Showing 21001 words to 24000 words out of 29993 words

Chapter 8 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf

12 Jul 2025

1716

ke faruwa ne to wani dan
siririn yaro mai kananan idanu ya shigo gidan
wai ana kiran aisha a waje Kande ta dubi yaron
cikin tsananin mamaki sannan ta dubi aisha
domin tunda Aisha take wani saurayi bai taba
kiranta ba musamman ma kuma yanzu da
sassafe.
.
Jeka kace tana zuwa
kande tace da yaron azuciyarta kuma ta kudiri
mugunta domin ta tabbata duk saurayin da zaiga
aisha cikin wannan tsummokarar bazai kara
sha'awar zuwa gurinta ba Kande ta juya ga aisha
tace
Sai ki fata kiga wanda ke kiran wani asararrane
shima da taya bera bari in banda sakarcin
samarin zamani ma menene abin sha'aqa
agurinki da har zaizo miki haka da sassafe aisha
ta share hawaye batace komai ba saita juya ta
nif kofar gidan itama zuciyarta cike da mamakin
wanda yazo nemanta da sassafe haka kamar
wadda tayi laifi da farko aisha tayi tsammanin ko
wata kawarta ce dake nan makwabta wai ita
SAFIYA to amma kuma idan Safiya ce ai shigowa
zatayi ba turowa zatayi ba.
Aisha ta fita kofar gidan zuciyarta nata sake sake
tana fita kofar gidan saitayi turus a zaune agaban

bakar mota marsandi kofarta a bude sanye da
shudin wando jeans da bakar riga damammiya a
kirjinta an rubuta 50 CENT kafafunsa sanye cikin
wani katon takalmi fari a mulmule kamar tamaula
gashin kansa bucu bucu ya rune shi fari fat
kamar gashin tunkiya idanunsa boye cikin bakin
tabarau SHAFI'U ne yake cin Cingam hannunsa
na hagu dauke da karan sigari tanacin wuta.
Kirjinsa na harbawa Das Das aisha ta matsa kusa
da kofar motar lokaci guda kuma tasa dan
yalolon gyalenta ta rufe hanci domin tuni warin
hayakin tabar ya fara shake mata makwogoro
shafiu ya lura da hakan cikin gaggawa ya jefar da
tabar waje yasa kasan takalminsa ya take.
Tunda bakya son warinta daga yau har abada na
daina shan taba Aisha
daka kyauta wa kanka aisha tace dashi cikin
damuwa tana dubansa
shafiu waya nuna maka gidanmu me kuma ya
kawo ka gidanmu? Shafiu ya dubi aisha cikin
damuwa yace
So da kauna ne yakawoni aisha zuwa gidanku
kuma tambaya nayi aka kawoni kinsan ance me
san tsuntsu shike binsa da jifa har cikin shekarsa
aisha tayi ajiyar zuciya ta sunkuyar dakai akwai
alamun damuwa karara a fuskarta
Shafiu ya dubi aisha sannan ya tausasa murya
bakiji dadin zuwana ba ko? Bakya kaunata ko
Aisha? Akwai alamun karaya karara a muryarsa
akaro na farko sai aisha ta dago kai ta dube shi
ta girgiza kai tace.
Ba kai bane bana so Shafiu ni irin dabi'unka ne
ke damuna shafiu ya dubeta sannan ya dubi
jikinsa cikin tsarguwa.
Dabi'una kamar wanne kenan? Fadamin su aisha
duk abinda bakya so wallahi nayi miki alkawarin
bazan sake yinsu ba har abada dama tuni na riga
nayi miki alkawarin daina shan taba ko?
Aisha ta dube shi cikin tausayi ko shakka batayi
ayanzu tasan da gaske shafiu yakeyi kaunarta
yake akwai wani abu a fuskarsa daya tabbatar
mata da hakan.
.

Dubi gashin kanka guduzumzum kalli faratan
hannunka zako zako kamar aljani fatar bakinka
har dani jan baki dubi irin wannan kwandalelen
zobe dake hannunka shafiu
Aisha tayi shiru shafiu ya shafa duguzumzum din
gashin kansa yace
Idan duk na rabu da wadannan abubuwa zaki iya
kaunata Aisha ?
.
BAKWAI. 7
Tsahon lokaci matasan biyun suna nan agurin
daya a zaune daya a tsaye kawunansu a
sunkuye...
KUDI DA MACIJI - 25
.
Tsahon lokaci matasan biyu suna nan agurin
daya a zaune daya atsaye kawunansu a sunkuye
wannan shine karo na farko da shafiu ya farajin
kunyar wata diya mace aduniya.
.
Bakice komai ba, aisha tayi ajiyar azuciya ta dago
kai ta dube shi akaikaice tace
Yanzu saboda ni duk saika daina wadannan
abubuwan shafiu?
Shafiu ya buga katon takalminsa daya akasa
yace duk abinda kike so na bari fadamin shi Aisha
wallahi nayi miki alkawarin zan bari saboda ke
indai zaki kaunace ni
Aisha ta sunkuyar dakai kasa na dan lokaci
sannan tace a sanyaye
kana Kaunata shafiu? Shafiu ya dubeta cikin
tsananin mamaki yace
saidai inso kike na maimaita miki amma ina
tsammanin aina fadi kalmar ina kaunarki tafi sau
dari tun farkon haduwarmu dake Aisha ta dada
yin ajiyar zuciya akaro na biyu
indai da gaske ne kana sona shafiu ina son ka
kudure aranka da kyakkyawar niyya cewa daga
yau ka daina duk wata muguwar dabi'a dabata
cikin addini amma saboda Allah badan ni ba
shafiu ya dubeta a rude
Ban fahimceki ba aisha
Abin da nake nufi shine ka nutsu kabar mugayen

dabi'a na sabon Allah ka kuma bari don Allah ba
don ni ba kaga sai Allah yabani ladan sanadin
shiriyarka da nayi shafiu ya kurawa aisha idanu
na tsawon lokaci sannan yace
Na fahimceki aisha in Allah ya yarda daga yau
zaki fara ganin canji acikin al'amaruna daga yau
din nan aisha ta dube shi da wani irin yanayi a
fuskar ta mai kamar murmushi tace
Amma danaji dadi shafiu
na fiki jin dadi aisha.
Tunda har nayi abinda ya faranta zuciyarki a karo
na farko ya danyi shiru sannan ai ya dubeta yace
Aisha ina son kiyimin wata alfarma.
Aisha ta dubeshi tace Alfarmar me kuma ni zan
iyayi maka?
Shafiu yace so nake kiyimin abinda ban taba
ganinsa a fuskarki ba Aisha ta dube shi a rude
Menene kuwa wannan abu?
Murmushi nake nufi Aisha tayi sauri ta rufe
idanunta sannan sai wani tattausan murmushi ya
subuce mata shafiu yaji wani dadi ya lullube
masa zuciya.
Daman zanfito kenan ka aiko yaro.
Shafiu ya janyo wata katuwar jaka dake kusa
dashi agaban motar ya ajiyeta akusa da kafar
aisha
mika wannan jakar cikin gida saikizo mu tafi
kinga mun kusan makara aisha ta dubi shafiu
cikin kaduwa sannan ta dubi jakar.
Shafiu wannan kuma jakar ta mecece? Shafiu yayi
murmushi
Atamfofi ne guda uku kawai da leshi guda biyu da
takalma kafa biyar kiyi hakuri aisha banida kudine
shiyasa ban sayo miki dan kwali da turare ba
aisha nta dubeshi cikin kaduwa ta girgiza kai.
.
Ina haba shafiu wannan kayan ai sunyi yawa ka
gan..... Shafiu ya daga mata hannu yace haba
Aisha kefa USTAZIYYA CE kinsan babu me mayar
da hannun kyauta baya sai shaidan Aisha ta
sunkuyar da kai shafiu ya fashe da dariya yace
Na daureki ko Ustaziyya Aisha?
** ** ** ** **

Tun karfe uku shafiu ya gama daukar darasinsa
yana fitowa daga dakin karatun bai tsaya kama
tasha ba kamar yadda ya saba sai ya wuce kai
tsaye zuwa cikin motarsa ya zurawa hanya idanu
yana jiran fitowar Aisha.
Karfe hudu da yan mintuna aisha ta fito tun daga
nesa shafiu ya hangota hakanan ma aisha ma ta
hango shi.
Shafiu ya daga mata hannu aisha ta nufi motar
shafiu
sannu da zuwa aisha yaya lacka din?
Aisha tayi murmushi mun gode Allah shigo daga
ciki mana ko kunya kikeji nasan halinku ustazan
nan Aisha tayi dariya lokaci guda kuma ta bude
kofar motar kusan duk a tsorace ta zauna kusa
dashi amma kafafunta na waje
kaima ai yanzu ka zama ustazun aisha tace tana
dariya shafiu ya fashe da dariya
Aisha ta dubi shafiu da murmushi tace
Kayi sallar la'asar kuwa? Shafiu ya girgiza kai
wallahi banyi ba yadanyi shiru
Yakamata ka daina barin lokacin sallah yana
wucewa gara ka dauke kanayinta akan lokaci
shafiu ya sunkuyar da kai ga mamakinsa sai ya
sami kansa yana mai kunyar hada idanu da ita.
.
In Allah ya yarda daga yau na daina bari sallah
na wuceni Aisha ta dubeshi da murmushi tace
wallahi kuwa daka burgeni shafiu ya dubeta cikin
murna
Jin dadinki aisha shine farin cikina aisha ta
lumshe idanu
ina fatan dai Sallar la'asar din ce kawai bakayi ba
ko harda azahar ma?
Shafiu ya danyi jim sannan sai yace
Gaskiya bazanyi miki karya ba aisha rabona da
salla tun asuba amma in Allah ya yarda aga
yanzu....
Aisha ta katseshi gami dayi masa murmushi cikin
wasa
Ah gaskiya tashi kaje kayi salla ka dawo kafin ta
rufe bakinta shafiu yafito daga motar ya rufe
kofar sannan saiya leka ta cikin tagar motar yace

Bari naje nayi sallar amma zakiyi kirana acikin
motar ko? Aisha ta gyada kai gamida juya masa
fararen idanunta ta gyara zama
Je Ka dawo (My One) Ina nan ina jiranka
.
My One shafiu ya nanata kalmar cikin zuciyarsa
ransa yayi dadi tunda yake wata mace bata taba
cewa dashi haka ba saidai ko shi yayi kokarin
fada musu hakan idan yana kokarin yaudarar su.
Shafiu ya ruga cikin sauri ya nufi Masallaci
.
Harkayi me?
Har nayi sallolin aisha ta rike baki
Kai shafiu wannan sallar taka da sauri take
CONCORD yanzu harka gama sallolin biyu?
Shafiu ya dubeta yace
Sauri....sauri nayi nagama aisha bana son na
barki kina ta jirana Aisha ta girgiza kai Idan ana
sallah...
KUDI DA MACIJI - 26
.
Idan ana sallah shafiu ba a tunanin kowa sai
Allah kuma nutsuwa ake bukata
ta danyi shiru sannan saitaci gaba da cewa
kamata yayi ka sayi yan litattafai na karatun
addini ka koma makaranta koka san Allah da
kuma yadda ake bauta masa shafiu ya gyada kai
idan na mayar dake gida saiki rubuto min
sunayen litattafan da yakama na saya dama
akwai wani malami anan bayan gidanmu saina
fara zuwa gurinsa da daddare
Yawwa shafiu ko kaifa aisha tace dashi sannan
sai idanunta suka kai ga rukuni balbelu dake
wucewa su takwas a sararin samaniya nan da
nan taji gabanta ya fadi Ras
(ARZIKIN KI YANA CIKIN WANNAN LAYAR)
Kalmar aljanar balbelar ya fadowa aisha
lafiya naga duk kamanninki sun sauya? Shafiu ya
tambayeta yana kallon canjin yanayin fuskar ta
cikin mamaki.
Babu komai Aisha tace dashi gamida murmushin
yake tuni har gumi ya fara sartu kyakkyawar
fuskarta me sheki kamar madubi arana shafiu ya

dada dubanta ya girgiza kai yace.
Kada kiyimin haka kefa ustaziyya ce bai kamata
kiyimin karya ba abinda baki sani ba shine duk da
gurbacewar tarbiyar nan tawa da kike gani Allah
ya hore min wata baiwa in dai har mutum yafada
min karya dana duba fuskarsa nake ganewa
musamman MATA sanin kanki ne aisha ni
kwararre ne a fagen mata duk da cewa dai ke kin
zama daban kin sami nasara akaina amma hakan
ba zai hanani na gane karya daga bakin abar da
nake kauna fiyeda komai a duniya ba Shafiu yayi
shiru aisha ma ta yi shiru ta sunkuyar da kai
Minti guda da yan dakiku suka shafe babu wanda
yace da wani Kala
Kada ki damu Aisha idan bakya son kifada min
abinda ke damunki shikenan bana son wannan ta
zamo sanadiyyar bacin farin cikin rayuwata Aisha
ta dago kai cikin cikin sauri tace.
.
Kayi hakuri shafiu kada kayi fushi dani....shafiu
ya saki murmushi yake duk kuwa da cewa ransa
ya sosu
ban taba yin fushi dake ba aisha kece me sa
fushina ma ya dawo farin ciki aisha tayi ajiyar
zuciya.
Fada masa kawai.
Wata zuciya ta fara yi mata kururwa shi kadaine
me kaunarki aduniya kinsan kuwa babu wanda
ake sirri dashi sai masoyi aisha ta dubi shafiu
tace
Shafiu jiya kace kana son na baka labarin layar
nan daka gani awuyana shin haryanzu kana son
jin labarin layar tawa.?
** ** ** **
Wata jibgegiyar budurwa fara jau ta sheke da
dariya sautin muryarta kamar bindiga tace Allah
ya kiyaye na auri Tsololo kamar ka cab. Dube ka
fa saikace Lawurje jiki duk ba nama.
Dan tsololon saurayin dake tsaye gabanta sanye
da wani kwabdeden tabarau fari ya dubi
budurwar da murmushin yake duk kuwa da cewa
muzantashi din datayi yayi matukar kona masa
zuciya

To ke in banda lalacewar zamani ma ina ni ina
zabiya abinda baki sani ba shine nifa jibgegiyar
mace irin ki ba kalata bace gaku da cin tsiya
kume ke yanzu in banda anayi miki alkunya ma
kullum fa sai kinyi tusa sau saba'in acikin aji sai
Kace BODARA
Wasu samari acan gefe guda suka tuntsire da
dariya har da shewa.
Shafiu yaso yabi sahunsu wajen kyakyatawa to
amma labarin layar da aisha ta gama bashi ya
cire duk wani nishadi dake cikin zuciyarsa domin
tun kafin ta gama bashi labarin yafara gumi
musamman ma sa'ar daya fahimci cewa maganar
dukiya ce a binne a cikin kasa duk da cewa dai
labarin Da aisha ta bashi yafi kama da almara
amma shafiu bai daina keta gumi ba.
Cabdin dukiya abinne?
Shin da gaskene gwala gwalai ne? Ko kuwa
zinariya ce me yiwuwa ma.
.
Tunanin me kake naga kayi shiru?
Aisha ta tambaye shi sa'ar dataga tun data
gama bashi labarin baice Uffan ba Shafiu yayi
ajiyar zuciya sannan ya dago kai ya dubeta akaro
na farko tun bayan da tagama bashi labarin.
Kina nufin kice min layar dake wuyanki shekararta
dari da shirin 120yrs ?
Aisha ta dubeshi cikin damuwa
Nima fa balbelar ce ta fadamin ta danyi shiru
daman nasan da wahala ma ka yarda domin abin
yafi kama da tatsuniya in ban da naga kamar
ranka ya baci ma da bazan baka labarin ba ina
ganin mu bar zancen kawai musa soyayyarmu
agaba kaji shafiu?
Shafiu ya girgiza kai yana kallon sararin
samaniya ta cikin gilashin gaban motar amma a
zahiri ba gilashin yake kallo ba kwakwalwarsa ce
ke kai kawo.
Bazamu bar zancen nan ba aisha kinajin abinda
tace dake fa
ARZIKIN KI NA BINNE ACIKI waya sani ma ko
lu'u lu'u ne aciki kin ko riga kinsan yadda suke
da matukar daraja awannan zamanin idan har

kika same su mun gama warkewa aisha.
Aisha ta dubi shafiu cikin mamaki
kana nufin kace dani ka gaskatani labarin dana
baka? Shafiu ya dubi aisha fuskarsa a murtuke
yace shigo da kafafunki cikin motar ki rufe kofar
aisha taso tayi gardamar yin hakan to saidai
abinda ta gani a fuskarsa shi ya gargadeta cikin
sauri ta janyo kofar motar ta rufe
Takardar da kika baro daga cikin layar tana ina?
Aisha ta dubeshi a rude tace Gata nan acikin
jakata
Daukota mu gani Aisha ta bude jakar hannunta
na rawa ta mika rubabbiyar takardar sannan ta
dauko sauran kwanson fatar layar data barke ta
dora masa a cinya shafiu ya warware takardar
ahankali ya kurawa rubutun ajamin idanu na
tsayin lokaci shafiu ya tsinewa jahilci a karo na
farko arayuwarsa domin bai iya karatun ajami ba
cikin takaici..
KUDI DA MACIJI - 27
.
Shafiu ya tsinewa jahilci akaro na farko
arayuwarsa domin bai iya karatun ajami ba cikin
takaici ya mikawa aisha yace a tausashe.
.
Sake karanta mana abinda ke ciki meyiwuwa mu
dan fahimci wani abu daga ciki Aisha ta dubeshi
da murmushi tace
Anya kuwa akwai abinda zamu iya fahimta aciki?
Shekara dari da shirin fa ni dai sau goma sha
biyu ina karantawa ban fahimci komai aciki ba
yanzu haka ma ba anan garin aka binne akwatin
ba ni dai aganina wannan duk shirme ne irin na
Aljanu ba gaskiya bane shafiu ya girgiza kai
gamida dada mika mata takardar.
Gaskiya ne aisha jikina ya bani hakan domin bai
kamata da kika buda kiga sakon rubutun aciki ba
inda karyane duk da yake dai nasan.... Ya danyi
shiru.
Ke dai sake karanta mana bi ahankali kadan
kadan me yiwuwa ma tashi ma tsinci dami a kala
aisha ta dube shi na dan lokaci sannan saita
zunkuda kafada ta saduda ta fara karanta

wasikar mai rubutun ajami.
Shafiu yayi fakare baya ko kwakkwaran numfashi
yana sauraron Aisha.
(KABI FADAMAR NAN TA DAN MASU DAKE DAF
DA GANDUN SARKI KABI BANGAREN AREWA)
Dan tsaya haka aisha. Shafiu ya tsayar da ita
cikin gaggawa aisha ta dago kai daga kan
takardar ta dube shi
Me yafaru? Shafiu ya nuna takardar da hannu
yace
Fadamar wa ma kikace? Sake karanto gurin Aisha
ta sake kurawa takardar idanu sannan saita daga
kai tace.
FADAMAR DAN MASU.
Shafiu ya dubi aisha cikin doki yace.
Haryanzu baki fahimci komai ba? Aisha ta gyada
kai cikin damuwa haba aisha Dan Masu fa duk
garin nan wanene bai san DAN MASU HOTEL ba?
Aisha taji zuciyarta ta harba cikin sauri tace.
Fadamar dan masu fa akace ba Otal ba shafiu ya
matso dab da aisha cikin doki yace da ita a
tausashe
Abinda baki sani ba shine otal din abakin katon
dam din nan na dan masu aka ginata shin ke baki
taba zuwa bane? Aisha ta girgiza kai sau daya
aka taba gayyatata liyafar bikin wata kawata
danaji an ambaci otal nace bazani ba shafiu ya
shafi dugunzunzum din gashin kansa da hannu
yace
saurara da kyau kiji Aisha wannan Otal din
danake baki labari gurin zuwana ne tafiyar
kilomita goma sha biyar ce daga nan mun sha
zuwa PARTY da yan mata akwai wani abokina
dake aiki a otal din sunansa USMAN TASKA ya
taba cewa dani asalin wannan dam din na
Danmasu wata katuwar fadamace aka mayar da
ita dam shafiu ya danyi shiru sannan sai ya daki
kan sitiyarin motar da karfi cikin doki.
Meye haka? Aisha ta tambaya atsorace
aisha inajin Allah fa yakawo arzikinmu shin kin
taba sanin Inda gandun sarki yake kuwa? Aisha
ta girgiza kai
Nifa kifin rijiya ce babu inda nake zuwa.

To bari in fada miki tsakanin gandun sarki da
danmasu dam baifi daga nan din nan da muke ba
zuwa dakunan kwanan mata aisha ta dube shi
cikin kaduwa.
Kana nufin kace dani anan aka binne akwatin
shafiu ya gyada kai yace Ko shakka ko shakka
banayi Aisha amma dai ki bari yau din nan in dare
yayi zan tafi otal din na sami abokina usman
taska zan so na karewa bakin dam din kallo me
yiwuwa ma har zuwa Gandun sarkin.
Aisha ta dubi shafiu da murmushi kai shafiu da
son duniya kake dubi duk yadda kabi ka
tsatstsara abin nan kamar da gaske Shafiu ya
bata rai ya dubi aisha
Aisha wallahi abinda nake fada miki ya wuce
wasa kada kiyi mamaki nan da sati guda mun
gama shigowar gari aisha ta fashe da dariya.
Allah yasa shafiu ya dubeta cikin murmushi yace
Zaki iya bar min takardar nan agurina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login