Showing 27001 words to 29993 words out of 29993 words

Chapter 10 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf

12 Jul 2025

1714

yace cikin zuciyarsa duk da
wannan alkawarin da akayi masa na wannan
makudan kudi zuciyar shafiu bata daina tunanin
dukiyar dake binne a karkashin kasa ba.
** ** ** **
Wani katon gyare yayi tsalle ya fada fuskar.
KUDI DA MACIJI - 31
.
Wani katon gyare yayi talle yafada faskeken
kunnen daya daga cikin yansandan dake bobboye
abayan bishiyoyin suna nazarin bakin ruwan.
.
Dansandan ya kaiwa kunnen mari katon gyaren
ya tashi dansandan ya mari kunnensa a banza.
Kai wannan masifa dayawa take dansandan yace
cikin zuciyarsa sau dayawa yakan zargi kansa da
kansa amatsayin mahaukaci domin wai in ba
mahaukaci ba wane ne zai shiga aikin dansanda
aikin da akullum bashida wata riba sai ta bakin
jini kullum kana gadin jama'a da dukiyoyinsu
sukuwa nabinku da tsinuwa.
Shekarunsa ashirin da biyu yana aikin dansanda
amma haryanzu bai wuce sajan ba idan karshen
shekarar yazo yake sa ran yin ritaya.
Wannan dansandan sunansa AUDU ada can baya
yasha niyyar barin aikin dansandan amma sai
wani abokinsa yace dashi Haba audu kada ka
jahilci aikinka mana wannan aikin da kake
rainawa fa babu abinda yafishi muhimmanci
domin daku yansanda da malaman makaranta
idan babu ku babu gari kaidai abinda zakayi
kawai shine ka tsarkake zuciyarka ka nemi Halali
acikin aikina sai Allah yabaka lada yakuma
albarkaci aikin Amma zancen wai kabar aiki
wannan duk bata taso ba.
Wannan kalami na abokinsa shi yasa audu kaiwa

har tsayin wannan lokaci yana aikin Dansanda
daga inda Audu yake fake yana iya hango
duhuwar sauran abokan aikinsa su bakwai duk a
rabe dauke da bindigogi suna nazarin bakin
ruwan
Audu na nan a makale zuciyarsa tana yi masa
sake sake domin matarsa nada tsohon ciki kuma
awatan zata haihu haka nan har izuwa wannan
lokacin bai sayi koda buzu ba.
Audu ya lalubi aljihunsa ya zaro kwalin taba cikin
damuwa.
Dan cin hancin ma da muke karba anyi mana
bakin ciki gashi dai ba wani kyautata mana akeyi
ba amma saboda bala'i kuma ance wai duk
hancin wanda mukaci yakaimu Kara...
Tunanin audu ya katse adaidai lokacin daya hangi
hasken fitilar mota ta nufi bakin dam din abinda
yabashi mamaki domin tunda aka kawo su
adaren jiya kimanin karfe goma sha biyun dare
har zuwa yanzun nan basuga motsin wani
mahaluki abakin ruwan ba. To me yakawo mota
kuma?
Cikin sauri jikinsa na rawa audu ya fito daga inda
yake labe bindigar dake hannunsa ta dada nauyi
in har akwai abinda audu yaki jiki shine akaishi
aikin da za'a iya yin bata kashi kullum addu'arsa
itace Allah yasa yagama aikin dansanda ido biyu
kafa biyu hannu biyu.
Kamar audu sauran yansandan ma sun ga zuwan
motar don haka sai suka firfito daga inda suke
make kamar yadda aka umarce su sukabi cikin
duhun kamar aljanu suka nufi inda sukaga motar
tayi.
.
Shafiu yafito daga cikin motar ya rufe sannan ya
zagaya ya budewa aisha itama ta fito amma
jikinta na rawa kamar mazari da za'a tsaga
jikinta alokacin zaiyi wuya a sami wani digo na
jini.
Shafiu ya zaro wata katuwar cocila sabuwa daga
aljihunsa sannan ya haske cikin ramin lokaci guda
kuma ya jiyo ya dubi aisha yace toh Aisha aiki ya
rage naki ga ramin nan munzo Ya dada haska

mata cikin ramin da cocilan.
Aisha ta kurawa ramin idanu na tsawon lokaci
har yanzun nan takasa imani da cewa wai
shekaru dari da shirin da suka wani daga cikin
kakanninta ya binne dukiya acikin wannan ramin.
Kinga ma bishiyar giginyar da nake fada miki
keda ganinta ai kinsan ta dade dubi fa saboda
tsayi harta lankwashe kamar macijiya.
Aisha ta zubawa bishiyar idanu na yan dakiku
sannan saita dawo da idanunta cikin Ramin.
Toh aisha yi maza kiyi kiranta koma koma gida
da wuri naga sha dayan har ta gota Aisha ta
sauke jakarta daga kafada sannan ta bude jakar
shafiu ya matso kusa da ita cikin sauri ya haske
cikin jakar da cocilan hannunta na rawa ta dauko
dutsen sannan ta murza shi atafin hannunta
Sabanin yadda sukayi tsammani guguwa zata
tashi awurin awannan karon lokaci guda balbelar
ta bayyana abakin ramin ta kada fiffike tace Ai ina
nan kusa daku bama sai kinyi bayanin komai ba
duk shawarar da kuka yanke jiya ina nan tare
daku inajinku In banda abinku ai ni ma ina iya
dauko muku akwatin don baku san irin kaunar da
mahaifinku ya nuna min bane shiyasa kuma nayi
masa alkawarin isar da duk wani sakon nasa.
.
Tana gama fadin maganar sai tayi girgiza nan da
nan kamar budar ido sai kasar wurin ta fara
tsagewa sannu ahankali sai sukaga akwatin ta
babbako daga cikin kasa ita kadai kaikace raine
da ita sannu ahankali ta sauka akusa da inda
motarsu take.
Balbelar ta kada fuffukanta sannan ta dube su
tace Shikenan kwadayinku ya kwanta?
Aisha da shafiu suka gyada kai lokaci a tsorace
domin abinda suka gano yayi matukar girgiza su.
To ni zan tafi sai kuma mun sake haduwa. Kafin
kiftawa da bismilla ta bace. Shafiu ya dubi aisha.
Aisha ta dubi shafiu jikinsu na rawa cikin sanda
shafiu ya matsa kusa da akwatin ya dallara
hasken cocilarsa kamar yadda yayi tsammani
haka ya ganta to saidai bata kai girman dayayi
tunani ba duk jikin akwatin jajur yake da tsatsa

tun da yake bai taba ganin irin akwatin ba ko da
kuwa a hoto ne domin wannan akwatin a dunkule
take sunduki sunduki.
Haka nan akwai wasu abubuwa masu kama da
madauki ajikin akwatin har guri shida awannan
lokacin ne to aisha tayi abinda ta baiwa shafiu
mamaki......
KUDI DA MACIJI - 32
.
Hakanan akwai wasu abubuwa masu kama da
madauki ajikin akwatin har guda shida awannan
lokacin ne to Aisha tayi abinda ta baiwa shafiu
mamaki domin yana tsaye akan akwatin sai yaga
Aisha ta matsa kusa da akwatin ta durkusa
sannan saita sa hannu ta dafa akwatin tsawon
lokaci tana nan a durkushe duk da yake baya iya
ganin idanunta amma jikinsa yabashi cewa kuka
take yi.
Kukan me kikeyi Aisha?
Babu komai. Tace dashi bakinta na rawa sannan
saita mike tsaye ta dube shi tace Tayaya zamu
iya sa ta acikin mota?
Shafiu ya bude baki kenan zai amsa sai wata
bushashshiyar murya daga cikin duhun tace da
can lokacin da kukayi satar bakuyi tunanin hakan
ba?
.
Aisha da shafiu suka juya a firgice sannan ne to
sukayi ido biyu da yansandan kowannensu rike da
bindiga suna zazazare idanu.
AISHA TA KWALLA IHU A RAZANE.
** ** ** **
Yansandan suka dubi juna a rude cikin tsananin
mamaki sa'ar da Aisha ta gama basu labarinta.
Lokacin da yansandan suka ritsa su sun yi niyyar
tafiya dasu ofishin yansandan gaba dayansu har
da akwatin to amma kukan da aisha tayi ta
rafsawa a tsorace tana magiyar cewa abarta
zatayi bayani shiyasa INSFETA ZAKARI ya amince
sannan yasa yansandan suka kawo motarsu
bakin ruwan aka jefa aisha da shafiu aciki sannan
aka nemi dasuyi bayanin abinda sukeyi abakin
ruwan da wannan uban daren kuma dasu fadi

inda suka samo akwatin in dai ba sato ta sukayi
ba.
Don haka sa'ar da aisha tagama basu labarin sai
sukaji abin kamar almara Insfekta Zakari ya
harari aisha gamida buga mata tsawa yace Ke
kada ki raina mana hankali yanzu ke kina nufin
mu yarda da wannan tatsuniyar da kika fara
mana?
Aisha ta fashe da kuka wallahi ba karya nakeyi ba
ai ga akwatin nan gakuma takardar wasikar nan
ma agurinsa ta nuna shafiu wanda ke zaune
bayako motsi saboda tsabar tsoro duk da
wayewarsa babu abinda yake matukar tsoro irin
DANSANDA.
Yanzu idan nace inason naga ita takartdar da
kakan naki yabaiwa aljanar tabaki zaki iya nuna
mana? Insfekta zakari ya tambayeta cikin sauri.
Aisha ta dubi shafiu tace Basu takardar nan
shafiu.
Jikinsa na rawa ya lalubo takardar daga aljihun
wandonsa ya mikawa Insfekta zaka.
Insfekta Zakari ya zurawa rubutun ajamin idanu.
Dayake wani zamani daya wuce yataba karatun
Allo rubutun ajamin bai wani bashi wahalar
karatu sosai ba amma duk da haka da kyar a
daddafe ya hada bakaken sannan ya karanta wa
sauran yansandan A Fili.
Jami'an tsaron sukayi shiru na tsawon lokaci
sa'ar da suka fahimce ashe akwatin dake nan
dab dasu acike take da dukiyar Milyoyin Kudi.
Insfekta zakari yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi
Aisha da shafiu yace na yarda da abinda kuka
fada amma fa hakan baya nufin bazamu iya cazar
ku da laifi kwata kwata bane kunga dai kayan nan
da kuka dauko suna da hadarin gaske tunda ko
shima kakan naki dukiyar ba tasa bace sata yayi.
Saboda haka kinga dolene hukuma tayi bincike
akai mai tsayin gaske kafin a gano wanda ya
mallaki dukiyar nan tun tsawon shekaru dari da
ashirin. Ya danyi shiru.
Aisha taci gaba da shishshikar kuka hakan ya
daya gani yayi matukar faranta masa rai don
haka sai yaci gaba da cewa amma duk da

wannan hadarin da kuke ciki idan kuna so zan iya
taimakon ku.
Aisha da shafiu suka dubi juna a tsorace
Muna....so suka amsa baki daya
Insfekta yayi gyaran murya yace to abinda nake
so daku shine kuyi gum da bakinku kada ku sake
wani yaji labarin akwatin nan sannan kuma zan
rike wannan wasikar agurina zamuci gaba da
bincike har zuwa lokacin da zamu gano mai
dukiyar ku kuma kuyimin alkawarin zakuyi shiru
da bakinku idan kukayi haka zan sallame ku
yanzun nan ku tafi gida idan kuka sake labari ya
riskemu cewa kun bada labarin acikin gari to
zamuyi muku kamun Yan Fashi kun yarda?
.
Cikin sauri su aisha suka gyada kai insfekta
zakari ya kunnewa sigari wuta cikin farin ciki
sannan ya lalubi aljihunsa ya dauko Albashinsa
cancakat da aka biya shi awannan ranar ya
mikawa Aisha yace ga wannan yan mata kya rage
bacin ran da zaki shiga nasan tuni kin gama
kasafin abinda zakiyi da dukiyar kakanki ko? To
hukuma bazamu amince da haka ba domin shima
ba nasa bane sata yayi da'ace wasikar ta nuna
cewa dukiyarsa ce to da babu abinda zai hanamu
baki kayanki.
Aisha ta karbi kudin a tsorace shafiu kuwa ji yake
kamar zuciyarsa zata fashe domin yanaji yana
gani an raba su da milyoyin kudi an basu dubun
naira
.
Ku tashi ku tafi ku kuma iya bakinku kunji?
Insfekta zakari ya umarce su
Jikinsu na rawa suka nufi marsandin shafiu har
suka shiga motar suka tafi babu wanda yace da
wani QALA
tafiyarsu keda sai Insfekta Zakari ya dubi sauran
yansandan ya fashe da dariya sannan yace to ku
saurara da kyau kuji yau Allah yakawo karshen
wahalar da muka dade muna sha shekara da
shekaru ina fatan kowa daga cikinku zai iya
bakinsa domin wannan wata kyautace daga Allah
ina ganin abinda ya dace kawai shine mu sa

bakin bindiga mu bude akwatin nan mu kasafta
dukiyar dake ciki kowa tasa ta fisshe shi ko kuwa
ya kuka gani? Kunsan dai ba aikin kama barayi
aka turo mu baki ruwan nan ba kwantar da
tarzoma muka zo
KUDI DA MACIJI - 33
.
Mu kasafta dukiyar dake ciki kowa tasa ta fisshe
shi ko kuwa ya kuka gani? Kunsan dai ba aikin
kama barayi aka turo mu bakin ruwan nan ba
kwantar da tarzoma muka zo.
.
Audu ne yafara cewa haka za'ayi yallabai sannan
sai sauran ma suka amsa baki daya mintuna
biyar da faruwar hakan yan sanda suka sa bakin
bindiga suka balle daddiyar akwatin yar shekara
dari da ashirin a karkashin kasa.
.
Insfekta zakari yakoma cikin mota ya dauko
cocila sa'ar da aka bude tsohuwar akwatin
yansandan guda takwas suka zagaye ta kowa na
hadiyar yawu zasu kwashi banza daga inda suke
tsaye suna iya hangen wasu abubuwa manya
manya acikin akwatin.
Koda Insfekta zakari yataho dauke da cocilan sai
yansandan suka dada marmatsawa domin su ga
zinare da lu'u lu'un dake ciki Insfekta zakari ya
haske cikin akwatin nan da nan yansandan suka
dauke Numfashi lokaci guda cikin kaduwa da
abinda suka gani.
Insfekta zakari yaji kamar hanjinsa ya tsinke.
A ajiye acikin akwarin GUMA-GUMA dasu har
guda biyar wasu manya manyan duwatse ne kan
kura.
.
Cocilar dake hannun insfekta zakari ta kwace ta
fada cikin akwatin fus ta fashe ya juyo bakinsa a
kafe ya dubi Audu yace Mun dauki adireshin
yaran nan kuwa ?
Audu ya girgiza kai cikin kaduwa gami da
GODEWA ALLAH DA BA KUDINSA AKA BAWA 'YAR
KYAKKYAWAR NAN BA yace.
Bakace mu dauki adireshinsu ba yallabai.

** ** ** **
Washegari misalin karfe hudu da rabi na yamma
shafiu yayi fakin da bakar marsandinsa a kofar
gidansu aisha zuciyarsa cike da bakin cikin ta
leko ta koman da suka gani adaren jiya.
Ga mamakinsa lokacin data fito saiyaga ita ko
ajikinta wai an mintsini kakkausa
(ASMA'U MATORI)
domin cikin farin ciki ta tare shi tana murmushi
SANNU DA ZUWA MY ONE.
Shafiu ya dubeta fuskarsa a murtuke yace na
fahimce ke Aisha ko jimamin asarar da kikayi
bakyayi Aisha ta dube shi gamida girgiza kai
daman ba rabona bane shafiu haka allah ya
kaddara domin idan abu ya kasance rabonka ne
Allah yabaka duk duniya babu wanda ya isa ya
hanaka shi haka nan ma idan ba rabonka bane to
fa babu wanda ya isa ya baka.
Ina fatan zaka manta da komai musa abinda yake
gabanmu acikin zuciyarmu Ta danyi shiru sannan
tace babu abinda nake kauna aduniya fiye da kai
Shafiu wallahi dukiya dana rasa ajiya bata kai ko
rabinka ba agurina Nagodewa Allah da bakaine ka
kubuce min ba.
.
Hakan datace shi ya tausasa zuciyar shafiu tayi
fari tas don haka ya saki wani fatalwan
murmushi yace Haba ai abin ne da ciwo...to
amma dai ta bakin naki domin duk dukiyar da zan
samu aduniya banza ce idan babu ke Aisha.
Aisha ta lumshe idanu naji dadin abinda ka fada
wallahi harkasa zuciyata tayi sanyi.
Yanzu ma ai shiryawa zakiyi mu tafi Aisha ta
bude baki cikin mamaki ina zamu?
Mahaifana ne suke son su ganki jiya nabasu
labarin ki.
Aisha ta rufe idanu a kunyace tace
'kai haka da wurwuri?
Shafiu ya harareta yace haba aisha shekarata
nawa ina kaunar ki? Don Allah je ki shirya kifito
mu tafi suna can suna jiran isowarmu.
.
Gani nan zuwa my one ta ruga gida aguje shafiu

yabita da kallo sannan ya girgiza kai cikin
murmushi
'Karfe biyar na yamma suka isa gidansu Shafiu
aisha ta caba ado da daya daga cikin leshin da
shafiu ya saya mata ya kuma sa akayi mata
dinkin gaggawa duk da yake duniya ta juyawa
mahaifin shafiu baya saida aisha ta rude da ganin
yadda aka tsara farfajiyar gidansu shafiu.
Shafiu ya bude mata kofa ta fito sannan sai ya
dubeta da murmushi yace zo muje bayan mota
nabaki abinda na sayo miki domin ki basu
amatsayin kyautarki ta musamman ga iyayena.
Aisha ta rike baki duk duniya banida mai kula
dani kamar ka.
Shafiu yayi murmushi sannan cikin farin ciki sai
ya zura dan makulli abayan motar domin bude
but din motar don ya dauko kyautar.
Yana bude bayan motar sai yayi tsalle gefe guda
a tsorace
aisha ta rike kafadarsa a firgice tana duban bayan
motar sannan ta karkada fuffuke tace
KUYI HAKURI NA TSORATA KU KO? Ina son ku
sano ba nufina na cuce ku ko na tsorata ku ba
nazo ne domin na baku dukiyarku da akaso a
zalunce ku adaren jiya yau Allah ya nuna min
ranar da zan cika alkawarina dana dauka tun
tsawon shekara dari da shirin da suka wuce.
Ku leka ku gani dukiyar ku tana bayan motar
nasan jiya kwana kukayi bakuyi barci ba kun
hadu da azzalumai bata gari ai nayi maganinsu
danasa musu GUMA GUMAN DUWATSU ACIKI.
.
Balbela tayi shiru sannan sai ta dubi aisha tace
To Aisha sai watarana daga yau bazaki sake
ganina ba tana gama fadin haka saita bace.
Shafiu ya dubi aisha murmushi ya subuce masa
tun kafin ma ya leka bayan but din motar ya
hangi haske da walkiya na tashi aciki.
Jikinsu na rawa suka leka numfashinsu ya dauke
cak sa'ar da suka ga but din motar cike da wasu
irin kananan duwatse masu kyawun gaske suna
haske da walkiya.
.

Dukiyarmu ta dawo aisha shafiu yace sannan yayi
tsalle sama ya dire yayi ihu cikin murna ga
mamakinsa saiyaga Aisha ba murna takeyi ba
maimakon hakan ma sai hawayene ke zuba daga
idanunta
Kukan me kuma kikeyi?
Aisha ta goge idanu tace shafiu kada fa ka manta
da cewa wannan dukiyar ba hakkinmu bace
domin shima kakan nawa..
.
KAKAN NAKI SHIMA ME??
KUDI DA MACIJI - 34
.
KARSHE.
THE END
.
Kukan me kuma kikeyi?
Aisha ta goge idanu tace Shafiu kada fa ka manta
da cewa wannan dukiyar ba hakkinmu bace
domin shima kakan nawa SATO TA YAYI.
.
Shafiu yaji kamar Aisha ta kwada masa guduma a
kirji To yanzu me kike nufi? So kike mu dauki
dukiyar aka mu shiga gari neman wanda akayiwa
sata shekaru dari da shirin da suka wuce ko me?
.
Ganin ransa ya baci sai Aisha ta matsa kusa
dashi ta dafa kafadarsa akaro na farko tace a
tausashe Shafiu abinda nake son ka fahimta
shine wannan dukiyar ba tamu bace bamuda
hakkin taba ta kanaji fa abinda yace shima sato
ta yayi.
Shafiu ya dubi asiaha a fusace yace To Idan
dukiyar ba tamu bace ta wacece?
Fada min mana aisha dukiyar wacece aduk fadin
garin nan?
.
Aisha ta fashe da kuka sannan ta girgiza kai tace
WALLAHI NIMA BAN SANI BA.
Shafiu ya matsa kusa da ita yace kada ki sani
ciwon zuciya Aishata Yaya Arziki yana binki kina
gudunsa ?
.

KARSHE.
.
NAZIR ADAM SALIHI (Nas).
.
KAMMALAWA.
.
Alhamdulillahi
Alhamdulillahi
Alhamdulillahi
.
Dukkan Godiya Yatabbata Ga Allah Madaukakin
Sarki Daya Bani Damar Kawo Karshen Wannan
Littafi Mai Suna
KUDI DA MACIJI (Maganinsu Kashewa)
Wanda Shahararran Marubucin Nan Wanda Yaga
Jiya Yaga Yau Kuma Muke Fatan Yaga Gobe Da
Jibi Insha Allah Sannan Jagoran Masu Tsara
Rubutun Labaran Fina Finan Hausa Ayanzu.
NAZIR ADAM SALIH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login