Showing 3001 words to 6000 words out of 11817 words
Chapter 2 - TSATSUBA BOOK 3 Complete Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf
lamsara da ita ne kadai zan sami nasarar hallaka
wannan yaro kamar yadda ka fada lokacin da sarki shardas yazo nan a zancensa sai boka
barwas ya tuntsire da dariyar farinciki sautin dariyar tasa ne ya janyo hankalin yarima Hulkas da
shadila suka Hangosu, cikin tsananin farin ciki yarima hulkas ya baro shadila a inda take tsaye
ya ruga da gudu izuwa kan matattakalar bene da zata kai shi inda su sarki shardas suke.
.
Koda sarki shardas ya hango yarima ya taho gareshi sai shima ya tareshi suka rungume juna
hulkas na hada idanu da boka barwas sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi wani irin tsoro ya darsu
a cikin zuciyarsa dama duk sa adda yarima yayi arba da boka barwas sai yaji haka Hulkas ya
janye jikinsa daga cikin na sarki shardas yace yakai abbana kayi sani cewa yanzu nake shirin
na tafi zuwa turakarka bayan mun gama raba kyaututtuka ga hadiman gidan nan na nemi wata
alfarma guda daya a wajanka.
.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi murmushi yace haba ya kai dana shin ka taba
neman wata alfarma ne a wajena na hanaka? Ai duk abinda kaji zuciyarka tana da muradi kayi
nayi maka izini muddin wannan abu ba zai zubar mana da kimarmu da mutuncinmu ba, yanzu
sanar dani alfarmar da kake so nayi maka Hulkas yayi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa
kas cikin alamun kunya da damuwa kamar ba zai iya magana ba sannan yace yakai abbana ka
sani cewa tun da aka haifeni a birnin nan ban taba zuwa ko da wani garin ba daga cikin sauran
manyan biranen dake kasar tamu ba, labari ya zo mini cewar hakimin birnin Istanbul ya shirya
gagarumar gasa ta jarumtaka kuma an gaiyato manyan jarumai daga bangarori da yawa na
duniya lallai ina son na halacci wannan gasa domin a rayuwata babu abinda nake so sama da
ganin mutum mai jarumtaka da iya yaki na dade
ina rokonka akan ka koya mini yaki a matsayina na jarumin da zai shahara a wannan nahiya
tamu amma kaki kuma baka taba gaya mun dalili ba tunda baka son ka sanar dani dalilin nima
bana bukatar na sani
ni dai yanzu ka amince mini nayi wannan tafiya zuwa birnin istanbul.
.
Koda yarima hulkas yzo nan a zancensa sai sarki shardas yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun
don haka sai ya yunkura da nufin ya juya ya dubi boka barwas domin ya nemi shawararsa
amma sai yarima hulkas ya kama hannayansa yace yakai abbana kayi sani cewa bai kamata a
sami shamaki ba a tsakanin da da mahaifi muddin wannan da ya kasance jinin mahaifinsa,
babu bukatar kayi shawara da wani akan alfarmar da zan nema a wajanka tunda dai nafi
karfinta a wajanka. .
Koda jin wannan batu sai jikin sarki ya yi sanyi kafin ya bude baki yace wani abu sai boka
barwas ya tari numfashinsa ya dubi hulkas yace haba ya kai yarima ai bai kamata kace zaka fita
daga cikin birnin nan ba kaje wani wuri ba tunda kasan cewa bincike ya nuna cewa duk ranar
da kayi dogon zango kasar nan zata shiga cikin fari da annobar talauci, kafin boka barwas ya
gama rufe bakinsa tuni shima hulkas ya tari numfashinsa yana mai cewa amma ai cewa kayi sai
idan na fita daga cikin yankin kasar nan gaba daya sannan hakan zata faru ya kai barwas kayi
sani cewa kana da iyaka a tsakanin da da mahaifi don haka bai kamata ka wuce gona da iri ba
yarima hulkas yayi wannan furuci ne fuskarsa a murtuke yana mai hararar boka barwas amma
da ya dubi sarki shardas sai fuskarsa ta juye zuwa annuri.
.
Kawai sai sarki shardas ya maida masa da martanin murmushin yace jeka abinka yakai dana
lallai nayi maka izinin ka tafi zuwa birnin istanbul domin idanunka su more da kallon abinda
zuciyarka ke so koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube yarima hulkas ya rungume sarki
shardas yana mai yi masa godiya nan take yarima hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki
shardas ya koma wajen mahaifiyarsa
shadila yana riskarta ya rungumeta yana mai yi mata bushatar cewar sarki ya amince masa yayi
wannan tafia nan take itama shadila ta cika da farin ciki amma koda ta dago kai tayi arba da
fuskokin sarki dana boka barwas tagansu a murtuke babu annuri sai hankalinta ya tashi nan da
nan cikin sauri ta kama hannun yarima hulkas taja shi suka juya da baya suka koma cikin gidan
sarautar cikin alamun tsananin fishi boka barwas ya dubi sarki shardas yace wannan shine
kuskure na uku wanda na gaya maka cewar kada ka aikatashi amma gashi idanunka sun rufe
saboda soyayyarsa ka aikatashi ko dajin wannan batu sai sarki shardas ya juyo da sauri ya
fuskanci boka barwas cikin tashin hankali yace ban gane abinda kake nufi ba yanzu saboda
kawai na bar yarima hulkas yaje yayi kallon gasar jarumtaka a birnin istanbul shine na aikata
babban kuskure?
.
Barwas yace kwarai kuwa rashin aiki da shawarata yasa ka aikata babban kuskure na uku
wanda nake ta kokarin hanaka ai tunda dai ka fahimci cewar ban son ka bar yaron nan yayi
wannan tafiya bai kamata ka barshi yayi ba bincike ya nuna mini cewar yarima hulkas zai sami
wata babbar dama ta yakarmu a cikin wannan tafiya da zaiyi amma kuma a dalilin tafiyar ne
shima zai sadu da abinda zai zamo sanadin ajalinsa anan gaba.
.
Lokacin da sarki shardas yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe yaji kamar ya kirawo yarima hulkas yace dashi ya janye izinin da ya bashi nayi wannan
tafiya amma kuma sai yaji ba zai iya ba.
.
Kafin ya budi baki yace wani abu sai kawai yaga boka barwas ya bace bat tamkar bai taba
wanzuwa ba a wajan, cikin alamun tsananin damuwa sarki shardas ya juya ya sauka daga kan
matattakalar barandar ya nufi cikin gidan sarautar zuciyarsa cike da sake sake da tunani abinda
ya fara fado masa a rai shine wai shin yaya akayi nema har ya bari son yarima ya shiga
zuciyarsa alhalin ya san cewa ba jininsa bane asalima ba shi da wani makiyi wanda ya fishi a
doron kasa tunda komai dare dadewa sai ya nemi daukar fansar ran mahaifinsa hailur a kansa
wata zuciyar kuma sai tace dashi hakika babu abinda yafi soyayya hadari a wannan duniya
domin inda tun farko bai kamu da son shadila ba da tun sa adda ya kashe mijinta itama zai
kasheta dashi kenan ya huta da fargabar komai don da yanzun bata haife masa alakakai ba
kuma kadangaren bakin tulu wato yarima Hulkas maimakon sarki shardas ya wuce zuwa
turakarsa sai ya wuce zuwa turakar shadila kai tsaye duk inda ya ratsa sai dai kaga hadimai
suna zubewa kasa suna kwasar gaisuwa da isarsa dakin sai ya iske shadila tare da hulkas a
zaune cikin nishadi da farin ciki suna cin tuffa a karon farko sai hulkas yaga babu cikakken
annuri a fuskar sarki shardas kafin hulkas yace wani abu sai shardas ya dubeshi yace yakai
dana ina son ka bamu dan lokaci zan tattauna da mahaifiyarka.
.
Koda jin haka sai hulkas ya mike tsaye yana mai yin
murmushi ya nufi kofar fita daga cikin dakin yace babu matsala fitarsa keda wuya sai sarki ya
tura kofar ya rufe ta sannan yazo daf da shadila ya zauna ya sumbaci wuyanta suka rungume
juna suna soyayya daga can sai yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin nata ya hankadata ta fado
kasa daga kan kujerar da take zaune ya cafi makoshinta ya shaketa. .
Nan take idanunta suka zazzaro suka kada sukayi jawur ta fara kakarin mutuwa a sannan ne ya
saketa ta zube kasa tana numfarfashi kamar ranta zai fita tana mai kurawa shardas idanu.
.
A fusace shardas ya dubeta yace wannan jan kunne ne nayimiki gami da tuni bisa alkawarin
dake tsakaninmu akan wannan yaro zakuyi tafiya tare kedashi zuwa birnin istanbul domin
halattar taron gasar jarumtaka na duniya da aka sabayi idan kikayi amfani da wannan dama
kika gayawa danki sirrin dake tsakani na dashi a bakacin ranki ki sani cewa duk abinda zai faru
tsakaninki dashi boka barwas zai gani a cikin madubin tsafinsa yanzu zan fita na barki kada ki
kuskura ki bari danki ya gane cewar nayi miki wani abu yanzu.
.
Koda gama fadin haka sai sarki ya juya ya fice daga cikin turakar yana fita sai shadila ta mike
zumbur a lokacin da hawayen bakin ciki da takaici ya zumo mata kawai sai tayi sauri ta dauko
wani farin kwalli ta sanya a cikin idanunta nan take idanun nata suka washe sukayi fari kal
tamkar bata taba yin kuka ba tana ajiye kwallin saiga yarima ya shigo idanunsa sun ga sa adda
ta ajiye kwallin don haka sai ya zargi
cewar akwai wani abu da ya faru tsakaninta da sarki
shardas domin baiga dalilin da zaisa tayi amfani da kwalli ba alhalin dama can ta gama yin
kwalliya cikin alamun zargi hulkas ya dubi shadila yace yake ummina menene ya faru tsakaninki
da abbana??
.
Shin ya gaya miki wata magana ne wacce ta sosa miki rai?
Koda jin wannan tambayoyi guda biyu sai shadila tayi murmushi tace babu wata magana wacce
ta sosa mini zuciya farinciki ne kawai yasa kaga alamun sauyin yanayi akan fuskata domin ya
shaida mini cewar zamuyi tafiya nida kai zuwa birnin istanbul koda jin haka sai murna ta kama
yarima ya rungumeta yana mai cewa burina ya cika yake ummina lallai idanuna zasu ga abinda
suka dade suna mafarkin gani.
.
A wannan rana gaba daya yarima hulkas bai sami damar hutawa ba ko tsayuwa a waje daya
saboda murna sai kai kawo yake yana ta shirye shiryen tafiyar da zasuyi gobe.
.
Lokacin da dare yayi sai bacci ya kauracewa hulkas da yake akan gado daya suke kwance tare
da sarki shardas sai yarima hulkas ya cika da matukar mamaki bisa ganin yadda shima sarki
shardas din ya
kasa yin barci sai juye juye yake yi kawai akan gado
Yarima Hulkas ya dubi sarki cikin alamun mamaki yace yakai abbana wai shin.
.
Mene ne ya hanaka barci ne a yau?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi murmushi yace yakai dana kai yarone don
haka baka son dacin rabuwa da masoyi ba tunda aka haifeka a cikin wannan gidan sarauta ban
taba rabuwa dakai ba tsawon sa a daya jal kullum muna tare dare da rana hatta kwanciyar barci
bata rabamu yau gashi an wayi gari zakayi tafiya zamuyi rabuwa ta a kalla tsawon sati biyu a
cikin wace irin damuwa da kadaici kake tunanin zan kasance?
.
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai Jikin yarima Hulkas yayi sanyi nan take idanunsa
suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa bai san sa adda ya rungume sarki ba yana mai
cewa.......
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part C.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da Hulkas yazo nan a zancensa sai shima sarki shardas jikinsa yayi sanyi ruwan
hawaye ya subuto daga cikin idanunsa ya janye jikinsa daga jikin na hulkas suka fuskanci juna
yana mai rike kafadunsa yace yakai dana kayi sani cewa ko kadan nima bana son abinda zai
sosa maka zuciya kuma babu abin da nake so sama da ganin farin cikinka amma in ba don
haka ba da tsawon sa a daya zan kasance a cikin zumudi da dokin dawowarku lafiya kaida
mahaifiyarka domin kune ginshikin rayuwata, haka dai sarki shardas da yarima hulkas sukayi ta
hira ta bankwana har asubahi ta riskesu basu sani ba a sannan ne hulkas ya fara gyangyadi
kafin a jima barci ya daukeshi faruwar hakan keda wuya saiga shadila ta shigo sanye da rigar
barci wacce ke baiyana kyakkyawar surar jikinta babban abinda ya daurewa sarki shardas kai
shine bai taba ganin murmushin shadila ba a duk sa adda zata shigo turakarsa da daddare sai
yau tun a farkon ranar da ya satota daga sansaninsu ya kawota wannan gidan sarauta saboda
ya tabbatar da cewar ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta kai tsaye shadila ta fado kan
sarki shardas ta fara jan hankalinsa domin ya kwadaitu da ita maimakon ya karbeta hannu biyu
sai kawai taga ya bangajeta ta fadi can gefe daya akan gadon ya dubeta a fusace yace menene
dalilin da yasa yau kika shigo cikin turakata kina mai murmushi alhalin baki taba yi mun
murmushi ba a dukkan dararen da suka shude na barcinmu?? .
Koda jin wannan tambaya sai shadila ta bushe damahaukaciyar dariya kamar ba zata daina ba
karfin dariyar nata baisa yarima hulkas ya faka daga barcin da yake yi ba mai nauyi saboda
kasancewar barcin mai nauyi ne daga can sai shadila ta tsuke bakinta ta daina yin dariyar tana
mai murtke fuska ta dubeshi tace yakai mijina na dole ka sani cewa ban taba jin kaunarka ba a
cikin zuciyata dai dai da darajar kwayar zarra kaine ka rabani da farin cikina kuma kaine ka
shayar dani gubar bakin cikin da har abada ba zan iya amayar da ita ba sai dai ajalina ya zame
mini saukin ciwon data sa mini Abinda yasa kaga na shigo cikin turakarka ina murmushi a yau
ba komai bane face farin ciki bisa sanin cewa gobe zan rabu da ganin wannan fuska taka kuma
ba zan sake ganinta ba har sai bayan a kalla sati byu ka sani cewa duk sa adda na kalli
fuskarka sai naji kamar bakin kumurci nake kallo haka kuma duk sa adda ka kwanta dani
nakanji mugun bakin ciki tamkar na kashe kaina saboda ba masoyina hailu bane yake amfani
da wannan kyakkyawan jiki nawa, yanzu na kawo maka kaina ne gareka domin ka more iya son
ranka saboda kwanaki goma sha hudu masu zuwa a mafarki jikin nawa zai zama na masoyina
wanda ka datse rayuwarsa ka mayar da dansa maraya koda shadila tazo nan a zancenta sai
zuciyar sarki shardas ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama tsuma ya daga hannu
da nufin shararawa shadila mari amma sai ya kasa saboda tsoron kada ya maretan hulkas ya
farka daga barci ya gane abinda ya faru tsakaninsu koda shadila taga sarki shardas ya kasa
marinta saita sake bushewa da dariya a karo na biyu ba tare da tace dashi uffan ba sai tasa
hannayanta biyu ta dauki danta hulkas ta rungumeshi a kirjinta ta juya ta fice daga cikin turakar
shi kuwa sarki shardas sai ya bita da kallo kawai cikin tsananin takaici da bakin ciki fuskarsa
nayin gatsine yana jin kamar ya zare takobi yaje ya sareta gari na wayewa sosai sai sarki
Shardas ya kirawo mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira sadauki marzanu ya dubeshi
yace ina son ka zabo zakwakuran dakaru mutum dubu biyu daga cikin manyan dakarunmu kayi
musu jagora a cikin rakiyar matata da dana yarima hulkas izuwa birnin ishtanbul kayi sani cewa
zan baku guzuri ishashshe kuma zan baku kudade masu yawan gaske domin ku kawai da
dukkan bukatunku amma ku sani cewa idan kuka dawo daga birnin istanbul naga kwarzane
guda daya a jikin matata ko dana ko kuma kuka dawo mini dasu babu lafiya ko babu rai a
bakacin rayukan iyalanku daku kanku.
.
Koda jin wannan batu sai sadauki marzanu yarisina yace an gama ya shugaban nan take
marzanu ya juya da sauri ya nufi wani bangare daban na gidan sarautar domin ya hado kan
dakarun daya dace suyi masa rakiya a cikin wannan gagarumar lafiyamai hadari kafin rana ta
take tuni kowa ya gama kimtsawa daga cikin jama ar da zasu yi wannan tafiya shadila da
yarima hulkas kuwa sai suka caba ado mai daukar hankali suka shiga cikin keken dokin
sarauta, sadauki marzanu da sauran dakaru kuwa suka hau dawakai cikin gagarumar shigar
yaki suka sa keken dokin a tsakiya sai kuma kuyangi guda uku kacal da aka tanada domin su
yiwa shadila da hulkas hidima a cikin wannan tafiya.
.
Ba tare da bata lokaci ba wannan zuga ta kama hanyar fita daga cikin gidan sarautar, abinda ya
daurewa yarima Hulkas kai shine rashin ganin sarki shardas a wannan safiya bare suyi sallama
har ya budi baki zai tambayi shadila dalilin da yasa sarki baizo sunyi bankwana ba sai.
.
Kawai ya hango sarki shardas a can saman bene yana dago masa hannu kuma idanunsa sun
ciko da kwalla nan take zuciyar yarima hulkas ta karaya shima ya ji hawaye ya zubo masa take
yaji kamar ya fasa yin wannan tafiya kawai sai hulkas ya daka tsalle ya duro kasa daga kan
keken dokin ya ruga da baya izuwa inda sarki yake can saman bene, babu shiri mai jan keken
dokin yaja linzami ya tsaidashi itama shadila sai ta duro daga cikin keken dokin a dimauce don
a zatonta wani mugun abune ya faru amma sai taga ashe yarima ne ya ruga izuwa inda sarki
yake.
.
Lokacin da sarki shardas yaga yarima hulkas ya rugo izuwa gareshi sai shima ya gangaro da
gudu daga saman benen da yake tsaye ya tari yarima a tsakiyar filin gidan sarautar suka
rungume juna kuma suka kama kuka a lokaci guda saboda bakin cikin rabuwa yarima hulkas ya
dada kankame sarki, yace yakai abbana mene ne dalilin da yasa kaki zuwa muyi bankwana tun
dazu alhalin kasan cewa ina ciikin kewarka da tunanin rashinka a kusa dani.
.
Sa'adda sarki shardas yaji wannan batu sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna
a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye sarki shardas ya numfasa yace yakai dana kayi
sani cewa ni jarumi ne kuma gwarzon mayaki wanda bai taba zubar da hawaye ba komai wuya
da azaba kuma komai farin ciki da bakin ciki tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana amma
yau gashi kai ka sani na zubar da hawaye ina mai tabbatar maka da cewa in banda
mahaifiyarka babu wani mutum wanda na taba