Showing 1 words to 3000 words out of 8839 words

Chapter 1 - TSATSUBA 6 Book Complete by Abdulaziz Sani .pdf

TSATSUBA
Littafi Na Uku (6)
Part A.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da sarki Hulbasu ya zo nan a zancensa sai Hailur ya jinjina kai gami da yin murmushi
sannan ya tattara hankalinsa gaba daya kan sarki hulbasu yace ina saurarenku yakai abokina ,
koda jin wannan batu.sai shima sarki Hulbasu ya mayar masa da martanin murmushin da yayi
masa sannan ya fara bashi labarin kamar haka.... ''KIMANIN SHEKARU GOMA SHA DAYA DA SUKA SHUDE, Sa adda satki shardas ke nahiyar
nan yana cinsu da yaki sai ya zama dodon maza kuma ki gudu sa gudu domin kuwa duk kasar
da ya durfafa sai ya sami nasara akanta, a wannan lokaci mahaifina ne akan karagar mulki ni
kuwa nine sarkin yakinsa, kuma nine kadai dansa a duniya kuma nima dana guda daya ne tal a
duniya wato YARIMA HUZEIN.
.
Lokacin da labari ya riski mahaifina cewar sarki shardas yaci kasashe guda ashirin da daya da
yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi da farko yayi shiri ya
dauki matakin yin yaki da sarki shardas don har ya bami umarni na tara gaba dayan
mayakanmu mu tanadi abinci da kayan yaki da nufin mu yi riga kafi muje mu tari sarki shardas
da yaki tun gabanin yazo ya yakemu amma sai wani tunani ya zo masa ya dakatar da fita yakin
yayi shiri ya tafi izuwa gidan wani mashahurin boka wanda ake kira ZAMARANU IBINI
KALBIYA,, boka zamaranu na zaune a cikin wani daji ne dake gabam iyakar wannan birni namu
kuma masana tarihi da bincike sun tabbatar da cewar boka zamaranu yafi shekara dari zaune a
ciki wannan daji shi kadai, babu wanda yasan abinda yake yi a cikin dajin ko kuma dalilin
zamansa amma dai an tabbatar da cewar da shi da bukkar da yake zaune a cikinta kwai rana
guda aka gansu sun wanzu ba a san mafarinsu ba, mahaifina Ya durfafi dajin DANYUL shi
kadai kai tsaye ba tare da fargabar komai ba alhalin tsawon bayyanar boka zamaranu a dajin
babu wani mahaluki daya sake shigarsa walau MUTUM KO ALJAN ba don komai ba kuwa face
sai don mugayen bakaken aljanun dake cikinsa, AA Misau Sunana, Komai gawurtar ayari na
fatake basa iya ratsa dajin duk tsautsayin da ya sa suka shiga kuwa shi ke nan sun bata har
abada ba za a sake jin duriyarsu na a tsawon shekara dari da baiyanar boka zamaranu a cikin
dajin Danyul fatake ko yan fashi ba sa sake shigarsa ba, don haka nema ake yiwa dajin lakani
da BIRNIN FATALWA.
.
Duk da sanin tsananin hadarin dake cikin wannan dajin haka mahaifina ya kunna kai cikinsa, kai
da ganin yanayin fuskar mahaifina a lokacin da yake tafiya bisa dokinsa a cikin dajin ka san
cewa babu batun tsoron mutuwa a ransa, in da ma mutuwar zata zo masa to zai marhaban da
ita ai kuwa tunda ya shigo cikin dajin ya rinka yin arba da wadansu irin mugayen bakaken aljanu
masu tsananin muni da ban tsoro, duk sa adda wadannan mugayen aljanu ska tasamma
mahaiina da nufin su dasa masa wawa sai su ga ko gezau baiyi ba alhalin duk bil adaman da

yayi arba dasu take yake zaucewa ko sumewa haka dai Aljanin suka yi ta kokarin firgita
mahaifina da razanashi amma ko kadan yaki razana wani lokacin ma sai yayi kamar bai gansu
ba ko baijisu ba, sai da ya shafe kwana tara yana tafiya kuma baya yarda ya yada zango a ko
ina ko barci zaiyi akan dokinsa yake yi, kuma a tsawon kwana taran.baiyi bawali ba ko bayan
gida, kuma baya tsayawa da tafiya face idan dokin nasa ya gaji
ya tsaya don kansa yana hutawa, a ranar kwana na tara ne ya iso kofar bukkar boka zamaranu
wacce ke tsakiyar dokar dajin Danyul.

++ ++

ACAN BIRNIN ASKANDARIYYA KUWA, hankalina dana yan majalisar sarki ya dugunzuma
ainun, domin mun nemi sarki sama da kasa a cikin birnin nan mun rasa babu wanda ya san
cewa ya tafi izuwa dajin Danyul, Ashe cikin tsakiyar dare ya sulale ya fice daga cikin birnin ta
hanyar batar da kamanninsa.
++ ++

MAHAIFINA NA isa can kofar bukkar boka zamaranu sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak !
Kafin ya sauko daga kan dokin nasa ne yaji an da dariya kuma sai yaji sautin dariyar yana
fitowa daga kowanne bangare wato gabas da yamma, kudu da arewa sarki ya leka cikin
wannan bukka sai yaga wayam babu kowa a ciki kawai sai yaji an dafa kafadarsa ta baya, a
firgice ya juya da sauri yayi arba da abinda ya dafa kafadarsa boka zamaranu ne!
.
Boka zamaranu ya kasance dogon mutum kuma siriri mai kwala kwalan idanuwa kunnuwansa
wasu iri ne kamar ba na mutum ba domin a tsaye suke tamkar na zomo yana da tarin gashin
girar ido mai kauri da tsawo kuma yana da dogon hanci tamkar alkalami, Gaba daya gashin
kansa gemunsa da sajensa fari ne saboda tsufa ga masana ilimin karanta shekarun dan adam ta hanyar lura da yanayinsa za su iya bashi
shekaru dari biyu da yaya na haihuwarsa, domin gaba daya fatar jikinsa ma ta yankwane ta
bushe kai kace ma ba mutum bane.
.
Siffofinsa gaba daya sun juye sun zama abin tsoro koda
sarki yayi arba da boka zamaranu sai yaja da baya a tsorace a karon farko tunda ya shigo cikin
dajin Danyul,
koda ganin haka sai boka zamaranu ya sake bushewa da dariya a karo na biyu yace haba yakai
sarki mai birnin askandariyya akan wani dalili Zakaji tsorona alhalin ka wuce abubuwan tsoro
sama da guda dubu a baya wadanda suka fini firgitarwa?
.
Ka sani cewa kaine kadai mahalukin da ya ratso wannan daji ya iso har nan a raye tsawon
shekara dari da suka gabata kuma kaima din bawai jarumtakarka ko sihirinka bane suka
kwaceka ba face cire tsoron da kayi a cikin ranka rashin tsoro a cikin zuciyar mutum shine sirrin
shigowa cikin wannan daji na Danyul har mutum ya cimma burin da yake dashi dashi acikin
dajin ba tare da ya hallaka ba, shin zaka iya gaya mini dalilin da ya saka siyar da ranka ka shigo

wannan daji alhalin ga mutanenka can sunyi shirin yin yaki da sarki shardas ?
.
Lokacin da boka zamaranu yazo nan a zancensa sai sarki yayi ajiyar zuciya ya kasa cewa
komai domin a sannan ne yaji bawali ya matse shi kuma wata irin azababbiyar yunwa da
kishirwa sun kamashi, saboda dama tun a kwana na takwas da tahowarsa dajin danyul
guzurinsa ya kare, da yunwa da kishirwa ya kwana. .
Kwatsam! Sai sarki yaji boka zamaranu ya sake bushewa da dariya sannan yayi nuni da cikin
bukkar sa yace da sarki sauko daga kan dokinka ka shiga cikin bukkata ka kawar da bukatarka
duk abinda kake so zaka samu a ciki koda jin wannan batu sai sarki ya sauko daga kan dokin
nasa da sauri ya ruga izuwa cikin bukkar. .
Yana shiga sai kansa ya juye ya firgita ainun domin ba a dakin bukka ya tsinci kansa ba, cikin
wata makekiyar fada ya tsinci kansa wacce ta kawatu ainun fice da tasa
take kofar wani makewayi ta bayyana tare da bude kanta
ba tare da wata fargabar komai ba sarki ya ruga izuwa ciikinta ya kawar da bukatarsa, yana
fitowa daga cikin kewayen kuma saiga Abinci da abin sha iri-iri akan wani dogon tebur na
alfarma sarki ya karasa kan wannan tebur jikinsa na tsuma zuciyarsa cike da tunani da mamaki
domin sa adda ya shigo fadar babu wannan teburi bare abincin dake kansa ba tare da fargabar
komai ba mahaifina ya zauna yaci gaba da sha sai da yayi gyatsa mai nuni da alamar Ya koshi
faruwar hakan keda wuya sai boka zamaranu ya baiyyana tsulum a gabansa yace yauwa tun da
yanzu ka sami nutsuwa saika bani amsar tambayata ?
.
Mahaifina yayi gyaran murya yace yakai wannan boka mai daraja kayi sani cewa ba komai ne
ya sa na sai da raina na shigo cikin wannan daji ba alhalin na san cewa duk wanda ya shigeshi
sai ya mutu face sai domin gudun kada nayi garaje na zuwa yakar sarki shardas saboda masu
iya magana sunce mai laya ya kiyaye mai zamani .
A iya sanina ban taba ganin sarkin da ya yaki kasashe ashirin da daya ba a wannan nahiya
tamu har ya sami nasara a kansu face sarki shardas duk da na san cewa a nahiyar nan tamu
kaf babu wata kasa mai yawan dakarun yakina, amma duk da hakan sai da zuciyata ta buga
kuma tsoro ya darsu a cikin raina bisa al amarin sarki shardas, naji daga bakin bokaye da yawa
cewa kaine kadai zaka iya gaya mini wani abu akan sarki shardas bisa wannan daliline yasa
nazo gareka domin ka sanar dani shin idan nayi yaki da sarki shardas zan samu nasara a
kansa? Baya ga wannan ina so nayi maka wata tambaya guda daya ? Tambayar kuwa itace
wai shin menene ya zaunar dakai a cikin wannan daji har tsawon shekaru dari ??
.
Lokacin da boka zamaranu yaji wadannan tambayoyi sai yayi shiru yana mai sunkui da kansa
kasa kamar ba zai ce komai ba, daga can kuma sai ya dago kansa ya dubi mahaifina cikin
nutuwa yace yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wani jarumi ko matsafi daga jinsin
MUTUM KO ALJAN wanda zai iya kashe sarki shardas a yanzu domin kuwa yana kan
sharafinsa ne kuma zamaninsa ne, ina tabbatar maka da cewa idan har ka ce zaka yakeshi sai
gaba dayan dakarunka sun kare, kuma sai ya shigo har cikin birninka ya yi maka KISAN GILLA

idan kana son ka tsira daga sharrinsa sai dai ka shirya masa kyauta ta dukiya da bayi mai yawa
ka aika masa kuma ka tambayeshi duk abinda yake bukata daga gareka domin kai da jama
arka ku zauna lafiya, dangane da tambayar dakayi mini kuwa ta karshe amsar tambayar ka
itace yau shekarata dubu biyu ina jiran zuwan ranar da wata hula zata bayyana wacce ake kira
da suna HULAR LAMSARA Zamana a cikin wannan daji ba na komai bane face na binciken
gano inda hular lamsara take da kuma yadda zan iya mallakarta amma har yanzu na kasa gano
hakan sa adda boka zamaranu yazo nan a zancensa sai mamaki ya kara kama mahaifina yace,
yakai wannan boka mai daraja da abin al ajabi an ce shekaranka dari a cikin wannan daji kuma
gashi a yanzu da bakinka ka gaya mini cewa yanzu shekararka dubu biyu kana jiran bayyanar
hular lamsara to waishin anya kuwa kai mutum ne ?
.
Ko a a zamanin baya sosai na kakannin kakanninmu mutane basa yin shekaru dubu biyu a
doron kasa, sannan kuma ita wannan hula ta lamsara yaushe ne za ta bayyana kuma me kake
so kayi da ita da har ka shafe shekaru dari a cikin wannan daji saboda ita?
.
Koda jin wannan tambayoyi sai boka zamaranu ya bushe da dariya mai karfi har Dariyar ta
kama amsa kuwwa ta cika fadar gaba daya, mahaifina yaji kamar kunnuwansa zasu dode ba
shiri ya sa hannayansa ya toshe kunnuwan nasa har sai da ya daina dariyar sannan ya dago ya
kalleshi, boka zamaranu ya mike tsaye yayi tafiyar taku biyar sannan ya juyo ya fuskanci sarki
yace ni mutum ne kamar kai ba aljan ba amma na fito daga cikin mutanen da suka fi kowanne
kabila dadewa a duniya domin a yanzu haka da kake ganina shekarun haihuwata sun kai dubu
biyu da dari hudu da arba'in, nine kadai mutum da ya rage a duniya daga cikin jinsinmu kuma
nine kadai na san sirrin kayan yakin MAZAN JIYA guda hudu makaman yakin da babu kamarsu
a duk fadin wannan duniyar gaba daya, idan na mallaki hular lamsara sai na mallaki duniyar
nan gaba dayanta, kuma a sannan ne kadai zan iya yin aure har na haifi irina wanda a gaba
zaiyi shekara dubu takwas yana mulkin duniya Jikana kuma zai karbi karagar a hannunsa ya
ninka shekarunsa haka dai zuri ata zata ci gaba da mulkin duniya har abada ba zan taba cika
wannan burin nawa ba face na mallaki hular lamsara yakai wannan sarki kayi sani cewa babu
wanda zai iya hallaka sarki shardas face wanda ya fara mallakar wannan hular ta lamsara, da
wannan furuci nake yi maka bankwana kuma ina mai shawartarka daka gaggauta barin dajin
nan ka koma izuwa ga kasarka domin idan ka kara dakika arba in anan zaka iya rasa
rayuwarka duk amsar da baka ji ba daga tambayoyinka ba zan iya sanar dakai bane gama fadin
hakan keda wuya sai boka zamaranu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen, koda
ganin haka sai mahaifina ya mike zumbur ya fice da gudu daga cikin fadar sai gashi ya bayyana
a gaban wannan bukka a dimauce ya karasa inda dokinsa yake ya daka tsalle ya haye kansa
sannan ya sakar masa linzami ya kama gudu ba sassauci sai da mahaifina ya sake shafe
kwana tara yana tafiya sannan ya dawo gida, yana isowa ya bayar da umarnin a janye batun
yaki nan take aka sallami kowa mayakan suka koma izuwa ga gidajensu tare da kwance
damarar yakin da suka daura suna cike da dumbin mamakin dalilin da ya sa aka fasa zuwa
yakin, kashe gari kuwa, da sassafe sarki ya tashi ayari na dakaru dubu uku dauke da bayi dubu
ashirin da kuma dukiya mai dumbin yawa ta dinare, lu'u lu'u da murjani cikin akwati dubu suka
tafi izuwa ga birnin sarki shardas da kuma wasika.
.

Lokacin da wannan ayari suka riski sarki shardas yaga dukiyar da mahaifina ya aiko masa
kuma ya karanta wasikarsa wacce ke nuna mubaya a gami da neman zaman lafiya sai ya
bushe da dariyar mugunta sannan yace' tabbas na cika zaki uban dawa a wannan nahiya kuma
dole ne sarakuna su durkusa a gabana su nemi tsira da jaddada muba ya arsu gareni nan take
sarki shardas ya sa aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da ita bayanin dake
cikin wasikar shine kamar haka...........
Danjin wani bayani ne sarki shardas ya aiko sai ku tarbeni a Post na gobe ehem Dafatan
wannan labarin yana kayatar daku Idan hakane kawai ku sauke mun comments dinku gami da
likes kafinnan Nidinne Dai #Abubakar_Saleh_AlQuyraemey.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (6)
Part B.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Nan take sarki Shardas ya aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da ita, bayanin
dake cikin wasikar shine...
Yakai mai birnin askandariyya kayi sani cewa sakonka
na bayi da dukiya ya riskemu, kuma mun gode da wannan karramawa da kayi mana gami da
mubaya'a, amma ka sani cewa ba mu karbi mubaya'arka ba har saika zo da kanka fadata ka
zube kasa a gabana ka kwashi gaisuwa sannan zamu aminta da mubaya'arka a garemu,
sharadi na biyu kuma shine dole ne duk shekara ka rinka kawo mini irin wannan kyauta daka
kawo mini ta bayi dubu ashirin da dukiya akwati dubu sharadi na uku shine dolene ka baiwa
wakilina matsayi da mazauni a kasarka domin su dinga kawo mini rahoto duk abin dake gudana
a cikin birninka da kauyukan kasarka, sako daga sarki mai cikakken iko kuma sarki dodon maza
gallabar sarakuna sarki shardas.

** **

Lokacin da wannan wasika ta riski mahaifina aka karanta a tsakiyar fada sai hankalin kowa ya
dugunzuma ni kuwa sai raina ya baci jikina ya kama tsuma, cikin tsananin fishi na mike tsaye
ina mai zare takobina na dubi sarki nace yakai abbana kayi sani cewa idan muka bi wannan
sharadi na sarki tamkar mun zamo bayin sane domin zamu rike masa saniyar tatsa ne ya rinka
tatsar nononta zamu zamo bamu da wani sirri na kanmu a cikin kasarmu kuma tattalin arzikin
mu zai raunana mutanenmu zasu iya fuskantar fatara da talauci kafin na gama rufe bakina tuni
sarki ya daka min tsawa yana mai tarar numfashina ya ce, idan muka ki bin umarnin sarki
shardas sai ya kashe kowa a kasar nan ya mallake komai namu idan mukace zamu yakeshi
komai yawan nan namu sai ya karar damu saboda yana kan sharafinsa abin da boka zamaranu
ya gaya mini kenan.
.
A matsayinka na dana kuma yarima mai jiran gado ya kamata ka zamo mai kishin kasarka da
jama arka, abinda sarki shardas ke bukata kawai shine na kaskanta kaina a gareshi kuma mu

bashi dukiya kada ka dubi matsayina da kimata a wannan nahiya, zan iya sallama rayuwata ma
gaba daya don kare jama ata da kasata dukiya kuwa shirme ce idan ka rasata zaka iya samun
wata, ina mai dada ja maka kunne babu batun yaki tsakaninmu da sarki shardas kuma kada ka
kuskura ka yi wani abu wanda zai jefa kasarmu ko jama armu cikin hadari ina mai umartarka da
ma za kaje kasa a shirya mana tafiya gobe gobe zamu durfafi birnin sarki shardas don amsa
kiransa, kuma dakarun da zasu yi mana rakiya kada su wuce su dari biyu don samun kariyar
hanya daga sharrin yan fashi da dabbobin daji, koda gama fadin hakan sai sarki ya mike tsaye
daga kan karagar mulkinsa ya shige cikin gidan sarautarsa, ni kuwa sai bakin ciki ya lullube ni
na sunkui da kaina kasa a lokacin da idanuna suka ciko da kwallar takaici a wannan lokaci ne
fadar ta watse kowa ya kama gabansa aka barni ni kadai a zaune babban abin da ya kona
zuciyata shine idan na tuna cewa mahaifina zaije gaban sarki shardas ya durkusa masa alhali a
nahiyar mu gaba daya babu wata masarauta mai tsohon tarihi da daukaka sama da tamu idan
har sarki ya durkusawa sarki shardas shikenan darajarsa da kwarjininsa a idanun jama a sun
zube har abada kuma ba za su kara

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login