Showing 3001 words to 6000 words out of 8839 words

Chapter 2 - TSATSUBA 6 Book Complete by Abdulaziz Sani .pdf

dawowa ba.
.
Ina zaune cikin wannan halina bakin ciki dana yarima huzein ya zo gareni ya dafa kafadata
koda na dago kai nayi arba dashi sai naga shima yana zubar da hawaye, cikin sanyin murya
huzein ya dubeni yace yakai abbana
ka zamo mai hakuri da juriya bisa wannan kaddara data same mu ina so ka sani cewa komai
nisan jifa kasa zai fado don haka komai dadewa akwai ranar da sarki shardas zai fadi duk
wulakancin da zamu fuskanta daga gareshi yanzu yana da iyaka wataran sai labari, ina mai
tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya kuntata mana a yanzu da zamaninka to nan gaba
namu zamanin
sai komai ya sauya sa adda huzein yazo nan a zancensa sai na cika da mamaki bisa dalilin yin
wannan jawabi tamkar wanda ya jiyo wani abu daga wajen bokaye nan take na rungume huzein
iana kuka nace yakai dana zan kasance mai fatan ganin ranar da sarki shardas zai fadi
kafin mutuwata.
.
Koda jin wannan batu sai huzein ya janye jikinsa daga cikin nawa ya dubeni cikin murna da
murmushi yace yakai abbana ina neman alfarma guda daya a wajenka cikin mamaki na
dubeshi nace yakai dana kai kuwa wacce irin alfarma kake nema a wajena?
.
Huzein yace ina son kuyi wannan tafiya tare dani gobe zuwa birnin sarki shardas, koda jin haka
sai idanuna suka zazzaro na dubeshi cikin alamun damuwa nace haba yakai dana ka tuna
cewa idan sarki baya nan
nima bana nan kuma babu kai babu wanda zai gajemu kenan koda tsautsayi yasa mun hallaka
wannan tafiya da zamuyi mai hadari ce komai zai iya faruwa a garemu ko akan hanya ko kuma
a can birnin sarki shardas, bugu da kari a halin yanzu mahaifiyarka na dauke da tsohon juna
biyu haihuwarta yau ko gobe idan babu ni babu kai a kusa da ita wa zata kalla taji dadi? .
Sa adda yarima huzin yaji wannan batu nawa sai jikinsa yayi sanyi amma duk da haka sai yaci
gaba da rokona akan na Rarrashi sarki ya amince ayi wannan tafiya tare dashi, muna cikin
wannan hali ne muka ji takun sawu a bayanmu cikin sauri muka waiga mukayi arba dashi, ba

wani bane face mahaifina fuskarsa cike da annuri kawai sai ya karaso garemu ya zauna a
tsakiyarmu sarki ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yayi murmushi yace naji duk abinda
kuka tattauna, kuma na amince zamu tafi tare dakai gobe koda jin wannan batu sai farin ciki ya
lullube yarima huzein ya rungume sarki yana mai sumbatar goshinsa kawai sai sarki ya janye
jikinsa daga cikin na huzein ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace
yakai jikana kayi sani cewa na amince muyi wannan tafiya tare dakai ne saboda dalili daya rak
dalilin kuwa shine nima sa adda na taso a wannan gidan sarauta daga san da aka haifeni zuwa
lokacin dana kai shekarunka wato shekaru bakwai a duniya sau daya rak aka taba barina na fita
wajen birnin na, bai kamata ace yarima guda wanda zai mulki al umma da yawa ba ya kasance
kifin rijiya yana da kyau ka shiga duniya kaga yadda talakawa ke rayuwa kuma kayi
gwagwarmaya kasha wahala sosai domin ka san menene rayuwa amma ka sani cewa akwai
sharadi guda uku a kanka daga ranar da muka fita daga cikin garin nan,
sharadina farko shine ba ka da ikon zuwa ko ina walau a cikin daji ko a cikin gari face da izinina
ko na mahaifina sharadi na biyu shine duk abinda zakayi saika shawarcemu sharadi na uku
kuwa shine ba zaka ci ko ka sha wani abu ba face wanda muka baka da hannunmu, shin ka
amince da wannan sharadai guda uku. .
Ko dajin wannan tambaya sai yarima huzein yayi murmushi kuma ya zube kasa a gaban sarki
ya kama godiya cikin farin ciki tare da tabbatar da amincewarsa
ga wadannan sharudda.
.
Kashe gari kuwa da sassafe aka yi shirin tafiya dakaru dari biyu ne suka yi mana rakiya dauke
da isashshen guzuri sai kuma kuyangi goma wadanda za su rinka yi mana hidima tsakanin yan
fashi da mugayen dabbobin daji sai da mukayi karo da rukuni rukuni har guda bakwai kafin mu
isa birnin sarki shardas amma sai da muka tarwatsa su muka kashe na kashewa masu gudu
suka tsere dakaru guda arba in kacal muka rasa a cikin wannan gumurzu da la asar sakaliya
muka iso birnin sarki shardas koda muka tsaya a bakin kofar gidan sarautar akaje akayi mana
iso sai sarki shardas yaki fitowa saboda jin izzarsa da takamarsa kawai sai ya turo wani
hadiminsa aka kaimu masauki bayan mun zauna munci abinci muna hutawa sai tunanin gida ya
fado min inda na tuno lokacin da muke yin bankwana da matata luzuraina wacce ke dauke da
tsohon juna biyu.
.
Sa dda ta rungumeni mu biyu ni da yarima huzein ta fashe da kuka tana mai cewa yakai mijina
kayi sani cewa bana son wannan tafiya da zakuyi domin ina bukatarku a kusa dani a yanzu fiye
da ko yaushe ba don komai ba sai don saboda ita haihuwa bata da tabbas zan iya rasa
rayuwata a wannan tafarki ko kuma na rasa abinda na ke dauke dashi haka zan iya rasaku
tunda kuma tafiya zakuyi mai hadari tun a jiya da sarki ya shirya wannan tafiya sai naji zuciyata
ta kama bugawa yadda naga rana haka naga dare ina mai tabbatar muku da cewa ba zan taba
samun sukuni da kwanciyar hankali ba face naga dawowarku lafiya, koda luzuraina ta zo nan a
zancenta sai ni da huzein muka kamu da tsananin tausayinta muka kara kankameta a jikinmu
mukaci gaba da kuka kamar ba zamu daina ba, daga can sai na janye jikina daga cikin nasu na
dubi luzuraina cikin nutsuwa da murmushin karfin hali nace yake matata kiyi sani cewa bana
son nayi wannan tafiya saboda rashin sanin halin da zaki iya shiga amma kuma idan har na bar

sarki yayi wannan tafiya shi kadai zan shiga cikin tashin hankali da wasi wasi akan halin da
shima zai iya shiga don haka dole ne na bishi ko don na bashi kariya ina son ki kwantar da
hankalinki ki sani cewa nayi miki alkawari duk wuya duk tsananin sai na dawo gareki a raye
kuma na dawo miki da yarima huzein cikin koshin lafiya gama fadin hakan keda wuya sai ga
babban hadimina ya shigo cikin falon nawa ya risina gareni yace ya shugabana sarki ya fto ku
kadai ake jira.
.
Koda jin haka sai ni da yarima huzein muka mike tsaye da sauri muka nufi kofar fita, a guje
luzuraina ta sha gabanmu tana kuka ta sake rungumemu sannan ta janye
jikinta ta dubeni tace idan na haihu baka nan wanne suna za a sakawa abinda na haifa ka sani
cewa yarima huzein zai samu kani koda jin wannan batu sai mamaki ya kamani na dubeta nace
yaya aka yi kika san cewa da namiji zaki haifa luzuraina ta ce sau uku ina yin mafarkin na haifi
da namiji don haka ina ji a jikina cewar lallai da namiji zan haifa, sa adda naji wannan batu sai
nayi murmushi sannan na dubi yarima huzein na ce na baka dama ka zabi sunan da za a sawa
kaninka yayin da yazo duniya cikin murna yarima huzein ya daga kansa sama yayi dan tunani
sannan ya dubi mahaifiyata yace ki sawa kanina suna YARIMA BASMAR, kuma kiyi masa
bushara da cewa ya jira yayansa yazo suyi wasa. Lallai nine zan koya masa yadda ake sarrafa
doki da takobi.
.
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa luzuraina ta sake rungume yarima huzein tana
mai sake fashewa da
wani sabon kukan. A dai dai wannan lokaci ne muka jiyo muryar sarki yana mai kwala mana
kira cikin hanzari na fisge yarima huzein daga cikin luzuraina na ja shi da gudu muka fice daga
cikin falon huzein na waigen mahaifiyasa yana hawaye itama tana kuka lokacin da na zo dai dai
nan a tunanina sai yarima huzein ya dafa kafadata na dawo cikin hayyacina yarima huzein ya
dubeni cikin alamun damuwa yace yakai abbana anya kuwa babu wani mugun nufi a zuciyar
sarki shardas a kanmu ?
.
Yakamata ace ya fito ya tarbemu a bisa irin matsayin mahaifinka da daukakarsa a wannan
nahiya amma kuma sai kawai ya aiko da hadimi aka taho damu nan masauki
sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi nace kada ka damu ya kai dana duk wannan ba
komai bane, babu wani mugun abu da sarki shardas zai yi mana, kawai dai wulakanci ne irin
nasa da son nuna isa, koma menene ai da zarar mun isa gabansa za a yita ta kare yaz sallame
mu mu koma izuwa kasarmu burina kawai shine mu koma gida mu iske mahaifiyarka ta haihu
lafiya kafin na rufe bakina saiga sarki ya shigo cikin dakin namu kuyanginsa guda hudu na biye
dashi dauke da abinci cikin hanzari muka zube kasa muka kwashi gaisuwa su kuwa wadannan
kuyangi sai suka ajiye wannan abincin
da abinshan a gabanmu suka juya da baya suka fice sarki ya zauna a gabanmu ya dubemu
cikin annashuwa yace na kasa cin abincina shi yasa na yanke shawarar na zo har nan dominku
muci tare.
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kamamu na dubi sarki nace yakai abbana kai kuwa
menene dalilin daya hanaka cin abinci? Sarki ya yi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kasa

sannan yace tun da muka shigo cikin garin na naji zuciyata tana bugawa abu ne mawuyaci mu
bar garin nan lafiya cikin farin ciki musamman idan muka yi duba da irin karbar da sarki shardas
mana ta wulakanci da rashin nuna muhimmancina a gareshi ya yinda sarki yazo nan a
zancensa sai nayi dariya nace haba yakai abbana akan wane dalili zakayi irin wannan tunanin
alhali mun kasance masu biyayya ga sarki shardas gami da bin umarninsa, ni na san cewa
babu wani tsautsayi da zai same mu lafiya kalau zamu koma gida kawai mu jira muga yadda
zata kasance tsakaninmu da sarki shardas
koda jin wannan batu sai sarki ya saki ransa hankalinsa ya kwanta nan take muka kama cin
abinci cikin raha da nishadi muna ta hira da ban dariya har sai da muka koshi......
.
Wow littafi fa yanzu ya fara tafiya domin yanzu ne zaku san an fara karanta TSATSUBA zakuji
yadda zata kaya tsakaninsu da yadda Ake tsantsan yaudara da cin amana gami da rashin
imani.
.
Kafinnan dai Nidinne
Abubakar Saleh AlQuyraemey
Ke cewa Ku huta Lafiya...
TSATSUBA
Littafi Na Uku (6)
Part C.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Nan take muka kama cin abinci ikin raha d nishadi muna masu hira ta ban dariya har saida
muka koshi.
.
A wannan rana sarki bai koma dakinsa ba anan dakinmu ya kwana saboda ko kadan baya son
nisanta damu sai da muka kwana uku a cikin gidan sarautar sarki shardas amma wai har
tsawon wadannan kwanaki sarki shardas bai kirawo mu ba duk da cewa kullum yana zama a
fada, duk sa adda ya bukaci ya gana da shi sai yace a gaya masa cewa ya kara sauraro a ranar
kwana na ukun ne da safe bayan mun gama kalaci sai ga hadimin sarki shardas yazo mana
take hadimin ya shaidawa mahaifina cewar sarki yace muje mu riskeshi a fada cikin farinciki
muka mike tsaye muka yi shiri sarki ya taramu gaba dayanmu dakarunsa da kuyanginsa
sannan aka debo wadannan bayi guda dubu ashirin gami da akwatunan dukiya guda dubu
muka wuce izuwa fadar sarki shardas fadar ta cika makil ta batse da mutane ko ina ka duba
saikaga fadawa dakaru da manyan attajirai da sauran masu fada aji a kasar.
.
A gefe daya kuma mutanen gari ne maza da mata a durkushe a kas babu wani mutum guda
daya a tsaye ko akan kujera face sarki shardas wanda ke kan karagarsa ta mulki, koda muka
shigo cikin fadar mahaifina na kan gaba muna biye dashi gaba dayanmu sai naga an zubawa
mahaifina idanu kawai mutane so suke su gani shin zai iya durkusawa a gaban sarki shardas ya
kaskantar da kansa? Babu abin takaici sama da ganin yadda mahaifina yayi gagarumar shiga ta

alfarma mai tsananin tsada wacce ta ninka ta jikin sarki shardas sau uku amma kuma gashi zai
kaskanta a gaban dubunnan talakawa a wannan lokaci ina rike da hannun yarima huzein muma
munci ado na kwatance domin ko a cikin fadawan sarki shardas da duk jama arsa babu wanda
ya sa suturar data kai tamu daraja ni da huzein ke bin bayan sarki sai kuma kuyangi da sauran
dakarun da muka taho dasu daga birninmu don yi mana rakiya lokacin da ya rage saura baifi
taku goma ba tsakanin mahaifina da karagar mulkin da sarki shardas ke zaune a kai sai yaja da
baya cak muma da muke bayansa sai dukkanmu muka ja muka tsaya cak a bayansa nan take
mahaifina da sarki shardas suka fara kallon kallo fuskar sarki shardas a murtuke take ko kadan
babu annuri kuma jikinsa ya kama tsuma har fuskar tasa na yin gatsine saboda fishi bisa
tunanin cewa ko mahaifina ba zai durkusa masa ba kawai sai akaga mahaifina ya durkushe
kasa bisa guiwarsa guda ya risina yana mai dukar da kansa ga sarki shardas cikin murya mai
dauke da ladabi yace gaisuwa gareka ya shubana a madadina da al umar kasata nazo domin
mu jaddaja mubaya armu a gareka ya sarkin duniya kuma na amsa kiranka, gani nazo da duk
abinda ka bukata.
.
Koda mahaifina yazo nan a zancensa sai fuskar sarki shardas ta fadada da murmushi ya mike
tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin matukar murna sannan ya tako yazo har inda mahaifina
ke durkushe
ya kama kafaduna ya tashe shi tsaye suka fuskanci juna yace lale marhaban da sarki mai birnin
Askandariyya lallai ka tsira daga dukkan fishinmu kuma daga yau ka zama amintaccenmu nan
take fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki shardas jinjina da kirari bisa ganin yadda sarki
mai daraja da cikakken iko kamar mahaifina ya mika wuya a gareshi a wannan lokaci takaicida
bakinciki suka lullubeni har idanuna suka ciko da kwallah ban sani ba, sarki shardas ya daga
hannu sama sai fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta , A sannan ne sarki shardas ya bushe da
dariyar farinciki ya kirawo wani hadimi nasa mai dauke da tambulan na ruwan giya gami da kofi
guda biyu da zuwan hadimin sai sarki shardas ya dauki kofi guda hadimin ya tsiyaya masa
ruwan giyar sannan ya dubi mahaifina yayi masa tayi, batare da fargabar komai ba mahaifina ya
dauki daya kofin shima aka tsiyaya masa ruwan giyar amma sai yaki yasha.
.
Koda ganin haka sai sarki shardas ya bushe da dariya sannan ya kurbi ruwan giyar har sau biyu
ya dubi mahaifina yace kwantar da hankalinka
abokina ai ba zan shayar dakai guba ba, saboda me kake tsoron shan wannan giya mai albarka
wacce nasa aka yi ta musamma don tarbarka?
Koda jin wannan batu sai mahaifina yayi murmushi yace ai ba komai bane yasa naki sha ba sai
don yin ladabi a gareka kada na rigaka dandana dadinta dajin haka sai sarki shardas ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya kamo kafadar mahaifina ya juyo dashi suka
fuskancemu sarki shardas ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yace wannan danka ne
yarima hulbasu mai jiran gado tare da dansa yarima huzein ko ?
.
Mahaifina ya gyada kai yace kwarai kuwa sune sannan ya dubemu yace kuyi gaisuwa ga.sarkin
duniya, da farko sai na dan noke a lokacin da huzein tuni ya duka kasa ai kuwa sai nan da nan
fuskar sarki shardas ta juye izuwa fishi har sai da nima na durkusa na gaisheshi sannan yayi
murmushi yazo ya dafani ta yadda har muna iya jin numfashin juna ya budi baki cikin karamar

murya yadda babu mai iya jinmu ba sannan yace, Samari nasan abinda kake ji a ranka bisa
kaskantar da kan da mahaifinka yayi a gareni domin jaddada min mubaya arsa amma ina mai
shawartarka da ka zamo mai biyayya idan har baka son daular birnin Askandariyya ta fadi, yana
gama fadin hakan sai ya wuce gabana ya shiga duba bayin da aka kawo masa guda dubu
ashirin har sai da ya tabbatar da cewa gaba dayansu lafiyayyune sannan yaje kan akwatunan
dukiya guda dubu sai da aka bude gaba dayan akwatunan yaga dukiyar dake cikinta nan take
sarki shardas ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dawo wajen mahaifina ya kama
hannunsa ya jashi har zuwa kan karagar mulkinsa suka zauna tare a wannan lokaci fadar tayi
tsit ko tsinke ne ya fadi kasa sai an ji kararsa.
.
Sarki shardas ya dubi mahaifina cikin nutsuwa ya ce ya.batun sharadin da muka gindaya maka
a cikin wasikarmu?
Shin ka amince zaka yi abinda muke so ko kuwa ba zaka bi ba ?
.
Sa adda mahaifina yaji wannan tambaya sai ya risina cikin biyayya yace ya sarkin duniya na
amince da duk bukatarka amma ina neman wata alfarma guda daya, alfarmar kuwa itace ina
son ka rage yawan bayin da zan rinka kawo maka duk shekara da kuma yawan akwatunan
dukiya su koma rabin wadanda na kawo maka yanzu ba don komai ba sai saboda hakan zai iya
kawo karyewar tattalin arzikin kasata domin a halin yanzu bayi sunyi karanci a kasata kuma
bayin nan sune suke yi mana aikin noma a gonakinmu noman kuma shine yake kawo mana
dukiyar da zamu tara mu kawo maka koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata ya
dakawa mahaifina tsawa yace babu ruwanmu da wannan matsala domin kai ta shafa bamu ba
don haka sai ka san hanyar da zaka bi ka nemi bayi koda kuwa sai kayi farautarsu ne a sauran

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login