Showing 1 words to 3000 words out of 10473 words
Chapter 1 - TATSUBA 7 Book Origal by Madakin Gini .pdf
TSATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part A
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Posting by..
Abubakar Saleh AlQuyraemey
Lokacin da Sarki Hulbasu ya gama fadawa dansa yarima Huzein wannan bayani sai ya rufe
idanunsa a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa ya yanga
Yarima Huzein tare jini yai tsartuwa daga cikin wuyan huzein a lokacin da Hulbasu ya kurma
uban ihu na takaici da bakin cikin ganin cewa ya yanka dansa da hannunsa shi kuwa mahaifin
Sarki hulbasu wato Sarki yana
ganin sa adda Hulbasu ya yanka yarima huzein da hannunsa sai nan take ya hadiyi zuciya ya
sulale ya baje a kasa matacce.
.
Koda sarki hulbasu yaga mahaifinsa ma ya mutu kuma ga gawar dansa yarima huzein a
gabansa sai ya kama sambatu yana kai kawo a tsakanin gawarwakin biyu tamkar mahaukaci
sabon shiga shi kuwa sarki Shardas sai ya bude da dariyar farin ciki yayi ta kyalkyala dariyar
tamkar ba zai taba dainawa ba da sarki hulbasu yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa hailur
sai yayi shiru sa adda hawaye ya zubo masa yana hada idanu da hailur sai yaga shima hawaye
ke sartu akan kumatunsa yana mai kurawa hulbasu idanu cikin tsananin tausayawa.
.
Hailur yaja dogon numfashi yace tabbas cin zarafin da sarki shardas yayi maka ya ninka nawa
saboda kai ya tilastaka ka yanka danka da hannunka kuma ya zamo sanadin mutuwar
mahaifinka kuma yanzu gashi ya mai daku bayinsa tunda duk arzikin kasarku wajansa yake
komawa, hakika damu daku yanzu bamu da wani makiyi a doron kasa wanda yafi sarki
shardas, kuma a halin yanzu yafi karfinmu babu abinda zamu iya yi masa kuma muna cikin
mugun hadari na masifarsa domin da zarar ya fahimci cewa ina raye kuma ina tare dakai mu
duka har iyalanmu tamu ta kare, koda hulbasu yaji wannan batu sai yai ajiyar zuciya cikin
alamun tsananin fargaba da takaici sannan sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone, yace to yanzu shike nan haka zamu cigaba da zaman jiran ranar da
sarki shardas zai gano sirrinmu sannan yazo ya gama damu hailur ya girgiza kai yace babu
wani abu wanda ba zai yiyu ba a cikin wannan duniya face ba a jarraba shiba komai nisan jifa
kasa zai fado kuma komai karfin mutun da isar mulkinsa akwai ranar da zai fadi babu wata cuta
wacce bata da magani kamar yadda boka zamaranu ya shaida maka cewa zaka iya hallaka
sarki shardas amma sai an mallaki hular lamsara to me zai hana mu tafi neman wannan hula
tunda ance mai nema yana tare da samu gwara mu rasa rayukanmu a kokarin neman wannan
hula da dai mu zauna har makiyinmu yazo ya samu nasarar hallaka mu muna ji muna gani ka
sani cewa ba karamin aiki bane a gabanmu idan har muna son mu ga bayan wannan babban
makiyi namu dolene sai mutum ya sadaukar da wani abu idan yana son ya sami wani da farko
dai dolene ka ajiye sarautarka kuma ka cire dukkan tsoro daga cikin zuciyarka dolene mu kawai
da gaba dayan dakarun sarki shardas da hadiman da suka rako matata domin mu aiwatar da
abinda ke gabanmu ka ayyana a ranka cewa zamu fita neman hular lamsara ne ba don komai
ba sai domin mu dauki fansa akan sarki shardas shin yanzu zaka iya hakura da karagarka ta
mulki da kuma kasarka da jama arka domin cika wannan buri naka?
.
Koda jin wannan batu sai hawayan takaici ya zubowa sarki hulbasu yace ai bani da wani zabi
wanda yafi na hakura da komai din nayi wannan gagarumar tafiya in ba haka ba kuwa zan rasa
komai da kowa nawa yanzu akwai abu daya nake tunanin yadda zamu sami nasarar yinsa a
cikin nasara wato yadda zamu iya kawai da dakarun da suka rako shadila, .
Koda jin wannan batu sai hailur yayi murmushin yake yace haba ya shugabana a cikin kasarka
fa suke wadannan dakaru ai kowa a gida sarkine, ni ina da shawara bisa yadda zamu kawai da
su cikin kankanin lokaci a saukake ba tare da mun fuskanci wata matsala ba shawarar kuwa
guda biyu ce da farko zamu iya amfani da sanya musu guba a cikin abincinsu duk suci su mutu
idan kuma wannan hikima bata yi aiki ba sai mu ritsasu a cikin masaukinsu mu da dakarun
masu yawan da ya ninka nasu sau uku mu yakesu, ni ka bar mini jagorancin dakarun da za suyi
wannan aiki iana mai tabbatar maka da cewa zan yi iya kokarina na tabbatar da cewar dayansu
bai tsira da rayuwarsa ba don kada yaje ya kai wa sarki shardas labarin abinda muka aikata,
lokacin da sarki hulbasu yaji wannan shawara guda biyu na hailur sai yaja dogon numfashi gami
da ajiyar zuciya kuma ya dubeshi cikin
alamun damuwa da fargaba sannan yace da farko dai idan muka yi yunkurin kashesu da guba
ba lallai bane ya kasance cewa dukkaninsu zasu ci abincin kaga kenan akwai yiyuwar wani
daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa kuma ya sulale daga cikin birnin ya gudu bamu sani ba idan
kuwa hakan ta faru asirinmu ya gama tonuwa haka kuma muka ce zamu yakesu anan cikin
birnina a masaukinsu jama a zasu jiyo kururuwar yakin koda kuwa cikin dare ne sannan kuma
ka san cewa suma fa zakwakuran mayaka ne wadanda suka san TUGGUN YAKI za a iya
samun wani daga cikinsu ya sami damar sulalewa ya gudu idan ma hakan bata faru ba babu
mamaki a cikin jama ar gari akwai dan leken asirin sarki shardas mai sa ido akan wadannan
dakaru Nasa da suka rako gimbiya shadila izuwa kasata don haka ko wani dan motsi ya gani
wanda bai yarda dashi ba yana iya garzayawa yakai labari, lallai akwai mummunan hadari a
cikin duk wadannan batu sai ya numfasa yace ya kai abokina yakamata ka sani cewa matsoraci
bashi zama gwani ko waye don haka dolene mutum ya siyar da ransa wajan neman sa a bisa
bukatar dake gabansa ko ka so ko kaki ko ka gudu ko ka tsaya watarana sai sarki shardas yazo
ya cika da yaki har gida tinda shi makiyi har abada a cikin kokarin ganin bayan makiyinsa yake.
.
Lokacin da hailur yazo nan a zancensa sai jikin sarki hulbasu yayi sanyi ya gamsu a ransa
cewar bashi da wani zabi wanda yafi ya yi amfani da wannan shawara ta hailur don haka sai
yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubeshi
yace na amince da duk shawarar da ka bani a daren yau zan hadaka da amintaccen sarkin
yakina domin ku shirya duk abinda kuke ganin ya dace akan wannan makiyi namu nidai kawai
na baku wuka da nama amma ina son ku gaggauta shirya yin wannan gagarumar tafiya tamu ta
neman hular lamsara.
.
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube hailur yayi godiya sannan ya mike tsaye da nufin
ya fice daga cikin dakin sai sarki hulbasu ya ruko hannunsa yace ya zaka tafi baka tsaya
kagana da tsohuwar matarka ba babu wanda ya isa ya raba Hanta da jini soyayyarka da
matarka shadila tafi gaban wani dan adam ya rubuta saboda tsoron sarki shardas ba zan
hanaka ka gana da ita ba tuni na shirya wannan ganawa naku. .
Koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya tafi zuwa bakin
kofar wannan daki da suke zaune ya kira sunan wani hadimi
nasa yace dashi ya ruga izuwa can cikin gidan sarautar bangaren matarsa ya taho da shadila
cikin hanzari hadimin yace an gama ya shugabana nan take ya ruga da gudu izuwa cikin gidan
sarautar shi kuwa sarki hulbasu sai ya yiwa Hailur sallama ya tafi tafiyarsa keda wuya sai farin
ciki mai dumbin yawa ya turnuke hailur yaji kamar duniyar nan gaba daya aka bashi don haka
sai ya mike tsaye ya kama kai kawo fuskarsa cike da annuri gami da farin ciki wanda ba zai
misaltu ba yana cikin wannan haline yaji an turo kofar dakin an shigo cikin sauri ya waigo kawai
sai yayi arba da shadila a tsaye ta kura masa idanu tana zubar da hawaye daki daki nan take
shima idanunsa suka ciko da kwallar ya fara zubar da hawaye tsawon yan dakiku sun kurawa
junansu idanu suna ta zubar da hawaye kamar ba zasu daina ba daga can kuma sai suka yi
murmushi a tare suka ruga suka rungume junansu kuma suka fashe da kukan farin ciki na sake
saduwa suna masu kankame juna sosai ba tare da son saki juna ba sai shadila ta ce yakai
mijina yanzu ashe kana nan raye a cikin wannan duniya amma ban sani ba?
.
Koda jin wannan tambaya sai hilairu ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna yace
yake abar begena dare da rana kiyi sani cewa ban taba mancewa dake ba tsawon dakika daya
daga sa adda muka rabu kawo i yanzu ban taba zaton cewa zamu sake saduwa ba a cikin
wannan duniya tunda ke kanki kin sa a ranki cewa na mutu na sani cewa sarki shardas ya
aureki bisa dole to amma abu daya nake so na gani shin kin haife cikin dana dana barshi a tare
dake ko kuwa sarki shardas ya kasheshi.
.
Koda jin wannan tambaya sai shadila tayi shiru ta kasa bashi amsa cikin hanzari hailur ya janye
jikinsa daga cikin na shadila ya girgiza kafadunta ya ce cikin daga murya ki gaya mini gaskiyar
ala amari kada ki boye mini komai shin dana yana raye ko ya mutu koda jin haka sai shadila ta
fashe da kuka ta kasa bayani saboda tsoron abinda zai biyo baya kwatsam sai sukaji an turo
kofar dakin an shigo duk su biyun
suka waiga bayansu a firgice da sauri don ganin ko wane ne ya shigo ba wani bane face yarima
Hulkas tsaye idanunsa suna zubar da hawaye kuma ya kurawa hailur idanu koda shadila taga
hulkas tsaye a gaban hailur kuma taga irin kallon da yake yi masa har yana zubar da hawaye
sai ta kamu da tsananin tsoro jikinta ya kama tsuma saboda ta fahimci cewar abinda take tsoron
kada ya faru ya gama faruwa.
.
Cikin sanyin jiki da alamun tsananin takaici hulkas ya nufi inda shadila ke tsaye a lokacin da
hailur yabi hulkas da kallo ko kiftawa baya yi domin ya gane cewa lallai wannan yaro hulkas
dansa ne domin hatta irin gabobin jikinsa iri daye ne nan take shima hailur yaji idanunsa sun
ciko da kwallah lokacin da hulkas ya iso daf da shadila sai ya kama hannayanta ya ruke yace
yake ummina menene dalilin da yasa tuntuni baki shaida mini cewa sarki shardas ba shine
mahaifina ba, kinsan irin tsananin son da nake yiwa sarki shardas, kuma kinsan yadda na
shaku da shi ainun tun ina kankani kawo i yanzu, yanzu da wanne ido zan fuskanceshi A
matsayin babban makiyina Alhalin shine ya rene ni ya inganta rayuwata ki sani cewa sarki
hulbasu ya bani labarinki kaf da asalinki da yadda sarki shardas ya murkushe jama arku kuma
ya jefe mahaifina karkashin wannan tsauni mai mugun zurfi sannan ya kamaki da karfin tsiya ya
Maisheki matarsa har da dub irin barazanar da yake yi miki akan kada ki sanar dani komai
sannan ya sanar dani yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dansa na cikinsa sanadin da
ya zamo mutuwar mahaifinsa ya kunsa masa bakin cikin da har abada ba zai gushe ba a doron
kasa tabbar sarki shardas ya cika babban azzalumi da babu kamarsa a doron kasa kuma
dolene na kasheshi da hannuna, koda yarima Hulkas yazo nan a zancensa sai ya kurma uban
ihu kuma ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa biyu ya fashe dda matsanancin kuka koda ganin
haka sai itama shadila ta fashe da kuka ta kasa rarrashinsa cikin sanyin jiki hailur ya dingisa ya
isa gaban hulkas ya sunkuya ya dafa kafadar hulkas, koda hulkas yaji hannun hailur ya tabashi
sai yai shiru tamkar daukewar ruwan sama sannan ya dago kai suka kurawa junansu idanu a
lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai
hulkas ya mike tsaye zumbur ya rungume hailur suka fashe da kuka a tare komai rashin
tausayin mutum idan yaga lokacin da wannan da da mahaifinsa suka rungume junansu alhalin
basu taba ganin juna ba basu san juna ba sai yau dolene zuciyarsa ta karaya ya tausaya musu.
.
Koda ganin abinda ya faru sai farin ciki ya lullube shadila sai da hailur da hulkas suka dan jima
a kankame da juna sannan hailur ya janye jikinsa daga cikin na hulkas ya dubeshi a cikin
nutsuwa yace yakai dana ina son ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka sani cewa komai
yana da lokacinsa ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu in da duniyar nan gaba daya
zata taru kaf ba zata iya kawar da sarki shardas ba saboda yana kan sharafinsa babu mai iya
ganin bayansa a yanzu face jarumin da ya mallaki HULAR LAMSARA; .
Bisa wannan dalili ne ni da sarki Hulbasu muka yanke shawarar mu rokeku kuma mu kawar da
dukkanin dakarun da suka rakoku sannan mu bazama duniya neman Hular lamsara saboda kai
kanka yanzu rayuwarka na cikin mugun hadari idan har shardas ya gano ka san cewa shine ya
tarwatsa rayuwar mahaifinka na asali ba zai barka da raiba to amma akwai wata matsala guda
daya, koda jin wannan batu sai hulkas ya dubi hailur cikin alamun matukar mamaki yace yakai
abbana me cece matsara kuma Hailur yace sarki shardas ma ba zai iya hallaka ka ba face ya
samo wannan hula ta Lamsara kuma a halin yanzu tuni shida bokansa sun fita farautar wannan
hula sun bar garinku a cikin mugun hali domin yanzu haka ana fama da fatara yunwa da fari a
kasar tun daga ranar da kuka baro birnin kai da mahaifiyarka ya zamana wajibi mu gaggauta
tafiya neman hular lamsara tun
gabanin makiyinmu sarki shardas ya rigamu samu.
.
Koda jin wannan batu sai hankalin yarima Hulkas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa
dadi a duniya musamman da yaji cewar mutanan kasarsu na can cikin mugun hali na fatara da
yunwa kuma ga batun gagarumar tafiyar dake gabansa ta neman hular lamsara hular da babu
wanda ya san inda take.... .
Kai bari dai na dakata A nan domin nima naje nayi shirin tafiya neman wannan hula saboda
naga Alamar sun tsorata suna tsoron fita nemanta amma akwai wanda zai iya rakani kuwa
hahahaha
Kafin nan Nine
Abubakar Saleh AlQuyraemey
Samaja
TSATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part B.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Hular da babu wanda ya san ina take...Shikuwa yarima barmas tunda suka shigo cikin wannan
daki tare da yarima hulkas ya zauna a gefe daya yana ta sauraran bayanin da Hailur ke yiwa
hulkas sai takaici da tausayi suka sashi ya kama zubar da hawaye dama da dadewa mahaifin
sarki hulbas ya bashi tarihin yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dan uwansa yarima
Huzein wato yaya ga yarima barmas sanadin da ya zamo na mutuwar kakansa kenan nan take
zuciyar yarima barmas ta kama tafarfasa kamar zata kone babu abinda ya tsana a duniya sama
da sarki shardas A cikin wannan haline aka ga kofar dakin ta sake budewa saiga Hulbasu tare
da matarsa Luzuraina da kuma jaruma siyama
tare da mahaifiyarta zalina har da sadauki ruhaisu tsohon yaron hailur.
.
Koda ruhaisu yayi arba da hailur sai ya kamu da tsananin mamaki kawai sai ya ruga gareshi
suka rungume juna cikin farin ciki mara misaltuwa suka kama kyalkyala dariyar murna sannan
ruhaisu ya janye jikinsa daga cikin na hailur ya risina a gareshi cikin girmamawa yace ya
shugabana ko a mafarki ban taba zaton zan sake ganin wannan fuska taka ba bare har na
rungumi jikinka mai daraja ka sani cewa har yanzu akwai sauran jama armu da yawa suna
rayuwa a boye cikin dazuzzukan wannan birni da muke ciki.
.
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake lullube hulkas yace nayi matkar farin ciki da jin
wannan albishir naka kuma lallai ina bukatarka tare da sauran wadannan jama a tamu, ka sani
cewa ga shadila Allah ya dawo mun da ita don haka akwai gagarumin aiki dake gabanmu
wannan yaro da kake gani wato yarima hulkas shine dan da nabar shadila tana dauke da
cikinsa.
.
Koda jin wannan batu sai hawayan farin ciki ya zubowa ruhaisu ya ruga wajan hulkas ya
rungumeshi a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas ya dubi siyama sa adda hawaye ya zubo
masa sannan ya bude hannayansa yace da ita ' ashe ke yar uwata ce ban saniba?
.
Taho gareni yake yar uwata rabin jiki cikin matukar murna siyama ta ruga izuwa ga hulkas suka
rungume junaa. A sannan ne zalina da shadila ma suka durfafi junansu suna murmushin
saduwa suna haduwa sai suma suka rungume junansu zalina na kuka tace yake gimbiya hakika
kaddara ce ta rabaki da mijin kwarai wanda babu kamarsa a wajena a cikin dukkan mazajen
duniya amma tunda gashi yanzu ubangijinmu ya dawo miki dashi inaso mu hadu mu biyu nida
ke mu bashi farinciki irin wanda bamu taba bashi ba a rayuwa ki dauka cewa yaune wannan
dare na farko na amarcinku ehm keda shi don haka na baki kwanaki goma domin jiya ta dawo
yau.
.
Koda jin wannan batu sai shadila ta sake kankame zalina a kirjinta da kyau cikin matukar farin
ciki tana mai yi mata godiya, nan take sarki hulbasu ya dubi matarsa luzuraina yace dake da
shadila da zalina ku tafi ku bamu wuri zamu yi ganawa ta musamman mu shida dinn nan ba
tare da wata gardama ba kuwa sai matan uku suka fice daga cikin dakin suka bar sarki hulbasu,
hailur da sadauki ruhaisu, siyama da