Showing 3001 words to 6000 words out of 10473 words

Chapter 2 - TATSUBA 7 Book Origal by Madakin Gini .pdf

hulkas da kuma barmas sannan kuma sai nan take
dukkaninsu suka zauna tsawon yan dakiku dayansu bai ce uffan ba can sai sarki hulbasu yayi
gyaran murya yace abinda yasa na taraku a nan shine kowannanku ya san cewa gimbiya
shadila tazo nan birnina tare da tsaro na dakarun sarki shardas su dubu bisa jagorancin
SADAUKI MARZANU, yanzu ina son na ajiye mulkina na tafi neman HULAR LAMSARA domin
mu kare kanmu gaba daya daga sharrin sarki shardas don haka ina neman shawararku bisa
yadda zamu yi dasu sadauki marzanu a mataki na farko da kuma yadda zamu kai ga cimma
burinmu lallai ina son kowannanku ya bude kwakwalwarsa yayi tunani mai kyau.
.
Koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai fara yin
magana koda ganin haka sai Hulkas yayi gyaran murya ya dubi sarki hulbasu cikin natsuwa
yace ya shugabana ni shawarar da zan bayar itace kada muce zamu kawar da su sadauki
murzamu a nan cikin birninka kawai a bari a gama kammala wannan gasa ta jarumtaka sai muyi
shiri gaba dayanmu a matsayin zamuyi musu rakiya izuwa can karshen gari muna isa can
saimu shammacesu mu afka musu mu kawar dasu gaba dayansu, mu tabbatar da cewar
dayansu bai tsira da rayuwarsa ba amma idan mukace anan cikin wannan gidan sarauta zamu
yakesu babu mamaki akwai yan leken asirin sarki shardas anan cikin garin wadanda suka sa
ido akan su murzanu wanda da zarar abu ya samesu zasu iya gaggauta sanar da sarki
shardas, koda hulkas yazo nan a zancensa sai ruhaisu ya dubi hailur da sarki hulbasu yace a
matsayina na wanda ya dade yana jagorantar mayakan hari na sumame na yarda da shawarar
yarima hulkas dajin haka sai hulbasu da hailur suka yi murmushi sannan sarki hulbasu ya dubi
hailur yace yau nima zan fara shirye shiryen wannan tafiya a sirrance ba
tare da kowa ya sani ba sai a ranar da zamu tafi ne zan tara yan majalisata na sanar dasu
cewar zan raka gimbiya shadila izuwa ga kasarta don tsoron kada a sami wata matsala.
.
Akan hanya na fuskanci fishin mijinta kuma nan take zan bar galadima jiran karagata saboda
shine kadai mutumin dana tabbatar da cewar zai iya rike amanata idan kuma akwai wani mai
wata shawarar ne a cikinku ya fada.
.

Koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai jaruma siyama tayi murmushi tace ina so ku sani
cewa sai munyi taka tsantsan sosai akan dukkan shirinmu saboda maso abinka yafika dabara,
kuma ma su iya magana sunce kifi na ganinka mai jar koma, ina mai tabbatar muku da cewa
sadauki marzanu da sauran dakarunsa mutum dubu biyu ba kanwar lasa bane domin sun zuba
ido sosai akanmu ko yaya suka ga wani mosti wanda basu yarda dashi ba sai sun dauki mataki,
abu na biyu kuma shine sarkin yaki sadauki darkus ma yanzu dolene su sa ido akanmu gaba
daya musamman bisa ganin cewa sarki ya bani kariya nida iyayena shin bakwa tunanin cewa
zasu iya hada kai dasu sadauki murzanu domin gano sirrinmu.
.
Koda jin haka sai sarki hulbasu ya girgiza kai yace tabbas hakan zata iya faruwa amma zanyi
amfani da damata ta sarki nima nasa amintattuna su zuba ido akansu suyi nazarin dukkan
motsinsu da shirye shiryensu abinda nake so daku shine mu dukkannan jarumaine don haka
ina son kowa ya jajirce iya yinsa a ranar da zamu gama dasu sadauki marzanu domin mu
tabbatar da cewar gaba dayansu ba wanda ya tsira mu bar ganin cewa zan tanaji amintattun
dakaruna masu yawa a ranar da zamu fita wannan yaki wadannan mutane suna da matukar
hadari da wannan furuci nake sallamarku amma banda abokina hailur.
.
Koda jin haka sai kowa ya mike tsaye ya nufi kofar fita daga cikin dakin amma banda yarima
hulkas domin tsayawa yayi yana ta kallon hailur har saida sarki hulbasu ya dubeshi yace kada
ka damu yakai yarima yau tare da mahaifin naka zaka kwana don haka kabi abokinka barmas
nan da wani lokaci ma a cikin daren yau zamu sake haduwa gaba dayanmu. .
Koda jin wannan jawabi sai yarima hulkas yayi murmushi sannan ya juya da sauri ya fice daga
cikin dakin fitarsa keda wuya sai sarki hulbasu da hailur suka mike tsaye Hulbasu ya kama
hannun hailur lafiyayyen ya jashi yana dingisa daya kafar suka fice daga cikin dakin suka durfafi
wani bangare daban a cikin gidan sarautar yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wani babban falo
wanda aka kawatashi ainun da shimfidu na koren kilishi da kuma korayen kujeru manya na
alfarma kai ! Hatta labulayen dakin koraye ne komai a wajen kore abin gwanin ban sha awa
babu mutum ko daya a cikin wannan katon falo kuma ga shi tsaf tsaf sannan an zuba kayan
Alatu iri iri a cikinsa masu tsananin ban sha awa akwai dakuna guda bakwai a cikin wannan falo
gami da kewaye guda biyar kowanne daki an sanya luntsumemen gado a cikinsa mai dauke da
shimfidu masu taushin gaske, su kansu kewayen sama da kasansu da jikin bangwayensu
dutsen lu'u lu'u ne kuma bahon wankan a cikinsu na zinare ne cike da ruwa mai kamshin
turaren miski ga furanni kala a cikinsa sai da sarki Hulbasu ya zagaya da hailur cikin gaba
dayan wadannan dakuna da kuma makewayin duka sannan ya dubeshi yace yakai abokina
anan nake son kaci amarcinka da matarka ta farko shadila.
.
Koda jin wannan batu sai mamaki turnuke hailur yace haba ya shugabana ya nida nake talaka
ba dan kowa ba zakace na zauna a cikin irin wannan kasaitaccen daki alhalin ni gaba dayan
rayuwata ma a daji nayi ta lokacin da sarki hulbasu yaji wannan batu sai nan take yaji ya kamu
da tsananin tausayin hailur har lwallah ta cika masa ido amma sai ya dubeshi cikin murmushi yana mai dafa kansa yace yakai abokina shin ka manta ne cewa kai shugaba ne
guda na kabila babba kaima sarkine kuma bana fidda ran cewa nan gaba zaka zama sarki don

haka komai kyan daki da cikar kawarsa dai dai ne dakai, ni yanzu zan tafi izuwa ga iyalina ka
zauna a nan ka jira Uwargidanka shadila zata zo ta riskeka nan ba da dadewa ba amma ka sani
akwai walima ta musamman wadda na shirya a tsakanin iyalina da naka iyalin kadai domin
tayaka murnar sake saduwa da danka da matarka a cikin daren yau don haka kayi zaton amsa
gayyata koyaushe, koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya juyaya fife daga cikin
kasaitaccen falon ya bar hailur a tsaye yanata kalle kalle cikin tsananin farin ciki domin ji yake
kamar a yau an mallaka masa komai
dake cikin wannan duniya.
'' '' ''
A can turakar gimbiya luzuraina kuwa wato matar sarki hulbasu tuni ta zauna tare da gimbiya
shadila zalina da siyama an kawo musu gasashshen naman kaji da yayan itatuwa suna ci suna
hira cikin nishadi amma kuma hankalin shadila a tashe yake domin ta kasa cin komai ta sunkui
da kanta kas tana tunani a lokacinda zuciyarta ke ta bugawa da karfi cikin alamun tsananin
tsoro da fargaba.
.
Koda luzuraina ta lura da halin da shadila ke ciki sai ta kama
hannayanta ta rike ta dubeta cikin alamun nutsuwa tace yake kawata wai shin wane irin tunani
mai zurfi kike yi ne haka wanda har ya hanaki sukuni ?
.
Koda jin wannan tambaya sai shadila tayi doguwar ajiyar zuciya. Sannan ta dubi luzuraina dasu
siyama tace a cikinku
kaf babu wanda yasan sharrin sarki shardas sama dani yaki dashi dai dai yake da mutum daya
jal yace zai tari gaba dayan halittun duniya saboda karfinsa da sharrinsa ya wuce tunanin mai
tunani, ta yaya kuke zaton cewa gaba dayanmu nan zamu iya tsira daga sharrinsa alhalin ya
fimu duk wani abu da muke takama dashi. .
Koda jin wannan batu sai luzuraina ta numfasa tana mai dafa kafadar shadila tace yake kawata
kiyi sani cewa masu iya magana sunce mai laya ya kiyayi mai zamani !
.
Ko shkka bana yi cewar komai nisan jifa kasa zai fado a saboda haka dole ne karen bana yayi
maganin zomon bana
ki sa a ranki cewa wannan yaki ne tsakanin Gaskiya Da Karya da karfin gaskiyar mu ne zamu
sami nasara akan wannan babban azzalumi wanda ya dade tsawon shekaru yana cutar da al
umma haka dai luzuraina tayi ta kwantar da hankalin shadila tana lallabata har ta shawo kanta
taci abinci ta koshi suna kammala wannan cin abincine sarki hulbasu da hailur suka shigo cikin turakar.
.
Koda ganinsu sai kunya ta kama shadila ta sunkui da kanta kas ta kama murmushi na murna da
farinciki ita kuwa zalina sai ta mike da sauri ta tarbi su sarki hulbasu tana mai yi musu barka da
zuwa sannan ta dubi hailur cikin raha da zolaya ta ce to ango saboda doki ma ba zaka bari
nakai maka amaryar taka ba shine ka biyota ? .
Caraf sai sarki hulbasu ya tari numfashin hailur ya dubi zalina yace ke kuwa waya gaya miki

cewa ta zama amaryar tasa ai dole ne da farko mu warware auren dake tsakaninta da sarki
shardas sannan a daura mata sabo da hailur a sannan ne ta cika amaryarsa, tuni na gama
shirya yadda za a tafiyar da bikin wannan aure a yau din nan cikin dare za a kara gabatar da
gagarumar walima. .
Koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya kama hailur da shadila har dama yarima dasu
siyama sarki hulbasu ya dubi luzuraina yace dama wannan sakon muka zo mu sanar da ku
kawai don haka idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku izuwa can inda za a
gabatar da ita, AlQuyramey nake cewa haka kuma idan lokacin cigaba da wannan littafi yayi
zakujini wato dai Gobe kenan.


.
TSATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part C.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku izuwa inda za a gabatar da ita, koda
gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya kama hannun hailur suka juya suka fice daga cikin
turakar, fitarsu keda wuya sai shadila ta rungume zalina tana mai cewa godiya a gareki mara
adadi yake abokiyar zamana domin na san cewa duk wannan shiri naki ne tabbas kin dawo mini
da farin cikin rayuwata wanda ya fiye mini komai a cikin wannan duniya kiyi sani cewa koda
zan sami dare daya ne jal na wannan farin ciki na mutu ya fiye mini shekaru dubu da zanyi nan
gaba na zauna tare da babban makiyi shardas.
.
Koda zalina taji wannan batu sai tausayin shadila ya turnuketa har hawaye ya zubo mata ta
sake kankameta a jikinta tace yake abokiyar zamana kiyi sani cewa dole ne nasoki kuma na
kaunaceki dari bisa dari kuma na san martabarki a cikin zuciyarsa kece masoyiyarsa ta farko a
rayuwa kece kika sha wahalarsa duk da cewa nima nayi wahala dashi amma ai kin kunshi
bakincikin dako rabinsa ni ban kunsa ba sa adda shadila taji wannan batu na zalina sai taji
itama ta kamu da sonta fiye da ko yaushe don haka sai ta kara kankameta a jikinta suka kama
kukan murna yayinda yarima hulkas da jaruma siyama suka ga haka si suma suka kamu da
tsananin tausayin iyayen nasu har hawaye ya zubo musu a tare, kawai sai siyama ta kama
hannun hulkas ta ja shi suka fice daga cikin dakin suka nufi wani bangare daban a cikin harabar
gidan sarautar sai da suka iso wani fili mai fadi inda babu jama a wanda ya kasance mai shirun
gaske sannan suka zauna tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan siyama tayi
gyarar murya tace yakai dan uwana kayi sani cewa nayi matukar farinciki dana san cewa ashe
ina da dan uwa a cikin wannan duniya wanda muke uba daya. A farkon haduwata dakai naji ina
sonka So irin wanda mace ke yiwa namijin da take fatan zama abokin rayuwarta amma yanzu
da na gane cewa kai muharramina ne sai naji nafi kaunarka fiye da ko yaushe a matsayinka na

jinina don haka
kukanka kukana ne kuma farincikinka nawa ne mahaifin nan namu ya dade yana bani horon
yaki saboda kawai na dauki fansa akan ubanka na karya wato sarki shardas ko a bayan ransa,
shin yanzu zaka bani hadin kai mu hada karfi da karfe domin cika wannan bavvan buri na
mahaifin mu? .
Ka sani cewa raina ba a bakin komai yake ba akan wannan al amari shin zaka iya cire soyayyar
sarki shardas dake cikin ranka ka kasheshi da hannunka.
.
Koda siyama tazo nan a zancenta sai idanun yarima hulkas suka ciko da kwallah nan da nan
hawaye ya kama sartu akan kumatunsa, Al amarin da ya karya zuciyar siyama ke nan ta
rungumeshi kuma itama ta fara kukan cikin sanyin jiki hulkas ya janye jikinsa daga cikin nata
suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye hulkas yace yake yar uwata
kiyi sani cewa bazan iya cire son sarki shardas daga cikin zuciyata ba amma zan iya kasheshi
da hannuna ba don komai ba sai domin a halin yanzu babu mutumin da na tsana sama dashi a
doron kasa na tsaneshi ne saboda zaluncin da yayiwa iyayena da kuma munafurtata da yayi ya
rinka wahalar da mahaifiyata tsawon shekaru da shekaru amma yana nuna mini cewa shi
masoyinta ne na kwarai, ban taba sanin cewa har dukanta yake yi ba a boye a bayan idanuna,
shin yanzu ke a cikin zuciyarki kina da yakinin cewa zamu iya gano inda Hular Lamsara take
har mu mallaketa mu sami damar da zamu dauki fansa akan sarki shardas alhalin bamu san a
inda take ba kuma bamu san wanda ya san inda take ba.
.
Koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jaruma siyama taja dogon numfashi sannan ta
kama hannayansa biyu ta rike suka kurawa juna ido sannan tace yakai dan uwana kayi sani
cewa a cikin wannan duniya babu abinda ba zai yiyu ba face wanda ba a jarraba yinsa ba shin
baka da labarin yadda akayi JARUMI HANTARU ya sami nasarar dauko Takobin SAIFUL
LUJARA ? yasha bakar wahala kuma yasha
gwagwarmaya da manyan sadaukai irinsu RABBASU wadanda suka fishi karfi amma saboda
sa a da naci gami da rabo sai da yakai ga gaci.
.
Shin baka da labarin jarumin nan mai mashin GALILUL HARAS ? wato SADAUKI SHADDADU
shima yasha bakar wuya gami da gwagwarmaya kafin ya mallaki wannan mashi to a yanzu ma
ina ji a jikina cewa kaine jarumin da zai mallaki HULAR LAMSARA sai dai kuma ......
.
Koda siyama tazo nana a bayaninta sai muryarta ta shake da kakarin kuka ta kasa karasa
abinda take son fada ta fashe da kuka sosai al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin
yarima hulkas kenan ya sake rungumeta a kirjinsa yana mai cewa haba yake yar uwata menene
na kuka me zaki boye mini alhalin ni dan uwanki ne na jini to ki sani cewa na san abinda kike
boye mini wannan abu ba komai bane face duk wanda ya mallaki wannan hula ta lamsara sai
ya rasa rayuwarsa kuma a tafarkin SOYAYYA zai hallaka kamar yadda ragowar JARUMAN
DUNIYA biyu suka hallaka. Tuni na dade da jin tarihin wannan manyan makaman yaki guda uku
kuma na sani cewa nine na ukun nasu nasan cewa mutuwa zanyi to amma ki sani cewa ni
yanzu nayi matukar farin ciki da ya kasance bake bace masoyiyar da zan mutu a tafarkin

soyayyarta ba ke yanzu yar uwata ce ta jini wadda na tabbata da cewar ko bayan raina zata iya
kula da mahaifiyata lokacin da yarima hulkas yazo nan a jawabinsa sai jaruma siyama taji
kaunasa ta kara linkuwa a cikin ranta don haka sai ta sake rungumeshi suka fashe da kuka
gaba dayansu sai da suka dan jima kankame da junansu sannan jaruma siyama ta janye jikinta
daga cikin na yarima hulkas ta mike tsaye kawai sai ta juya masa baya tace wane shiri ka fara yi
domin ka kai ga wannan matsayi na zama JARUMIN DUNIYA na uku mai
hular lamsara?
.
Yakai dan uwana kayi sani cewa ba a zama wane a banza dole sai an sha bakar wuya da tarin
gwagwarmaya, koda jin haka sai yarima hulkas ya mike tsaye yasha gaban siyama yace yanzu
wane irin shiri kike nufi zanyi ?
.
Jaruma siyama tayi murmushi tace dole ne ka cigaba da baiwa kanka HORON YAKI har ka
sami wanda zaka iya zuwa inda hular lamsara take ka daukota a halin yanzu bincike ya nuna
cewa kai da sarki shardas kuna bukatar wannan hula ta lamsara kafin dayanku ya sami nasarar
hallaka daya shi dai sarki shardas a halin yanzu yana da karfin da zai iya zuwa wannan wuri da
hular lamsara take bisa taimakon bokansa to amma inda matsalar take shine dashi da bokan
nasa basu san a inda hular lamsara take ba sai dai kuma akwai wanda suka nema wanda shine
kadai zai iya yi musu jagora izuwa wajen ba wani bane ba wannan jagora nasu face wani
hatsabibin Tsohon Aljani wanda a halin yanzu duk fadin duniya babu Aljanin da yafishi yawan
shekaru babbar magana yafi kowa sanin sirrin wadannan manyan makaman yaki guda uku
wato takobin saiful lujara, mashin galilul haras
da kuma hular lamsara shidai wannan tsohon aljani ana kiransa da suna ARWASUL
MASADUL.
.
Aljani Arwasul masadul yana da tsananin karfin gudu a cikin sararin samaniya domin daga
birnin hindu yana iya zuwa birnin sin a cikin abin da bai wuce sa a biyu da rabi ba don tafiyar da
bata wuce ta kwana talatin ba kuwa a cikin abinda
bai wuce wasu yan dakiku ba yake kammalata ya kasance bashi da takamaiman wajan zama
kuma yana iya zagaye duniya kaf a cikin yini daya kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login