Showing 3001 words to 6000 words out of 7235 words

Chapter 2 - TSATSUBA 4 Complete by Madakin Gini .pdf

kuma ance a dade ana yi sai gaskiya domin dadewar da jaruman biyu sukayi
suna fafata wannan masifaffen fada yasa aka gane jimrau a tsakaninsu kuma aka fahimci
wanene mayakin kwarai
cikin kankanin lokaci kumar ya kuntata mulagus ya hanashi sakat ya zamana cewa kwata kwata
mulagus baya iya maida martani sai kokarin kare kai, koda kumar yaga ya sami wannan nasara
sai ya shammaci mulagus ya daka tsalle sama ya doki fuskarsa da kafa, saboda kargin dukan
sai da mulagus ya juya sau biyu a tsaye, kafin kumar ya duro kasa tuni ya sa takobinsa ya
sarewa mulagus hannunsa na dama mai rike da takobi, take hannun ya fice fit jini ya kama feshi
da tsiri daga cikin dungulmin a lokacin da mulagus ya kwarara uban ihu wanda ya firgita komai
da kowa dake wajan har dama halittun dake cikin gari da kewaye take mulagus ya kife kasa
sumamme, ai kuwa sai filin gasar ya rude da shewa gami da jinjina a lokacin ne shima kumar ya
durkushe kasa bisa guiwoyinsa sakamakon gani da yake dishi-dishi da idanunsa da kuma jinin
dake zuba a jikinsa nan take likitoci suka rugo cikin filin gasar da dakaru aka dauke jaruman
biyu aka shige dasu izuwa cikin wani babban daki dake gefe daya a cikin filin gasar wanda aka
tanadeshi a matsayin asibitin da za a rinka duba jaruman gasa, ganin yadda aka zubar da jini
ne a filin wannan gasa yasa hankalin yarima hulkas ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci
take ya aiyana a ransa yace in da zan zamo wani babban sarki a wannan nahiya tamu da sai na
hana gabatar da irin wadannan wasanni wadanda ake zubar da jini domin ban ga amfanin ace
zubar da jini shine Jarumtaka ba.
.
Bayan an gama dauke jaruman gasar biyu daga cikin filin gasar sai mai gabatar wa ya kirawo
sunan jarumi na gaba wanda yayi
wasa waishi DURKUS, koda yan kallo sukaji sunan wannan jarumi sai filin ya cika da shewa
tamkar dodon kunne zai dode, shidai wannan jarumin Dukrkus din a gaba daya nahiyar babu
wani jarumi da ya kaishi girma, da iya yaki tare da kuma daukaka kuma duk shekara shine yake

lashe wannan gasa ta jarumtaka dukkanin jaruman da suke zuwa wannan gasa daga
sauran kasashe na duniya komai girmansa da iya yakinsu suna tsoron durkus babu wanda yake
son a hadashi dashi, ba don komai ba sai don sadauki Durkus ya kasance gabjejen kato mai
kirar mutanan Farko sannan kuma yana da tsananin karfi na Allah ya isa gashi da tsawon tsiya
kamar ba mutum ba kuma kakkaura ne sosai a takaice dai kirarsa ta samudawa ce baya ga
wannan rashin imanin Darkus yayi yawa domin duk jarumin da ya hadu dashi sai ya mutu
sadauki Darkus bai taba yin wasa ya bar abokin gwaminsa da raiba don tsantsar zaluncinsa,
kuma kafin ma ya kashe abokin gasar tasa sai ya sassare masa gabban jiki yai gungudwa
gungudwa da sassan jikinsa sannan ya kashe shi kisan wulakanci bisa wannan daliline yasa
duk sa adda zaiyi yaki a filin gasa masu raunin zuciya basa iya
kallon wasansa, domin duk sai dai kaga suna ta kumallo a filin gasar suna koke koke yayinda
yake aiwatar da zaluncinsa ga abokin gasarsa.
.
Koda aka kirawo sunan wannan Jarumi wato Darkus ya shigo tsakiyar filin gasar sai aka kama
yi masa jinjina da kirari sai shima ya kwarara uban ihu mai karfi da firgitawa ya fara dukan
kirjinsa da tafkeken hannunsa ya shiga rerowa kansa kirari yana mai cewa,,,
Ina bakon lahira to ya fito ya tareni, Nine bakin takobi mai raba kowa da masoyi, nine dajin
mutuwa kowa ya shige ba rai zai fita ba a raye ba. Kuma nine ISKAR ANNOBA kowa ya
shakeni sai ya kwana kiyama. Guguwar kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya sawun giwa
nake wanda na take na dukkan dabbobi Ina mai jida jarumta da juriya da naci to ya fito ga
dillalin mutuwa hm Ni AlQuyraemey sai naji kamar na fita haka dai Darkus yaci gaba da yiwa
kansa kirari har ya gama ya tsaya cak a waje daya yana huci da muzurai tamkar wani bakin
kumurci kai yaran dake cikin wannan filin gasa boye fuskarsu
suka kama yi domin da zarar sun hada idanu da darkus sai suga kamar dodo ne tsaye a
gabansu wanda zai suresu da hannu daya ya jefa baki ya lankwame...
Nima dai bari na dakata a nan wajan saboda tsaro Amma
kafinan Nidinne dai mai deɓe maku kewa.

TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part C.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi

A dai dai wannan lokaci ne filin gasar yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kawai sai mai gabatarwa
ya kira sunan jarumin da zai kara da darkus ba wani bane jarumin face jaruma SIYAMA.
.
Koda jama a sukaji an ambaci sunan ya mace sai kowa ya gwale idanunsa domin yaga ko
wacce jaruma ce haka mai tsautsayi wadda ta gaji da zaman duniya. Domin manyan mazaje
ma da suka kasance sadaukai kuma wadanda suka sha gwagwarmaya iri iri a filin daga suna
tsoron a hadasu gumurzu da darkus don su san cewa ajalinsu ne ya zo. .

Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga wata yar matashiyar budurwar yarinya ta taso daga
wajan da su sarki ke zaune tana sanye da kayan yaki ta shigo cikin tsakiyar filin gasar ko
garkuwa babu a hannunta kuma takobinta ma na cikin kube sakale a kuibin cinyarta ta hagum
nan fa mamaki ya turnuke jama a wasu suka kamu da tsananin tausayin siyama har suna zubar
da hawaye saboda suna ganin cewa mugun kisan gilla darkus zaiyi mata.
.
Wasu mutanan kuwa sai suka kama tsinewa
mutanan da suka yi sanadiyyar shigar wannan kyakkyawar yarinya cikin wannan gaasa yarima
hulkas da barmas kuwa hankalinsu ne yayi matukar dugunzuma ainun har jikinsu ya kama
tsuma bisa ganin cewa Siyama zatayi Yakine da DARKUS hm Nimafa nayi mamaki kamar na
tsaya da typing amma muje kawai. .
Duk da cewa sun ga irin jarumtakarta sai da zuciyoyinsu suka karaya yarima barmas bai san sa
adda ya taso daga inda yake zaune ba
yaje inda sarki da mahaifin siyama ke zaune ya dubi mahaifin siyaman a dimauce yace haba ya
abul siyama yanzu kana gani za a kashe yarka amma kayi shiru hm AlQuyraemey nake tabbas
wannan hadi da akayi babu adalci acikinsa kawai so ake a kashe yarka koda jin wannan batu
sai mahaifin siyama yayi murmushi ya dubi yarima barmas cikin girmamawa yace kwantar da
hankalinka yakai yarima babu abinda zai sami yata, ka koma wajanka ka zauna ka morewa
idanunka da kallon abin mamaki cikin alamun tsananin damuwa yarima barmas ya juya ya nufi
can wajen zamansa yana waigen mahaifin siyama amma duk sa adda ya waigo din sai yaga
shima ya kurawa hulkas idanu yana yi masa wani irin kallo mai dauke da ayar tambaya.
.
A wannan lokaci ne sarki Hulbasu ya dubi mahaifin siyama cikin alamun mamaki yake yakai
abokina wai shin mene ne dalilin da yasa ko yaushe kake rufe fuskarka ne da mayafi, ni kaina
ban taba ganin irin kamanninka ba kuma ko yaushe a haka kake koda kuwa a cikin daji kake
shin ina dalilin yin hakan? .
Sa adda mahaifin siyama yaji wannan tambaya sai yayi murmushi ya ce ya shugabana kayi
hakuri ba zan iya baka amsar wannan tambaya ba a yanzu saboda wani muhimmin dalili da ya
shafi rayuwata amma nayi maka alkawarin idan lokacin da ya kamata ka sani yayi zaka sani,
ina boye wannan sirri ne sabo da samar da tsaro ga rayuwata data iyalina ya shugabana idan
ba zaka damu ba nima ina da wata tambaya guda daya a gareka wai shin wane ne wancan
yaro wanda ke tare da danka yarima barmas daga ina ya fito kuma mene ne dangantakarsu da
sarauta?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarki hulbasu ya kyalkyale da dariya sannan yace akan wanne
dalili zan baka amsar wannan tambaya da kayi mini alhalin nima ina da nawa tambayoyin
kwatankwacin irinsu a kanka kuma kaki ka bani amsa tun daga ranar da na fara ganinka ?
.
Nima ba zan iya baka amsar wadannan tambayoyi na ka ba saboda tabbatar da tsaro a kan
wannan yaro domin kuwa idan wani abu ya sami lafiyar wannan yaro bama niba gaba daya
jama ar dake cikin wannan nahiya tamu sai sun shiga uku, sa adda mahaifin siyama yaji

wannan batu daga bakin sarki sai kansa ya daure ya cika da mamaki fiye da ko yaushe har ya
budi baki da nufin ya sake yiwa sarki wata tambaya sai kawai yaga dakus ya ruga da gudu
izuwa kan siyama yana mai daga takobinsa sama kuma yana mai kwarara uban ihu mai
tsananin firgitawa irin wanda ka iya tarwatsa dubunnan dakaru a filin daga kuma ya furta tane a
cikin mugun nufi na gamawa da ita farat daya ita kuwa siyama sai ta tsaya cak a inda take to
gezau batayi ba kuma ko kifta idanunta ba tayi ba koda dakus ya iso daf da ita sai ya kawo
mata wani irin wawan sara a wuya da nufin ya cisge mata kai cikin bakin zafin nama jaruma
siyama ta tale kafafunta tayi kasa, takobin darkus din ta bysari iska ya sake kai mata wani
mugun sara a fusace siyama tana durkushe a kasa tayi wata irin alkafira cikin gwaninta ta
kaucewa harin nasa, koda takobin darkus tasari kasa sai ta nutse izuwa cikin karkashin kasar
gaba dayanta saboda tsananin karfin saran nasa da nauyinsa kafin darkus ya zaro takobin tuni
siyama ta doki kasa da tafin hannunta na hagu tayi sama sai
kawai ta doki gadon bayansa da kafafunta biyu darkus yaji kamar wani dankareren kato ne yayi
masa dundu a gadon baya kuma duk da tsananin girmansa da nauyinsa sai da ya tafi taga taga
da gaba kamar zai kife kasa, da kyar ya iya cijewa ya tsaya kyam a tsaye.
.
Al amarin da yai matukar razanashi da bashi haushi kenan, domin wannan ne karo na farko da
aka taba samun jarumin da ya sami nasarar
.
Dukan jikinsa har ma ya kusan kaishi kasa, koda yan kallo sukaga wannan gagarumar
jarumtaka da siyama tayi sai suka cika da tsananin mamaki filin ya kaure da ihu gami da shewa
aka shiga yiwa siyama kirari gami da jinjina, yarima hulkas kuwa saboda murna ma bai san sa
adda ya daka tsalle ba daga kan kujerar da yake zaune yana shewa shewar tasa ce tasa har
siyama ta juyo ta dubeshi kawai sai tayi masa murmushi, take hulkas yaji wani irin farin ciki
mara misaltuwa da dadi ya lullubeshi saboda wannan murmushi da tayi masa shi kuwa sadauki
Darkus fusata yayi ainun ya juyo da sauri ya sake rugowa izuwa kan siyama aikuwa itama sai
tayi wuf ta zare takobinta ta tareshi suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro
da razanarwa, gaba daya jama ar dake filin wannan gasar sai da hankalinsu ya
dugunzuma gaba daya saboda tun da aka fara wannan gasa ta jarumtaka tsawon shekaru ba a
taba ganin gumurzu ba irin wannan mai tsananin hadari wow.
.
A can gidan sarauta kuwa gimbiya shadila bata farka ba daga barci har sai bayan lokaci mai
dan tsawo koda ta bude idanunta taga ashe ma tuni gari ya dade da wayewa har rana ta kwalle
kuma taga babu jarumi hulkas kwance a kusa da ita akan gadon da take kwance sai ta mike
zaune zumbur a lokacin da zuciyarta ta buga da karfin gaske, kawai sai ta sauko daga kan
gadon da sauri ta leka bandaki don tunanin ko hulkas na ciki yana wanka amma sai ta iske
bandakin wayam babu kowa a cikinsa a gigice shadila ta gaggauta tayi wankanta sannan ta
kimtsa gama shirinta keda wuya sai taji an kwankwasa mata kofa saiga wata kuyanga ta shigo,
kuyangar ta zube kasa bisa guiwoyinta ta ce ya shugabata sarauniya ta turoni nayi miki jagora
zuwa can turakarta domin tana jiranki kuyi kalaci, cikin mamaki shadila ta dubi yadda rana ta
kwalle ta cikin tagar dakin nata sannan ta dubi kuyangar tace yanzu kina nufin kice har yanzu
sarauniya bata yi kalaci ba, kuyangar ta sake risina tace ai saboda kina barcine shi yasa taki
tayi kalacin da kanta, amma tafi sa a biyu da gama kimtsawa har ma sarki dasu yarima sun

dade da tafiya kallon GASAR JARUMTAKA.
.
Koda jin wannan batu sai shardila taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta ji babu abinda take so
sama da ta ganta a filin wannan gasa, don haka cikin sauri tace da kuyangar yi maza ki kaini
wajan sarauniya ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai kuyangar ta juya da sauri ta fice daga
cikin dakin shardila na biye da ita, luzaira na zaune akan teburan cin abincin dake falonta ita
kadai tana jiran sai ga kuyanga tare da shardila sun shigo, cikin murna luzaira ta mike tsaye da
sauri ta taryo shardila ta kamo hannunta ta kawota izuwa kan kujera suka zauna tare, ba tare
da bata wani lokaci ba suka kama cin abincin har suka kusan gama cin abincin dayansu baice
kala ba a sannan ne shardila tayi gyarar murya ta dago kai ta dubi luzaira tace yake kawata ki
gafarceni na bata miki lokaci da kika kawo har yanzu baki yi kalaci ba domin barcina ne yayi
nauyi, kafin shardila ta gama wannan magana sai luzuraina ta tari numfashinta tana mai
kallonta cikin murmushi tace haba yake kawata kada ki sawa kanki damuwa akan hakan domin
danki ya gaya mini cewar yana
zaton jiya bakiyi barci da wuri ba shin kina da wata lalura ne ta rashin lafiya ko kuwa akwai wata
matsala dake damunki.
.
Koda jin wannan tambaya sai shardila ta yi murmushi tace kawata babu abinda yake damuna
kuma bani da wata matsala haka kawai dai naji idanuna sun bushe jiya da daddare wata kila
bakunta ce ta janyo hakan
koda jin haka sai luzuraina ta kyalkyale da dariya ta yiwa shardila wani irin kallo na rashin yarda
domin ba ta yarda da abinda ta fada ba sai dai ta dubeta tace ko dai kewar sarki shardas ce ta
hanaki barci kinga tashi mu hanzarta mu tafi filin gasar nan domin na san cewa yanzu tuni an
dade da fara wasa babu mamaki ma an shiga kewaye na uku. . .
Kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni shardila ta wanke hannayanta ta mike tsaye saboda
dokin zuwa wannan filin gasa, nan dai suka gama kimtsawa suka nufi wani babban fili inda aka
tanadar musu keken dokin da zasu hau tare da dakarun da zasuyi musu rakiya tun daga nesa
shardila ta hango dakarun sai tayi sauri ta rufe fuskarta da wani bakin kyalle ya zamana cewa idanunta kadai ake gani ba komaine yasa shardila ta rufe fuskarta
ba face a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da mutane suyi ta kallonta, abinda bata sani ba
shine tsananin kyawun fuskarta da kyan surar jikinta ne ya janyo mata kallon da ake yi mata
nan dai su luzuraina suka shiga cikin keken dokin aka ja aka fice daga cikin gidan sarautar aka durfafi filin GASAR JARUMTAKA.
.
NIMA KUMA sai na dakata anan na nufi Filin daga Wato neman na Abinci Kuma sai Allah ya
kaimu Gobe zamu ci gaba
Nidinne dai

TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part D.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.
A can filin gasat kuwa lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin sadauki darkus
da jaruma siyama sai da suka shafe rabin sa a cif suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin
tsananin zafin nama juriya da bajinta amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya
ba .
Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan da yawa daga cikin yan kallo dai sun
firgice ne da al amarin siyama kai harni AlQuyraemey da nake wannan typing din na rikice da
lamarinta, Kai wasu ma sai suka rinka cewa siyama ba mutum bace Aljana ce don babu yadda
za ayi ace tana ya mace yar shekara tara kacal a duniya ta sami irin wannan gagarumin karfin
damtse da iya yaki haka, lallai akwai aikin sihiri acikin lamarin.
.
Abinda basu sani ba shine siyama tasha Sadaukantaka ne a nono kuma tun tana da shekaru
hudu kacal a duniya mahaifinta ya far bata horon yaki. Ana cikin wannan haline aka jiyo sautin
tashin tambura da bushin Algaita alamar cewar ga sarauniya Luzuraina nan ta iso, take farinciki
ya kama sarki hulbasu ya dubi mahaifin jaruma siyama yace abokina ga matata nan ta iso tare da kawarta babbar bakuwarmu
.
Koda jin haka sai abul siyama ya budi baki da nufin ya tambayeshi ko wacece bakuwar, amma
sai ya kasa sakamakon ganin wani irin mugun naushi da darkus ya yiwa siyama a fuska cikin
tsananin shammace, saboda karfin naushin sai da jini yai tsartuwa daga cikin hancinta kuma ya
yi feshi daga cikin bakinta ta tafi luuu ! Kamar zata kife kasa da baya amma sabo da tsananin
juriya sai ta mike tsaye kyam ta doki kasa da kafarta guda tayi sama cikin shammace itama ta
doki fuskar darkus da tafin kafarta ta dama tana mai jera masa duka uku a saman, sannan ta
duro kasa ai kuwa sai gashi shima hancinsa da bakinsa na yoyon jini har shima yaji wani jiri ya
kwashe shi ya tafi luuu ! Zai kife da rub da ciki amma sai yai sauri ya tokare jikinsa da hannu
guda ya taso sama kamar sifirin suka ci gaba da sabon masifaffen yaki kamar ma lokacinne
suka fara yakin, A dai dai wannan lokaci ne gimbiya luzuraina da shardila suka shigo cikin filin
gasar suka durfafo inda su sarki ke zaune dakaru na take musu baya, tun daga nesa Abul
siyama ya hango

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login