Showing 6001 words to 9000 words out of 11817 words
Chapter 3 - TSATSUBA BOOK 3 Complete Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf
jin ina sonsa dari bisa dari a cikin zuciyata sai
kai kuma a halin yanzu soyayyata a gareka ta linka dari bisa dari fiye da komai kuma kai kadai
ne mutumin da nake jin cewar ba zan iya cutar da shi ba bisa duk irin laifin da zakayi mini koda
kuwa bakin cikin abin dakayi min zai zamo sanadin ajalina.
.
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya sake rungume sarki ya fashe da matsanancin kuka
yace yakai abbana tabbas nasan kana kaunata fiye da kima amma ni ina jin kusancinka a raina
fiye da kusancin jini da hanta inaji a raina cewar idan babu kai a wannan duniyar ba zan rayu ba
kuma ina jin cewar rashinka a kusa dani dai dai yake da jefani cikin kurkukun da babu ci ba sha
kuma babu hasken da mutum zai iya ganin ko da tafin hannunsa face matsanancin duhun daba
zai misaltu ba koda jin haka sai sarki shardas ya janye jikinsa daga cikin na yarima hulkas
kansa na sunkuye yana zubar da hawaye kawai sai ya daga hannu ya yiwa sarkin yaki marzanu
inkiya nan take marzanu ya rugo ya dauke yarima hulkas ya ruga da shi izuwa bakin keken
dokin ya sashi a ciki itama shadila sai ta koma cikin keken dokin ta zauna nan take aka sakarwa
dawakan linzami keken dokin yayi gaba su sadauki marzanu sukabi keken dokin a baya suna
maiyi masa kawanya gaba daya gefe da gefe don tabbatar da tsaro.
.
Nan dai sarki shardas ya bisu da kallo har sai da suka kule ya daina ganinsu sannan ya juya ya
koma cikin gidan sarautar cikin tsananin bakin cikin rabuwa da yarima hulkasa bai ankara ba
saiji yayi hawaye ya kara zubo masa a wannan lokaci kuma inda yake wucewa akwai dakaru a
tsaitsaye kuma ga bayi barori da kuyangi suna ta kai kawo da hidimomi
duk wanda yaga hawaye a idanun sarki sai kaga ya firgice domin kowa ya san cewa a tarihin
rayuwar sarki shardas babu wanda ya taba ganin hawayansa sai yau da yake an san irin
shakuwar dake tsakanin sarki shardas da dan sa yarima hulkas kuma an san cewa yau sun
rabu sai kowa ya gane dalilin zubar da hawayan nasa. .
Abin da mutane basu sani ba shine wannan hawaye bana soyayyar hulkas bane ba kadai har
da takaicin tunanin ainihin alakarsa da hulkas gami da sanin cewa hulkas ba jininsa bane da
kuma bakin cikin rashin samun soyayyar shadila a gareshi ta gaskiya kai tsaye su sadauki
marzanu suka durfafi cikin daji suka sukayi ta tafiya babu sassauci babu tsoro ko shakkar wani
abu saboda sun yarda da kansu.
.
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace dole a ce da mijin iya baba hakika komai
yawan yan fashi da shirinsu idan suka hango wannan runduna ta su sadauki marzanu saikaga
sun fasa taresu sun bace daga kan hanyarsu, ba komai bane ya haddasa hakan ba face
kwarjininsu kuma ido ba mudu bane ammma yasan kima ma ana kai da ganin dakarun marzanu
kasan sun cika zaratan jarumai masu tarwatsa maza domin dukkansu sun kasance manya
manya masu kirar mutanen farko, gashi jikinsu a murde yake kuma sun tara kwanji da jijiyoyi kai
kace da dutse aka yi gabobin jikin nasu irin shigar yakin da sukayi kuwa mai ban tsoro ce domin
kowannansu yana daukeda miyagun makami yaki irin wanda idanu basu saba gani ba kai ba
wai yan fashi ba hatta mugayan dabbobin daji da bakaken aljanu wadanda suka kasance
azzalumai suna ganin wannan runduna sai kaga sun bace daga wajan saboda boka barwas ya
shirya wadannan dakaru tuntuni da karfin sihirin tsafi mai tunkararsu sai cikakken shiryayye
abin kwatance a duniya.
.
Kwana uku kacal wadannan dakaru suka shafe suna
tafiya suka iso birnin askandariya suna shigowa suka iske birnin a cike makil da jama a duk inda
mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan jama a fiye da rabin jama ar da suke gani
baki ne wadanda sukazo halattar gasar jarumtaka mafi akasarin bakin kuwa sarakai ne da
attajirai da yayansu da kuma fatake da shahararrun bokaye tabbas gaba da gabanta aljani ya
taka wuta lokacin da keken dokin gimbiya shadila ya kunna kai cikin birnin sadauki marzanu da
dakarunsa na biye dashi sai gaba dayan jama ar dake wajan suka dare suka basu hanya kuma
kowa ya zuba ido ana kallonsu aka zama kauyawa ba komaine ya haddasa hakan ba face
ganin irin dukiyar da aka kashe wajan kera keken dokin da gimbia shadila ke ciki da kuma
kayan yakin da dakarunta ke sanye da su domin an sanya jarin wani sarkin ne gaba daya nan
fa sarakuna masu ji da kansu ma suka ringa raina kansu basu san sa dda suka rinka leken cikin
keken dokin ba domin suga wanda yake ciki amma da yake an saki labulan keken dokin damar
hakan bata samu ba a gunsu nan fa aka bi keken dokin a baya duuu har izuwa kofar gidan
sarautar birnin ana isa sai akayi cirko cirko.
.
Kawai sai sadauki marzanu ya zaro wata wasi ka ya baiwa masu gadin gidan sarautar yace su
kaiwa sarkinsu, wasikar na isaga sarki hulbasu yana budeta yayi arba da hatimin sarki shardas
cikin zumudi ya mike tsaye zumbur ya taho da sauri izuwa kofar gidan sarautar yazo gaban
keken dokin yana mai cewa lale marhaban da gimbiya shadila matar sarki shardas na Birnin
Romaniya.
.
Koda jin wannan batu sai jama a suka zuba idanu domin suga gimbiya shadila saboda labarinta
ya gama bazuwa a nahiyar gaba daya ana ta surutun tsananin kyawunta santaleliyar kafarta ta
fara zurowa kasa daga cikin keken dokin tun kafin ma jama a suga ragowar jikin nata suka fara
gigita da dimauta ai kuwa tana fitowa gaba dayanta aka yi arba da kyakkyawan surar da Allah
yayi mata sai mutane suka kama sambatu wasu kuwa basu san sa adda suka kama dalalar da
yawu ba tamkar masu hauka sabon shiga.
.
A wannan lokaci shadila na sanye da wata shudiyar doguwar riga damammiya wacce ta
baiyana dukkan siffofin jikinta a fili.
.
Wohoho! kyawu kyauta ce daga Allah. Mutum ba zai iya baiwa kansa ba, kai ko namijin da bai
cika namiji ba idan yayi arba da wannan gimbiya a wannan lokaci sai ya zama namiji domin
mace ce doguwa wacce bata kasance siririya ba kuma ba kakkaura ba tana da dara daran
idanuwa masu dan karen haske da fari hancinta dogone siriri tamkar fikakken alkalami a
kasansa an dasa mata dan kankanin baki kamar yankan wuka, cikinta a shamule yake tamkar
bata taba cin komai ba kugunta mai fadi ne sosai ga mazaune masu tudu kirjinta a cike yake fal
kamar bata taba shayarwa ba gashin ta baki ne sidik kuma dogo ya zuba har kasan marar ta sai
haske da kyalli yake kamar madubi ganin wannan kyan yasa na kasa ci gaba nake cewa sai
Allah ya kaimu gobe.
.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part D.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Tana gama fitowa daga cikin keken dokin saiga danta yarima hulkas shima ya fito sanye da
koren tufafi na alfarma irin nasu na sarakai shima take tsananin kyawunsa ya tafi da hankalin
kowa dake wajan domin albasa tayi halin ruwa cikin farin ciki da girmamawa shadila ta risina ta
gaida sarki hulbasu har ta budi baki zatace wani abu sai sarki Hulbasu ya tari numfashinta yace
yake tauraruwar sarki shardas
ai nan ba muhallin yin magana bane kece bakuwa mafi daraja daga cikin dukkan bakin da suka
shigo wannan birni nawa ina tsoron dukkan abinda zai bata miki rai koya taba lafiyarki don haka
dolene na riritaki tamkar rai guda daya zaifi kyau mu karasa ku sami hutu da nutsuwa keda
danki yarima hulkas. .
Koda gama fadin hakan sai sarki Hulbasu ya kira sarkin Yakinsa ya hadashi da sadauki
marzanu yace yaje a basu nasu masaukin shi kuwa sarki hulbasu sai ya juya Ya nufi cikin gidan
sarautar Gimbiya shadila da kuyanginta su uku tare da yarima hulkas suka bi bayansu basu yi
wata doguwar tafiya ba suka iso turakar gimbiya LUZURAINA matar sarki hulbasu inda suka
isketa tare da danta yarima Basmar wanda shima yarone dan kimanin shekara tara wato ya
girmi yarima hulkas tazarar shekara uku
koda yarima hulkas da basmar sukayi arba da juna sai nan take sukaji jininsu ya hadu kafin ma
luzuraina ta taso ta taryi gimbiya shadila tuni basmar ya taso da sauri ya tari hulkas yana mai
mika masa hannu domin su gaisa ba tare da shakkar komai ba kuwa hulkas ya baiwa basmar
hannu suka gaisa basmar ya gabatar da kansa a gareshi a sannan ne sarki hulbasu ya gabatar
da gimbiya shadila a wajan matarsa suka rungume juna cikin farin ciki.
.
Nan take sarki hulbasu ya juya ya fito daga cikin turakar ita kuwa luzuraina ta karbi shadila
hannu biyu cikin matukar farin ciki kamar taga yar uwarta ta jini wadda suka dade basu hadu ba
nan da nan tasa aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka ci tare sama wadannan
kuyangi guda uku na gimbiya shadila sai yan uwansu kuyangi suka janyesu suka fice dasu suka taf dasu izuwa nasu
bangaren koda aka fara cin abincin sai yarima basmar ya kama hannun yarima hulkas ya jashi
suka fice daga cikin turakar luzuraina yana mai cewa da umman tasa zamuyi dan tattaki domin
na nuna masa gidan nan cikin daga murya luzuraina tace da basmar lallai kada ka fice daga
cikin harabata domin sarki ya gargadeni akan na kula da abokinka sosai ko sauraronta basmar
baiyi ya yaci gaba da jan hulkas da gudu suka nausa cikin harabar gidan basu tsaya a ko ina ba
sai da sukaje wani babban fili wanda aka kawatashi da suke shuke furanni kala kala kuma aka
shirya kayan hutu dana wasa a wajan kamar su lilo dawakan katako da wadansu irin gadaje na
wasan yara da zuwansu wannan wuri wanda aka kirkireshi musamman saboda yarima basmar
sai wajan ya burge yarima hulkas suka hau lilo suna shela kansu suna ta kyalkyala dariyar
farinciki daga can sai yarima basmar ya dubi hulkas a lokacin da ya tsaida lilonsa cak yace
yakai hulkas kayi sani cewa kaine abokina na farko a duniya kuma na lura cewa kaima nine
abokinka na farko.
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke yarima
hulkas ya dubi basmar yace kai kuwa yaya akayi ka gane haka basmar yayi murmushi yace ai
na lura ne da duk irin yanayinka kuma da irin tsananin farin cikin da kake ciki a yau wanda ke
nuni da cewar baka taba samun sakewa ba irin na yau sa adda hulkas yaji haka sai yayi ajiyar
zuciya cikin alamun takaici yace ai ni nan da kake ganina in ba don albarkacin wannan tafiya da
mukayi zuwa wannan gari naku ban taba ma fita daga cikin gidan sarautarmu ba saboda
mahaifina baya son naje ko ina dare da rana muna tare babu abinda yake rabamu saboda
tsananin shakuwar da ke tsakaninmu.
.
Koda jin wannan batu sai yarima basmar ya cika da tsananin mamaki yace ai kuwa rayuwarka
da tawa tazo kusan iri daya domin nima haka mahaifina ya kafa min takunkumin fita baya barina
naje ko ina amma sai dana shammaceshi ya zamana cewa ina shiga har cikin gari ba tare da
kowa ya sani ba a yanzu hakama akwai wata jarumar yarinya da na hadu da ita wacce tayi
matukar burgeni kuma ta bani tsoro domin ban taba ganin karamar yarinya mai jarumtaka
kamarta ba don a gabana tayi gumurzu da karti goma duk ta bazar dasu a kasa da karfin
damtsenta ba makami ina mai tabbatar maka da cewa shekarunta ba zasu fi namu ba wato ina
nufin sa'armu ce, koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai hulkas ya bushe da dariya yace
haba yakai abokina wannan kuma wace irin tatsuniya ce haka kazo min da ita ai wannan kawai
almara ce kazo mini da ita sai dai idan harkar tsafi ce amma ba zahiri ba.
.
Koda jin haka sai yarima basmar ya kama yin rantse rantse yana cewa lallai al amarin wannan
yarinya ba tsafi bane yarima hulkas yace idan har kana son na yadda da wannan labari daka
bani sai dai ka kaini naga yarin yar a zahiri da Idanuna yanzu ta yaya kake ganin zamu iya fita
daga cikin wannan gidan sarauta taku harmu shiga cikin gari muje ka kaini inda wannan yarinya
take?
.
Sa adda yarima basmar yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ai wannan mai sauki ne
kamar cire silin gashi daga cikin tandun mai muddin zaka iya yin duk abinda zanyi hulkas yace
ai yanzu tuni zuciyata ta kwadaitu da son ganin wannan yarinya da ka bani labari kuma raina ya
kagu damu tafi can inda take saboda a rayuwata babu abinda nake so sama da jarumtaka da
iya yaki gashi kuma ko sau daya ban taba jarraba yin suba kai in dai wannan labari daka bani
gaskiya ne zan iya biyan wannan yarinya dinare dubu domin ta koya mini yaki da jarumtaka ina
mai rokonka daka tashi mu hanzarta shiga cikin wannan gari naku koda jin haka sai yarima
basmar ya kama hannun yarima hulkas suka duro kasa tare daga kan lilon suka ruga izuwa
wani bangare daban dake gidan saida sukayi gudu na tsawon yan dakiku masu yawa sannan
suka iso karshen gidan sarautar suka shiga cikin wani kwararo wanda ya kaisu inda
matattakalar shaddar gidan sarautar take gaba daya da zuwa suka iske wadansu wulakantattun
bayi suna ta debo kashi suna lodashi a cikin wani amalanke, koda bayin sukaga shigowar
yarima basmar tare da hulkas sai bayin suka zube kasa gaba dayansu suka gaida basmar a
lokacin da doyin kashin ya ishi hulkas ya kama kau da kai yana toshe hancinsa shi kuwa
basmar ko kadan bai damu ba ga dukkan alamu ma ya saba da zuwa wajan basmar ya dubi
shugaban bayin yace yau mu biyu ne nida abokina, ina son ku fitar damu zuwa cikin gari kamar
yadda kuka saba a sirrance.
.
Koda jin haka sai shugaban yayi dariya yace an gama ya shugabana bamu ladan aikinmu
kamar yadda ka saba cikin alamun damuwa yarima basmar ya ce yau na sha afa ban taho da
shiri ba ama ai kasan ba zanyi muku wasa ba gobe zan baku ladanku gama fadin hakan keda
wuya sai suka jiyo takun sawun dakarun dake kulle dasu cikin hanzari bayin suka boye su
yarima hulkas a karkashin amalanken da suke loda kashin faruwar hakan keda wuya sai ga
wadansu dakaru biyu sun shigo wajan rike da bulalai da shigowarsu sai suka tsaya a gaban
amalanken dai dai inda su yarima basmar suke har daya daga cikinsu ya take danyatsan hulkas
guda da katon takalminsa har hulkas zaiyi ihu sai yarima basmar yayi sauri ya toshe masa baki
da tafin hannunsa daya daga cikin dakarun ya dubi shugaban bayin ya daka masa tsawa yace a
cikinku waye mai murya irin ta yara tabbas daga can nesa na jiyo muryar yaro a nan har
shugaban bayi ya budi baki zaice wani abu sai wani daga cikin yaransa ya tari numfashinsa yayi
magana da karamar murya iri daya sak da ta yarima basmar al amarin da yayi matukar baiwa
kowa mamaki kenan koda jin hakan sai dakarun suka kyalkyale da dariya wanda yayi magana
da farko ya dubi bawan da yayi muryar yarima basmar yace tabbas kana da hikima watarana
zan gabatar dakai gaban sarki domin ka debe mana kewa.
.
Koda gama fadin hakan sai dakaru biyu suka juya suka fice daga cikin wannan kwararo da ake
aikin kashi fitarsu keda wuya sai bayin suka sauko buhuhuna da suka dura kashi a ciki suka
zura yarima basmar da hulkas a kansu suka kulle bakin buhuhunan amma sai suka yi dabaara
suka farka buhun a dai dai kan fuskokinsu yadda zasu iya shakar numfashi duk da haka sai da
yarima hulkas ya kama kakarin amai saboda doyin kashi gashi an labta wadansu buhuhunan a
samansu nauyi ya damesu nan take yarima hulkas yaji kwalla ta cika masa idanu yace oh
duniya juyi juyi kwado ya fada ruwan zafi wai yau ni yarima hulkas nine a cikin buhun kashi
saboda kawai ina son shiga cikin gari naga abin al ajabi tabbas neman duniya ba wasa bane
kuma ba a samunta cikin sauki sai ansha wuya yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaji
an ja amalamken da suke kai anyi gaba dasu nan fa akayi ta tafiya dasu ana wucewa ta cikin
sako sako da lungu lungu na gidan sarautar har sai da aka wuce dasu ta cikin kofofi shida duk
kofar da aka zo sai sun tsaya an caje buhuhunan kashin wani lokacin ma sai dakaru sun
caccaka tsinin takobi a cikin buhuhhunan saboda zargin ko an sato wani abu a ciki in ba don
Allah ya kiyaye ba saura kiris takobin wani badakare ta tsire ido guda na yarima Hulkas,
shikuwa yarima barmas ma sai da aka dan sokeshi a kafada jini yayi tsartuwa yaji kamar ya
kurma ihu amma sai ya daure a haka dai aka samu aka fice dasu ba tare da asirinsu ya tonu ba
kafin a isa bakin kogin garinne yarima hulkas yaji nadama ta zo masa bisa wannan ganganci da
sukayi na sai da ransu don kawai suna son su shiga cikin gari.
.
Ana isowa bakin kogin ne aka sauke buhunhunan dasu yarima hulkas ke ciki ko da aka fito
dasu aka ga yarima barmas ya sami rauni a kafadarsa sai hankalin bayin ya dugunzuma ainun
suka firgice, shi kuwa yarima Hulkas yana ganin rauni a kafadar barmas bai san sa adda ya
kama rigarsa ya yagata ya daurewa barmas raunin don tsaida jiniba. .
Cikin rudewa hulkas ya dubi barmas ya ce yakai abokina tunda dai ka sami wannan rauni zaifi
kyau. Mu hakura mu koma cikin gidan sarauta mubar batun ganin wannan jarumar