Showing 3001 words to 6000 words out of 8267 words
Chapter 2 - TSATSUBA BOOK 5 Complete by Madakin Gini .pdf
ka tsandara wannan uban ihu haka shin wani mugun mafarki kayi ko
kuwa wani mugun abune ka gani. .
Sa adda naji wannan tambaya sai hawaye ya zube mini na dubi dattijon cikin nutsuwa nace me
yasa kuka ceci rayuwata baku barni na mutu ba yanzu menene amfanin rayuwata a doron kasa
tunda na rasa komai da kowa nawa kuma na rasa lafiyata ina mai rokonku daku gaggauta
kasheni yanzu domin na huta da bakin cikin dake nukurkusar zuciyata yayin da na zo nana
zancena sai dattijon da wannan kyakkyawar budurwa suka kamu da tsananin tausayina.
.
Dattijon ya kalleni yace samari hakika kana da nisan kwana a duniya domin a tarihin wannan
tsauni wanda ka fado daga kansa fiye da shekaru dari bakwai baya ba a taba samun mahalukin
daya fado daga kansa ba ya rayu sai kai muma nan da ka ganmu muna zaune a cikin wannan
daji mun fitone daga cikin wata babbar kabila da ake kira BANU IKHLAS. kamar yadda sarki
shardas ya karar da kabilarka haka muma ya karar da tamu kabilar ni da wannan ya tawa ce
zalina kadai muka tsira da rayuwarmu alokacin.
.
Sa adda ya kawo farmaki zuwa kauyanmu nida ita
bama nan muna cikin daji muna yin farauta bayan mun dawo mun iske iyayanmu da yan
uwanmu da duk danginmu sun zama gawa sai muka kama kuka mutum daya kacal muka samu
da sauran numfashi a jikinsa shine ya gaya mana cewa sarki shardas ne da kansa shida
dakarunsa suka zo sukayi mana wannan mummunar barna da dai muka ga cewa ba zamu iya
daukar fansa a kan sarki shardas ba sai muka hada kayanmu muka sake komawa cikin daji
muka ci gaba da farauta, amma bamu zauna a waje daya ba sai muka ci gaba da tafiya muna
ketawa ta gefen garuruwa da kauyuka amma bama zama a inda babu cibiyar ruwa. Tabbas
ruwan dake kasan wannan tsauni da ka fado ne ya kawoka nan domin daga can zuwa nan
tafiya ce ta kwana saba in da hudu, sa dda mahaifin zalina yazo nan a zancensa sai na cika da
tsananin mamaki kuma na sake kamuwa da bakin ciki mara misaltuwa don haka ban san sa
adda na fashe da kuka ba ina mai cewa ina ma na mutu ban rayu ba sakamakon fadowa daga
kan wannan tsauni tun da yanzu bani da kowa kuma bani da komai a wannan daji, koda jin
wannan batu sai tausayina ya kama zalina da mahaifinta zalina ta dubeni tace yakai wannan
jarumi ma aboci kwarjini da jarumtaka ka yi sani cewa yadda baka da komai da kowa a wannan
duniya haka muma muka kasance ni da mahaifina amma tunda yanzu kaddara ta hadamu mun
sameka ka samemu, zaifi kyau mu rungumi kaddara bisa yadda ta samemu mu ci gaba da
rayuwa ko don nan gaba mu ga yadda karshen mulkin sarki shardas zai kasance koda kuwa mu
bazamu iya ganin karshen nasa ba, ka sani cewa babu wani abu madawwami kuma komai
nisan jifa kasa za fado, don haka duk abinda sarki shardas ke takama dashi watarana sai ya
fado kasa tunda idan ba mutuwa akwai tsufa akwai lokacin da yanaji yana gani ba zai iya yin
zaluncin da yake yi ba yanzu koda mu bamu ga wannan lokaci ba ina son ire irenmu sugani.
.
Lokacin da zalina tazo nan a zancenta sai jikina dana mahaifinta yayi sanyi saboda mun san
cewa duk abinda ta fada gaskiya ne, tun daga wannan rana zalina da mahaifinta sukaci gaba
da jinyata har na sami lafiya ya zamana cewa ina iya mikewa tsaye na dogara sanda na bisu
izuwa daji don yin farauta amma fa duk sa adda na dubi hannuna na hagu naga babu shi kuma
naga kafata ta dama ta shagude sai na fashe da matsanancin kuka na bakinciki domin gani
nake kamar rayuwata bata da wani sauran amfani duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina
da mahaifinta sunyi da gaske sannan suke rarrashina na dawo cikin hayyacina....
TSATSUBA
Littafi Na Uku (5)
Part C.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da mahaifinta sunyi da gaske sannan suke
rarrashina na dawo cikin hayyacina wani abin mamaki wanda ya daure min kai shine duk da
cewar na rasa hannu daya da kafa daya ko kadan ban rasa karfin damtse na ba da kuma iya
yakina don haka duk sa adda muka shiga daji farauta duk muguwar dabbar da ta zo gabanmu
take nake gamawa da ita, komai yawan gungun yan fashi kuwa idan mukayi gamo dasu ni
kadai nake tarwatsa su, amma zalina da mahaifinta suna taimaka mini saboda sun kware ainun
a iya harba kibiya. A lokaci guda kowannansu na iya harba kibiyoyi bakwai sai dai kaga maza
na zubewa kasa yayinda tsinin kibiyoyinsu suke ratsa kirazansu, A kwana a tashi sai na sami
wata bakwai tare da su zalina ya zamana cewa na shaku dasu ainun musamman zalina wacce
komai tare muke yi shimfidar barci kawai muke rabawa. A hakane na fuskanci cewa soyayya ta
shiga tsakaninmu amma dana tuna cewa ni fa yanzu masaki ne bani da hannu daya da kafa
daya sai na ga cewa idan na nemi soyayyar zalina na cutar da ita. kuma idan na tuna cewa na
rasa masoyiyata shadila sai naga cewa ai na gama soyayya a duniya don ba zan taba samun
wacce zan sota ta soni ba
kamarta bisa wannan daliline na rinka danne soyayyar zalina a cikin zuciyata kuma duk sa adda
naga zata nuna mini soyayyar tata saina bagarar.
.
Ni abinda yake bani mamaki ma shine me zata yi da masaki muna cikin wannan hali ne
mahaifin zalina ya kamu da cuta mai tsanani wacce takai shi ga kwanciya, abu dai kamar wasa
kullum sai ciwo ya rinka gaba ya zamana cewa ba a samun sauki. Al amarin da ya dugunzuma
hankalinmu kenan muka rasa sukuni da kwanciyar hankali ita kuwa zalina kullum bata da aikinyi
sai kuka da bakin ciki da kyar nake iya rarrashinta, ba komai ne yake sata
wannan yawan kuka ba sai ganin cewa babu alamar samun lafiya ga mahaifinta kuma ga
dukkan alamu ciwon nasa bana tashi bane, wata rana na tashi da sassafe ina shirin tafiya daji
domin naje nayi farauta naman da zamu ci da rana a lokacin zalina na can wajan kogon da
muke kwana ta dora tukunya akan wuta tana dafa mana abincin kalaci sai mahaifin zalina ya
kira sunana a lokacin da nake daf da fita daga cikin kogon. Cikin tsananin mamaki na juyo na
dubeshi saboda rabonsa da ya budi baki yayi magana tun daga ranar da ya kwanta wannan
cuta, cikin matukar sanyin jiki na karasa daf dashi na tsugunna a gabansa inamai kura mas
aidanuna ya shi kuma sai ya kamo hannuna ya dora akan kirjinsa ya dafe hannun nawa da
dukkan hannayansa biyu sannan ya budi baki da kyar yace yakai hailur kayi sani cewa wannan
ciwo nawa bana
tashi bane mutuwa zanyi kuma a koyaushe wa adina zai iya cika ina neman Alfarma guda daya
jal a wajanka alfarmar kuwa itace ina son ka auri zalina, koda jin wannan batu sai zuciyata ta
buga da karfi na dubeshi cikin mamaki nace yakai abul zalina ai idan kace na auri zalina bakayi
mata adalci ba domin kana sone ta auri nakasashshe koda jin haka sai tsohon yayi murmushin
karfin hali ya dubeni cikin nutsuwa yace yakai hailur kayi sani cewa a zahiri kake nakasashshe
amma a zuciyarka kafi ta lafiya sannan kuma har yanzu sadaukantakarka da jarumtakarka suna
nan basu ragu ba dai dai da matsayin kwayar zarra ina son ka sani cewa yata ta kamu da
tsananin sanka a cikin wannan hali da kake ciki na nakasa kaga kenan ashe soyayyarta itace
soyayyar gaskiya ka auri yata zalina ko don saboda ka samu zuri ar da zasu ga bayan babban
makiyinmu sarki shardas ka sani cewa kowacce mace tana son ta auri namijin da zai iya kare
mutuncin ta da rayuwarta koda kuwa shine yafi kowa nakasa a doron kasa lallai ku cika mini
burina na ganin bayan sarki shardas wannan itace kadai wasiyyata a gareku, ashe duk wannan
bayani da mahaifinta yake yimini zalina dake can kofar kogo tana sauraro don haka sai ta kasa
cigaba da aikin da takeyi ta koma gefe daya ta zauna tana ta faman kuka, koda na fito daga
cikin kogon dutsen rataye da takobina da nufin na shiga daji don gabatar da farautar sai naga
zalina tana ta kukanta..
.
Al amarin da yasa na gane cewa lallai duk taji abinda muka tattauna kenan dani da mahaifinta
cikin sanyin jiki na karasa gareta na zauna daf da ita kanta na sunkuye sai na tallabo habarta da
lafiyayyen hannun nawa kuma na share mata hawaye muka kurawa junanmu idanu sannan na
dubeta nace shin kin amince na zama abokin rayuwarki. .
Koda jin wannan tambaya sai zalina ta murtuke fuska daga can kuma sai ta rungumeni ta kama
kyalkyala dariyar farinciki muna rungume da juna mukaji motsi a bayanmu a firgice muka juya
da sauri sai mukaga she mahaifin zalina ne ya fito daga cikin kogon dutsen yana dogara sanda
da kyar yana numfashi sama sama. .
A guje na janye jikina daga cikin na zalina na karasa gareshi na rukoshi na zo dashi wajan
zalina itama ta kamashi muka zauna gaba daya sannan ta dubeshi cikin alamun tsananin
damuwa tace haba ya kai Abbana yaya kai da kake cikin wannan hali zaka taso kayi tafiya sa
adda abul zalina yaji wannan tambaya daga bakin yarsa zalina sai ya dubeta yayi murmushin
karfin hali yace yake yata ai dole ne na taso ko don naga abin farinciki na karshe wanda
idanuna zasu gani wanda shine amincewar junanku akan aure lallai ina so naga wannan aure
naku da idanuna kafin rai yayi halinsa, nan take tsohon ya yiwa hailur bayanin yadda zasu
daura auren bisa al adar su kabilar wato kowannansu ya yanki dan yatsansa ya diga jininsa
a cikin ruwa bayan jinin biyu ya gauraye sai kowannan su ya sha ruwan nan take kuwa muka
aiwatar da hakan, muka rinka shan ruwan muna kallon juna cikin murmushi har sai da ruwan ya
kare kaf.
.
A dai dai wannan lokacine farinciki ya lullube abul zalina ya dubi hailur yace yakai babban
gwaro kayi sani cewa yanzu ka zama na zalina kuma zalina itama ta zama taka babu abinda zai
rabaka face kaddara ko mutuwa, wannan dama shine manufar shan jinin juna da kukayi, bisa al
adar kabilarmu a ranar da miji ya mallaki matarsa babu abinda zasu fara face zuwa daji farauta
tare, don haka yanzu saiku tafi sannan da ku ka samo shi zaku kawo a gasa muci muyi walima
da farin cikin aurenku, koda
jin wannan batu sai na dubi abul zalina cikin alamun damuwa nace haba yakai abul zalina yaya
za ayi mu tafi daji mu barka kai kadai a nan alhalin kana cikin wannan halina rashin lafiya,
.
Koda jin haka sai abul zalina ya dubeni cikin murmushi yace kada ka damu dani lallai zakuje ku
dawo kuma ku sameni cikin koshin lafiya da sauki fiye da ko yaushe wannan shine abinda na
gani a mafarkina na daren jiya bisa wannan dalili ne ma a yau din nan na sami saukin da har na
iya mikewa tsaye na taka kafafuna na fito daga cikin wannan kogo haka dai abul zalina yaci
gaba da rarrashinmu har ya samu ya shawo kanmu muka amince da barinsa a wajen amma
kafin mu tafi sai da ya rungumemu yana ta dariyar farinciki bayan ya janye jikinsa daga cikin
namune mun juya zamu tafi izuwa cikin daji sai zalina ta waigo ta dubeshi take ta hango kwalla
a cikin idanunsa.
.
Al amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan ta dubeni tace yakai mijina nifa zuciyata bugawa
take da karfi ji nake kamar idan muka dawo ba zamu riskeshi a raye ba ni kaina naga alamun
hakan a tare da mahaifin nata kuma duk kalaman da yake yi na bankwana ne amma don kada
hankalin zalina ya tashi sai naki sanar da ita haka dai muka nausa cikin daji muna waigen Abul
siyama shi kuma ya bimu da kallo yana yi mana murmushi har muka kule muka daina hangoshi.
.
A sannan ne kuma muka falfala da azababbn gudu izuwa cikin daji mukayi ta tsala gudu ba
sassauci muna neman dabbar dajin da zamu samu babu abinda zai baka mamaki face yadda
nake iya gudu ina dogara sanda alhalin kafata guda daya bata da kyau kuma har tserewa zalina
nake yi a gudun ni ina rike da takobi ne kuma karshen sandar da nake dogarawa mashi neita kuwa zalina a hannunta kwari ne kuma ta rataya kwanson kibiyoyin
kwarin a bayanta don haka ita bata rike wani makami sai kwari da baka.koda muka nausa cikin
daji sai muka rabu ni kuma nayi gaba ita kuma tayi yamma sannan kuma muka baiwa junanmu
tsawon rabin sa a akan mu hadu a bakin wani dutse dake can tsakiyar dajin kowannanmu na
rataye da kaho a bayansa wanda duk sa adda ya shiga wani hadari wanda ba zai iya kubutar
da kansa ba sai ya busashi komai nisan inda yake dan uwansa zai iya jiyowa har yakai mas
dauki shidai wannan kaho na sihirine kuma gado ne a kabilar tasu zalina kuma mutum ba zai
iya mallakarshi ba face ya kasance dan kabilarsu ko kuma ya auri jinin Kabilar.
.
Bayan mun rabu a cikin daji nida matata zalina sai muka wanzu muna masu neman abin farauta
baji ba gani, lokacin da naga na shafe dan dogon lokaci ina neman abin farautar ban samu ba
sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda ina ganin cewa ai abin kunyane ace a ranar daurin
aurena na kasa farauto abincin da zamu ci nida amaryata... .
Zan dakata nan sai kuma Allah Ya kainu gobe insha Allahu afin nan daga mai ɗebe maku kewa
AlQuyraemey nake cewa ku huta lafiya.
Ehm Al amin Ahmed Misau, Guyson ko A square
Ina cikin wannan haline naga wata barewa ta
nufo inda nake cikin azababben gudu gashi dai
barewar ta hangoni a gabanta rike da makami
amma ko shakkar tunkaro ni batayi ba
dada durfafo ni takeyi al amarin da yasa na fahimci
cewar lallai masifar da ta korota ta nufoni don tsira
da rayuwarta ta wuce tawa hadari, ai kuwa ban ankara ba
sai naga ashe wani murjejen zaki ne ya tasota a gaba
tun daga nesa dana hango zakin ya falfalo da azababben gudu
har tashi sama yake saboda karfin gudun nasa
kuma harshensa na zazzagowa waje daga cikin bakins ana gane
cewa lallai
wannan zaki a cikin muguwar yunwa yake
koda naga cewa barewar nan so take ta wuce ta gabana
domin ta tsira da rayuwarta sai na yunkura cikin zafin nama na
daka tsalle sama a lokacin da itama barewar ta daka tsalle da nufin ta shallakeni
muna haduwa a saman na soketa da mashina ta
zama gawa na duro kasa bisa kafafuna barewar
na sakale a jikin mashin nawa, ai kuwa sai wannan zaki
yayi tirjiya a lokacin da tazarar dake tsakaninmu
bata wuce taku goma ba
nan fa muka fara kallon kallo tsakaninmu da murjejen zakin
nazarin da zakin yake yi shine ni zai farwa sannan
ya dauke barewar ko kuwa barewar zai karba
ni kuwa nazarin da nakeyi shine ta yaya zan iya
.Ya kasance shi ba karamin tashin hankali bane
duk da na san cewa na sha yin gumurzu da manyan
dabbobin daji ina samun nasara a kansu sai da
zuciyata ta karaya akan wannan zaki domin ban
taba yin gamo da tsohon zakimai girma da kwarjinin wannan ba
nikam tuni na gama aiyanawa a raina cewa
duk rintsi ba zan iya sallama barewar ba ga wannan
zaki koda hakan na nufin zan rasa rayuwata
kawai sai na cake mashin nawa a cikin kasa
wanda ke dauke da barewar sannan na buda hannuna
mai rike da takobi ina mai
gyara tsayuwata kuma na koma gefe daya na tsaya ina
mai baw azakin zabi tsakanin barewar da ni kaina
ya zabi wanda zai fara afkawa
take zakin yayi wani irin
gurnani mai ban tsoro wanda yasa hantar cikinsa ta kada amma da na tuna cewa
amaryata
zalina na can fa tana farauta a cikin wannan daji
wata kilama yanzu ita ta dade da samo nata abin
farautar taje inda mukayi zamu hadu ta zauna
tana jirana sai naji zuciyata ta kekeashe ga barin dukkan tsoro.....
Kamar hadin baki sai nida zakin muka falfalo
da gudun tsiya izuwa kan juna muka dako tsalle
sama a tare kafin nayi wani yunkuri na saran zakin
ko sukarsa da takobina tuni shi ya sa kirjinsa ya
bangajeni
ai kuwa sainaji kamar aksusuwan kirjina sun
kakkarye nayi can baya da karfi bayana ya gwaru
da jikin wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice
ina aman jini ta hanci da baki, koda zakin yaga
halin da na shiga sa adda shima ya duro kasa sai
ya wangame baki ya kwalla wani uban ruri anda
ya fi wanda yayi a baya mai nuna kuranta kansa
da dai yaga na kasa tashi ina ta numfashi sai
ya wuce ta gabana ya daka tsalle da nufin ya suro
wannan barewa dake sakale a jikin mashina
ni kaina ban san yadda akayi ba na sami gagarumin
karfi da kuzari kawai gani nayi na mike tsaye zumbur
na daka tsalle daga inda nake na rungumo zakin
kafin bakinsa ya cafi barewar mun fado kasa tim !
Nan fa muka kama kokawa a kasa muna ta birgima
idan zakin ya danneni yana kokarin kafa min
hakoransa sai na juye dashi nima ina kokarin
turmushe shi da karfin tsiya domin na hallakashi
sai da muka shafe kusan sa a daya muna ta bakin
artabu ya zamana cewa zakin ya karkarce jikina
da kaifin faratan hannayansa yai mini raunika
masu yawa jini na