Showing 1 words to 3000 words out of 11817 words
Chapter 1 - TSATSUBA BOOK 3 Complete Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part A.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar ita kuma ta
bishi da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa da tashin hankali kamar yadda sarki
shardas ya bukata haka al amarin ya kasance, wato daga wannan rana suka ci gaba da renon
juna biyun nata tare, ya zamana cewa fiye da rabin rana sarki shardas na bata lokacinsa tare da
shadila, yana bata kulawa ko yaya yaga wani abu na damunta take zai tura a kirawo likitoci su
dubata sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba kwana a tashi sai cikin shadila ya
tsufa ya zamana cewa bata iya yin komai da kanta sai dai ayi mata.
.
A ranar da cikin ya cika wata tara da kwana tara ne nakuda ta zo mata, tana fara nakudar sai
kawai akaga yanayi ya sauya ba tare da wanzuwar hadari ba ko tasowar iska sai akaji an fara
tsawa da walkiya; al amarin da ya razana jama'a kenan aka kama guje guje.
.
A wannan lokaci da rana ne tsaka ana ta gabatar da hidimomin yau da kullum, nan fa kasuwa ta
watse jama'a suka rinka rugawa izuwa cikin gidajensu suna
rufe kofa wasu kuma suka ruga izuwa fada domin a sanar da sarki abindake faruwa don ana
zaton ko allolin da ake bautawa ne a kasar suka yi fishi zasu
hallakar da mutanen kasar.
.
Koda jama a suka iso fada sai suka iske boka marwas a tsaye a tsakiyar fadar shi kadai
fuskarsa a murtuke yana muzurai koda ganin haka sai jama a suka zube kasa a gabansa aka yi
tsit kamar mutuwa ta gifta, wani tsoho mai shekaru da yawa ya dago kai ya dubi boka marwas
yace ya kai dirkar birnin Romaniya wannan kuma wace irin masiface tazo mana? .
Ta yaya tsawa mai ban tsoro gami da walkiya suke faruwa a sararin samaniya alhalin babu ko
alamar hadari?
.
Koda jin wannan tambaya sai boka barwas ya bushe
da dariya. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan boka barwas ya turbune fsuka yace
matar sarkice zata haihu yu zata haifi wani yaro dan baiwa wanda sunansa zai shahara a ko ina
cikin wannan duniya daga yau za a sami yalwar arziki a wannan birni namu mai albarka za a
sami zaman lafiya da kwanciyar hankali irin wanda ba a taba samu ba har izuwa ranar da
wannan yaro zaiyi wata tafiya manufa ya fita daga cikin wannan gari namu.
.
Koda jin wannan batu sai mutane suka rasa abinda zasuyi tsakanin murna da bakinciki domin ta
leko ne ta koma, babban abinda ya dugunzuma hankalin mutane a cikin bayanin boka barwas
sunji cewar da zarar wannan yaro da za a haifa ya bar birnin duk farin ciki zai yaye don haka sai
wasu suka fara tunanin to ai gwara rashin aihuwar yaron da dai a shiga farinciki da farko a
karshe kuma a shiga tasku.
.
Nan fa mutane suka kama kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa. Ana cikin wannan
haline aka yi wata irin tsawa mafi karfin gaske wacce ta firgita komai da kowa har gidajen birnin
gaba daya saida yayi rawa, kasa tayi girgiza bishiyoyi suka kama cin wuta dabbobi suka kama
guje guje suna shigewa maboya, mutane kuwa suka rude suka dimauce kamar zasu haukace,
A dai dai wannan lokaci ne kukan jaririn Shadila ya cika birnin gaba daya har da amsa kuwwa
izuwa cikin dazuzzuka.
.
Faruwar hakan keda wuya sai aka kece da ruwan sama kamar da bakin kwarya wata irin iska
mai dadin sanyi ta rinka kadawa kamar ana cikin tsakiyar
damina alhalin ana ranine kuma a lokacin zafi ya addabi mutane faruwar wannan sabon yanayi
keda wuya sai murna ta kama kowa gami da mamaki nan fa jama a suka ci gaba da cincirindo a
kofar gidan sarautar birnin kowa burinsa shine yayi arba da wannan sabon jariri da aka haifa ko
ya sami tabarrakinsa domin tuni kowa ya gama yarda cewa wannan jariri dan baiwa ne tunda
gashi ni'ima ta sauka a birnin a irin lokacin da ba ataba samunta ba
shi dai wannan ruwan sama da ya sauka ba ruwa bane daga Allah, ruwane daga shaidanu
domin kawai su juyar da hankalin mutanen dake wannan nahiya su dada dulmiyar dasu a cikin
hanyar bata mabaiyaniya tunda sunyi imani da shaidanun a matsayin ababan bautarsu, bayan
kofar fada ta cika makin da mutane.ana ta turereniya, gashi ruwan sama na dukan mutane
sanyin iskar dake kadawa har ya fara addabar jama'a amma saboda naci sunki su tarwatse sai
tsulum akaga sarki shardas ya fito daga cikin gidan.sarautar dauke da jaririn da shadila akan
tafin hannayensa, jaririn tsirara yake ko al aurarsa ba arufe ba, ga sabon yankan cibi a jikinsa
ruwan saman nata dukan jaririn amma ko a jikinsa sai dariya yake kyakyatawa yana ta wutsil
wuts irin ta jarirai masu koshin lafiya.
.
Koda sarki shardas ya iso gaban dandazon jama'a sai ya daga jaririn sama yayi kuwwar murna
take jama a suka amsa masa kuwar muryoyinsu suka cika birnin gaba daya sai da aka yi haka
har sau uku
sannan sarki shardas ya mikawa boka barwas jaririn ya karba, ya fuskanci jama a yace yaku
jama ar wannan birni na Romaniya kuyi sani cewa yau allolinmu sun dubi kukana sun bani da
alhalin na shafe shekara da shekaru ina neman haihuwar ban samu ba ina mai tabbatar muku
da cewar wannan da dana samu rahama nega kasarmu gaba daya don haka ina son kowa ya kaunaceshi kamar yadda zai kaunaci dan cikinsa,Koda sarki shardas
yazo nan a zancensa sai jama'a suka amsa masa da cewar sunyi Alkawari zasu so wannan da
tamkar dan cikinsu.
.
Cikin matukar murna sarki shardas ya juya ya dubi boka barwas ya mika masa hannu domin ya
karbi jaririn kawai sai yaga fuskar boka barwas a murtuke babu annuri nan dai ya karbi jaririn ya
sallami jama'a kowa ya watse aka tafi ana ta murna ana ta kade kade da bushe bushe bayan
jama a sun watse sai sarki shardas da boka barwas suka juya suka nufi cikin gidan sarautar
suna masu jera kafada tsawon dan lokaci suna tafiya dayansu baice uffan ba sai sarki shardas
ya dubi boka barwas yace yakai abin dogaro na yakai shamakin dake tsakanina da allolinmu ina
son ka gaya mini dukkan dalilin da yasa ka murtuke fuskarka a lokacin da na umarci jama a
dasu so wannan jariri na shadila.
.
Koda jin haka sai boka barwas yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki shardas cikin
alamun takaici da damuwa yace ya shugabana ai wannan abu da kayi shine babban
kuskurenka na farko a kan wannan yaro da aka haifa, shin ka manta ne cewa a duniya kaf baka
da wani makiyi wanda yafi wannan yaro? Shin ka manta ne cewa a halin yanzu yana matayin danka ne na cikinka, tabbas yadda suke
son ka kuma zasu so ya gaji karagarka anan gaba, a lokacin
da ni dakai zamu yi shiri mu tafi neman hular lamsara shine zai hau karagarka ta mulki kuma
idan muka je muka samo hular lamsara muka dawo saukeshi daga kan karagarka ba abu bane
mai sauki duk da cewar zamu iya hallakashi farat daya a wannan lokaci saboda zamu fuskanci
fishin jama a domin a sannan suna kaunarsa fiye da kai kuma suna matukar jin dadin mulkinsa,
dolene sai daimu hallakashi a sirrance ta yadda babu wanda zai gane cewar dasa hannunmu,
ni abinda nake so dakai kawai shine duk yadda za ayi kada ka kuskura wannan yaro ya san
cewa ba kai bane uban sa ba har izuwa tsawon shekaru bakwai da zaka rabu dashi akwai
ragowar kurakurai guda biyu wadanda bana son kayi kuskuren aikatasu, a nan gaba domin idan
ka aikatasu tofa koda ka mallaki hular lamsara saimun sha bakar wahala kafin mu sami nasarar
hallaka wannan yaro kuskuren kuwa shine kada ka kuskura ka bari son wannan yaro ya shiga
ranka domin hakan zata iya faruwa don yaron zai taso da tsananin farin jini da shiga rai.
.
Akwai wani magani da zan baka ka rinka sha bayan kowane kwana talatin, indai kana shan
wannan akan lokaci babu yadda za ayi son wannan yaro ya shiga ranka shi kuwa kuskuren da
zaka yi na uku ba yanzu
zan sanar dakai ba sai idan lokacin da ya dace ka sani yayi.
.
Koda jin wannan batu sai jikin sarki shardas yayi sanyi yana mamaki da tunani har suka kule a
cikin gidan sarautar bai kara cewa uffan ba.
.
Da ranar suna ta zagayo sai aka yi gagarumin taro aka gaiyaci sarakaim attajirai, bokaye,
jarumai da sauran manyan mutane na nahiyar gaba daya boka barwas ne ya radawa jaririn
suna Yarima HULKAS, nan fa aka shiga shagalin suna sai da aka kwana ashirin da daya kullum
ana gabatar da walima a gidan sarki abinci da abinsha kuwa saida akayi ta almubazzaranci
tamkar a bola ake tsunto su hatta talakawan gari ma sai da suka rinka shirya walima tsawon
wadannan kwanaki sarki shardas a cikin tsananin farin ciki yake kai kace yarima Hulkas dansa
ne na cikinsa wato jininsa ne hm daga wannan rana wani abin mamaki ya fara wanzuwa a cikin
birnin romani ya zamana cewa fatake suna ta tururuwa a cikin birnin suna tahowa daga manyan
kasashe na duniya suna kafa tushen kasuwancinsu
a birnin.
.
Nan fa kasuwanci ya sami gagarumar bukasar da bai taba yi ba a nahiyar gaba daya nan da
nan talauci da fatara suka yaye, arziki ya yawaita a hannun talakawa, kayayyaki iri iri akayi ta
shigowa da su birnin da hajoji kala kala, kai irin kasuwancin da baya juyuwa ma a nahiyar fiye
da shekaru daruruwa da suka wuce sai da akazo dashi ana yinsu tamkar dama can an saba
dasu.
.
Al amarin shadila kuwa itama ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa ta farinciki tamkar bata
taba tsintar
kanta a cikin wata damuwa a baya amma da zarar ta tuno da mahaifin hulkas na gaskiya wato
Hailur saita kefe kanta a cikin daki tay ta kukanta ta more bata yarda sarki yasan halin da take
ciki duk da cewar sarki shardas ya fara shan wannan magani wanda boka barwas ya bashi don
kada soyayyar Hulkas ta shiga ransa saida yaji yana kaunar Hulkas din tamkar Dansane bana
wani ba a ranar da ya sha maganin ne kadai yake jin ya tsaneshi domin a ranar ne yake tunawa
da cewa nan gaba fa wannan yaro ne zai kasheshi muddin bai rigashi mallakar Hular Lamsara
ba a wannan rana daga safiya zuwa dare sarki shardas baya kusantar shadila don kada ma
yayi arba da Jarumi Hulkas hmm Domin zai iya hallakashi nan take saboda zuciyarsa tana
tafarfasa ne kamar zata kone bisa jin tsananin kiyayyar hulkas a cikin zuciyarsa kuma jikinsa na
tsuma da kyarma yana jin kamar idan bai kashe jariri Hulkas ba shi zai mutu ne a ranar.
.
A kwana a tashi sarki Shardas yana kiyayewa gami da jure duk irin abinda zuciyarsa ke raya
masa akan wannan yaro Hulkas har dai aka sami tsawon shekara Uku. A sannan ne ya tsinci
kansa a cikin tsananin so da kaunar yarima Hulkas harma yana ji kamar ba zai iya yin rayuwa
ba idan babu shi wani iko na Allah Kuma sai shima yaro Hulkas ya shaku da sarki Shardas ya
zamana cewa yama shaku dashi fiye da yadda ya shaku da uwarsa Shadila har takai cewa ko
abinci baya yarda yaci sai tare da sarki shardas in ba haka ba kuwa sai dai ya kwana da yunwa
shima sarki shardas din baya iya cin abincin shi kadai idan ba tare da hulkas ba kai hatta telan
da yake yiwa sarki shardas dinki iri daya dana Hulkas yake dinka musu kullum sai dai kaga
sunyi anko sunzo fada tare sun zauna akan karagar mulki duk da rana babu abinda yake
rabasu kullum ..
.
Sai bayan hulkas yayi barci akan kirjin sarki shardas sannan shadila ke daukeshi tayi masa
shimfida a kusa da gadon sarki domin ko cikin dare idan ya farka baiga Sarki ba sai dai ya
fashe da kuka kuma babu mai iya rarrashinsa yayi shiru face sarki din ita kanta shadila lokacin
da taga shakuwar sarki da yarima hulkas ta wuce saninta ta wuce duk tunanin mai tunani sai
hankalinta ya dugunzuma ainun taji zuciyarta ta fara yi mata gargadi kada ta kuskura ta sanar
da yarima hulkas asalin abin dake tsakaninsu a nan gaba idan hulkas ya girma
.
A duk sa adda ta tuno da alkawarin da ta dauka na rufe wannan sirri dakuma gargadin da sarki
shardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrin sai hankalinta ya
dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki........
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part B.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Idan ta tuna gargadin da sarki Hsardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona
sirrinsa sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki haka dai aka ci gaba da wannan
rayuwa har yarima hulkas ya cika shekara shida ya zamana cewa gaba daya mutanen kasar
Romaniya suna matukar kaunarsa kai ba ma yan kasar ba hatta baki sonsa suke saboda
kyawunsa da farin jininsa da kuma kyawawan halayansa da irin hankalin da Allah ya bashi
tamkar bai kasance yaro karami ba sannan ga shi Allah ya bashi jin kai da tausayin talakawa
sabanin sarki shardas wanda ya kasance Kasurgumin Azzalumin bawa.
.
Gaba daya zaluncin da sarki shardas ke yiwa talakawa sai da yarima hulkas ya hanashi kamar
matsa musu wajan karbar haraji mai yawa kai sumame na mamayar bazato a kamo bayi a
kwashe dukiyar talakawa sai dai takai cewa duk inda yarima Hulkas ya gifta a cikin nahiyar
kasar sai dai kaga jama a suna yi masa kirari da sarkin Gobe Yadda ake yi masa ladabi,
biyayya, da girmamawa kuwa ko sarki shardas ba a yi masa haka duk da cewa kuwa ana
tsananin tsoronsa hatta a cikin gidan sarautar kwau Bayi, barori, kuyangi da dakari ma suna bin
umarnin yarima hulkas tamkar sarki shardas ne yake basu umarnin, kai sai da takai cewa
yarima hulkas yana zartar da abubuwa da yawa ba tare da yayi shawara da sarki ba ko da
kuwa shi sarki shardas baya son wannan abu ba zaice uffan ba bare ya hanashi.
.
Ashe duk wannan abu dake faruwa tsakanin sarki shardas da yarima hulkas boka barwas na
lura da shi amma sai yayi shiru baice kala ba wata rana da yammaci sarki shardas na tsaye a
can saman ginin wata baranda yake cikin harabar gidan sarautar sai ya hango yarima hulkas
tare da mahaifiyarsa shadila sun fito rangadi suna kewaye a cikin gidan sarautar sunta rabawa
bay dakaru barori da kuyangi kyaututtukanna suturori kala kala. koda ganin wannan al amari sai
ran sarki ya baci zuciyarsa tayi bakikirin ya tuna cewa tunda fa aka haifi wannan yaro hulkas
rayuwar kasar gaba daya ta sauya duk wani iko nasa kwarjininsa da tsarin mulkinsa ya dakushe
ya zama kamar mutum mutumi sai abinda hulkas ya zartar a fada shi ake bi su kansu fadawan
sarki shardas basa karbar umarnin sa sai abinda yarima Hulkas ya zartar domin a gaba daya
sarakai, attajirai da talakawa sun dauki hulkas fiye da kima wasu ma gani sukeyi kamar ya
cancanci a bauta masa kamar yadda ake bautawa sauran alloli na kasar saboda ganin irin
abubuwan al ajabin da suka faru daga sa adda aka haifeshi kawo iyanzu duk da cewar yarima
hulkas ya sami wannan dama da daukaka bai dauki wani girman kai ba ya dorawa kansa kuma
hakan ba ta sa ya raina mahaifinsa ba sarki shardas face ma tsananin sonsa da yake karuwa a
cikin ransa, duk abubuwan da yarima hulkas yayi a fada ko yasa aka zartar a kasar sai yaje ya
sanar da sarki a yayin da suka kebe kuma ya tambayeshi idan akwai gyara a cikin abubuwan
da ya aikata domin yaje ya gyara ko sau daya sarki shardas bai taba nuna cewar akwai abinda
hulkas yayi ba dai dai ba bare ma ya nuna masa fishinsa a zahiri ko a badini, haka kuma duk
abubuwan da yarima hulkas keyi basu sa shakuwarsa da sarki ta sami rauni ba face ma karuwa
da takeyi a kullum su kansu fadawan sarki shardas da duk masu fada aji a kasar suna matukar
mamakin yadda wannan al amari ya kasance domin ko a mafarki babu wanda ya taba zaton
cewa akwai wani mahaluki wanda zai zo ya iya sauya halayan sarki shardas haka sarki shardas
na tsaye a can saman barandar gidan sarautar yana hango yarima hulkas da mahaifiyarsa
shadila suna ta raba kyautar suturori ga hadiman gidan sarautar sai tsulum yaga boka barwas
ya baiyana a gabansa take boka barwas ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya juyo ya leka
kasan barandar ya dubi yarima hulkas da mahaifiyarsa, barwas ya dago kai ya dubi sarki
shardas yana mai ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ya shugabana hakika in ba don ina
kusa da kai da tuni ka tafka babban kuskuren da zamu hallaka gaba daya duk da cewa kana
shan wannan magani dana baka a karshen kowane wata, kaunar wannan yaro a cikin ranka ta
gama yin katutu idan baka yi da gaske ba makiyinka zai samu nasara a kanka.
.
Koda jin wannan batu sai idanun sarki shardas suka zazzaro zuciyarsa ta kufulo har fuskarsa ta
kama yatsine saboda fishi ya dubi boka barwas yace yakai dirkar birnin romaniya kayi sani
cewa har gobe ban manta da asalin yarima hulkas ba na sani cewa bani da wani makiyi a doron
kasa wanda ya fishi don haka duk wannan soyayya da nake yi masa ta banza ce tunda lokaci
kawai nake jira wanda zamu tafi neman hular