Showing 24001 words to 27000 words out of 29993 words

Chapter 9 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf

12 Jul 2025

1715

zuwa
gobe? Aisha ta gyada kai riketa ma nan da wata
daya ka dawo da ita
bana fatan sati guda ma ya wuce ban gano inda
dukiyar nan take boye ba y danyi shiru sannan
sai ya dubi aisha da murmushi
idan dukiyar nan tazo hannunmu dame dame zaki
saya ma'ana me zakiyi da kudaden? Aisha ta
sake fashewa da dariya tace Oh na shiga uku
wannan fa shine zakin mazallako wai 'Da daga
ciki yana rokon uba kwabo tun kafin dukiyar tazo
tun kafin ma kayi tunanin inda zaka sayar harka
fata kasafi shafiu ya dubeta cikin dariya.
Haba aisha ai dillalin wada shiyasan kudin jariri
ke dai a sami kudiyar ai sayarwa ba aikibane
agurina ya danyi shiru
Duk da haka dai ya kamata ki fara kasafin abinda
zakiyi da kudin kinga da sunzo hannu shikenan
sai Yi aisha ta sake fashewa da dariya domin ita
harga Allah bata taba kawowa aranar za'a sami
wata dukiya binne a kasa ba to amma gudun
kada yaga kamar bata goyon bayansa saita
dubeshi tace cikin dariya.
To ni yanzu shafiu idan na sami wadannan
kudade masu dimbin yawa me zanyi dasu ne?

Shafiu ya wangame baki cikin kaduwa da mamaki
yace
Me zakiyi dasu fa kikace? Haba aisha ai KUDI DA
MACIJI MAGANINSU KASHEWA.
Aisha ta fashe da dariya Allah nuna mana ranar
kashe su.
Shafiu ya lumshe idanu cikin farin ciki Yace
Ameen Ameen Aishata.
** ** ** **
Karfe tara saura kwata daidai ya karaso Danmasu
hotel zuciyar nata sake sake da zane zane idan
banda nufin Allah ma da tun a hanya zaiyi hadari
domin sau uku manyan motoci suna auna shi dan
ko kusa ko alama tukin kawai shafiu yakeyi
amma hankalinsa baya kan motar haka nan duk
kusan minti biyu sai ya shafi aljihunsa ya
tabbatar tana nan domin ga shafiu takardar
tamkar Cek din milliyar dubu take. Shafiu...
KUDI DA MACIJI - 28
.
Domin ga shafiu takardar tamkar cek din milliyar
dubu take.
.
Shafii yayi mamaki sa'ar da yayi fakin da
motarsa ya nufi farfajiyar otal din ba wani abune
sashi mamaki ba sai ganin babu kowa a farfajiyar
otal din ko ina ka duba a bushe kamar makabarta
sai jifa jifan ma'aikatan otal din nan da sunan
sunturi
Shafiu ya nufi dakin tarbar baki na otal din kenan
sai ya hangi usman taska shi kadai yana zaune
akan kujerar roba ya jingina da bishiyar dabino
tsinken tsire a hannunsa na dama ha nan
hannunsa na hagu na rike da sigari yana ta
karawa sararin samaniya hazo abinda idan ka
dube shi da kyau alokacin saika rantse da Allah
babu abinda ke damunsa aduniya nan kuwa idan
da za'a rutsa shi ko naman jikinsa za'a saya ba
zai biya kudin bashin da ake binsa ba.
Shegen sama me ya kawoka haka yau tunda
wurwuri naga kuma kamar ma kai kadai ne ba
joni ko?
Usman taska ne ke magana shafiu ya matsa kusa

dashi suka tafa sannan ya zauna akan wani
katon dutse fari dake kusa da bishiyar dabinon ya
dubi Usman taska yace.
.
Me yafaru ne naga Otal din naku haka So Dry
kamar an share naga kuma banji hayaniyar yan
duniya agurin wanka ba Usman taska yayi
murmushi yace.
Yaushe rabon ka da otal din nan ne?
Shafiu ya dan karkata kai gefe kamar zakara yana
tunani
nafi sati guda rabona da nan kasan ni yanzu
nafara girma aure ma nake son yi na huta kune
dai kullum jiya ya yau ba kwa girma usman ya
fashe da dariya yace.
Haba shafiu girma dai ai mun riga munyi shi tun
da dai ba haka aka haife mu ba saidai ko
HANKALI ya danyi shiru yana kyakyata dariya
wacce lalatacciyar ce zata yarda ta aureka shafiu
ya dubi usman da murmushi.
.
Yanzu dai ni ba wannan bace ta kawo ni tashi
zakayi mu dan zagaya zuwa can bakin dam gurin
yan wanka saika bani labarin abinda ke faruwa
din cikin sauri usman taska ya mike tsaye daman
wallahi nagaji da zama gashi kuma yau Otal din
babu kowa duk sai gundura.
Suka fara tafiya ahankali zuwa bakin katon dam
din dake fuskantar otal din daga inda suke suna
iya hango ruwan dam din yana tambal tambal
abin gwanin ban sha'awa gashi kuma bishiyoyi da
sukayi sahu sahu abakin dam din duk anbisu da
kananan kwaya kwayen lantarki saisi sukeyi
kamar rana hakan shi ya baiwa ruwan dam din
launin tsanwa tsanwa shudi shudi idan ka
hangeshi daga nesa.
Wai me yake faruwa ne usman? Shafiu ya
tambayi usman ya busa hayakin sigarinsa sama
sannan ya yagi dunkulen nama daga jikin tsinken
tsiren ya fara tauna cakam cakam kamar me cin
cingam.
Wasu yan iska ne wallahi sukazo daga cikin gari
zasuyi fati kawai sai suka kaure da fada har an

kashe mutum uku kuma abin haushi wai duk akan
wata Bebi.
An kashe mutum ? Shafiu ya tambaya cikin
kaduwa
an kuma raunata mutum ashirin bashiyasa ai
kaga bakin ruwan ba kowa tun jiya yan sanda
suke kame har mutum abin ya tabamu har an
kama mutuniyata ma MONIKA shafiu ya fashe da
dariya.
Saika tafi beli usman ya girgiza kai yace Allah
sawwaka kai nifa yanzu wallahi so ma nake na
tuba na koma ga Allah wadannan al'amuran duk
sun fara isata domin na fahimci kamar duk babu
riba
Da ka kyautawa kanka wallahi shafiu yace.
Koni nan ma da kake ganina na tuba wata
yarinya na samu ustaziyya mai yawan wa'azi duk
ta karyamin gwiwa wallahi.
Usman ya fashe da dariya yace
Uhm.. Uhm fa shafiu kada kayi tuban muzuru.
Allah ya sauwake shafiu yace gamida murtuke
fuska ganin hakan sai usman yayi shiru sukaci
gaba da tafiya zugum zugum abakin dam din.
.
Wai ina zamu ne? Usman ya tambaya sa'ar da
yaga tafiyar tayi nisa har sun fara tunkarar
Gandun sarki
Akwai abinda nake son nagani kasan kwana biyu
ban zagaya bakin dam din nan ba sukaci gaba da
tafiya sannu ahankali har suka kawo daf da wasu
manya manyan bututu na ruwa an tara su jibgi
guda abakin dam din.
Wadannan kuma bututun na menene?
Shafiu ya tambaya lokaci guda kuma yana kallon
katon ramin mai mai tsayin gaske dake gabansu
tuni har an fara binne wasu daga cikin bututun
ruwan acikin dogon ramin.
Kamfanin ruwa ne ke kokarin kafa wasu manya
manyan injinansu wadanda zasu ringa tura
isashshen ruwa cikin gari da tuni ma aikin yayi
nisa in badan ma'aikatan dake haka sun tarar da
dutse ba shafiu ya dubi usman cikin mamaki
dutse fa kace ainaga duk fadin dam din nan babu

wani babban dutse ballantana ma har a sami
wani dutse a karkashin kasa.
Usman ya zuki guntuwar tabar dake hannunsa ya
jefa sauran cikin ruwa.
Abinda yayi ta baiwa mutane mamaki kenan
yanzu kokarin da akeyi shine a kokarta fasa
dutsen idan kuma ba zai fasu ba sai a karkata
ramin yabi ta wata hanyar daban shafiu yayi
shiru yana sauraron usman da ace rana ne babu
abinda zai hana usman ganin fuskar shafiu jike
shakaf da gumi hakanan bugun zuciyarsa ya karu
akan na da.
.
Adaidai inane aka sami dutsen usman ya dubi
usman shafiu yace Ga ramin nan abayanka kusa
da BISHIYAR GIGINYAR CAN shafiu yaji yawun
bakinsa ya kafe cikin sauri ya dubi usman taska
yace
Ko zan sami cocila a otal dinnan naku?
Usman ya dubi shafiu ya girgiza kai kaifa baka
rabuwa.......
KUDI DA MACIJI - 29
.
Kaifa Baka Rabuwa da rigima me kuma zakayi da
cocilar? Shafiu yayi masa murmushi yace
'Ka dauka kai kaine taska makunshin labarai? So
nake nima naga dutsen da idanuna yana rufe baki
sai ya nufi ramin cikin sauri ya gangara ciki
idan ka gama tsurkun ka sameni anan usman
yace sannan sai ya kunnawa sabuwar sigari wuta
ya zauna akan yashi ya zurawa ruwan dam din
idanu yana tambal tambal
Shafiu na shiga cikin ramin sai yaji ya taka wani
abu mai taurin tsiya kamar dutse jikinsa na rawa
ya lalubi aljihunsa ya zaro wayar salularsa
sannan ya danna wani madanni nan da nan
haske yazo a fuskar wuyar salular tsahon lokaci
shafiu yana nazarin abin ko shakka babu abin
yaso yayi kama da dutse amma shafiu ya tabbata
ba dutse bane domin tun sa'ar da kafafunsa suka
dirga akan abin yaji sautin baiyi kama da na
dutse ba.
To amma saboda ya matsu daya tabbatar da

abinda yake zargi sai wata dabara ta fado masa
jikinsa na rawa ya fito daga cikin ramin yafara
dube dube ba a dade ba ya hangi wani dan
madaidaicin dutse ya buga akan abin da karfin
gaske maimakon yaji sautin yabayar da KWAS.
Sai yaji yabada wani DUM.. Nan da nan shafiu ya
mike tsaye ko shakka bayayi abinda yake zargine
dukiyar masoyiyarsa sa ce Aisha Allah ya nuna
masa ita a saukake.
.
Usman ya mike tsaye gamida hamma sa'ar da
shafiu ya nufo inda yake cikin sauri
harka gama tsurkun?
Shafiu bai bashi amsa ba sai yace
yaushe ne masu hakar ramin nan suke tunanin
fasa dutsen? Usman ya fesa hayaki sama.
Me yiwuwa sai nan da sati guda kasan rigimar da
akayi anan shekaranjiya tasa jami'an tsaro sun
sa dokar tabaci anan harna tsawon sati guda
kafin su gama bincike binciken su na Al'ada.
Kana nufin kace daga yanzu har zuwa sati guda
ba'a son aga kowa agurin ? Usman ya gyada kai
yace Koda da rana ne kuwa ballantana da
daddare shafiu yaji yawun ya dada yin sallama
daga bakinsa tuni har yafara tsammanin yazama
milloniya wai gashi nan ma har yan maula sun
zagaye shi yana ta bari da naira.
Samarin biyu sukayi cirko cirko na tsawon lokaci
suna kallon juna can sai shafiu ya dubi doguwar
bishiyar giginyar nan yace wai usman irin wannan
bishiyar giginyar takanyi kamar shekara nawa
aduniya kafin ta mutu? Usman ya busa hayaki
sama acikin tsananin mamaki domin ya lura
akwai wani abu a tattare da al'amarin shafiu.
Wani kakana ya taba cewa dani bishiyar giginya
na iya kaiwa shekaru casa'in aduniya koma fiye
da haka in har ba sareta akayi ba nan da nan
shafiu yaji gumi ya fara sartu abayan rigarsa.
Shafiu me yafaru ne kaketayimin irin wadannan
tambayoyi kamar wani dan sandan ciki? Shafiu
yayi shiru bai amsa ba wai tunanin me kaketayi?
Shafiu ya juyo firgigit sannan sai ya dubi usman
da murmushi yake yace.

Tunani nake ina ma ace bishiyar giginya tanada
yawan inuwa dana shukata a tsakar gidanmu.
.
TAKWAS 8
Haba Aisha kinsan dai ai ba zanyi miki karya ba
wallahi saida na taba saman akwatin da hannuna
na tabbata itace ke har bishiyar giginyar da aka
fada aciki wasikar na gani Aisha tayi shiru tana
sauraronsa cikin tsananin kaduwa ta fara
fahimtar abinda take dauka amatsayin tatsuniya
ne ke naman ya zama gaske.
Yanzu abu daya nake son kiyimin Aisha indai
kikayi hakan na tabbata gobe iyanzu dukiyar tana
hannunki Don ba'a jira lamarin kudi ba kuma a
bata lokaci ko kankani
Me kake son nayi maka?
Shafiu ya danyi shiru sannan yace Ina dutsen da
kikace Aljanar nan ta baki?
Aisha ta bude baki cikin kaduwa me zakayi
dashi?
So nakeyi kiyi kiran ta mu tambayeta inda
hakikanin akwatin nan take koma kara
tabbatarwa domin in dai abindata fada gaskiyane
yakamata tasan inda aka binne dukiyar taki.
Ko bahaka ba?
Aisha tayi shiru na tsawon lokaci tana kallon
kofar gidansu alokacin karfe goma da rabi na
dare domin shafiu na barin otal din gidansu Aisha
ya wuce kai tsaye da yake uwar rikonta kande ta
dauke daya daga cikin atamfofin da shafiu yabata
ba'a sami wata matsala ba wajen fitowar aisha.
Abin mamaki kande ce ma turo ta da kanta.
Yi sauri ki fita mana sai wani nuku nuku kikeyi
wannan yaro ai ya isa dan arziki wallahi ga shi
daga zuwansa har ya fitar damu daga cikin
tsummokara.
To aisha kefa nake jira kinyi shiru.
Aisha ta dubeshi a tsorace tace wallahi shafiu
tsoron kiran Aljanar nan nakeyi kaga....
Shafiu ya ya daga mata hannu menene abin
tsoron bayan tace bazata cutar da ke ba?
Aisha tayi batace komai ba.
In kuma kina ganin dai tsoron bazai barki kiyi

kiranta ba to kirawo ta mana yanzu tunda ina
tare dake.
.
Aisha tayi ajiyar zuciya in dai kana tare dani bana
tsoron komai shafiu bari na kirawota ta bude
jakarta ta fara laluben farin dutsen abinda bata
sani ba shine tuni cikin shafiu ya fara kugi domin
shima a bala'in tsorace yake to amma da yake
ransa yana kan dukiyar dake binne saiya dake
zuciyarsa amma gumi tun daga goshinsa har
zuwa kan babban dan yatsan kafarsa zuba yake.
Aisha ta dauko dutsen daga cikin jakar ta dorashi
akan tafin hannunta ta lumshe idanu sannan
ahankali saita fara murza dutsen a tafin
hannunta.
Shafiu yayi mutuwar tsohuwa ko kwakkwaran
numfashi bayayi.
KUDI DA MACIJI - 30
.
Shafiu yayi mutuwar tsohuwa ko kwakkwaran
numfashi bayayi.
.
Wata guguwa mai karfin gaske ta turnuke
zagayen motar sannan sai sukaji motar ta fara
girgiza kamar za'a dauke su sama tsawon lokaci
ana girgiza motar sannan kwatsam sai balbelar
ta bayyana a gaban motar.
Matasan biyu suka zura mata idanu cikin kaduwa
Kada kuji tsorona ku tambayi duk abinda kuke so
daman nasan zaki neme ni ta dubi Aisha.
San..nu da...zuwa aisha tace bakinta na rawa
Yawwa aisha yi sauri ki fadi abinda kike son fada
ina BIRNIN SIN fa kuka kirawoni sauri nakeyi zan
koma na baro yarana acan.
Aisha ta dubi shaiu sannan ta dubi balbelar cikin
hali So...muke mu san inda aka binne akwatin.
Balbelar ta girgiza kafadunta sannan ta dubi
shafiu tace Ramin daka shiga dazun nan anan
akwatin take kasan akwai wani bawana dana
ajiye shi yayi gadin akwatin yau shekara dari da
shirin yana zaune agurin yana gadinta. Ko dazu
ma saida ka taka shi baka ganshi ba.
Shafiu ya dubi aisha duk da yake a bala'in

tsorace yake saida ya daga mata gira to in
bakuda wani abu kuma da kuke son tamaba ni
zan tafi
Mun...gode Madalla sai kuma wani jikon Aisha
tace bakinta na rawa.
Balbelar ta dubi shafiu tace idan Allah ya kaddara
auranka da ita ka riketa da kyau yarinyar kirki ce
sannan ta bace.
Matasan biyu sukayi ajiyar zuciya lokaci guda
shafiu ne yafara magana to sai yaya kuma? Saiki
shirya gobe warhaka muna can in Allah ya yarda
ko sha biyun dare bazatayi mana acan ba zamu
dawo da dukiyar
kana nufin har dani zamu tafi? Aisha ta tambaye
shi a tsorace.
Shafiu ya fashe da dariya cikin farin ciki yace
Haba Aisha kiyi amfani da hankalin ki mana ai
idan bakya agurin akwatin bazata dauku ba don
bana tsammanin karama ce maiyiwuwa mai
nauyin tsiya ce.
Kuma ni me zan iyayi ina mace?
Shafiu ya dubeta kana ya matsa dab da ita har
tanajin numfashinsa afuskar ta yace Bakiji abinda
tace ba? Akwai wani bawanta dake gurin yana
gadin akwatin shi zamu sa ya janyo mana
akwatin daga karkashin kasa.
Aisha ta bude baki cikin kaduwa.
Shafiu kada fa son abin duniya yasa ka zarewa in
banda abinka a ina zamu ganshi Aljani ne fa
shafiu ya sake fashewa da dariya wannan shine
dalilin daya nace dake zamu tafi idan munje bakin
ramin saiki murza dan dutsenki idan balbelar ta
bayyana saiki roketa alfarma tasa wannan bawan
nata dake gadi agurin ya zaro mana akwatin ko
kuwa ya kika gani?
Aisha ta dube shi da murmushin farin ciki adaidai
lokacin ne to Aisha ta kula da kansa Kai shafiu
yaushe ka aske wannan gashin naka?
Shafiu ya fashe da dariya sai yanzu ma kika lura?
Aisha bata iya bashi amsa ba saitaci gaba da
kallonsa sama da kasa Alokacin ne ma ta lura
ashe har zako zakon faratan dake hannunsa duk
ya yanke.

Wallahi daka aske gashin saika zama kamar ba
kai ba.
Shafiu yayi murmushi sai nayi muni ko?
Aisha ta girgiza kai tace haba dai ai haka ma
wallahi kafi kyau inama ace ina iya kallon ka
sosai batareda jin kunya ba
SUKA FASHE DA DARIYA.
** ** ** **
Washegari tun da asuba shafiu ya tashi yayi
sallah. Wannan shine karo na farko acikin
shekaru goma sha takwas da shafiu ya tashi
sallah da suba rabonsa da sallah tun yana dan
shekara goma aduniya alokacin bai gagari
mahaifansa ba.
Mahaifin shafiu zaune a dakin shakatawa suna
karin kumallo sai suka ga shafiu ya shigo falon
ahankali kamar maiyin sanda mahaifan suka kura
masa idanu cikin kaduwa domin sun san shafiu in
har ba makaranta zashi ba babu abinda zai tashe
shi da karfe takwas na safe.
Mahaifinsa ALHAJI SADIQ ya kalle shi sama da
kasa cikin kaduwa domin ya lura da cewa
dugunzunzum din gashin nan da yayi matukar
tsana shafiu ya aske shi.
Ina kwananku shafiu ya gaishe su a durkushe
Lafiya lau shafiu... Suka amsa baki daya cikin
mamaki tsawon lokaci babu wanda yace kala can
sai Alhaji sadik ya dubi dansa yace a sanyaye
shafiu yau kuma shiriya ce Allah ya kawo ma?
Shafiu kansa a durkushe yace Eh baba.
Zuwa ma nayi na roke ku gafarar abinda nayi
muku abaya. Nayi muku alkawarin daga yau
nabar shirme da sakarci mahaifiyar shafiu ta
fashe da kukan farin ciki Mun yafe maka shafiu.
Allah sadik ya tashi tsaye sannan ya dubi dansa
cikin farin ciki Na godewa Allah daya shirya min
kai kuma tunda Allah yasa shiriya tazo maka
saika nemo wacce kake so ayi maka aure.
Shafiu ya dago kai cikin farin ciki yace Gobe in
Allah ya kaimu zan zo muku da ita baba
mahaifansa suka dubi juna sukayi murmushi toh
ai shikenan shafiu kuma indai naga ka zarce
ahaka zan mika ma ragamar harkokina

ahannunka duk da yake dai ba wani abu nake
dashi kamar da ba amma In Allah yakaimu jibi
za'ayimin wani tsohon biyan bashi na kusan
naira Milliyan hudu da zarar an kawo min su kai
zan Dankawa.
Wannan wani abu ne daga Allah lallai babu
abinda yafi komai dadi aduniya irin bin hanya
madaidaiciya shafiu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login