Showing 6001 words to 8839 words out of 8839 words

Chapter 3 - TSATSUBA 6 Book Complete by Abdulaziz Sani .pdf


kasashen da ke kusa daku ka sani cewa gobe goben nan zan hadaka da wakilina mutum uku
wadanda zaka tafi dasu izuwa fadarka a dinga gabatar da harkokin mulki tare da su domin su
rinka kawo mini
rahoton duk abubuwan dake gudana, a karshe ina mai gargadinka da cewa digon jini daya na
wadannan wakilai nawa dai dai yake da digon jinin saba in na jama arka don haka a kula da su
da kyau kuma a basu
duk abinda suke bukata.
.
sa adda sarki shardas yazo nan a zancensa sai nayi wuf na matso gaba kusa da karagar mulkin
sa na dubeshi nace yakai wannan sarki
ka yi sani cewa idan ka hadamu da wadannan wakilai naka tamkar ka rushe karfin mulkin
mahaifina ne gaba daya tunda ba shi da ikon yin wani sirri a cikin harkokinsa na mulki kuma ba
shi da ikon zartar da komai sai da saninka da amincewarka, wannan ba adalci bane zalunci ne
da kaskantarwa....... Kafin na gama wannan jawabi tuni jikin sarki shardas ya kama tsuma
saboda fishi har gumi ya fara tsatstsafowa daga fuskarsa shi kuwa mahaifina a wannan lokaci
ya firhita ainun so yake ya hanani ci gaba da magana amma ya kasa, kawai sai sarki shardas
ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ya zo daf dani ya zare takobinsa ya dora kaifinta
akan wuyana yana mai ci gaba da tsuma ni kuwa ko gezau ban yi ba.
.
A lokacin gaba dayan mutanen dake fadar sun firgita ainun kowa ka kalla sai kaga jikinsa na

bari don gudun kada laifin wani ya shafeshi, sarki shardas ya daka min tsawa ya ce kai dan
samari kaine mahaluki na farko wanda ya taba shigowa har cikin fadata yayi mini bakar, don
haka yanzu zan kasheka domin na gusar da kishirwar karya wannan lago nawa da kayi, koda
gama fadin hakan sai sarki shardas ya daga takobinsa sama da nufin ya sareni amma sai
mahaifina yayi wuf ya janyeni daga gabansa sannan yayi sujjada a gareshi ya dago kai yace ya
sarkin duniya ina nemawa dana afuwa ka san cewa har yanzu akwai kuriciya a tare da shi.
.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas ya sake bushewa da dariyar mugunta sannan ya mayar
da takobinsa cikin kufe ya dafa kafadata yace samari ka tsira daga kaifin takobina yau, amma
ka sani cewa idan ka sake aikata kuskure irin wannan ba zaka taba tsira ba yana gama fadin
hakan sai ya juya ya fuskanci fadawansa ya kirawo wadansu mutane uku daga cikin dan
uwansa wanda ake kira MUHAIRU wanda ya kasance dan yayarsa sarki shardas ya dubi
muhairu ya ce yakai dan uwana daga yau na cireka daga matsayin gwamnan birnin DAILUFA a
yanzu kaine shugaban wakilaina na birnin Askandariyya saboda haka kaje ka fara shirin binsu
gobe amma kafin goben ina so ka zauna da yarima hulbasu ya sanar dakai iya adadin
biranensu da kauyukansu da kuma duk harajin da suke tarawa a kowacce shekara ka rubuta
komai ka kawo min.
.
Muhairu ya risina yace an gama ya shugabana kawai sai sarki shardas ya juya ya fice daga
fadar ya wuce izuwa cikin gidan sarautarsa, shi kuwa muhairu sai ya zo gabana ya tsaya yana
mana wani irin murmushi na mugunta da raini ya dubeni yace ka saurari zuwana nan da lokaci
kankani yana gama fadin hakan sai ya kyalkyale da dariyar mugunta ya wuce abunsa sauran
wakilai guda biyu na take masa baya suma suna kyalkyala mana dariya.
.
Nan take dakarun sarki shardas suka ingiza keyar bayin da muka kawo guda dubu ashirin aka
wuce dasu izuwa can wani bangare na gidan sarautar sarki shardas, kuma aka kwashe
Wadannan akwatunan dukiyar da muka kawo , A sannan ne fadar ta watse ya zamana cewa
daga mu sai jama armu kacal a tsaye cikin tsananin bakin ciki da takaici. .
A dai dai wannan lokaci ne zuciyata ta kama tafarfasa kamar zata kone ban san sa adda na
kurma uban ihu ba mai tsananin firgitarwa na durkushe kasa ina mai fashewa da matsanancin
kukan bakin ciki.
.
Al amarin daya janyo hankalin dakarun sarki shardas kenan suka zare takubba suka rugo izuwa
kanmu, koda suka ganni durkushe a kasa ina
kuka sai suka kama dariya suka tafi suka barni a wannan lokaci ne mahaifina da yarima huzein
suka durkusa a gabana sa adda suma suka fara zubar da hawayen bakinciki kawai sai sarki ya
rungumeni tare da fashewa da kuka sosai mu duka sai muka kama kukan, sai da muka dan
jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan muka mike tsaye muka tafi izuwa masaukinmu....... .
Wow Zan dakata A wannan guri saikuma Allah ya kaimu Gobe
zan cigaba daga nan. Amma kafinnan Nidinne Dai Abubakar Saleh AlQuyraemey Angon farar
mace alkabbar mata.

TSATSUBA
Littafi Na Uku (6)
Part D.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.
Sai da muka dan jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan ka mike tsaye muka tafi izuwa
masaukinmu.
...Bayan mun isa masaukinmu mun zauna cikin bakinciki muna tunanin wannan hali da muka
tsinci kanmu a ciki na takaici da wulakanci, sai sarki ya dubeni a lokacin da hawaye ya zubo
masa yace yakai dana ka yi sani cewa wadannan sharadai da sarki ya gindaya mana sai sun
janyo fari da talauci a kasarmu kuma wannan shine lokacin da na dade ina tsoron gani a
rayuwata fadin hakan keda wuya sai sarki ya fara wani irin tari mai karfi kafin a jima kuwa sai ya
kama aman jini cikin rudewa na kwallah ihu ina mai kiran likitan sarkiwanda muka taho tare
dashi tun daga birninmu domin duba lafiyarmu, nan da nan wata kuyanga ta ruga taje ta kirawo
likitan yazo ya shiga duba mahaifina dan ceto rayuwarsa da kyar likitan ya samu ya shawo kan
cutar sarki ya tsayar da jinin dake zuba a bakinsa sannan kuma ya bashi magani ya sha faruwar
hakan keda wuya cikin dakika kadan nannauyan barci mai karfi ya sace sarki a wannan lokaci
ne ni da huzein muka dawo cikin hayyacinmu na dubi likitan sarki cikin alamun mamaki nace
yakai likita wannan wane irin ciwo ne ya sami mahaifina alhalin ina tare dashi tsawon shekaru
amma ban taba ganinsa a cikin irin wannan hali ba sai yau.
.
Koda jin wannan batu sai likitan ya sunkui da kansa kasa yayi shiru kamar ba zaice komai ba
har sai da na daka masa tsawa sannan ya dago kai ya dubeni a tsorace bakinsa na rawa yace
ka gafarceni ya shugabana ka sani cewa sarki ya haneni da na sanar da kai komai dangane da
rashin lafiyarsa, sa add anaji wannan batu sai na sake fusata na zare takobina na dora kaifinta
akan wuyan likitan nace na rantse da darajar sarki idan baka sanar dani wannan al amari ba
yanzun zan kashe ka.
.
Koda jin haka sai jikin likitan ya kama tsuma ya budi b baki cikin in ina ya ce tun ranar da
wasikar sarki shardas ta iso birninmu na askandariyya fadar mahaifinka yaji sakon da ta kunsa
a lokacin ya kamu da ciwon zuciya ina mai sanar dakai cewa wannan ciwo yana da tsananin
hadari domin zai iya zama sanadin ajalinsa a ko yaushe cikin kankanin lokaci muddin zai rinka
fuskantar abinda zai bata masa rai koda likita yazo nan a zancensa sai na durkusa kasa na
fashe da matsanancin kuka.
.
Al amarin da ya karya zuciyar yarima huzein kenan, shima ya fashe da kuka nan take naji na
tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma na kudurce a raina cewar in dai wannan ciwo
ya zamo sanadin ajalin mahaifina sai na yaki sarki shardas gaba da gaba duk da na san cewa
hallaka zanyi muna cikin wannan haline muka ji an kwankwasa mana kofa sai ga wakilin sarki
shardas kuma dan uwansa mubairu ya shigo cikin dakin da muke, koda ya ganmu muna kuka

kuma ya ga sarki a kwance a gefe daya yana barci ga likita zaune a kusa dashi sai yayi dan
guntun murmushi sannan ya dubeni yace yakai yarima hulbasu ka sani cewa nazo ne gareka
domin ka sanar dani abubuwan da sarkina ya umarceka daka sanar dani domin na rubutasu
nakai masa, koda jin haka sai na dago kai na dubeshi cikin tsananin fishi nace ashe baka da
hankali da nutsuwa?
.
Kana ganin halin da mahaifina yake ciki ne zaka zo min da wannan maganar banzar ? Ta yaya
kake tsammanin zan iya maka bayani a yanzu bayan ina cikin tashin hankali da damuwa, koda
jin haka sai ran mubairu ya baci ya daka min tsawa mai karfi tare da nunani da dan yatsa yace
babu ruwana da batun halin da mahaifinka yake ciki domin kuwa umarnin sarkina na gaba dashi
maza ka sanar dani abinda nazo sani kafin fishin sarki ya tabbata a kanka yana gama fadin
hakan sai ya zauna a kusa da ni ya fiddo littafi, tawada da alkalami domin yin rubutu
ni kuwa sai na tattare hannun rigata kamar zan zauna a gabansa amma sai na shammaceshi
na gabza masa wawan naushi a fuska sabo da karfin naushin sai da ya wuntsila da baya sau
uku a lokacin da jini yai feshi daga cikin bakinsa, ai kuwa sai ya taso da alkafira yai tsalle ya
doki tawa fuskar da kafarsa, nima na gwaru da bango na fasa baki kafin na mike tsaye ya
danneni kuma ya zaro wata wuka zai caka min a kirjina sainayi wuf na rike hannunsa, a sannan
ne likita da sauran
hadimanmu suka kurma uban ihu suka ruga waje da gudu suna kiran dakaru domin su kawo
dauki, yarima huzein ne kadai tsaye a gabana yana kallon abinda ke faruwa jikinsa na karkarwa
sabo da tsananin razana mubairu yaci gaba da kokarin dannan wukarsa a cikin kirjina, ni kuma
naci gaba da kokarin hanashi samun nasara, amma sai karfinsa ya rinjayi nawa har wukar tasa
ta dan sokeni na kwalla ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da naji, a lokacin da jini ya fara
bulbulowa daga cikin kirjina duk wannan abu dake faruwa sarki na kwance a gefe daya yana
shara barci bai sani ba.
.
Koda yarima huzein yaga saura kiris mubairu ya sami nasarar hallakani sai yai wuf ya zare
wuka a jikinsa ya dako tsalle sama ya sokawa mubairu a wuya take wukar ta lume ta faso
makogwaronsa ya sulale
kasa matacce huzein ya sunkuya a rikice ya kama Wukar tasa domin ya zareta daga cikin
wuyan mubairu.
.
A dai dai wannan lokaci ne dakaru sarki shardas suka rugo izuwa cikin dakin su da yawa rike da
makamai, koda suka ga yarima huzein yana zare wuka a cikin wuyan muhairu kuma gashi ya
zama gawa sai suka yi caraf suka daureshi ni kuwa sai na taso da sauri izuwa kansu na hausu
da sara da suka domin na kwaci dana a hannunsu duk da cewa suna da yawa amma sai da na
tarwatsa su na kashe sama da mutum arba in ina cikin tsakiyar yin yaki dasu ne naji anyi min
wani wawan duka a kirji saboda karfin dukan sai da nayi sama na gwaru a jikin katangar dakin
na fado kasa a galabaice lokacin dana farfado sai na tsinci kaina a tsakiyar fadar sarki shardas
kwance a kasa.
.
A gefen damata yarima huzein ne a daure cikin sarka a haguna kuma mahaifina ne tare da
dukkan dakarunmu da kuyanginmu suma duk a daure cikin sarka zaune akan karagar mulki

sarki shardas ne rungume da gawar dan uwansa muhairu yana ta faman rusa kuka, nan take
zuciyata ta buga da karfin gaske na kamu da tsananin tsoro irin wanda ban taba jinsa ba a
rayuwata ba komai ne ya sa ni jin wannan tsoro ba face tunanin cewa sarki zai kashe mune
gaba dayanmu, idan ya kashemu kuma matata luzuraina ta mutu a wajen haihuwa shike nan fa
duk burinmu ya tarwatse kuma lokacin faduwar kasarmu yazo a dai dai wannan lokaci ne
yarima huzein ya dubeni a lokacin da hawaye ya zubo masa yace yakai abba na ka gafarceni
domin na janyo mana abinda zai kawo karshen mu gaba daya.
.
Sa adda naji wannan batu sai hawayen takaici ya zubo min na dubeshi nace yakai dana baka
bukatar rokona gafara domin baka aikata laifin komai ba tabbas ka kashe muhairu ne domin ka
ceci rayuwata babu wani da da zai bari a kashe mahaifinsa a gaban idanunsa muddin zai iya
hanawa. .
Koda jin wannan batu sai mahaifina ya dubi yarima huzein cikin alamun tsananin tausayi a
lokacin da shima hawaye ya zubo masa yace yakai jikana huzein hakika kayi babban kuskure
daka ceci rayuwar mahaifinka a hannun muhairu domin hakan zai janyo asarar da babu abin
da zai biyata gama fadin hakan ke da wuya sai sarki shardas ya mike tsaye daga kan karagar
mulkinsa ya ajiye gawar muhairu akan karagar sannan ya share hawayansa ya dubi mahaifina
fuskarsa a murtuke sannan ya dubeni kuma ya dubi huzein yace yaro ka kashe mini dan uwa
wanda shi kadai ne ya rage mini a duniya inda zan kashe gaba dayan mutanen kasarku
mazanku da matanku jininku ba zai goge bakincikin abinda na rasa ba zan dasawa mahaifinka
bakin cikin da har ya mutu ba zai manta da ni ba domin hakan ne kadai zai sa zuciyata ta lafa
daga ruruwar wutar bakinciki.
.
Koda gama fadin haka sai sarki shardas ya sa aka kwanceni daga cikin sarkoki sannan ya zare
wata sharbebiyar wuka ya cillo mini ita na cafe kuma ya zare takobinsa yace nine na doki
kirjinka dazu ka suma sa adda kake kashe dakaruna.
.
Koda ka manta cewa na gaya maka cewa digon jinin daya na wakilaina da zan tura birninku dai
dai yake da digon jinin mutanenku saba in to ku sani cewa a yanzu jinin mutum saba in ba zai
zamo fansar dan uwana ba abinda nake bukata shine ina son uba ya yanka dansa da
hannunsa yanzu a gabana ko kuma na kashe ka da dukkanin jama arsa gaba daya. .
Koda jin wannan batu sai mahaifina ya fashe da kuka ya risina ga sarki shardas kuma ya zube
kasa gaba daya ya yi masa sujjada sannan ya dago kai ya dubeshi a lokacin da hawaye ke
shatata bisa kumatunsa ya kuma dubi gaba dayan fadawan sarki shardas da mutanan gari yace
yakai sarkin duniya ka dubi yadda na kaskanta kuma na wulakanta haka a gaban talakawanka
a matsayina na sarkin da ya gawurta a wannan nahiya tamu ka dubi darajarr sarauta ka canja
wannan nufi naka, koda jin haka sai sarki shardas ya girgiza kai yace ai bana yin magana biyu
na gama yanke hukunci ko danka ya yanka nasa dan yanzu take ko kuma na kasheka a gaban
idansa kuma na kashe gaba dayan dakarunka da kuyanginka da duk hadimanka, mahaifina ya
fashe da kuka yace yanzu jinina ni kadai ba zai fanshi jinin dan uwanka ba ?
.

Sarki shardas ya dubi katon badakarensa mai rike da wata katuwar gudumar danko yace dashi
yakai KALBAN ka buga gangarka sau goma idan yarima hulbasu bai yanka dansa ba kafin
bugu na goma zan kashe mahaifinsa da duk jama arsa.
.
Koda jin wannan umarni sai kalban ya daga gudumarsa ya doki wata katuwar ganga dake
rataye a jikin wani dogon karfe take sautin gangar ya cika birnin gaba daya a dai dai wannan
lokaci ne huzein ya kama jan guiwarsa kasancewar a daure yake cikin sarka ya iso gabana ya
kwanta kasa ya dubeni yana mai murmushi gami da zubar da hawaye yace yakai abbana ma za
ka yankani domin ka kubutar da mahaifinka da jama armu.
.
Ka sani cewa zan mutu a cikin farin ciki tunda da jinina ya zama fansa ga rayuka masu yawa a
wannan lokaci kalban yaci gaba da buga gangarsa har yayi bugu na biyar, sa adda naji wannan
batu na dana huzein sai hawaye ya zubo mini na dubeshi nace ka gafarceni yakai dana kayi
sani cewa zan yanka ka ne ba don na ceci rayuwata ba ko ta ubana ba sai don Rayuwar jama
armu ga su can wadanda suka sallama rayuwarsu don biyayya a garemu lallai ina son su koma
gida a raye domin su rungumi iyalinsu.........
.
BABBAR MAGANA KENAN
.
SHIN HULBASU ZAI YARDA YA YANKA DANSA YARIMA HUZEIN ?
.
IDAN YA KASHE SHI IDAN YA KOMA BIRNIN ASKANDARIYYA MAI ZAICE DA
MAHAIFIYARSA ?
.
SHIM MAHAIFIYAR YARIMA HUZEIN TANA HAIHUWA LAFIYA?
.
INA LABARIN JARUMA SIYAMA DASU YARIMA HULKAS ?
.
Marubucin Littafin Yace Mu Hadu A Littafin Tsatsuba Na gaba Don Jin Ci Gaban Wannan
Kasaitaccen Labari.
Marubucin Littafin Wato
The King Of Adventure Story
Malam Abdul aziz Sani M/Gini
Saikuma Ni Abubakar Saleh AlQuyraemey wanda nake jagorancin typing din wannan littafi nake
cewa Mu zama lafiya saimun hadu a littafi na bakwai....
Dont Forget My Name

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login