Showing 1 words to 3000 words out of 8267 words
Chapter 1 - TSATSUBA BOOK 5 Complete by Madakin Gini .pdf
TSATSUBA
Littafi Na Uku (5)
Part A.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus suka bingire kasa suna fitar da numfarfashi kamar
ransu zai fita a dai dai wannan lokaci ne aka buga gangar tsayar da yaki sannan alkalin gasa ya
rugo izuwa cikin tsakiyar fili ya fuskanci jama a yace yaku jama a kuyi sani cewa wannan
gumurzu tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama babu zakara a tsakaninsu wato sunyi
MUTUWAR KASKO don haka zasu sake haduwa a zagayen karshe na wannan wasa wanda za
ayi rana i ta yau don haka yanzu zamu kirawo jarumai na gaba domin aci gaba da wannan
gasa, gama fadin hakan keda wuya sai aka dauke sadauki Darkus da jaruma siyama daga cikin
filin aka kaisu can gefe daya maimakon a shigar dasu cikin wannan asibiti wanda aka tanada
domin yiwa jaruman gasar magani, dalilin da yasa kuwa ba a shigar da su cikin wannan asibiti
ba shine babu mai wani babban rauni a cikinsu akan hancinsu da bakunansu ne kadai jini ke
diga lokacin da jaruma siyama ta dawo cikin haiyacinta sai ta dubi inda su sarki hulbasu ke
zaune tana mai mamakin dalilin da ya hana mahaifinta zuwa inda take a lokacin da hankalinta
ya gushe bayan an tsayar da wasansu, bisa mamaki sai siyama taga babu mahaifinta a inda
yake zaune amma kuma sai taga shardila ta kura mata idanu ko kiftawa batayi duk da cewa
kuwa ta rufe fuskarta da bakin kyalle idanunta kadai ake gani nan fa hankalin siyama ya
dugunzuma ainun in ba don ma ta hango mahaifiyarta ba ta taso daga inda take zaune ta taho
wajenta ba da mikewa zata yi ta bazama mahaifin nata Hailur, da isowar zalima wato mahaifiyar
siyama sai ta rungumete cikin murna tana mai yi mata jinjina bisa bajintar da ta nuna a wannan
wasa da tayi.
.
A dai dai wannan lokaci ne wani likita yazo garesu da nufin zai duba tafiyar siyama amma sai
zalina ta tsaidashi tace babu wani likita da zai duba lafiyar yata face ni don haka mun gode
bama bukatar taimakonka, koda gama fadin hakan sai zalina ta bude wani kullin tsumma dake
hannunta ta dauko wani ruwan magani a cikin wata yar doguwar kwalba ta mikawa siyama
siyama ta karba ta bude murfin kwalbar ta sa abakinta tasha mukurwa biyu kacal sannan ta rufe
kwalbar ta mai dawa zalina.
.
Faruwar hakan keda wuya sai jinin dake yoyo a hannun siyama da bakinta ya tsaya cak kamar
bai taba diga ba kuma nan take taji duk gajiyar dake jikinta ta dauke fuskarta ce kawai da
idanunta a dan kumbure sakamakon naushin da darkus ya yi mata a can gefe daya kuma likita
ne ke duba sadauki darkus ana sa masa magani a kan hancinsa don tsaida jinin dake yoyo
koda darkus ya dawo cikin hayyacinsa ya waiga bayansa yayi arba da jaruma siyama sai ya
daka mata harara yaji ya tsaneta fiye da komai a rayuwarsa, nan take zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone bisa ganin cewa yarinya karama ta gagareshi a filin gasa, nan fa ya
fara tunanin cewa ta kowanne hali sai ya kaita kas a zagaye na biyu da zasu hadu wato a
wasan karshe da za ayi na gasar idan rana ta zagayo kuma babu abinda zai yi ya dawo da
kimarsa da mutuncinsa a birnin face ya kashe wannan karamar yarinya siyama ya zamana
cewa ta mutu murus har lahira a cikin filin gasa.
.
Koda mai gabatarwa yazo tsakiyar fili yaci gaba da jawabi sannan ya kirawo sunayan jarumai
na gaba wadanda zasuyi fafata a wannan gasa.
.
A dai dai wannan lokaci ne sarki hulbasu ya dubi Hailur yace yakai abokina hakika ka baiwa yar
ka horon yaki na ban al ajabi domin ta bani mamaki matuka kuma akwai alamun cewa zata iya
lashe wannan gasa amma ka sani cewa lashe wannan gasa ba abune mai sauki ba saboda
babu irin abinda jaruman gasar nan basayi don ganin sukai gaci, suna yin tsafi tuggu da makirci
iri iri don ganin sun sami nasara ta kowacce hanya don haka dole ne kasa ido akan yarka domin
daga yanzu rayuwarta na cikin hadari kada ka tafi izuwa gida kai tsaye daganan ina son ku
biyoni izuwa cikin gidan sarautata domin ku dauke hankalin makiya dolene ku sauya gidan
zama kuma nima zan baku shawarwari da taimako.
.
Wai shin ma kasan kuwa irin ladan da yarka zata samu idan ta lashe wannan gasa ta jarumtaka
? Koda jin wannan tambaya sai hailur ya sunkui da kansa kas saboda yaga shardila ta kalleshi
don kada taga kwayar idanunsa ta shaidashi sai yaki yarda ya dago kansa sa ar ma da yayi ko
kadan bata jin abin da suke tattaunawa shi da sarki kasancewar suna magana ne cikin kus kus
yadda babu mai iya jin abinda suke tattaunawa
.
Hailur ya risina cikin girmamawa yace yakai abokina wane irin lada za a baiwa yata idan ta
lashe wannan gasa sarki hulbasu yayi murmushi sannan yace da farko dai za a bata babbar
gona guda daya daga cikin manyan gonakan garin nan gami da dinare dubu dari bakwai
sannan kuma zan bata mukamin shugabar dakarun dake tsaron lafiyata muddin zata iya
rantsuwa bisa rike amanata da kuma siyar da rayuwarta don kare tawa idan har ta sami wannan
mukami zata rinka samun albashi mafi tsoka a kan duk albashin da ake biyan dakaruna daga
wannan matsayi kuma zata iya zama sarkin yakin birnin nan gaba daya bayan ta fuskanci
wadansu jarrabobi da matakai.
.
Duk mutumin da ya sami wannan dama wacce yarka ta samu dole ne ya fuskanci makiya da
yawa daga cikin manyan fadawana domin sun san cewa zai zone yafi su matsayi da arziki,
lokacin da sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin hailur ya dugunzuma ainun take yaji
yayi nadamar sanya siyama a cikin wannan gasa saboda dalilai guda biyu dalili na farko shine
yanzu ya sanya rayuwar siyama a cikin hadari domin zata tara abokan gaba wadanda za su
rinka farautar rayuwarta kamar yadda mai jin kishirwa ke neman ruwan sha, abu na biyu kuma
idan ta tsallake kowanne hadari da dukkan matakai da zata nisanta dashi inma bai yi sa a ba ya
rasata gaba daya kamar yadda ya rasa matarsa shardila wacce ya tabbatar da cewar tana
dauke da juna biyu a lokacin da suka rabu.
.
A yanzu da hailur yaga yarima hulkas sai ya fara tunanin ko dansa ne wannan yaro ko kuma
dan sarki shardas ne
tabbas babu mai bashi amsar wannan tambaya face shardila da kanta kuma yana shakkar ya
sadu da ita domin idan wani daga cikin dakarunta ya gansu komai ya dagule kenan domin sai
sarki shardas ya samu labarin cewa yana raye to ba mashi ba matarsa zalima da yarsa siyama
ma rayuwarsu ta shiga hadarin da shiba zai iya kare suba hailur ya tambayi kansa a cikin
zuciyarsa yace ta yaya zan iya saduwa da shardila a sirrance ba tare da kowa ya ganni ba ko
yaji babu wanda zai iya taimaka mini na iya ganawa da shadila asirrance face sarki hulbasu,
hailur baya son sarki hulbasu ya san cewa shine ainihin abokin gabar sarki shardas wanda tuni
aka dauka cewa ya mutu tun shekaru bakwai baya, hailu na cikin wannan tunani ne yaji an
ruguntsume da wani masifaffen azababben yaki a tsakiyar filin gasa koda ya daga kansa yayi
arba da jaruman biyu dake fafatawa a filin gasar sai ya cika da mamaki, ba komai ne ya sashi
wannan mamaki ba face ganin cewar dayansu amintaccen yaronsa ne sadauki Ruhaisu jarumin
da ya aminta dashi dari bisa dari a cikin dukkanin yaransa lokacin a yake kan matsayin
shugaban kabilarsu.
.
Koda hailur yayi arba da ruhaisu sai farin ciki ya lullubeshi domin indai ruhaisu na tare dashi zai
iya nemo masa ire iren sauran jama arsu da sukayi saura a raye domin su sake tayar da
kabilarsu kuma su taimaka
masa wajan bashi kariya dashi da iyalansa jarumin da yake karawa da ruhaisu kuwa wani
narkeken katone wanda ya ninkashi girma da tsayi sau uku kuma a zahiri ma yafi shi surar
sdaukantakada jarumtaka ana kiransa da suna Jamar, amma suna fara artabu sai jamar ya
raina kansa domin ruhaisu yafishi zafin nama da iya yaki nan da nan ya rikitashi kuma ya
kuntatashi sai gashi Jamar yana ta ja da baya kuma yana ta kokarin kare kansa baya ma iya kai
hari koda ruhaisu ya tabbatar da cewar yafi jamar iya yaki da fadan hannu sai kafa sai ya
shammaceshi ya daka tsalle sama ya doki habarsa da guiwarsa ta dama saboda karfin dukan
sai da jamar yayi sama a lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa yana saman kafin ya
fado kasa sai ruhaisu ya kara dukan kirjinsa da karfin gaske kawai saiji akayi jamar ya fado
kasa tim kamar giwa ta fadi kuma ya baje kas a sume ko kyakkyawan motsi ba yayi.
.
Koda ganin haka sai filin gasar ya rude da shewa aka kama yiwa ruhaisu tafi da jinjina ba don
komai ba sai don saboda shine jarumi na farko da ya fara lashe wasansa na farko a cikin
kankanin lokaci da fara gasa tunda ko rabin sa a ba ayi ana gumurzun ba ya sami wannan
nasara ana cikin wannan yanayi ne hailur ya dubi sarki hulbasu yace hakika wannan jarumi ya
burgeni matuka zan so na gana dashi, koda jin haka sai
sarki hulbasu ya yi murmushi yace ai wannan mai saukine zan shirya duk yadda zaka gana
dashi nan ba da dadewa ba yanzu ina so kaje ka ruko yarka da matarka ka shigo cikin tawagata
domin mu shiga cikin gidan sarautata tare
.
Koda jin haka sai hailur ya dubi sarki hulbasu cikin alamun damuwa yace bana son na shiga
cikin filin nan ranka ya dade ka taimaka min ka aika wani daga cikin hadimanka ya taho da
siyama da zalina koda jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi murmushi yace shikenan an
gama, nan take sarki ya kira wani hadiminsa ya turashi yaje ya taho da jaruma siyama da
mahaifiyarta suka shigo cikin tawagar sarki hulbasu.
.
Koda hailu ya yunkura zai mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune sai santsi ya kwashe shi
ya zame zai fadi kasa a lokacinne rawanin da hailur ya rufe fuskarsa dashi ya zame kafin ya
mayar da rawanin kan fuskarsa shadila ta yi arba dashi domin ya hada idanu da ita cikin
kaduwa yai sauri ya mayar da rawanin ita kuwa shadila sai ta kame a inda take tsaye saboda
tsananin mamaki da kaduwa da murna bata san sa adda hawaye ya fara zubo mata ba...
.
Duk da cewa itama ta rufe idanunta da bakin kyalle sai da sarki hulbasu ya lura da halin da take
ciki amma sai ya basar yayi kamar bai fahimci komai ba ita kuwa luzuraina sam bata lura da duk
abinda ke faruwa ba yarima hulkas ne ya lura da irin satar kallon da mahaifiyarsa ke yiwa abul
siyama kuma yaga sa adda hawaye ya zubo mata, nan take hankalinsa ya dugunzuma ainun ya
rasa dalilin faruwar wannan lamari don haka sai zuciyarsa ta kama zargi da wasu wasi amma ya
kasa gane abin ma da yake zargi da wasi wasin a kansa haka dai sarki da mukarrabansa suka
mimmike tsaye a cikin filin gasar aka kawo musu dawakansu suka hau sannan suka fice daga
cikin filin gasar dakaru na zagaye dasu gaba da baya da kuma tsakiyarsu.
.
Ashe tun sa adda aka gama fafatawa tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama tuni sadauki
darkus ya kebe da wadansu zakwakuran yaransa ya basu umarni akan cewa da zarar sun ga
jaruma siyama da iyayanta sun fito daga cikin filin gasar a kashe su a sirrance ba tare da kowa
ya gane abinda ya kashe sun ba baya ga wannan mugun abu da sadauki darkus ya shirya ashe
shima sarkin yakin sarki hulbasu ma ya tura wadansu yaran nasa ma a sirrance sun je can
hanyar bayan gari sun labe rike da da kwari da baka sun dana kawai jira suke suga giftawar
jaruma siyama da iyayenta akan hanyarsu ta komawa gida su sakar musu harbi su kashesu
lokacin da shi sarkin yaki wanda ake kira suna RINZALU da kuma sadauki darkus suka ga
cewa siyama tare da iyayanta sun shiga cika da mamaki kuma hankalinsu ya tashi saboda sun
san cewa lallai dukkan shirinsu ya watse, nan take sarkin yaki rinzalu ya nufi tawagar ta sarki da
nufin ya shiga cikinsu amma sai yaga dakarun sarki na musamman masu tsaron lafiyarsa sun
shiga gabansa sun hanashi shiga cikin tawagar. Al amarin da yai matukai baiwa sarkin yaki
rinzalu mamaki kenan kuma ransa ya baci saboda ba a taba hanashi shiga cikin tawagar sarki
ba sai yau nan take ya fara tunani a cikin zuciyarsa yace wai shin wane irin matsayi ne da
jaruma siyama da iyayanta a wajan sarki hulbasu haka har da yake kare rayuwarsu wai shin ma
yaushe ya san su har da suka sami matsayi a wajansa kamar haka amsoshin da rinzalu ya
kasa baiwa
kansa kenan haka dai ya hakura yana ji yana gani ya juya da baya yaje ya shiga cikin sauran
yan uwansa.
.
Ayi hakuri mu kwana anan sai kuma Allah Ya kaimu gobe da yardar Allah, kafin nan dai ni ɗin
ne Abubakar Saleh AlQuyraemey.
--
TSATSUBA
Littafi Na Uku (5)
Part C.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
.
Lokacin da aka iso cikin gidan sarautar sarki Hulbasu sai ya kama hannun hailur ya jashi har
izuwa cikin kuryar turakarsa suka zauna aka kawo musu abinci da abinsha shi kansa hailur yayi
mamakin yadda sarki hulbasu ya aminta dashi haka cikin kankanin lokaci alhalin sau daya rak
suka taba ganin junansu ma wannan haduwar ta yau itace ta biyu amma ya aminta dashi kamar haka Hailur yace a cikin
ransa wata kila saboda abin karamcin da nayi masa ne a daji shi yasa ya saka mini da irin
wannan tarba, bayan an kawo musu wannan abinci da abin sha na alfarma sai sarki yayiwa
hailur tayi amma sai hailr ya kasa cin abincin ya kura masa idanu kawai a lokacin da tuni Sarki
ya gabatar da wajan loma biyu yana shirin kai ta uku kenan sai ya lura da cewa hailur baya cin
abincin kuma yayi shiru fuskarsa na nuna alamun tunani.
.
Koda ganin haka sai sarki Hulbasu yai murmushi a gareshi yace kwantar da hankalinka ya kai
abokina kayi sani cewa a halin yanzu matarka da yarka jaruma siyama suna can tare da matata
da kuma gimbiya shadila matar sarki shardas cikin aminci suna cin irin wannan abinci dake
gabanmu koda jin haka sai hailur ya saki ajiyar zuciya tare da jinjina kai alamar gamsuwa da
furucin da sarki Hulbasu yayi masa nan ya saki jikinsa ya fara cin abincin, har suka ci suka
koshi dayansu bai kara cewa uffan ba sai bayan sun nutsu sannan sarki ya dubi hailur yace
yakai abokina kayi sani cewa hankali shine yake gani amma ba idanu ba tabbas akwai
boyayyen al amari a tare dakai wanda kake boye mini amma ina so ka sani cewa ba a boyewa
abokin kuka mutuwa yakamata ka gane cewa shi masoyi na kwarai har abada masoyi ne shi
kuwa masoyi zaka sameshi mai rike amana da kare masoyinsa da sallama rayuwarsa a gareshi
a koda yaushe komai RINTSI DA TSANANI, na rantse maka da girman iyayena da kakannina
ba zan taba cin amanarka bakona juya maka baya musamman idan kayi la akari da irin
taimakon da kayi mini a cikin daji wanda har na mutu ba zan manta dashiba, ina son ka saki
jikinka da zuciyarka ka sanar dani duk abin dake faruwa shin menene tsakaninka da shadila
matar sarki shardas?
.
Na lura da duk abin da ya faru dazu a tsakanin kai da ita a filin GASAR JARUMTAKA, naga
hawaye na zuba a cikin idanunta sa adda rawanin fuskarka ya kwaye tayi arba dakai, shin kun
san juna ne dama ?
.
Ka sani cewa ko ka sanar dani wannan sirri ko ka ki tuni yanzu rayuwarka da ta iyalanka tana
hannuna domin inda ban shigo daku nan ba cikin gidan sarautata tuni kun dade da zama gawa,
lokacin da sarki yazo nan a jawabinsa sai hailur yaja dogon numfashi ya ajiye sannan ya
dubeshi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace yakai wannan sarki mai Adalci kayi
sani cewa gimbiya shadila matatace a baya kafin sarki shardas ya mallaketa, koda jin wannan
batu sai idanun sarki hulbasu suka zazzaro tsoro ya kamashi kuma jikinsa ya kama kyarma shi
hailur sai yaci gaba da bayani yana mai cewa a ranar angwancina da ita ne sarki shardas da
dakarunsa.suka kawo ma kabilarmu harin Mamayar bazato sukayi ta ragargazar dakarunmu
kuma suka kame matayanmu da yawa a matsayin bayi ni ne kadai jarumin da na gagaresu har
ma nayi gumurzu da sarki shardas amma a karshe ya jefani kasa daga saman wani tsauni mai
tsananin tsawon tsiya sanadiyar da na rasa hannuna guda daya na hagu kenan kuma kafata
guda daya itama ta sami wannan nakasa ta shagidewa, nidai kawai farkawa nayi na tsinci kaina
a cikin wata bukka a tsakiyar daji koda na yunkura domin na mike zaune sai naji na kasa domin
gaba daya jikina babu kuzari, yayin da na sake yunkurawa domin na yaye mayafin da aka
lullube ni dashi akan shimfidar da nake kwance sai naji babu hannuna guda daya na dama, nan
take na kwarara wani uban firgitaccen ihu cikin tsananin bakin ciki da razana.
.
Faruwar hakan keda wuya sai ga wani dattijo tare da wata kyakkyawar budurwa sun shigo
izuwa cikin bukkar da shigowarsu sai suka durkusa a gabana dattijon ya dubeni a dimauce yace
yaro me ya faru gareka