Showing 33001 words to 36000 words out of 71336 words

Chapter 12 - BABAN YARO BOOK 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf

24 Jul 2025

4215

saboda tsabar kokari da k'arfin hali har tana
buge get man d'insa tana shigowa ko ubanta ta aje masa a gida ihu! A fili yace." Kome ta zo tayi
min a gida oho cike da mamaki yake kallonsu ita dasu rambow tana fada suna fad'a kamar zata
tsokane musu ido Wayarshi ya d'auka dake aje a gefansa ya nemo numbar Rambow yana
d'auka yace." Barsu su shigo" ya kashe wayar ba tare da ya tsaya yaji me rembow zai ce ba.

Rambow yace." Kun fi sa'a Boss yace" Ku shiga amma da badan haka ba wallahi ba zaku shiga
ba" hararsa nayi nace" shima ogon naku nakusa karya alkadarinsa" cike da mamaki Rambow
ya bita da kallo jin abunda take cewa, hannun munnu naja muka shige DOMIN naga Mimi sai
wani ja baya take.
Muna wucewa Doh-doh yace"wallahi ina jin tausayin yarinyar nan duk ranar da zata shiga
hannun Oga sai ta gane shayi ruwa ne" Rambow yayi k'wafa tare da fadin" k'aryar rashin kunya
ta dama.

A hankali muka tura kofar parlor muka shiga, sanyi kamshi ne ya buge mu mu dukan mu sai
muka fara zare ido sosai nake karewa parlor kallo DOMIN zuwana na farko ban kalle shi ba,
wow gaskiya na yaba da tsarin parlor gami da k'yatuwar sa, komai na parlor orange color ne ina
mutukar son Abu orange Munnu tace."Asama mun banu kizo mu koma kawai na fasa" nace ke
dallah can tsorone daku wallahi Ku zauna ni inje dakin shi si na sani mybe ma baya ciki.


Mimi ta rik'o hannuna tana girigiza mun kai wai kar inje fuzge hannuna nayi nai gaba ba tare da
na wai wayo su ba."


Ganin tana nufo kofar shigowa ne yasa ya mike da sauri haske dakin ya kashe ya tsaya jikin
bango yana sauraron shi gowarta. Ina bude kofa naga duhu d'un d'um!! Na gane inda makkuni
yake aikuwa nafara lalube zab kunna". Wani abu naji ina tab'awa shi ba gashi ba shi ba fatar
jikin mutum ba gashi dai yafi yawa a jiki, gabana ya fara fad'uwa jin kamar hucin nuffashin
mutum, hannuna na daga da niyyar in kunna futular domin na fara tsorata, da k'arfi! *Amjad* ya
jawo ta kirjinta ya daki nasa ya zura hannunsa kasanta ya rik'o kwankwanso ta sosai inda baza
ta iya guduwa ba, sannan ya mik'a d'aya hannunsa sama ya kunna futula, haske ya gauraye
dakin.

Cike da tsoro na kura masa ido fuskarsa a murtuke shima nasa idon ya samun kamar zai cinye
ni danya, munfi minti uku muna kallon_ kallo kafin nace." Sake ni inyi abunda ya kawo in tafi."
Shiru yayi min bai CE komai kuma har yanzu idonsa na kaina yana kare min kallo inda naga ya
fi kalla a jikina na kalla ina dubawa, sai naga kwaurina da ya futo waje dalilin yanayin dinki bayin
saurin Jan mayafi na rufe ina hararsa, hannunsa yasa ya janye gyalen ya jefar kasa ya cigaba
da bin jikina da kallo kamar tsohon Maya. Cikin ikon Allah kuma time din banji wannan azabban

fleengs din Dana ke ji ba in ya kusance ni.


Karfina nasa da gaske nake k'okarin ture shi. Ko motsi kirki ya kiyi . muryar shi a harhad'e
yace." Me kika dawo kimin a gida"? Ko nuffasawa ban bari yayi ba nace." Bana munafurci na
dawo d'aukar handbag dina ne."
[10/22, 8:58 AM] BintaUmarAbbale👄: Kallo yake min kamar Wanda be tab'a ganina ba, gashi
ya wani had'e fuskarsa tamau!! Yace." Karya kike da akwai dai abunda ya kawo ki,babu wata
handbag da kika manta." Fuzge jikina nayi ina galla masa harara gefe na matsa ina bin dakin da
kalo ko a ina zan ga handbag din oho min... Cikin tafiyar shi ta jarumai ya nufi bed d'insa ya
zauna tare da Dora kafa daya kan d'aya yace." Zo ki duba kayan ki inda kika aje ki fuce min
daga d'aki". Kai tsaye.. Na nufi bed d'in na fara duba bayan shi da lukunanshi,aikuwa sai na
hango ta, da sauri na zura hannuna na d'auko abata. Bayansa na kalla naga ki juyo bai yi sai
danna waya yake. Rike da ita a hannuna na tsaya a kanshi nace." Sai sak'on da aka bani na
bak'a" ya dago kanshi tare da cewa." Ina jin fad'a min ki fuce ki bani waje" cike da taikacin
yanda yake kyarata wai in fuce!!! Sai kace wata tinkiya nace." Kai kaga bafa komai ne yasa
nazo gidan ka ba da har kake k'okarin gaya min magana dama ko baka ce na fuce ba zan fuce
in bar maka d'akin ka..... Ya katse ni ta hanyar fadin " naji ki fad'i sak'on ki, ki futa min a d'aki
fitinanniya kawai wa zakiyi wa preetanding ni nasan abunda ya k'ara kawo ki gurina kuma baza
ki samu ba" ya k'arashe maganar cikin sigar rashin mutumci" zuciya ta kamar ta tsage saboda
zafi nace." Ni ba shashashar mace bace kuma ni ba irin 'yan Matan ka bane wallahi ni nafi
k'arfin ka bare in kawo kaina gurin ka ko abunda kayi min baya ma Allah ya isa."

Murmushin gefan baki yayi ya d'an sosa sumar shi kad'an da Jan ido ya kalle ni still da
murmushi a fuskarsa yace." Ok naji ba abunda ya kawo bane kin tsaya kina Jan magana fad'a
min sak'on ko in sa yanzu ayi waje dake domin bana bukatar ganin wannan mummunar fuskar
ta ki bak'akirin!!!!!!!!!! Asamau da tsani ace mata mummuna lokaci guda hankalin ta ya tashi taji
wani irin hawaye me zafi na k'okarin zubo mata da sauri! Ta aro jarumta da dauriya ta aza a
ranta, wani kallon Tara saura kwata ta mai tace." Wa kake da suna *Amjad* ko me?? Kai dai ka
sani, bari kaji wani Abu da baka sani ba, kyau ba shi bane kyawun hali da nasaba me kyau da
shi a ke tunk'aho Allah Ubangiji ya raba mu da kyau irin naku babu kyawun hali da nasaba me
kyau Wanda nasan ni nafi ka nasaba da tarbiyya me kyau duk wannan iskancin da kake rashin
tarbiya ne da rashin samun iyaye jajirtattu saboda haka tun wuri gwara ka koma islamiyya ka
samo ilimin addini domin kasan meye banbanci kyau da muni." Ina karasa maganar na nufi
kofar futa ina da na sanin zuwa gidan. Kofar nake k'okarin budewa taki nayi-nayi na juyo a
fusace! tare da kaurara murya ta nace" zo ka bude min kofa in futa daga wannan annobar" ina
kallonsa ya mik'e ya nufo inda nake, fuskarsa na tsurawa ido kamar mala'ikan mutuwa take naji
tsoro ya shiga raina na kauce daga bakin kofar, cike da k'arfin hali na dinga watsa masa kallo ko
kallona bai ba ya bude kofar zai futa na biyo bayansa, da sauri hannunsa guda ya sanya ya
ingiza ni ciki dakin na fad'i kasa, ko juyo wa bai ba ya rufe kofar tare da murza key! Na mike a
zafafe! Na daki! Kofar dak'afata ina janta tun karfina ko motsi tak'iyi ihu!!!!! Na kurma sosai ina
fad'in "Idan baka bud'e mun kofar nan na futa ba kai ba d'an hakan bane, d'an iska asharari"!!
Duk yana jin haukan da take wai shi take zagi harda su d'an iska asharari wai ma meye alk'ar

shi da yarinyar ne da har ta samu dama akan shi shine Mara tarbiyya Wanda iyayensa suka
lalata shi, ya zama dole yarinyar ta karb'i hukunci a gurin shi, fuskarsa ya kara hadewa ya Isa
tsakiyar parlor inda ya hango su Mimi tsaye bakin kofa suna zare ido dama yasan dasu tunda
ya gansu cikin CCTV Camera, Cikin jarumta ya durfafe su,sai ga Munnu tana rawar k'afa ganin
wani ingarmar namiji na kusan to su, cike da tsoro ta zube bakin kofar. Ita ko Mimi suma ne
kawai bata yi ba daga ninsa tunda ya futo ta tsora mishi ido tana kallonsa wata muguwar
soyayyar sa na kara nunkuwa a cikin zuciyarta. Kallonsu yayi a nutse yace." Ku ne 'yan rakiyar
ta"? Munnu ta gyad'a kanta alamar "Eh bakinta na rawa tace" ina wuni" ko kallonta baiyi ba ya
bud'e kofar parlor ya futa, minti biyar ya dawo yana kallonsu tare da fad'in" Ku tashi a mai daku
gida". Cikin dauriya Mimi tace" Asma'u fa". Da gefan ido ya kalleta ya d'auke kansa tare da
fadin." Nace tazo a kai ku gida tace baza ta tafi ba so kuyi tafiyar Ku kawai Ku k'yaleta duk
sanda ta ga damar tafiya sai ta tafi." Jikinsu ya soma b'ari Mimi tace" kayi hakuri don Allah kaji""
miskilin murmushi yayi ya Dan Sosa kansa Wanda hakan ya zame masa jiki yace." Ke ba laifina
bane fa nata ne, kunga ni ita ta kawo kanta har gidana ta bude min daki ta shiga ta zage ni ta
fad'a min duk maganar da tazo bakinta to babu laifi na" hanya ya nuna musu da hannu a karo
na biyu yace." Doh-doh na jiran Ku a mota a sauka lafiya." Simi-simi suka wuce suna waiwaye
gefe guda kuma suna mamakin abunda Asma'u ta aikata domin sun gazgata maganar sa
saboda sanin halin kaifin harshe na Asma'u. Zama yayi a parlor ya rik'e kansa zuciyarsa na
masa zafi sosai yake tunanin hukunci da ya kamata yayi wa yarinyar, murmushin mugunta ya
saki da ya tuno wani abu kawai ya mike ya isa gaban TV ya kunna ya zauna cikin kujera yana
kallonshi wani american film yake kallo ya manta da wata Asma'u dake d'akinsa a kulle sosai
film din ya d'auke masa hankali.


Gajiya nayi da dukan kofar na zube bakin kofar ina mai da nuffashi wani abu me nauyi yazo ya
tokare min a mak'ogwaro na a fili nace "wai me guy nan yake nufi ne da nine? Babu me bani
amsa Mik'ewa nayi da sauri na Isa window na yaye labule INA lek'en waje tunani nake ko zan
samu hanyar futa, ko alama babu wata hanya, nafi minti goma a tsaye a gurin gabana na
fad'uwa, na juyo na kalli a gogo dake manne a dakin 9:53 na dare goma shaura minti bakwai
kenan. Sai naji kafafuna baza su iya daukata ba, na duba wayata da sauri nake lalubar numbar
Mimi na kira babu kudi a cikin wayar, da sauri na tafi cin bashi, da k'yar suka bani naira Hamsin
dama suna bina bashi, Mimi na daga wayar nace." Kuna ina ne"? Tace." Muna gidan su Munnu
yaushe zan koma gida ni kadai in cewa Umma me? Murya na rawa nace Mimi guy nan bai da
mutumci wallahi ya kulle ni a d'akinsa" Mimi tace" Yace ke ce kika ce baza ki tafi gida ba". Cike
da mamaki nace" Mimi sharri yayi min kawai kyaleshi" tace" nasan kin masa rashin mutumci
shiyasa yayi miki haka" ga yanayin yadda Mimi tayi magana na gane ranta a bace yake nace."
Mimi nayi masa din in zaki rama masa bisimillah" na katse wayar cike da taikacin ta wato ita
bata jin ciwon kulle ni da yayi shi take k'okarin karewa,

Zarya na fara a dakin ina kaiwa ina kawo wa, da sauri naje na daki kofar! Da kafata kamar wata
wacce ta samu tab'in hankali da k'arfi nace Idan baka bude min kofar nan ba kai ba d'an halak
bane wallahi!!!Abunka da dare shiru ko INA yasa magana ta ta cika parlor murmushi ya saki a
hankali yace." Yarinya inan zuwa gurin ki,zaki fada min wace irin alk'ace a tsakanin dake da har

kika samu dama a kaina....











*22/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA
FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN
TA.


*22*




Sama-sama Asma'u take jin Mimi tana magana wani irin sarawa kanta yakeyi ga wani sanyi me
ratsa jiki tana ji a jikinta,dishi-dishi ta ke kallon Mimi tana sallah lumshe idonta tayi tana kara
takure jikinta.Mimi ta idar sallahr ko addu'a bata yi ta mike tana ninke abun sallah ta futa waje
da sauri.Umma na kicin tana k'okarin raba abinci tace." Umma In Kin zuba mana namu bani in
je muci domin muje chamis din kinsan dole su taimabaya ko ta ci abunci nasan dai allura ce za
ayi mata." Umma ta mik'o mata Fula's MA dai-dai ci cike da shinkafa da faduka da kifi d'anya
abunci dai-dai na talaka tace." Aikuwa domin Kin San wannam zazzab'in na maleria dole sai da
allura." Su duk a tunaninsu maleria ce take damun Asma'u. Mimi ta wuce da sauri tana shiga ta
hau kiran sunanta "Asma'u tashi muci abunci muje a dubaki." Bude idona nayi a hankali
nace."Mimi k'yaleni da chamis din nan don Allah." Sakin baki tayi tana kallona naja bargo na
rufe kaina gaba daya ina takure wa." Tace "Dole fa ki tashi WALLAHI ke taurin kanki ne
matsala." A hasale nace." Dallah ki kyale ni wai jikin ki ko nawa da zaki dame ni." K'arar!a
kunnen Umma ta daga labule ta shigo rai a bace tace." Gwara ma ki tashi tun kafin ranki ya
b'aci ita meye laifin ta kawai Dan ta damu da lafiyarki shine kike mata tsawa." Nace." Umma nifa

lafiya ta lao". Tsaki taja tace." Kin saba karya dama duk abunda ya same ki ke kika jawowa
kanki wanka da magariba saboda haka ki tashi tun kafin raina ya b'aci." Tana gama maganar ta
ta fuce daga dakin.
Cike da jin haushin Mimi na tashi zaune ina hararta had'e cinyoyina nayi ina ya mutse fuska
tace." Ki sauk'o kasa mana." A hasale nace." Anki a sauko ki d'auko Fula's din abunci ki dawo
dashi kusa dani in kin damu."Mimi tace." Banza masifaffiya." Shiru nayi mata ina hararata gefe
guda ina matse cinyata Dan karta gane halin da nake ciki. Ta kalle ni cike da nazari tace." Wai
meye tun d'azu kike matse cinjyar ki kamar wacce taji ciwo." "Ban sani ba." Abunda nace da ita
kenan na sha kunu. Tab'e bakinta tayi tace." Mutum babu lafiya ma sai masifar tsiya." Share ta
nayi kawai na fara cin abunci a ya tsine.Kad'an na iya ci na mike a daddafe na futa waje domin
wanke hannuna, sauri sauri Mimi ta gama ci itama ta futo hannuta rike da hijabai ta mik'a min
na sanya itama tasa ta wanke hannunta muka tafi. Ko da Anas me chamis ya gama duba ni
sam bai ga wata maleria ba maganin zazzab'i kawai ya bani muka dawo gida, nace." Ki damu
sai munje to munje muguwa kawai allurar dai da kike min fata bata samu ba." Dariya Mimi ta
sanya tana zolaya ta ni ko na sha kunu.muna shiga gida na dauki buta na d'aura alwala can
dakin Umma na shiga nayi sallahr mariba da Isha'i na kwanta kan daddumar ina addua'a Allah
yasa bacci ya d'auke ni. Aikuwa Allah ya taimaka ni bacci me nauyi ya kwashe ni, Umma
tace."tunda na samu bacci shikkinen Mimi ma ta dawo dakin a takaice nan muka kwana.

******

Granny ce take ta fama dashi ya fad'a mata abunda ta faru tunda ya shigo gidan take aikin
rarrashin sa yana jin ta yak'i tanka mata sai kallon guri guda yake.cike da takaici tace." Wannan
a cikin musklan ma k'arshe ne kazo ka zauna kana min dacin rai nayi tambar duniya kamin
shiru shikkenan." Ta k'arashe maganar cike da takaici."
Kallon gefan ido yayi mata yaji ta bashi tausayi Sam bata son damuwar sa ko kankanuwa
yace." Granny kin san Alhaji Hashimu abokin Dadyna ko." ? Tace." Ni ko nasan Hashimu me
citta." Yace." To zan mai dashi prison wallahi." !! "K'ull!! Tafad'a tana kallonsa ta cigaba da
cewa." Me yayi maka mutum magidanci me iyali zaka dauki hakkin su." Murya a sama yace."
Yau ya assasa taro DOMIN a ci ma Dadyna mutumchi." Shiru tayi saboda tasan da kiyayar
dake tsakaninsu ba tun yau ba, amma dake tsohuwa ce me hangen nesa tace." Sai ka kyaleshi
ai da me rai ake ba da Wanda ya mutu ba. Mik'ewa yayi a zabure! Ya kai ya kawo a parlor
yace." Impossible ina Raye a duniya granny babu mahalukin da ya Isa ya taba min dadyna ban
ta kurawa rayuwrsa ba." Granny ta mike cike da tsoro tace." To me zakayi masa? Ka k'yale shi
mana ba sa'anka bane." Ta k'arashe maganar tana kamo damtsen sa wai ita dole sai ta zaunar
dashi kan kujera kamar tana Jan dutse yak'i motsa wa. Tace." Dube ka sai wani huci kake jiki a
murde kamar dan danne"zama yayi cikin kujera yana huci yace." Granny yau me citta ya hada
min taro har dasu governor da jama'a kan lallai sai na rushe company na na Magwan." Tace."
Abunda bazai yiwu ba kenan lallai me citta Ashe yanan nan da bak'ar zuciyarsa. "
Granny ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin. " Allah wannan bawa naka kai ka hallice shi kanai
ka dora masa nauyin wannan dukiyar da ta hau kansa ina rik'on ka ka dafa masa cikin
al'amuranshi ka tsare shi daga sharrin mahassada."

Ta k'arashe maganar tana shafa kansa cike da tsantsar soyayya. Gyara kwanciyarsa yayi cikin
kujerar ya lumshe idonsa yaji dadin addu'ar da kakarsa tayi masa a yanzu bashi da wacce ta
fita a duniyar nan sai dangin mahaifiyar sa da ba wani sha kuwa yayi dasu ba, granny tace."
Ina Neman alfarma daya a gurinka." Bude idonsa yayi amma be kalleta ba, tace." Abunda ka
kudurta kan Alhaji Hashimu ka hanye shi in ya kara sai ka dauki mataki." Kallonta yayi da
jajayen idonsa yace." Kin samu amma da bakin ki kika ce idan ya k'aramin wani Abu in dauki
mataki ko."? Granny ta daga kanta tana murmushi yace." Shikkenan ya wuce." Dariya tayi
tace." Ho!! Dan nema kai dama soja ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login