Showing 9001 words to 11817 words out of 11817 words

Chapter 4 - TSATSUBA BOOK 3 Complete Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf

yarinya
domin muje ayi maka magani da sauri koda jin wannan batu sai yarima barmas yayi murmushi
yace aini idan nayi gaba bana komawa baya kuma idan har muka koma gida bamuga wannan
yarinyar ba ai mun sha wahalar banza kenan mun sayar da rayuwarmu a wofi, tunda dai ka
tsayar da jinin dake zuba a jikina babu komai zan iya gabatar da abinda muka fito yi lafiya har
mu kammala, yanzu sai mu shiga cikin kogin nan mu wanke kashin dake jikinmu don kada muje
wajan ta muna wari nan take yarima basmar ya sallami bayin akan cewa idan sun kawo sawun
karshe na kashin suyi tafiyar kada suyi shakkar komai don haka suka saba yi shi dasu domin
shine ya san dabarar da yake yi yake komawa cikin gidan sarautar ba tare da an ganshi ba.
.
Ba tare da bata lokaci ba yarima barmas da yarima hulkas suka ruga zuwa cikin kogin suka
kwabe kayan jikinsu sukayi tumbur sai da suka wanke kayan nasu tas sannan suka fito suka
shanyasu akan wata bishiya suka sake komawa cikin gefen kogin suka kama wanka a wannan
lokaci ne yarima hulkas ya tsinci kansa a cikin wani iein nishadi wanda bai taba jinsa ba na
farinciki walwala da annashawa abin da yafi burgeshi shine ganin yadda yau ya sami yancin
kansa har yake yiwa kansa wanka da wanki alhalin bai taba yiwa kansa wata hidima ba sai dai
ayi masa komai sai da kayan da suka shanya suka bushe sannan suka fito daga cikin kogin

suka je suka sanya kayan nasu sannan yarima basmar ya wuce gaba hulkas na biye dashi suka
nufi wata siririyar hanya wacce zata kaisu cikin gari. A wannan lokaci yammaci ne mai dauke da
yanayi mai kyau da dadi domin wata irin iska ce mai sanyi ke kadawa kafin su iso cikin garin sai
yarima basmar da yarima hulkas suka rude fuskokinsu da rawaninsu ya zamana cewa idanunsu
kadai ake gani don kada a shaidasu haka dai suka ci gaba da tafiya suna ratsawa ta cikin
unguwanni har suka iso wata unguwa dake can karshen gari kuma suka tunkari gida na karshe
a unguwar wanda shi ne mafi muni da kaskanci. Da ganin gidan kasan cewa na talakawa ne
fitik marasa gata ko kuma bako wanda bai kasance dan gari ba saboda an gina gidanne da
katako ko kyakkyawan tsari baiyi ba tun daga nesa su yarima hulkas suka hango wani mutum
mai kwarjini zaune a kofar gidan fuskarsa cike da kasumba amma kuma hannunsa guda na
hagu a yanke yake sannan kafarsa guda a lankwashe take sai da sanda yake dogarawa
mutumin na tsaye a can gefe daya yana kallon wadansu tsuntsaye dake ta wasa akan wata
bishiya saiga matarsa wata yar kyakkyawar mace yar kimanin shekaru talatin da doriya wacce
ba zatafi sa ar gimbiya shadila ba ta fito daga cikin gidan dauke da kofin shayi ta nufi mijin nata.
.
A dai dai wannan lokaci ne mijin matar ya hango su
yarima hulkas sun durfafoshi shi da matar tasa sai suka kurawa su yarima hulkas idanu kawai
cikin sanyin jiki da mamaki.
.
Dama A wannan lokaci su yarima basmar sun cire rawanin da ya rufe fuskokinsu kyawunsu da
kwarjininsu irin na yayan sarakai ya baiyana a fili kururu bisa mamaki sai yarima hulkas yaga
mijin matar ya kura musu idanu ko giftawar ba yayi, koda suka iso daf dasu sai yarima basmar
ya risina a cikin biyayya ya gaishe da mutumin da matarsa sannan ya gabatar da kansa yace nine yarima
basmar dan sarkin garin nan wanda kuma abokina ne sunansa hulkas munzone wajan yarka
siyama domin muga baiwar da take da ita ta jarumtaka da iya yaki saboda abokina bai amince
da tana da wannan baiwar ba a sa adda na bashi labarinta........
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part E.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai mutumin da matarsa suka dubi junansu sukayi
murmushi sannan mutumin ya dubi basmar yace hakika wannan abokin naka zai sha mamaki
kuwa domin a yanzu hakama tuni siyama ta shiga gasar jarumtakar da za ayi a fadar
mahaifinka wacce za a fara gabatar da ita gobe kuma ina sa ran cewa itace zata karbi kambun
wannan gasa.
.
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya kyalkyale da dariya yace haba ai wannan ma almara
ce ya za ayi karamar yarinya wacce aka ce batafi sa a taba zata shiga wannan gasa wacce

manyan mutane zasuyi kuma jarumai na daga sassa daban daban na
duniya har ace talashe gasar.
.
Koda jin wannan batu sai ran mahaifin siyama ya baci ya murtuke fuskarsa nan take cikin fushi
ya kwalawa siyama kira itakuwa, sai gata ta fito daga cikin gidan a cikin shigar yaki.
.
Siyama ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance duk da cewar yarinya ce yar
shekara shida sai mutum yayi zaton takai shekaru goma sha saboda ta kasance doguwar gaske
sai mutum ya dubi fuskarta sannan zai gane cewa yarinyace tana da cikakkiyar sura da zati irin
na cikakkun mata ababan kwatance. .
Koda yarima hulkas yayi arba da siyama sai yaji nan take ya kamu da tsananin kaunarta amma
da yaga ta kalleshi tana mai gabza masa harara sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya bai
bayeshi yaji kamar ya ruga da gudu saboda kwarjininta, siyama ta karaso gaban iyayanta ta
risina a garesu tana mai amsa kira kawai sai mahaifin nata ya daga sandar dake hannunsa da
hannun nasa lafiyayyan yayi nuni a gareta ko da ganin haka sai siyama ta zare takobinta ta
kwala ihu sannan ta daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota ta fada kansa suka
ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro ga dukkan mai kallo nan fa duk su biyun
suka wanzu suna masu kaiwa junansu mugayan hare hare cikin bakin zafin nama duk sa adda
takobin siyama ta hadu da sandar mahaifinta sai dai kaji kal sautin haduwar karafa gami da
tartsatsin wuta na tashi tunda yarima basmar da hulkas suke ganin gumurzun mazaje masu
tsananin zafin nama da jarumtaka ba kamar siyama da mahaifinta siffanta jarumtakar tasu da
kwatantata ba zai yiwu ba, sai dai abinda idanu suka gani babu wani jarumi daya fadowa yarima
hulkas a rai dayaga jarumtakar siyama da mahaifinta sai mahaifinsa sarki shardas hulkas ya
numfasa sannan yace a cikin zuciyarsa babu, wani jarumi da zai iya fafatawa da wadannan
mutumin ko yarsa siyama ya samu galaba a kansu face mahaifinsa sarki shardas
kash ina ma tare da sarki mukayi wannan tafiya da yaga wadannan jarumai masu ban al ajabi
da idanunsa yanzu dama she a wannan duniya akwai irin wadannan jarumai.
.
Sai da siyama da mahaifinta suka shafe sa a daya da rabi suna fafatawa amma dayansu bai
sami nasarar koda kwarzanar jikin dayan ba duk da cewar suna yakinne a fusace da dukkan
karfinsu da iyakar kwarewarsu tamkar abokan gaba masu neman hallaka juna.
.
Koda sukaga sun kasa cutar da junansu da makami sai sukaja da baya sukayi cirko cirko suna
haki da kallon junansu tamkar zakaru kuma suna murmushi
shidai mahaifin siyama murmushin da yake yi bana komai bane face na farin ciki bisa ganin
abinda ya koyawa yasa ta kware a a kansa ainun harma ta fishi kwarewar a matsayinta na ya
mace, ai dama ance kyan da ya gaji ubansa kuma barewa batayin gudu ba danta yayi rarrafe
babban abinda ya daurewa su yarima hulkas kai shine ganin yadda mahaifin siyama ya iya yin
wannan bkin gumurzu alhalin ya kasance mai hannu daya kuma gurgun da yake dogara sanda.
.
Kwatsam! sai siyama da mahaifinta suka ajiye makamansu a kasa gefe daya wato shi ya ajiye
sandar karfen dake hannunsa itakuma ta ajiye takobinta faruwar hakan keda wuya sai sukayi

alkafira a kasa suka afkawa juna suka ci gaba da kaiwa juna naushi da bugu hannu da kafa sai
gashi siyama tana shanye naushi da bugu kai kace wata katumar namiji ce ba mace ba, kuma
yarinya karama yar shekara bakwai tabbas horon da siyama ta samu zata iya gumurzu a
tsakiyar miliyoyin dakarun yaki ma kuma ta dade tana fafatawa tana mai taka rawar gani a
wannan fadan hannu ma sai da siyama da mahaifinta suka shafe kusan sa a biyu gashi dai sun
hadawa junansu jini da majina kuma sun gaji likis amma saboda tsananin juriya naci da
dakakkiyar zuciya sunki su daina fadan.
.
Koda matar mahaifin siyama taga abin ya wuce gona da iri ta ruga ta shiga tsakiyansu ta tsaida
fadan, a sannan ne siyama da mahaifin suka zube kasa suna haki da dariya daga can mahaifin
siyama ya dago kai ya dubi yarima hulkas yace shin yanzu ka gamsu kuma ka yarda cewar yata
zata iya shiga wannan gasar jarumtaka da za ayi a fadar birnin nan? .
Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas yayi murmushi yace tabbas na gamsu kuma na
yarda dari bisa dari, zata iya ya kai abul siyama idan ba zaka damu ba ina son na nemi wata
alfarma guda a wajanka.
.
Cikin mamaki mahaifin Siyama yace yaro ina sauraronka fadi tambayarka naji in dai na sani zan
baka amsarta, hulkas yayi gyaran murya yace ina son ka bani takaitaccen tarihin rayuwarka
sannan ina son na sani shin wannan lalura da na ganka da ita ta rashin hannu da kafa daya ta
sameka ne da girmanka ko kuwa a haka aka haifeka kai mutumin wace kasa ne kuma ya akayi
kazo nan birnin domin ga dukkaln alamu kai bakone a garin nan bisa lura da yanayin gidanka
da na gani wanda ya banbanta da dukkan gidajen birnin nan.
.
Lokacin da yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jikin mahaifin siyama yayi sanyi yayi sauri
ya sunkui da kansa kas don hawaye ne ya subuto masa kawai saiyayi shiru baice komai ba,
caraf sai matarsa wato
ummul siyama ta dubi yarima hulkas tace ka tambayi mijina tambayoyinda idan ya tuno da
amsarsu yake shiga cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa lallai a yanzu ba zaka sami amsar
wadannan tambayoyi ba sai dai wani karon.
.
Koda jin haka sai yarima hulkas da barmas sukaji sun kamu da tausayin mahaifin siyama nan
take hulkas ya tako kafafunsa yazo har gaban mahaifin siyama ya dafa kafadarsa ta dama da
tafin hannunsa yace ka gafarceni yakai abul siyama inda na san cewa tambayoyina a gareka
zasu sosa maka zuciya su tuno maka da wani abin damuwa da ba zan gabatar dasu ba a
gareka mun barku lafiya sai gobe a filin fada zamu hadu idan kunzo filin gasar jarumtaka.
.
Koda gama fadin haka sai su hulkas suka juya da nufin ya kama hannun barmas su tafi amma
sai yaji abul siyama ya dafa kafadarsa cikin mamaki hulkas ya juyo suka fuskanci juna yaga
abul siyama yana yi masa wani irin kallo mai nuna alamar kamar ya sanshi kuma akwai alamun
dumbin magana a zuciyarsa wacce ya kasa amayar da ita daga bakinsa har abul siyama ya budi baki zaice dashi wani abu sai kuma ya kasa yace yaro mun gode bisa
ziyarar da kuka kawo mana amma nima ina rokon alfarma guda daya a wajanku amma bata

komai bace face ina son kada ku sake xuwa nan wajanmu domin a duk sa adda na kalli
fuskarka ina fama wani mugun rauni dake cikin kahon zuciyata.
.
Abu na biyu kuma ina rokonku da kada ku bayar da labarina ko na yata ga waninku saboda
wani babban sirri na rayuwarmu har sai bayan an kammala gasar jarumtakar da akeyi a garin
nan, koda gama fadin hakan sai abul siyama ya dafa kafar matarsa da hannunsa lafiyayyan ita
kuma siyama sai ta tallafa kugunsa suka taimaka masa suka juya suka nufi cikin wannan gida
nasu na katako.
.
Koda suka isa daf da bakin kofar gida zasu shiga sai ab siyama ya juyo ya yiwa hulkas wani irin
kallo idanunsa cike da kwalla take hulkas yaji tsigar jikinsa gaba daya ta tashi kuma kaunar abul
siyama ta kara shigarsa tamkar dama can sun kasance yan uwan juna nan fa yarima hulkas ya
kasa motsawa daga inda yake kuma yaji kamar yace da yarima basmar ya barshi ya kwana a
nan gidansu siyama domin ji yayi babu abinda yake so sama da kasancewa tare dasu kawai sai
hulkas ya bisu da kallo har suka kule a cikin gidan.
.
Koda ganin haka sai yarima basmar ya rugo ya kama hannun yarima hulkas ya jashi da gudu
suka bi hanyar da zata mayar dasu can gidan sarautar maimakon su wuce kai tsaye izuwa
gidan sarautar sai yarima basmar ya kaisu gidan wani dan kasuwa mai suna abul yamzin
wanda kullum sai ya kaiwa sarki hulkasu tulunan ruwan giyar da yake sha gami da ruwan inibi
sarki hulbasu ya aminta dari da attajirin abul yamzin don haka ko caje tulunan giyar sa da na
inibi ba ayi a duk sa adda ya shige dasu cikin gidan sarautar.
.
Tsakanin yarima basmar da attajirin abul yamzin akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna don
haka sun san sirrin junansu sosai da zuwan yarima basmar da hulkas gidan attajiri sai aka
sanyasu a cikin manyan tuluna guda biyu wadanda babu komai a cikinsu aka hada da wadanda
ke dauke da ruwan giya guda goma dana ruwan inibi goma aka zuba su a cikin dana ruwan inibi
aka zuba su a cikin wannan amalanke aka tura aka tafi dasu gidan sarki a can gidan sarki kuwa
hankalin gimbiya shadila dana luzuraina ya tashi ainun domin ganin cewa tunda su yarima suka
fita basu dawo ba har bayan tsawon sa a uku nan da nan aka baza dakaru zuwa kowani sako
na gidan ana nemansu koda aka duba ko ina ba a gansu ba sai hankalin su shadila ya sake
tashi suna shirin su tura aje a sanar da sarki hulbasu kenan saiga yarima hulkas da basmar sun
shigo cikin turakar.
.
Koda ganinsu sai shadila ta ruga izuwa yarima hulkas cikin matukar farin ciki ta rungumeshi
daga nan ta jashi zuwa cikin dakin barcinta da aka bata ta kulle kofa ta dubeshi cikin fishi da
matukar damuw atace ina kukaje kuka buya haka har kukayi matukar tayar mana da hankali.
.
Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya sunki
da kansa kas ya tuna cewa shifa a rayuwarsa bai taba yin karya ba dan haka take ya yanke
hukuncin ya sanar da ita gaskiyar duk abinda ya faru tun daga
lokacin da sukaje bangaren da ake aikin kashin gidan kawo sa adda aka kaisu bakin kogi sukayi
wanka sannan suka wuce gidansu siyama hatta kamannin siyama dana mahaifinta dana

babarta sai da ya zaiyana mata har dama irin tsananin jarumtakar baban Siyama a matsayinsa
na musaki mai hannu daya da kafa daya sai da ya shaida mata
koda shadila taji siffifin baban siyama da yadda yake yakinsa sai nan take zuciyarta ta kama
bugawa da karfi, ba komaine ya haddasa hakan ba face tunowa da tsohon masoyinta hailur
wato mahaifin hulkas na gaskiya domin shine kadai yake da siffa da sura irin wacce hulkas ya
shaida mata yanzu kuma shine kadai mutumin da ta san cewa yana irin salon yakin da aka
fada.
.
Cikin firgici da razana shadila ta mike tsaye zumbur
ta kama kafadun hulkas ta girgiza dakarfi tace a ina kaga wannan jarumi mahaifin siyama ya za
ayi ka kaini inda yake na ganshi, cikin alamun matukar mamaki yarima hulkas ya dubi shadila
yace yake ummina shin kinsan wannan mutum ne ko kuwa kun taba jin labarinsa ne a jana wani
baniba? .
Koda jin haka sai shadila ta tuno da gargadin da shardas yayi mata akan cewar idan ta kuskura
ta shaidawa hulkas cewar bashi bane mahaifin sa na gaskiya sai ya kasheta ya lalata dukkan
rayuwarta nan take shadila ta wayance ta bagazar da maganar ta nunawa hulkas cewar kawai
jarumtakar baban siyama ce ta burgeta nan dai ta lallaba hulkas yaje ya kwanta saboda ya
mance da komai ita kuma saita juya masa baya a lokacin da hawaye ya zubo mata tace a ranta
duk yadda za ayi sai nayi naje na ga mahaifin siyama domin na gani da idanuna ko tsohon
mijina ne ya zama nakasashshe kai ba zata yiwu bama ya za ayi ace hailur yana na a raye a
duniyar nan amma har ya manta dani yayi wani auren harma ya haifi ya alhalin yana tsananin
kaunata fiye da komai a rayuwarsa......
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMO SAURAN ABOKAN
TAFIYARSU..??
.
SHIN SHADILA ZATA SAMI DAMAR ZUWA INDA MAHAIFIN SIYAMA YAKE??
.
SHIN ZARGIN DA TAKEYI CEWAR TSOHON MIJINTA NE MAHAIFIN SIYAMA GASKIYA
NE???
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI FARA MALLAKAR HULAR
LAMSARA
.
Mu hadu A Littafin Tsatsuba Na hudu (4) Don jin Cigaban wannan labarin naku koda yaushe

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login