Showing 1 words to 3000 words out of 7235 words
Chapter 1 - TSATSUBA 4 Complete by Madakin Gini .pdf
TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part A.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da Shadila ta tambayi kanta a cikin zuciyarta cewar 'Anya kuwa Hailur yana raye a
duniya amma bai nemeta ba? Kuma ta kasa baiwa kanta amsa sai idanunta suka kekashe ga
barin barci ta kasa koda risinawa a wannan dare haka dai taci gaba da mutsu mutsu akan
gadonta taci gaba da tunanin jarumi hailur. .
A wannan rana dai shadila kwata kwata bata rintsa ba har sai da alfijir ya keto a sannan ne
barcin ya saceta ba tare da ta sani ba.
.
Al'amarin su yarima hulkas kuwa lokacin da gari ya waye ya farka yaga mahaifiyarsa na ta
barci bata ma da niyyar farkawa sai ya ki tashinta cikin doki da zumudi hulkas yaje yayi wanka
ya kimtsa gama hakan ke da wuya sai ga yarima e ka ya shigo cikin dakin shima ya caba ado
fuskarsa cike da annuri ko da yaga hulkas ma ya gama shiri tsaf sai yayi murmushi yace hakika
naga alamar cewa ka fini dokin son zuwa kallon wannan gasar jarumtakar da za ayi Yau.
.
Hulkas ya maida masa da martanin murmushin yace Ai ji nake ina ma kamar na tafiyar da
rayuwar da tsuntsu na ganni a can ba don komai ba sai don ma kawai na sake ganin
kyakkyawar fuskar nan ta jaruma siyama kuma naga yadda zata fafata yaki da manyan mazaje
barmas ya kyalkyale da dariya yace Ai dama nasan cewa tatsuniyar Gizo Bata wuce ta Koki, to
ai saikayi sauri kazo muje muyi buda baki a can turakar mahaifiyata amma me ya faru naga har
yanzu mahaifiyarka tana yin barci bata farka ba?
.
Koda jin wannan tambaya sai yarima Hulkas yayi ajiyar zuciya yace ina kyautata zaton cewa
jiya da daddare ba tayi barci da wuri ba shi yasa yanzu take ramuwarsa cikin alamun damuwa
yarima barmas yace aukuwa NA kwanaki t ke Kai by tt tttt I will t a few minutes ago rr I t I r a
little more time I t a little more time t r I will have a talk a rt I t tr I have a meeting at a t a t tr a r f I
r tr I will forward it t a little more time I will be rr I will be in touch soon to be in the office
tomorrow and tr to get the kids to the park and ride from my account ff for Friday rr for TR he is
a good guy and I think the office and I can get tytt ummina ma ba zatayi buda baki ba sai tare da
mahaifiyarka don cewa tayi nazo na tafi da ku muje muyi buda bakin gaba daya kuma tare
zamu tafi can filin yin yoga gasa har da sarki da kansa kana ganin cewa ba zaka tasheta daga
barcin ba?
.
Hulkas yace A'a bai kamata na tasheta ba tunda akwai bashin barci a tare da ita muje a yiwa
mahaifiyar taka bayani koda jin haka sai yarima barmas ya juya ya fice dagacikin dakin shi
kuma yarima hulkas ya bishi da sauri suka durfafi turakar Luzuraina.
.
Turakace babba wadda aka cikata da kayan kawa irin na sarakai. A gefe daya an ajiye wani
dogon teburin cin abinci mai
dauke da kujeru goma sha biyu, A kan wannan teburi an shirya abincin kalaci iri iri har kala
goma sha daya bisa farantai luzuraina ce kadai zaune akan wannan babban tebur tana jiran
isowar sushadila.
.
kwatsam ! Sai ta hango yarima hulkas tare da danta barmas su biyu kacal sun shigo cikin falon.
Al amarin da yai matukar bata mamaki kenan domin su uku ya kamata ta gani tun kafin su
karaso gareta luzuraina ta dubi yarima hulkas cikin alamun damuwa tace ina mahaifiyarka?
.
Me yasa bata biyoku ba kun taho tare, yarima hulkas ya risina cikin biyayya ya gaida luzuraina
yace ina zaton cewa ummina batayi barci ba jiya da wuri sakamakon labarin dana bata akan
inda muka je jiya nida barmas.
.
Koda jin wannan batu sai luzuraina tayi shiru tana tunani na tsawon yan dakiku sannan ta mike
tsaye ta dubi yarima barmas tace ku zauna kuyi kalaci kai da abokinka ni ba zan yi ba har sai
shadila ta tashi da kanta idan kun gama cin abincin kuje ku jira sarki a falonsa domin yana
fitowa sai ku tafi filin gasa tare idan ya tambayeni ku gaya masa cewa zamu riskeku a can nida
kawata shadila koda gama fadin hakan sai luzuraina ta mike tsaye daga kan kujerar da take
zaune ta tafi can cikin turakarta ta barci, barmas da hulkas kuwa sai suka zauna suka yi buda
bakinsu cikin sauri, suna kammalawa sai suka tafi zuwa can falon sarki hulbasu ba tare da bata
wani lokaci ba kuwa sai ga sarki hulbasu ya fito a cikin gagarumar shiga ta alfarma da kasaita
fuskarsa cike da annuri kallo daya mutum zaiyi masa ya gane cewa yana cikin walwala da
murnar zuwan wannan rana ta gasar jarumtaka wacce ake yi a birninsa a karshen kowacce
shekara, koda sarki hulbasu yaga yarima hulkas da yarima barmas su biyu kadai a zaune babu
iyayansu sai annurin fuskarsa ya dauke ya dubi barmas cikin alamun damuwa yace ina iyayan
naku mata?
Me yasa basu zo nan ba tare daku?
Nan take barmas ya yiwa sarki hulbasu bayani kamar yadda luzuraina tayi masa. Koda jin haka
sai sarki hulbasu ya dubesu yace shi ke nan ku tashi mu tafi filin gasar nan domin na san cewa
tuni an gama hallara ni kadai ake jira a fara wannan gasa
nan take su hulkas suka mike tsaye suka bi sarki a baya suna isowa babbar haraba ta
bangaren turakar sarki hulbasu sukayi kicibis da dakaru a tsai tsai cikin shigar yaki bisa dawakai
wadanda za su yiwa sarki rakiya izuwa filin gasar a gefe daya kuma ga dokin sarki tare
wadansu dawakan guda hudu .
Ba tare da bata wani lokaci ba aka kawo wa sarki dokinsa ba tare da bata
.
Wani lokaci ba aka kawowa sarki dokinsa ya hau barmas da hulkas ma sai aka kawo musu
biyu daga cikin wadannan dawakai guda hudu suka hau aka dunguma gaba daya aka nufi filin
gasar.kuma hardani kaina AlQuyraemey Ina binsu a baya
sai dai wannan filin anyi shine a tsakiyar gari kusa da babbar kasuwa ta garin wacce take
gagarumin ci a duk ranar da za ayi wannan gasa.
.
Filin ya kasance katon gaske kuma an kewayeshi da katanga doguwar gaske daga cikinsa an
kewayeshi da kujeru sama da guda miliyan biyu amma duk ranar da za ayi wannan gasa sai
mutane sun rasa wajan zama saboda cikowa sai dai ka rinka ganin jama a akan katanga, kai
wasu ma basa samun damar shigowa cikin filin gasar sai dai su hau saman benayen gidaje da
bishiyoyi suna hango abinda ke faruwa a cikin filin.
.
A gefe daya ne na filin aka gina inda sarki da mukarrabansa ke zama don kallon wannan gasa
duk wanda bai kasance jinin sarauta ba to bai isa yaje ya zauna ba a wannan wuri ba face ya
kasance babban attajiri ko mashahurin boka ko kuma makusancin sarki kamarni Al Quyraemey
ke tare da ku.
.
Al' amarin siyama kuwa da iyayanta lokacin da gari ya waye suka gama shirin tafiya filin gasa si
mahaifinta ya rufe fuskarsa da rawani ya zamana cewa idanunsa kadai ake gani sannan suka
hawo dawakai guda uku suka durfafi filin gasar jarumtakar. Lokacin da suka iso bakin kofar filin
gasar sai suka iske gurin ya cika makil da mutane babu masaka tsinke ganin hakan ne yasa hankalinsu ya
dugunzuma ba don komai ba sai don sun san cewa siyama ce kadai za a bari ta shiga cikin filin
gasar tunda tana da shaida ta jaruman takara su kuwa sai dai su hau kan bishiya ko wani gidan
mai bene. .
Koda siyama ta lura da irin damuwar da iyayanta ke ciki sai ta nunawa masu gadin filin
shaidarta ta jarumar gasa kuma ta gaya musu cewa ga iyayanta a tsaye tana son ta shiga tare
dasu ciki koda jin haka sai shugaban masu gadin wani narkeken katon badakare ya dubi
siyama sama da kasa cikin raini ya bushe da dariya yace yanzu ke wane ganganci ne ya sa
kika shiga wannan gasa kina matsayin mace, kuma yarinya karama haka ? Shin iyayan naki
sun gaji da ke ne shiyasa suke so su ga irin kisan gillar da za ayi miki? Toki sani cewa indai fili
ya cika babu mai sake shiga ciki face sarki da mukarrabansa, ko ki shiga ke kadai ko kuma ki
fasa yin gasar gaba daya, a wannan lokaci su kansu tsirarun 'yan kallon dake tsaye a kofar filin
wasan kallon siyama suke yi kawai wasu suna mamaki wasu suna ta sheka mata dariya suna yi
mata kallon mahaukaciya wacce ta gaji da zaman duniya, wasu ma sai suka kama tsegumi
suna cewa bata da iyaye, baiwa ce kawai iyayan gijinta suka gaji da ita.
.
Lokacin da jaruma siyama ta ji cewar ba za a bar iyayanta su shiga filin gasar ba sai ranta ya
baci ta yunkura zata bude kofar da karfin tsiya su kunna kai ciki kawai sai mahaifinta ya dubeta
yayi mata inkiyar kada ta aikata hakan ta hakura, cikin sanyin jiki ta juyo ta fuskanceshi tace
yakai abbana yanzu mene ne abinyi? Zamu koma gida ne ko kuwa zamu hau sama ne muyi kallo abul siyama ya gyada kai yace mu
dakata har sarki ya iso na tabbatar muku da cewa zamu shiga wannan fili na gasa yayin da
sarki yazo nan, koda jin wannan batu sai mamaki ya kama siyama domin bata ga dalilin da zai
sa a barsu su shiga cikin filin wannan gasa ba idan sarki yazo tunda dai su basu kasance masu
sarauta ba ko wani matsayi haka dai siyama tare da mahaifanta suka koma gefe daya suka
tsaya suka zuba idanu kawai.
.
A wannan lokaci tsirarun attajirai da masu fada aji ne kadai ke wucewa cikin filin gasar kuma
suna shiga sai a janyo kofa a sake rufewa kawai jim kadan kuwa sai ga sarki Hulbasu tare da
yarima basmar da yarima Hulkas sun nufo kofar filin gasar bisa dawakai dakaru na take musu
baya ana busa Algaita gami da buga tambura nan da nan jama a suka dare aka basu hanya
jama ar gari kuwa suka kama yiwa sarki Hulbasu kirari gami da jinjina sabo da nuna soyayyarsu
a gareshi. .
Koda ganin wannan al amari sai yarima hukas ya tuno da rayuwarsa ta can birninsa yadda jama
ar gari ke sonsa da nuna masa soyayya sannan kuma ya tuno da yadda talakawa ke tsananin
tsoron sarki Shardas saboda rashin imaninsa da cin zalinsa nan take hulkas ya tambayi kansa a
cikin ransa yace wai shin menene dalilin da yasa mahaifina ya kasance azzalumi ? Kuma sabo
da me halayansa suka banbanta da nasa alhalin ance barewa bata gudu danta yayi rarrafe
amsar da yarima hulkas ya kasa baiwa kansa kenan yana cikin wannan haline sarki hulbasu da
tawagarsa suka sake kusanto wajen tun daga nesa dasu yarima barmas suka hango jaruma
siyama tsaye a wajan tare da iyayanta sai suka cika da mamaki
sabo da kamata yayi ace ta dade da shiga ciki tun daga nesa da sarki hulbasu ya hango
mahaifin siyama tare da matarsa a tsaye da kuma 'yarsu siyama sai ya kura musu idanu kawai
har
suka iso bakin kofar shiga filin gasar da isowarsu sai mahaifin siyama ya risina ya gaida sarki
ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Saboda tsananin
mamaki da kuma ganin wannan mahaifina siyama a wajan nan, amma kafin nan zanso ku
biyoni a labari na gaba domin jin yadda za a kaya a tsakanin su shin meye dalilin da yasa shi
tsayawa yana kallonsa hm Nima ban sani ba.
Sai Kuma Allah ya kaimu Gobe kenan ku huta lafiya.......
TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part B.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja lin zamin dokinsa ya tsaya cak, take kowa dake
bayansa ma ya tsaya sarki ya sauko daga kan dokinsa fuskarsa cike da annuri ya durfafi
mahaifin siyama, yana riskarsa sai ya rungumeshi sannan ya janye jikinsa daga cikin nasa ya
dubeshi cikin mamaki yace yakai babban masoyi menene dalilin da yasa baka amsa kirana ba
bayan mun rabu a daji a wannan rana.
.
Koda jin wannan tambaya sai mahaifin siyama yayi murmushi
yace ya shugabana kayi hakuri mu sami lokaci saimu tattauna yanzu kamata yayi mu shiga
cikin filin gasa domin zuwanka kadai ake jira.
.
Koda jin haka sai sarki yayi murmushi ya kama hannunsa yaja shi izuwa cikin filin gasar shima
sai ya ruko matarsa yarima barmas da yarima hulkas kuwa sai suka jera tare da jaruma siyama
suka shiga cikin filin gasar, yayin da shima.
.
Koda su sarki Hulbasu suka shiga cikin filin gasar sai kowa ya mike tsaye don nuna girmamawa
a gareshi filin ya cika da shewa aka ci gaba da yiwa sarki jinjina da gaisuwa ehm har sai da
sarki da mukarrabansa suka je suka zauna a inda aka tanadar musu sannan filin yayi tsir aka yi
shiru kamar mutuwa ta gifta a dai dai wannan lokaci ne mai gabatar da taro ya tashi yayi jawabi
kamar yadda aka saba sannan yaci gaba da fadin sunayan jaruman da za su yi gasar a yau da
gobe har tsawon kwanaki bakwai, a wannan lokaci jaruma siyama na zaune a tsakiyarsu yarima
hulkas da yarima barmas amma sai ta lura da cewar yarima hulkas yana ta satar kallonta kuma
yana son yayi mata magana, haka ma yarima barmas koda ganin haka sai ta murtuke fuska taki
yiwa dayansu magana kuma taki basu damar yi mata magana ta hanyar kin sakar musu fuska,
ba tare da bata wani lokaci ba aka buga gangar fara gasa aka kirawo sunan wadansu jarumai
guda biyu suka shigo cikin filin kowannansu na rike da takobi da garkuwa daya dogo ne kuma
kakkaura mai kwarjini da kirar sadaukai ana kiransa da suna MULAGUS, dayan kuwa gajere ne
amma shima yana da kirar sadaukantaka ana kiransa da suna KUMAR, A cikin dokar wannan
gasa an yarda a soki mutum ko a sareshi da a ko ina koda kuwa hakan zai iya zama sanadin
ajalinsa amma ka idar nasarar gasar shine kawai akai mutum kasa ya kasa mikewa tsaye kafin
a kirga bakwai, Malagus da kumar suka gyara tsayuwarsu suka fara kallon kallo kowannansu
yana nazarin abokin gwaminsa, a dai dai wannan lokaci ne Hulkas ya dubi yarima barmas yace
yakai abokina a ganinka wane ne zai lashe
wannan gasa tsakanin Mulagus da Kumar?
.
Koda jin wannan tambaya sai Barmas ya tuntsure da dariya sannan yace haba ai da ganin kura
an san taci mutum Ga abu nan a zahiri kowa yana gani ai ko a ba a gwada ba linzami yafi
karfin bakin kaza....
.
Kafin Hulkas ya budi baki ya sake cewa wani abu sai jaruma siyama ta tari numfashinsa tace ai
sai an gwada akan san na kwarai tunda komai zai iya faruwa a ko yaushe. Koda hulkas da
barmas sukaji siyama ta tsomo baki a cikin zancensu sai farin ciki ya lullubesu hulkas ya dubeta
ya ce ashe dama mahaifinki da sarki sun san junansu amma baki gaya mana ba
.
Sa adda siyama taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace ni kaina nayi mamaki ban san
cewa sun san junansu ba sai yanzu, amma dai abin da na ke zargi shine a daji suka hadu a
wajan farauta sabo da duk su biyun babu abin da suke so a rayuwarsu sama da farauta, zan
tambayi abbana dai naji daga gareshi, gama fadin hakan keda wuya sai sukaga mulagus da
kumar sun ruga izuwa kan juna sun kacame da azababben yaki suna masu kaiwa juna SARA
DA SUKA cikin zafin nama juriya da bajinta, ana fara gumurzun ne filin yayi tsir ba a jin sautin
komai face karar takubbansu ihunsu da karajinsu da takun sawayan kafafunsu, nan take kowa
ya gane cewa Mulagus yafi karfin damtse to amma kuma shi Kumar yana da tsananin naci
juriya da kwarewar iya yaki da farko duk sa adda mulagus ya kawowa kumar sara idan kuma ya
kare da takobinsa sai kaga har darkushewa kasa yakeyi saboda karfin saran da nauyinsa, wani
lokacin kuma sai kaga mulagus ya gabzawa kumar naushi ko bugu da hannu ko da kafa har
kumar na durkushewa kasa amma kafin mulagus ya kaiwa kumar sara ko suka sa adda yake
durkushen tuni kumar ya mike tsaye zumbur ya ci gaba da kare kansa kuma yana maida
martani.
.
Abin ka da wanda yafi ka karfi cikin kankanin lokaci mulagus ya hadawa kumar jini da majina
kuma ya sami nasarar yankarsa da takobinsa har sau uku ya zamana cewa jini na zuba a jikin
kumar kuma jiri na dibarsa amma saboda masifaffen naci da azababbiyar juriya yaki yarda ya
fadi a wannan lokaci gaba daya jama ar dake wajan sun saddakar da cewar mulagus ya gama
samun lagon kumar don haka a ko yaushe zai iya bazar
da shi kasa a haka dai suka ci gaba da gumurzu har tsawon rabin sa a mulagus bai sake
samun wata nasara ba akan kumar abin ka da jiki da jini sai shima mulagus ya fara gajiya haki
ya yawaita gareshi da yawan numfashi shi kuwa kumar sai ya samu karfi a wannan lokaci
tamkar ma a sannan ne ya fara gumurzu sai gashi nasa karfin Saran da sukan yafi na mulagus
nauyi da karfi hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace sai miya ta kare sannan ake
sanin maci tuwo !