zama dai dai".
ba tare daya ce komi ba ya kashe wayar, kiran Ammi ne ya shigo jikinsa amatuƙar sanyaye ya
ɗaga kiran, gamida gaishe ta cike da ladabi sai dai ransa babu daɗi gamida alƙawarin da ta
ɗauka na yi masa aure.
"Haidar inaso gobe kaje ku gaisa da Najma, saboda kaga abubuwa suna ƙara ƙaratowa kuma
ta sanar dani cewar haryanzu bakaje gidansu ba".
jin taja wa'adin maganar sai ya ɗan ja fasali sannan ya ce" zanje in sha Allah".
daga nan bai ƙara ce wa komi ba, sanin hali yasa ta katse kiran baki ɗaya, zuciyarta duk babu
daɗi akan auren da za ta yiwa ɗanta namiji tilo, sai take ganin kamar tayi masa ƙarfa ƙarfa ne
ko kuma auren dole, domin sanin kanta ne Haidar mutum ne wanda bai damu da rayuwar mace
ba, xata iya rantsewa da Allah tunda take bata taɓa ganin yarinyar da Haidar ya buɗe bakin
ƙasaitarsa ya ce yana so ba, sai dai su suce suna sonsa wanda kusan duk macen da tayi katari
dashi sai ta ƙyasa.
Ganin tayi shiru yasa Baby ma yin shirun, ta tafi duniyar tunani domin har ga Allah bataji daɗin
wannan haɗin ba, domin tasan yasan wacece Najma yarinya ce wadda iyayenta suka lalatata,
batasan komi ba sai shashanci da danna waya, chart da game sai kuma tiktok domin Najma
tana ɗaya daga cikin ƴammatan da suke Tiktok, a ɓangaren hausawa kuwa za a iya ce mata
don, domin tasan ta kan Tiktok duk inda wasu selebiriti suka kai a tiktok tasan dasu, suma kuma
sunsan da ita.
Ammi ta ce" Baby bansan me yasa nayi wannan haɗin ba, saboda harga Allah wannan yarinyar
ba kalar Haidar bace, yadda bai da magana da son tashin hankali na haɗasa da Najma,
yarinyar da agidansu ta fitinesu idan tana gida hatta karnukan gidan nutsuwa suke, amma inaji
ina gani saboda ƙawancan da muke da mahaifiyarta muka haɗa wannan haɗin, addu'ata Allah
ubangiji ya basu zaman lafiya me ɗorewa".
"Ammi ni dai nasan za'a samu matsala wallahi, gata da shegen yawo da kuma ƙaryar tsiya duk
da ansan mahaifinta yana da kuɗi kuma kowa yasan da hakan amma gaskiya idan kika ga
rashin arxiƙin da suke aclub Allah Ammi abin ba daɗi, tamkar ba yaran musulmi ba".
Wata gauruwar ajiyar zuciya Ammi tayi sannan ta ce" to yanxu ya zanyi ne Baby? ai aikin
gama ya riga daya gama, addu'ata ɗaya Allah ya daidata kansu ai mutumin banza yana
komawa na gari, haka zalika mutumin ƙwarai yana komawa na banza, saboda haka ni na yarda
da ƙaddara daman can Najma tana cikin allon ƙaddararsa wanda babu wanda ya isa ya goge
hakan".
*******
WASHE GARI.
Shi kaɗai ya fito amotarsa ba tare da kowa ba, yasan gidansu Najma yana nan a Nasarawa
G.R.A saboda haka awaje yayi fakin ɗin motarsa ya daɗe yana nazarin yadda zaiyi ya kirata,
domin har ga Allah jin tsanarta yake sosai aransa tamkar dai yadda ya tsani ɓatawa
mahaifiyarsa, ba don bin umarnin uwa ba da ko ahanya bata isa ya ɗaga kai ya kalle ta ba,
saboda sam bata da wani tsarin matar daya yarjewa zuciyarsa wajen neman aurenta, domin
manzonmu annabi Muhammad (S.A.W), ya horemu da mu auri mace don tarbiyyarta da
addininta, ba don kuɗi ko kyau ko mulki ba idan ma kuɗi ne shima yana dasu kuma har yafi
nasu ma, saboda haka dole ne ya samarwa kansa mafita domin ko ganin murmushinsa baza
tayi ba, ballantana ma har ta ce zata faɗa masa wata magana irin tasu ta ƴan duniya ƴan tasha.
daga can nesa ya hangota cikin mota ƙirar corolla, ita da wani yana jan motar sai dariya take
har tana wani ƙamesa tamkar da mijinta take hira, kana ganinsa kasan ƙwararran ɗan duniya ne
wanda duniya ta gaji dasu a gidan ɗan kande, daga can gefen gidansu ya ajjeta ta fito ya yafito
ya da hannunsa yana wani kashe mata idanu tamkar wanda yayi shekara ɗari rabonsa da
mace.
haushi da nadamar zuwa suka ishi Haidar ƙiris ya rage zuciyarsa tsinkewa ya tafi, amma sai ya
tuna umarnin da mahaifiyarsa ta basa tuno da hakan yasa ya sauke kansa ƙasa, zuciyarsa sai
tsinkewa take tana wani irin luguden dakan masara.
Har ta shige gidansu bata kawo komi aranta ba.
ganin zata shiga gida kuma bata gansa ba yasa ya fito ahankali, cike da takun nan nasa mai
matuƙar burge ƴam mata, daga nesa da ita ya tsaya sannan ya kira sunanta acan cikin
maƙoshi.
"Najmah".
wani irin magana ɗisu ne ya kamata, tayi saurin juyowa domin tunda take arayuwarta ba'a taɓa
kiran sunanta taji daɗin sunan irin na yau ba, ta amsa da sauri.
"Na'am".
Ganin Haidar yasa ta saki wata irin ajiyar zuciya gamida yin wani ƙayataccen murmushin daya
gaza ɓoyuwa har sai daya fito fili ya zama kamar dariya".
wani irin baƙin ciki ne ya turniƙesa ganin murmushin da tayi, ya haɗe girar sama da ta ƙasa bai
ƙara ce wa komi ba ya ɗan dafa jikin motarsa yana kallon wani waje na daban.
Cike da garaje ta ƙaraso tana yaƙe haƙora, da rashin kamun kai tamkar kurar da taga abin
hararta har wani tuntuɓe take tana lilo tamkar zata faɗo kansa.
"sannu da zuwa yaya Haidar, baka faɗamin zaka zo ba ai da ban fita ba".
ya ɗan ja numfashi sannan ya ce" no ba komi".
Tasan halinsa da jin kai, da kamun kai saboda haka yasa ta ce" to mu shiga daga ciki ka