Showing 6001 words to 7235 words out of 7235 words

Chapter 3 - TSATSUBA 4 Complete by Madakin Gini .pdf

shardila sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi irin bugawar da bai tabaji ba a
rayuwarsa
.
Koda ya sake yin arba da dakarun dake yi mata rakiya wato su sadauki Murzanu sai jikinsa ya
kama tsuma nan da nan gumi ya fara karyo masa domin a sannan ne ya tabbatar da abin da
yake zargi duk da cewar kuwa shardila ta rufe fuskarta da bakin kyalle.
.
Al amarin shardila kuwa tunda ta shigo filin sai ta kama raba idanunta a cikin yan kallo ba don
komai ba sai domin taga Abul Husna wanda danta yarima Hulkas ya bata labari domin ta gusar
da wasu wasin dake cikin zuciyarta bisa wannan daliline ta yi ta ware idanuwa ko zata ga
mutum mai hannu daya da nakasashshiyar kafa kuma ta rinka kallon fuskokin mutane don ta

tabbatar da cewa tana yin arba da fuskar tsohon mijinta take zata shaidashi, amma har suka iso
inda su sarki hulbasu ke zaune amma bata ganshi ba, abin da ya sa ko kadan hankalinta bai
kawo kan Abul Siyama ba shine ta san cewa babu mai ikon zuwa kusa da sarki Hulbasu ya
zauna face ya kasance jinin sarauta ko kuma wani mai fada aji a birnin, bugu da kari kuma
fuskar Abul siyama a rufe take cikin rawani kuma ya lullube gaba dayan jikinsa da wanibabban
mayafi na alfarma, luzuraina da shardila suka zo suka zauna kusa da sarki hulbasu daga
hagunsa shi kuwa abul siyama yana zaune a damansa tun da suka zauna abul siyama bai
yarda ya kalli inda suke ba shi kuwa hulbasu da yake gaba daya hankalinsa ma yana kan
gumurzun da ake yi a tsakiyar filin gasar tsakanin jaruma siyama da sadauki durkus ko tunanin
gabatar da Abul siyama bai yi ba awajan su Luzuraina yayin da shardila ta kyalla ido ta hango
siyama a tsakiyar filin gasa wacce ke ta faman gumurzun yaki tayi arba da fuskarta sai taji
zuciyarta ta buga da karfi ba komai ne ya haddasa hakan ba face jaruma siyama tana matukar
kama da mahaifinta, nan take shardila ta gane cewa lallai jaruma siyama yar tsohon mijinta ce
wanda take tunanin cewa ya mutu fiye da shekaru bakwai baya lallai hakan ya tabbatar mata da
cewar kenan Hailur na nan a raye kuma a cikin wannan gari.
.
Koda gama aiyana hakan sai shardila taci gaba da kalle kallen ko ina a cikin filin gasar ko
zataga Hailur shi kuwa Hailur da ya lura da ita da kuma halin da take ciki sai ya noke yana mai
sunkuyar da kansa kasa yaki yarda su hada idanu, saboda ya tabbatar da cewa suna hada
idanu zata shaidashi duk kuwa da cewa ya rufe fuskarsa da rawani idan kuwa ta shaidashi a
gaban kowa zata fashe da kuka ta rungumeshi, tana yin hakan kuwa asirinsa zai tonu su
sadauki Murzanu su shaidashi idan kuwa suka shaidashi komai ya tabarbare ke nan domin sai
labari ya riski sarki shardas cewa har yanzu yana nan a raye, da zarar hakan ta faru kuwa hatta
sarki hulbasu ya shiga cikin tashin hankali kenan da masifa don sarki shardas Cewa zaiyi ya
boye babban makiyinsa a birninsa don haka sai ya yakeshi ya kau dashi kuma ya mallake kasar
ma gaba daya, nan take idanun Hailur suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye domin
shi a zatonsa ma tuni shardila ta dade da mutuwa, amma yanzu da ya ganta a cikin shiga ta
alfarma irin ta sarakai, kuma yaga su sadauki Murzanu na take mata baya sai ya kamu da
tsananin bakinciki mara misaltuwa domin ya gane cewa lallai a yanzu ta zama matar sarki
shardas, aikuwa bayan su shardila sun zauna sai hailur yaga yarima
hulkas ya mike zumbur ya tafi izuwa wajan shardila ya rungumeta nan take zuciyar hailur ta
sake bugawa da karfin gaske a karo na biyu ya tambayi kansa acikin zuciyarsa yace ' shin
wannan yaro dana ne ko kuwa dan sarki shardas ne tabbas wannan yaro da uwarsa yake kama
don haka bani da tabbacin cewa dana ne, tabbas shardila na dauke da cikin dana, wai shin
kana zaton cewa sarki shardas zai amince ne shardila ta haife danka a cikin gidan sarautarsa,
kai hailur ! Idan ma mafarki kake yi toka farka ''
.
Wannan shine gargadin da zuciyar hailur takeyi masa nan fa yaji cewar babu abinda yake
bukata sama da ya sami damar tattaunawa da shardila domin ta bashi amsar wadannan
tambayoyi dake yi masa yawo a cikin zuciya lokacin da shadila tayi arba da jaruma siyama taga
fuskarta a zahiri sai hankalinta ya dugunzuma ainun kuma taji zuciyarta taci gaba da dukan uku
uku ba komaine ya janyo hakan ba face ganin cewa tabbas siyama tana tsananin kama da
tsohon mijinta hailur babban abin ma da ya kara dugunzuma hankalinta shine ganin irin yanayin

yadda take yin yakinta iri daya ne sak dana tsohon mijinta Hailur.
.
Kafin shardila ta ankara tuni ta fara kuka tana mai zubar da hawaye gami da ci gaba da kalle
kalle da waige waige a cikin filin gasar ko zata hango masoyinta hailur amma shiru kamar maye
yaci shirwa ashe duk wannan hali da ta shiga Hailur ya lura da ita duk da cewar fuskarsa a rufe
take cikin rawani kuma yana zaune a daman sarki ita kuma tana tare da luzuraina abarin hagun
sarkin.
.
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
sukaci gaba da fafata kazamin yaki a karo na biyu sai ya zamana cewa karfi yazo daya an rasa
wanda zai iya cutar da wani a cikinsu, duk da tsananin karfin damtse irin na darkus sai gashi
naci da juriyar siyama da tsabar horon yaki da ta samu a wajen mahaifinta yasa ta iya kwatar
kanta awajensa tun suna kaiwa junansu sara da suka da takubban hannayansu har sai da suka
gaji ainun makaman nasu suka subuce daga hannayansu suka ci gaba da gabzar juna da
hannu, Duk irin naushin da darkus yayiwa siyama sai aga ta rama wato dai itama tayi masa
irinsa. Kai ! Tun suna tsaye akan duga dugansu tsabar masifar yaki sai da takai ga sun
durkushe kasa a tare kuma a lokaci guda suka ci gaba da gabzar junansu a hakan kowannansu
ya kama layi kamar wanda ya sha giya suka bugu har izuwa lokaci mai tsawo suna cikin
wannan hali daga can kuma sai duk su biyun suka bingire da baya luuu ! Suka baje a kasa tare
suna numfarfashi kamar ransu zai fita...........
.
A nan ne Littafin Tsatsuba Na Hudu Yazo Karshe Marubucin Littafin yace....
.
YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZATA KASANCE TSAKANIN SADAUKI DARKUS DA
JARUMA SIYAMA ???
.
WAYE ZAI SAMU NASARAR ZAMA ZAKARAN GASAR JARUMTAKA A TSAKANINSU ?
.
MAI ZAI FARU IDAN GIMBIYA SHARDILA TA GANE MASOYINTA KUMA TSOHON MIJINTA
HAILUR DA SUKA RABU TSAWON LOKACI ?
.
SHIN ASIRIN ABUL SIYAMA YANA TONUWA HAR LABARI YA KAI KUNNEN BABBAN
MAKIYINSA SARKI SHARDAS WANDA ABUL SIYAMA KE ZARGIN YA AURI MASOYIYARSA
KUMA MATARSA?
.
MAI ZAI FARU IDAN YA SAMU LABARI ?
.
Marubucin littafin yace mu hadu a littafi na 5 donjin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen
labari Daga mai debe muku kewa a ko yaushe Ni ne dai Abubakar Saleh AlQuyraemey nake
cewa Mu zama Lafiya.
.
Amma Ku meye kuka hango a haduwar Hailur da shardila wata irin Dambarwa za a yi ne kam
sai naji daga gare ku...

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login