Showing 69001 words to 71336 words out of 71336 words
Chapter 24 - BABAN YARO BOOK 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf
kaina
dake." Fuzge hannuna nayi tare da fad'in" nasa ni ai suma nayi, haka nake yi duk lokacin da
naga mage me kuma zan gani, ai da ka bari na mutu kan kayi min abunda kayi a yanzu, saboda
ni nak..... Shiru tayi bata karasa ba jin tana nema ta tonawa kanta a asiri
Mik'ewa yayi daga kusa ni tare da fad'in" Kar ki dame ni da surutun banza malama na k'yale ki,
amma kafin in futo daga toilet ki rufe wannan balo din naki idan ba haka idan na futo na gani
zaki raina wayon ki."
Da sauri na kalli jikina naga Ashe ban sanya rigar ba, tana dai hannuna, saurin gyara zif din
nayi na hau zurawa da sauri.
Toilet ya shige abunshi ba tare da ya kara tanka min ba.
Bayan na sanya rigar tawa na fara neman inda mayafi na, kan kujerar ban gan shi, cike da
mamaki na fara duba dube a dakin Sam babu alamar sa, takure jikina nayi kan kujerar ina
kallon yanda Mamana suka bulutsu ta saman rigar kasan cewar ya matse ni sosai dama rigar
tayi min kad'an sanya ta kawai nake, kuma ka'ida ne duk d'inkuna na kananu ne bana tab'a
yadda ayi min babbar Riga. Motsin bude kofar toilet din naji nayi saurin kauda kaina daga
kanshi, gabana na fad'uwa yana daure da k'aramin towol iya cinya zuciya ta nace shi kam bashi
da kunya ko guda wallahi, INA kallonsa ta wutsiyar idona Yana shafefensa minti biyar ya futo da
kayansa, mai makon ya sanya su sai ya k'araso inda nake zaune rike da kayan a hannunsa, na
kauda kaina da sauri ina kara gyara fuskata addu'a kawai nake Allah ya bani rinjaye a kansa,
zama yayi kusa dani tsigar jikina ta tashi na dake! Sosai ban kalle shi ba, cikin wani iri voice
yace." Ungo balle min botoran rigar nan." Satar kallonsa nayi cike da mamaki sai ya dinga
sanya ni Abu kamar wata matarsa.Nace." kan wane dalili da ni CE nake b'alle maka botiran
rigar ka, ni ka k'yaleni kawai." Matsowa yayi jikina sosai naji wani sanyi a fatar jikinsa, nan take
na tsinci kaina da wata irin a zababbiyar sha'awar sa, yace." Yanzu na ganki a arha shiyasa
nace ki b'alle min kuma na da lokaci k'ank'ani hakan zai zama aikin ki domin baiwa ta zaki zama
ta ko wace siga." Kallonsa nayi ina ya mutsa fuska nace" wannan duk kana fad'a ne domin kaji
dadin bakin ka, ni dai na farko ba matarka bace balle kace haka ni baka da iko dani da duk
wani abunda ya shafe ni."
Murmushi yayi hade da shafa fuskarsa as'usuel yace." Karya kike ko yanzu na gada zanyi iko
da abunki kuma babu yanda zakiyi dani, wallahi kuma na kara ganin kina rigima a kan titi sai
ranki yayi mugun b'aci sai na miki horo me tsanani, kullum kina kiran kanki mace me daraja
amma kin kasa hankali kina shashanci, rigima da 'yan iska ki kiyaye wallahi."!!! Yafad'a. Da
murya a kausashe.
Mamaki yaba ni sosai nace "To kai meye damuwar ka meyasa da ka ganmu bakayi tafiyarka ba,
duk abunda nayi rayuwa ta ce."!!! Na fada haka cikin tsiwa da sigar bada haushi.
A zafafe! Ya juyo dani muna fuskantar juna, fuskar sa a hade yace." Ina magana kina girgiza
jiki don baki da kunya, wa ya fad'a miki saboda ke na tsaya a gurin? K'ifk'ifta ido nake tsoro ya
fara shiga ta ganin yanda yake wani muzurai duk wannan fara'ar babu ita a fuskarsa.
Ya cigaba da cewa"Saboda Mimi na tsaya na lura yarinyar kamila ce ita yafi kamata ta kira
kanta mace me daraja bake ba, tunda duk ganin da zanyi muku bata tab'a aikata mummunan
abu ba, ke kuwa fa.? Yafad'a yana zare min ido! Kasa nayi da nawa cike da tsoro! Girgiza
kafad'a ta yayi da k'arfi yace." Ki bani amsa mana".? Shuru babu magana. Yace." Mimi tafi kirki
tafi ki kyau ta fiki hankali da sanin ya kamata, Ko ba haka bane."? Shiru nayi masa bakina na
rawa, tsaki! Yaja had'e da fad'in." Ko kwana uku ba ayi na 'yan uwanki suka zo nan suna
tuhumar ki, kan rashin yarda saboda sun San halin ki, hakane koba haka ba ne."?
Wasu zafafan hawaye ne suka soma zubo min a fuska na fara kifta idona domin in mai dasu
Sam bana son yaga gazawata.
Sakina yayi yace." Wannan ya zama na farko da k'arshe a gurin ki, wallahi wallahi kar in kara
kama ki da aikata Abu makamcin haka, zan tsaurara bunkice a kanki domun nima ban yarda
dake b........... Hannu na d'aga masa murya ta na rawa na mik'e tsaye cikin tsananin b'acin rai
nace." Duk abunda zaka fad'a ka fad'a akaina dai-dai ne a gurin ka, ka fad'e shi son ranka, Idan
iyayena sunyi zargina kai meye alak'arka dani da zaka tasa ni a gaba kana zagina had'e da
fad'amin bak'ar magana, idan iskancin nakeyi Kaine ka koya min, tunda nake a rayuwata babu
namijin da ya tab'a kusanta ta sai kai, me yasa na rufa maka asiri a don duniya? Meyasa na
rufa maka asiri a gidanmu?! Ka sani ina da damar da zan shiga ko ina ne in b'ata maka suna
me yasa ban yi ba?!! Sai kai ne zaka turke ni kana tuhumata kan abunda ban aikata shi ba. To
wai ma meya shafeka dani idan a *Ibedi* nake ina karuwanci! Babu abunda ya shafeka dani,
zan dauki hakan daga makusanta na, wato iyaye na, amma bazan dauki raini da k'azafi ba daga
gurin wani gardi."!!!!!! Ganin ya mik'e a zafafe! Ne yasa na ruga da gudu bakin kofar futa ina
k'okarin bude wa, kulle gam!! Finciko ni yayi da hannu guda ya jefar kan kujerar a zafafe ya
Fidda hannu ya gaura min mari, Wanda sai da naga wasu taurari, yana haki! Yake cewa." Ni
kike fad'awa wannan maganganu ko."
Hannu na nasa na dafe kuncina zuciyata nayi min suya, tsura min ido yayi fuskarsa kamar
Wanda aka aikowa da mala'ikan mutuwa yace." Ana fad'a miki meye rayuwa kina k'okarin zagin
mutane, Dan kinga na damu ke shine kike wannan iskancin!? Kije ki tambayi waye. *Amjadu* a
gari zasu fad'a miki, ko kuma kije ki tambayi 'yan mata irin ki, wad'anda suke da kyau da
wayewa ilimi kud'i ba irin ki ba bagidajiya da ko kwalliya baki iya ba, idan kika tambaye su zasu
fad'a miki wanene ni, idan mace bata yi min ba, ko kallo ba ta ishe ni ba, duk kyawun ta da
waye warta don ke kin samu wannan damar shine kike mun iskancin har da su zagi,."!!!!
Hannuna na sanya ina dukan k'irjinsa da yayi min rufa dashi INA kuka nake fadin" Babu ruwana
dasu tunda ba Kai ne a gabana ba, da kake maganar Mimi tafi kyau tafi ni kirki da komai, to sai
me? Idan sonta kakeyi to Bari kaji wani Abu, itama sonka take sai me? Ni babu abunda zai
dame ni, daku kuma daga yau ka futa daga rayuwata in huta da jaraba! Idan haka gaskiya take
to bana bukatar ta a gurin ka, duk halin da na fad'a kai ne sila."!!!!!!!! Na k'arashe maganar ina
kuka wiwi! Bakin ciki kamar ya kasheni, wai ni suke zargi!! Lallai na yarda da maganar hausawa
da suke cewa namiji sai yayi Abu ya zama ado a gare shi, mace ko da tayi sai duniya ta ji ta.
Yanzu dubi babu sata babu zina babu mayyata amma suna zarginta.
Kuka nake ina dukansa a k'irji hade da ya kushin sa, so nake kawai ya d'aga ni. Yak'i sai kace
wani maye ya zuba min idonsa da suka yi jazur dasu. Minfi minti goma a haka sannan ya sauka
daga kaina, na mik'e da sauri! Had'e da d'aukan k'ananun pillows ina jifansa dasu hade da
fad'in"I hit you! I hit it."! Kayansa ya ke sanyawa ranshi a mugun b'ace ya zama dole ya cire
yarinyar nan daga ranshi domin ya lura tana da mugun taurin kan tsiya ga rashin kunya dole
yayi nesa da ita da rayuwarta dama tausayin maraicin su yake ita kuma bata duba wannan.
Dole ya aje ta gefe guda ya fuskanci abunda yake gabansa bata tab'a b'ata masa rai ba irin
yau. Yana jinta har ilayau tana jifansa hade da surutai share ta kawai yayi ya dauki turaransa ya
fesa jikinsa, dashu. Juyo wa yayi muka hada ido, gani fuskar sa nayi kamar ta zaki! Da sauri na
jefar da pillow hannuna hade da zubewa kan kujarar ina shashshekar kuka.
Ba tare da yace min komai ba ya bude kofa ya futa, zumbur na mik'e nima na bi bayansa, Mimi
ta mike da sauri hade da mikomin mayafina na yafa muka sauka k'asa.
Ina kallonshi shida rambow suna magana sai kuma naga Rambow ya nufi parking spece da
sauri ya bude wata lafiyyayr mota yana buge ta shiga yayi ciki ya futo da ita kana ya fito daga
ciki hade da bude murfin motar.
Cikin yanayin tafiyar sa ta jarumai ya k'araso gurin hade da karb'ar key din motar hannun
Rambo ya shiga ya zauna mazaunin dravar, rbow ya k'araso kusa damu tare da fadin" kuje Ku
shiga motar.
A zuciyata nace"Yau shi zaiyi dravin din kenan Mtssss. Baki na tab'e kawai INA d'auke kaina
muka Isa gurin motar
Mimi ta kama murfin kofar baya zata shiga yace.'"Mimi dawo nan kusa dani." A hankali ta saki
murfin ta bude na gaba ta shiga ta zauna tana sink'e kai. Tsaki nayi a fili na bude na shiga.
Kunna motar yayi had'e da kallonta da murmushi a fuskarsa yace." Ko kina so in zama dravar ki
ne." Mimi ta sunkuyar da kanta cike da kunya tana mamakin yanda yake mata magana, cikin
nutsuwa motar gidan, ta hau kan kwalta. Music na tashi kad'an-kad'an.. Sam naki dago kaina in
kalle shi balle in San wane irin kaya ne a jikinsa, shiru motar kusan minti goma yace." Mimi naji
wata magana gurin 'yar uwarki hakane."? Mimi gabanta ya fad'i kaddai Asma'u ta fad'a masa,
sai ta sanya mayafin ta ta rufe fuskar ta, naji kamar ina mangarta, saboda haushi tsaki naja me
k'arfin gaske Wanda nasam duk sunji ni,amma abun mamaki ita dashi babu Wanda ya kulani.
K'asa-k'asa naji yace." Kinyi shiru my Mimi hummm! Wai ya sunan ki ne na gaskiya ne."? A
hankali Mimi tace." Sunana Aisha." Cike da kulawa ya kalleta yace." Mommah na ce ashe haba
shiyasa naji ina kaunar ki, kin San duk me wannan sunan tana da daraja irin sune ya kamata su
kira kansu da mata masu daraja."!!! Gabana ya yanke ya fad'i. ! Babu shiri na dago kaina ina
kallonsu, ni YAKE fad'awa magana kenan. Zuciya tayi min bak'ik'ikirin, haushi ya turnike ni,
ganin yanda yake sakin wani murmushi yana kashe muryarsa Wanda sai na kasa kunne sosai
nake jin abunda yake fad'awa Mimi.
Yace." Yaushe ne party naku."? A hankali tace." Asabar ta jibi." Gyad'a kansa yayi fuskar da a
sake yace." Wane guri za'ayi."? Tace" cikin makaranta ne." "Hakan yayi wane irin tanadi kuka
yi." Mimi tace"mun gama komai ma."
"A'a ki fadamin ko akwai taimakon da zan miki kinji ko." Mimi ta dago kanta muka had'a ido da
ita ta mirror wani banza kallo na watsa mata gami da d'auke kaina, cike da mamaki ta d'auke
kanta tana mamakin kallon da nayi mata. Ni kaina sai bayan nayi mata shi na dawo ina da nasa
ni.
Yace." In kuna son a futa sai a ka ma muku guri ko."? Girgiza kanta tayi tare da fad'in" gidanmu
baza'a bar mu ba." Murmushi yayi kawai, minti uku yace." Tom ya maganar mu dake." Mimi duk
ta diririce tana kauda kanta. Dariya yasa har sai da hak'oran sa suka bayyana. Yace." Ko dai
k'arya take miki ne? Ita ce ta aiko kanta. " Mimi ta girgiza kanta alamun A'a. Ji nake kamar in
shako wuyan Mimi in ta dukanta ko na huce takaicina a zuciyata nace "Banza wacce ta rako
mata kawai.!!!
Hira suke dashi sosai duk k'arfin hirarar shine yake yi ita dai sai Umm da umum kawai take yi, ni
zaune a baya sun bawa banza a jiya ta, Allah-Allah nake mu sauka daga motar ko na samu in
samu sassaucin rad'adin da zuciyata take min a game dashi.
Dai kwanar gidanmu yayi parking din motar, da sauri na bude na futo, babu Wanda ya kula ni a
cikinsu, shiru-shiru Mimi bata futo ba, ga glass din motar duhu balle inga me ya tsare ta a ciki,
kawai sai na tsinci kaina da k'urawa motar ido ina jin wata irin hajijiya na k'okarin ta yar dani a
gurin
Duk abunda take yana kallonta, yaji mutukar dad'i ganin yanda ta tada hankalinta,sai ya nuna
mata batada wayo wallahi tunda bata da kunya ita. Rike Mimi yayi da hira, Mimi kuwa ta saki
jikinta suna ta hira abunka da zuciyar da ta narke a kan so. Idona ne ya fara kawo ruwa ganin
kusan mintina goma Mimi bata futo ba yasa na fara k'okarin tsallaka titi nai tafiya ta duk sanda
ta gama soyayyar ta tawo.
Wayarsa guda ya dauko hade da sanya mata wani sabon sim card Mimi taga ya mik'o mata
dalleliyar waya k'arar Infinx yace." Ungo wannan ki sanya chaji na sanya miki sabon sim card
zan dinga kiran ki muna gaisawa." Mimi taki karb'a tana sink'e kanta yace." Ashe ba so na kike
ba ko."? Girgiza kanta tayi ta sanya hannu biyu ta karb'a tana godiya yace." Yawwa ko kefa."
Bude mata kofar yayi da kanshi suka yi sallama.
Motar ya ja da sauri ya bar gurin.Mimi kuma ta fara Neman inda Asma'u take bata ganta ba,
zuciyarta ta ayyana tabbas tayi tafiyar ta, sai ta tsallake titi cikin sauri ta nufi gida itama............
*Yanzu aka fara*