Showing 6001 words to 9000 words out of 10473 words
Chapter 3 - TATSUBA 7 Book Origal by Madakin Gini .pdf
kullum sai ya zagayetan ma ana dai
baya zama waje daya tamkar shanshani komai karfin sihirin tsafin boka bai isa ya iya ganin a
inda aljani arwasul masadul yake ba kuma bai isa ya kirashi ya amsa kiransa ba haduwa da
aljani arwasul masadul sai babban rabo da sa a kawai neman Aljani arwasul masadul dai dai
yake da neman jaki mai kaho idan kuma har mutum yayi dace haduwa dashi tofa duk abinda ya
bukata daga gareshi indai akwai shi a cikin wannan duniya to zai kaishi inda abin yake a cikin
kankanin lokaci Inda matsalar take shine aljani Arwasul masadul baya yawo a cikin siffarsa
gaskiya Littafin nan nikaina da nake typing dinshi duk da na jima da karantashi yana sake
kayatar dani uhm kufa ? Yakan rikida ne izuwa siffar bil adama sau tari ko ta dabba ko ta kwaro
don haka sai mutum yaci jarrabawarsa sannan yake taimakonsa babbar illar aljani arwasul
masadul itace ba a rudarsa da dukiya ko mace ko mulki, kuma bashi da tausayi ko jin kai shi
kawai yana da wadansu ka'idoji ne wadanda sai ka cikasu sannan zai taimakeka kuma dole sai
ya zauna tare dakai tsawon kwana uku yaga ka cika ka'idojin babu wanda yasan wadannan
ka'idoji na aljani arwasul masadul, baya ga haka aljani arwasul masadul yana da karfin damtse
na rikakkun zakuna guda dubu dari da tamanin kuma duk duniya babu mai karfin sihirinsa na
tsafi amma wani abin al ajabi a tare dashi shine babu abinda ya tsana sama da kudi ko mulki
kuma babu abinda yake so sama da jarumi mara tsoro kuma mai sa a ya kai dan uwana kai
mutum ne mai tsananin sa a bisa duk abinda kasa a gabanka sannan kuma na fuskanci cewa
ko kadan baka da tsoro bisa wannan dalili ne nake da yakinin cewa zaka mallaki hular lamsara
kafin sarki shardas ya fita nemanta, ka sani cewa sammako anema ba shine samu ba kai dai
kawai ka nemi sa a da dace, lokacin da jaruma siyama tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas
ya kamu da tsananin mamaki ya dubeta yace yaya akayi kika san duk wadannan al amura koda
jin wannan tambaya sai siyama tayi murmushi tace na taba haduwa da Aljani Arwasul masadul
kuma na cinye jarrabawarsa a lokacinda nake yawon farauta a cikin daji kuma nayi mu amala
da shi ta tsawon kwana uku ba tare da na san ko shi waye ba lokacin da yagabatar da kansa a
gareni kuma ya fito mini a siffarsa ta ainihi sai ya tambayeni abinda nake bukata a cikin wannan
duniya ya kaini inda abin yake domin na mallakeshi.
.
Koda naji wannan tambaya daga gareshi sai nayi murmushi nace abinda nake bukata ba zaka
iya bani shi ba cikin mamaki aljani arwasul masadul ya dubeni yace ke yarinya kin yi babban
kuskure da kika fadi haka ki sani cewa komai yawan dukiyar da kike bukata zan kaiki inda take
kuma na kwasheta nakai ta inda Kikeso a cikin dakiku kadan idan mulki kike so na kowacce
kasa a cikin wannan duniya zan iya baki shi koda karfin tsiya a cikin dakiku kadan ke idan ma
duniyar gaba daya kike sonki mulka zan iya yi miki sanadin hakan to menene kuma abinda kike
ganin cewa zai iya gagarata sa adda naji wannan batu na aljani arwasul masadul sai nayi
murmushi a karo na biyu nace yakai wannan aljani ka sani cewa duk abinda ka ambata bana
bukata ko daya daga cikinsu face ina son ka hana aikata zalunci a doron kasa a tsakanin al
ummar mutane da aljanu da kuma tsakanin dabbobi da kwari sannan ka hana zubar da jini a ko
ina na duniya ya kasance duk duniya kowa na son kowa ana zaman lafiya babu batun sata ko
kwace babu fyade kuma babu bambanci tsakanin attajiri da talaka da kuma tsakananin bawa da
sarki wadannan abubuwa sune kadai cikar burina na duniya idan har ka har ba zan gansu da
idanuna ba bana fatar nayi doguwar rayuwa a cikin wannan duniya domin takaicin rashinsu ne
zai zama babban bakin cikina.
.
Koda nazo nan a zancena sai naga hawaye ya zubowa Aljani Arwasul masadul yasa
hannayansa biyu ya dafa kafaduna ya ce kece bil adama ta farko a duniya data taba burgeni a
cikin jinsin mata kuma ban taba haduwa da mai irin wannan ra ayi naki ba ba wani abu bane
yasa kika ga na zubar da wannan hawaye baface takaicin kin tambayeni abinda har na mutu ba
zan iya samarwa da wani shi ba ina mai tabbatar miki da cewa aduniya ba za a taba zama
lafiya ba domin a hakan ta fara kuma a hakan zata kare wannan shine tarihin da na riska a
wajan kakana na dari da ashirin kuma nayi imani da wannan tarihi, yake wannan jarumar mata
hakika ba zan taba mancewa dake ba a rayuwata domin ni a wajena kece jarumar jarumai
wadda bata damu da komai na duniya ba yaune ranar karshe ta saduwata dake kuma ba zaki
sake ganina ba har izuwa ranar da zan mutu ko ke ki mutu amma ina fatan nayi miki taimako a
sirrance ba tare da kin sani ba kafin karshen rayuwata ina mai yi miki fatan nasara da sa a a
rayuwarki bisa wannan buri naki da naji kin ambata daga yau nayi alkawarin cewar ba zan sake
zaluntar wani bil adama ba a doron kasa kuma ba zan taba taimakon wani azzalumi ba amma
lallai ki bar wannan al amari sirri karki gayawa kowa face jarumin da kika tabbatar da cewa
shine zai kawo karshen zalunci, shugaban azzalumai na wannan zami a cikin jinsinku na bil
adama da wannan furuci nake yi miki bankwana na karshe.
.
Koda aljani Arwasul masadul yazo nan a jawabinsa sai hawaye ya zubo mini na rungumeshi ai
kuwa sai naji shima ya fashe da kuka daga can kuma sai haji babu shi a jikina ina bude idanuna
na nemeshi sama da kasa na rasa yau shekara uku kenan da faruwar wannan al amari kuma
ban taba baiwa kowa labarin abinda ya faru ba sai yanzu da nake sanar dakai saboda zuciyata
ta yarda kuma ta aminta cewa kaine jarumin da zai kawo karshen zaluncin shugaban azzalumai
na bil adama wato sarki shardas.
.
Koda siyama tazo nan a zancenta sai yarima hulkas yaji gaba daya tsigar jikinsa ta tashi kuma
yaji cewa a zuciyarsa ta aminta da duk abinda siyama ta fada dari bisa dari saboda haka sai ya
sake kamo hannayanta ya rike yace yake yar uwata kiyi mini Alkawarin cewar zaki kasance a
tare dani a cikin wannan doguwar tafiya da zamuyi ta neman hular lamsara kuma zaki taimakeni
da ranki da dukkan karfinki kuma babu abinda zai rabamu face mutuwa domin a yanzu ne na
tabbatar da cewa kece rabin jikina idan babuke babu abinda zan iya aiwatarwa na dangane da
babban burin dake gabana saboda ra ayina ya kasance iri daya da naki kinga kenan burinmu
duk iri daya ne ni dake.
.
Koda jin wannan batu sai siyama ta rungume yarima hulkas ta fashe da matsanancin kuka. Al
amarin daya karya zuciyar sa ke nan shima ya fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi
wani a cikinsu.
.
Lokacin da dare ya soma yi ne wata kuyanga ta taho turakar gimbiya luzuraina ta risina ta
kwashi gaisuwa gareta sannan tace ya shugabata sarkine ya aikoni nayi muku jagora zuwa
dakin walima ke da amarya shadila koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube luzuraina da
shadila dama tunda aka watse aka barsu su biyu suna ta hira ko gyangyadi basuyi ba tuntuni
duk su biyun sun caba ado don haka sai suka mike tsaye zumbur da nufin su fita amma sai
shadila ta rike hannun luzuraina suka tsaya ta dubeta tace ba zan iya zuwa wannan dakin
walima ba face bisa jagorancin abokiyar zamana zalina don haka sai dai mu biya ta dakinta mu
tafi tare, koda jin wannan batu sai luzuraina tayi murmushi tace ai rashin hakuri kikayi ai dole ne
mu nemi sa hannun uwar gida a cikin wannan al amari don haka muje gareta yanzu Nima kuma
bari naje ga neman kudina yanzu.
.
Kafinnan Nidinne dai
AlQuyramey
Littafi Na Bakwai (7)
Part D.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa sai luzuraina ta kama hannun shadila tajata suka fice daga
cikin dakin itama wannan kuyanga da tazo domin tayi musu jagora izuwa dakin walimar sai ta
koma bayansu sukayi ta ratsawa ta gaban dakarun dake tsaron gidan sarautar suna wucewa ta
cikin kofofi. .
Abinda ya daure musu kai shine a wannan dare gaba daya hadiman gidan sarautar babu su
wadanda komai dare a cikin kai kawo suke suna gabatar da ayyukansu su kansu dakarun
tsaron a yau sun kasance kalilan basu da yawa kuma sune amintattu wadanda koyaushe suna
tare da sarki basa rabewa. .
Koda ganin wannan sauyin yanayi sai mamaki ya turnuke shadila ta dubi luzuraina a cikin dan
alamun tsoro tace yake kawata menene dalilin daya sa naga komai na gidan nan ya sauya a
wannan dare ba haka na saba ganin abubuwa suna gudana ba, koda jin wannan batu sai
luzuraina tayi murmushi tace ba komai ne ya kawo haka ba face tabbatar da sirrin daurin
wannan aure da zai gudana daga sanin makiyanmu.
.Tsatsuba Na 1 Complete Littattafin Yaki By Abdulaziz Sani M/Gini |
https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-1-littattafin-yaki.html
Koda jin haka sai farinciki ya lullube shadila ta kama murmushi tayi shiru bata ce komai ba,
haka dai suka cigaba da tafiya suka iso kofar dakin da zalina take, da isowarsu sai luzuraina ta
kwankwasa mata kofar tace yake uwargidan hailur ki fito ki raka amaryarki izuwa ga angonta
kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni an bude kofar dakin kawai sai suka ga zalina tsaye a
gabansu ta caba ado na gaban kwatance tamkar itace amaryar kuma fuskarta cike da annuri
gami da murmushi kana kallonta ka san cewa
tana cikin matukar farin ciki tana ganin shadila sai ta rungumeta tamkar wacce taga yar uwarta
ta jini sannan ta kama hannunta tajata suka yi gaba tana mai cewa muje na damkaki a hannun
masoyinki na kwarai koda jin wannan batu sai shadila da luzuraina suka cika da mura nan take
wannan kuyanga ta shige gaba tayi musu jagora izuwa dakin walimar, falo ne babba mai
matukar tsawo da fadi wanda sarki hulbasu ke yin babban taro a cikinsa musamman a lokacin
da ya gaiyato manyan baki daga kasashen duniya babu kowa a cikin wannan babban falo face
sarki hulbasu hailur da yarima hulkas dakuma jaruma barmas sai kuma amintattun hadiman
sarki hulbasu
da amintattun kuyanginsa gaba daya teburan dake cikin wannan falo an cika samansu da kayan
alatu na abinci dana shaye shaye kala kala na alfarma babu irin kalar da babu, a gefe daya
kuma wadansu makadane da mawaka na sarki suma amintattunsa ne wadanda babu yadda za
ayi su bayyana sirrinsa domin tun zamanin kakansa suke yin wannan aiki. .
A can wani bangare na daban kuma wadansu kyawawan yan mata ne su takwas sanye cikin
fafaren tufafi wadanda suka kasance yan rawa sun kama tamkar gumaka da babu ruhi a jikinsu
koda shigowar amarya shadila da su zalina cikin wannan babban falo sai makada suka fara
wani irin kida mai taushi da dadin gaske su kuma wadannan yan mata yan rawar dake kame
suka fara yin rawar Mawakan kuwa sai suka kama rera wata irin waka mai dadi suna ambaton
sunan shadila suna kodata gami dayi mata kirari nan take wannan al amari yayi matukar burge
kowa a wajan Abdul Aziz sani Madakin gini yace' Hatta ni da nake baku wannan labari ban san
sa adda na kama yin rangaji ba ina jin waninirin nishadi da farinciki a zuciyata'
.
Bayan mawakan sun gama koda amarya shadila saikuma suka kama wasa ango hailur shima
suna yi masa kirari bisa irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa tamkar a gabansu komai ya
wanzu dolene abin ya burge mutum saboda irin hikimar da aka yi amfani da ita kuma dole ne
mutum yaji ya kamu da tsananin tausayin wannan ango da amarya domin kuwa a takaice aka
bayar da tarihin soyayyarsu da yadda aka rabasu da karfin tsiya hatta sarki hulbasu dasu
yarima hulkas basu san sa adda suka kama zubar da hawaye ba marubucin littafin ma yace
Nikaina a yanzu naji idanu na sun ciko da kwallah ana cikin yin wannan waka ne falon yayi tsit
tamkar babu wani mahaluki daya mai numfashi a cikinsa sakamakon tsayuwar masu kida da
wakar suma yan matan nan yan rawa suka kame kam.
.
A dai dai wannan lokaci ne kofar falon ta bude sai ga sadauki Ruhaisu ya shigo tare da wani
dattijo wanda shima asalinsa dan kabilar su hailur ne
kai tsaye suka nufi inda hailur da shadila suke suka kamo hannayansu suka taho dasu izuwa
tsakiyar falon suka daura musu sabon aure bisa al ada irin tasu faruwar hakan keda wuya sai
yanayin sararin samaniya ya sauya nan take ya zama tamkar na damina hadari ya gangamo
aka fara wata irin TSAWA DA WALKIYA mai tsananin ban tsoro. A dai dai lokacinne da wannan
abu ya faru sarki shardas na cikin wani kurgurmin daji tare da bokansa abin dogaronsa sun
yada zango a cikin wani kogon dutse suna barci amma ana tafka wannan tsawa sai sarki
shardas ya farka firgigit A firgice zuciyarsa na daka da karfi, babu abinda ya fado masa a Rai
face matarsa shadila, take yaji a jikinsa cewa lallai wani abune ya faru ga shadila domin
wannan tsawa da walkiya da aka tafka ba na zahiri bane ishara ce, Aljanunsu na tsafi suka yi
masa bisa abinda ya faru cikin gigita sarki shardas ya tashi bokansa daga barci ya dubeshi
yace yakai abin dogarona kayi sani cewa lallai akwai wani abu ya sami matata shadila maza ka
duba mini abinda ke faruwa.
.Tsatsuba Na 1 Complete Littattafin Yaki By Abdulaziz Sani M/Gini |
https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-1-littattafin-yaki.html
Koda jin wannan batu sai bokan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi sarki
shardas cikin nutsuwa yace ya shugabana ai dama tun kafin mu baro gida idan baka manta ba
na gaya maka cewa a cikin wannan tafiya da yarima hulkas zaiyi ne zai sami damar da zai iya
cutar da kai to ka sani cewa duba maka wannan al amari ba zai haifar da komai ba face
dakushe maka zuciya gami da karyar da ita akan babban aikin dake gabamu na nemo inda
hular lamsara take ka sani cewa baka da wata mafita wacce tafi ka hanzarta mallakar wannan
hula ta lamsara kafin makiyanka su rigaka lallai kana da babbar dama ta samun haka tunda ka
rigasu fitowa neman nata amma ko yaya ka darsa batun soyayyarka akan shadila a cikin ranka
to lallai zaka rasa nasara.
.
Koda bokan yazo nan a zancensa sai hankalin sarki shardas ya dugunzum ainun fiye da ko
yaushe ya dubeshi a fusace sa adda zuciyarsa ke tafarfasa yace ka gaya mini cewa mun fito ne
neman wani Aljani wai shi arwasul masadul kuma tunda muka baro gida muke ta keta
dazuzzuka birane da kauyuka barkatai amma ko alamun wannan aljani bamu gani ba bamu san
yaushe zamu hadu da shi ba, kuma bamu san a inda zamu ganshi ba anya kuwa baka ganin
cewa wahalar banza muke yi ?
.
Koda sarki shardas yazo nana a zancensa sai bokan ransa ya baci yace ashe akwai ranar da
zaka yi kokwanto akan abinda zan gaya maka shin ka manta ne cewa nine na tsareka na baka
dukkan kariya daga sharrin dukkan makiyanka tun kafin ka hau karagar mulki shin ka manta
cewa zuri ar gidanmu sun shafe sama da shekaru dari suna bauta a gidanku cikin amince da
kauna ??
.
Babu yadda za ayi na bata yaudararka ko na gaya maka karya dolene ka kasance mai hakuri
gami da juriya komai dadewar shekarun da zamu yi muna yin wannan tafiya kafin mu hadu da
aljanu Arwasul masadul koda kuwa sai mun tsofe tukuf fatanmu dai shine nasara da sa'a.
.
Koda gama fadin hakan sai bokan ya koma ya kwanta yaja bargonsa ya lullube jikinsa gaba
daya saboda hunturun sanyin dake kadawa a cikin dajin
yaci gaba da barci abinsa tamkar a cikin dakin matarsa yake a lokacinn da kuune baya jin
sautin komai face na manyan dabbobin daji ababan tsoro shi kuwa sarki shardas saboda
zuciyarsa na suya don tsananin fushi idanunsa sun bushe babu alamar jin barci kuma ko kadan
baya jin uban sanyin da ke kadawa haka dai ya zauna yana ta tunanin zuci gami da wasu wasi
a ransa bisa yin abinda yake ganin cewa shine zai fishsheshi wata zuciyar tace dashi : wai shin
yama za ayi ace duk irin wannan masifaffen karfin damtsen nawa da kuma karfin sihirin tsafi
ace ba zan iya kashe wannan yaro hulkas ba ?
.Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini |
https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-2-littattafin-yaki-na.html
Wai shin ma menene dalilin da yasa duk abin da wannan bokan yazo mini
dashi sai na amince shin bokaye basa yin karya ko kuskure ne a bincikensu da furucinsu,?
.
Aljanu ne fa suke sanar dasu komai kuma su kansu aljanun suna shirya karya kuma suna yin
son zuciyarsu kamata yayi na yi watsi da shawarar wannan boka akan batun neman wannan
hula ta lamsara kawai na juya da baya na tafi izuwa birnin hulbasu naje na kama yarima hulkas
a gaban mahaifiyar tasa shadila nayi masa yankan rago duk da cewa ina kaunarsa !! .
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa kuma wata zuciyar tasa ta
daka masa tsawa tace shin baka da hankali ne yanzu kana nufin kace zaka yanka yaron da ka
raina da hannunka wanda ka kaunaceshi tamkar dan cikinka, idan