Showing 15001 words to 18000 words out of 31021 words
Chapter 6 - SIGN MARRIED BOOK 3 BY OUM HAIRAN .pdf
saba da ƙwaƙuleta
bazai iya jurewa rashinta ba" har sukaje gidan bai tsaida mafita ba ya riƙe hannunta daka ganta
kasan a firgice take sai hawaye kawai da yakebin idanunta, a kulle suka tarar da kofar ya danna
pin ɗinta ta buɗe wani ƙauri ya daki hancinsu dukkansu tayi baya da sauri saboda aman da taji
ya taso mata daidai lokacin Samha ta shigo gidan ita da Deen suka shiga shi kuma ya tsaya
gurinta Saida ta gama ta tashi sannan suka nufi cikin gidan nasu abin mamaki ko ina na
parlourn a shirye yake tsaf yanda suka barshi TV tanayi amma babu hoto sai wani ja da scream
ɗin yayi da wani irin gurnani me kaɗa hantar ciki da yake tashi a gurin, ƙara shigewa tayi jikinsa
bakinta bai daina ambaton Allah ba inda ta kafe TV da ido, gurnanin yana ƙara yawa har ya cika
É—akin gabaki É—aya inda TV ta kawo maimakon hoton mutane sai wani shirgegen maciji wanda
ya zarce girman TV, abinda ya kuma kaÉ—a musu ciki yanda macijin yake gashi a cikin TV ya fito
amma a hankali yake ƙara girma yana mamaye parlourn suka kuwa zubawa sarautar Allah
idanu inda bayan ya gama girmansa ya kece da wata dariya.
Wadda take fidda sautin jiniiiii, duk dakiya irinta Ma'eesh yau Saida tsoro ya shigeshi ya kuwa
ƙara ƙanƙameta ya fara karanto wasu addu'o'i da Shaikh Muhammad Saleem ya bashi lokacin
da tunaninsa yake yawan gushewa ya fara karantawa yana tofawa a inda macijin yake
dukkansu suks fara addu'o'i inda Deen yayi ƙarfin halin ɗaukar remote ya canza channel zuwa
ta karatun Kur'ani nan take wannan maciji ya saki wata ƙara ya matss daga jikin TVn ya fara
ƙanƙancewa ƙur'anin na ƙonashi yana wani irin ƙara me tada hankali can ya fara magana cikin
harshen Russian yana cewa “Karka ƙonamin ruhi Son Ni mahaifinka ne Inason ka shiyasa
nakeson rabaka da wannan yarinyar da rabani da kai ta kashemin gangar jiki Son karka zaɓi
mace a kaina itan zatayi maka butulci nine bazan butulce maka ba, Ahhhhhhh!....." Ya ƙwalla
wata ƙara tare da cewa “Na rantse da kabarin Babana ruhina bazai mutu shi kaɗai ba idan kuka
konani sai na kashe É—ayan biyu son ko na kasheka ko na kasheta ko kuma na kashe Æ´arku....."
Basu tsaya da addu'o'in ba TV bata tsaya da karatun ba haka suka wanzu macijin da ruhin Dad
yake jiki yanata ihu yana tumami amma basu barshi ba Saida sukaga ya fara narkewa wani jan
haske ya fita a jikinsa ya ratsa bango ya fice take Batul ta durƙushe a gurin ta saki wata ƙara
saboda wata azaba da ta zagaya ruhinta ta zube a gurin cikin wani yanayi na ficewa daga
hayyaci abinda ya janyo Ma'eesh ya durƙushe ya dafe cikinta da yaga tana riƙewa wanda yaga
lokacin da wani abu me kamar kifiya ya taho da gudu ya daki cikinta kafin yakai ga janyeta.
Dafe cikin yayi amma ina ƙaddara ta riga fata cikin ƙasa da ƙiftawar idanu jini ya ɓalle mata,
Kinkimar Ma'eesh yayi yayi suka fice sai asibiti suna zuwa gwajin farko suka tabbatar da
miscarriage zatayi ko kuma ince haihuwa ce aka janyota babu shiri cikin wata bakwai, duk
wanda ke asibitin ya tabbatar da yau aiki ya biyo ta kan manyan mahaukata domin kuwa ya
hargitsa kowa ya rikitawa kowa lissafi yanda take naƙudar shima haka yake naƙudar azaba
goma da ashirin ga haihuwa ta tabbata amma kuma taƙi zuwa shifa saboda bazai iya jure
wannan wahalar da takesha ba yace kawai ayi mata aiki, yayi sign kenan za'a shiga da ita take
ta haifi ɗanta Namiji lafiyayye kuma ƙosasshe yanayin kukan farko ya mayar da hannunsa cikin
bakinsa ya inda ita kuma taga wani hannu ta bayanta ya sauko daga sama zai É—auke mata
É—a...............
OUM HAIRAN
[7/21, 2:24 PM] Oum Hairan: *Book 3 page 13-14*
*Oum Hairan*
*Paid book VIP 1k regular 500 via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*
*Send evidence of payment for direct chat me í ½í±‡í ¼í¿½*
https://wa.me/message/FJFZD6227PBYP1
Cikin wata wata muguwar azama da bata taɓa sanin tanada ba tayi wuf ta tashi daga
kwanciyar da take ta É—auke jaririn dake cikin jini ko cibi ba'a yanke masa ba, daidai lokacin ne
kuma Ma'eesh dake waje zaman jiran tsammani domin iyakar dauriyarsa bazai iya zama a
É—akin da zata haihu ba saboda azabar ta girmi tunaninsa, ya shigo a sukwane tsayawa yayi cak
ganinta É—auke da jaririn da ko rabashi da cibiyarsa baayi ba idanunta a rintse ta matse yaron a
ƙirjinta bakinta yana motsawa da alamun addu'a takeyi
, a speed ya ƙarasa gabanta ya fara kiran sunanta amma batajin me yake cewa saboda
hankalinta ba'a gareshi yake ba hannu ya miƙa da niyyar rabata da yaron da yaketa kuka
saboda matsar da tayi masa, amma maimakon yaga hannunsa ya sauka ga jaririn É—an nasa sai
yaji wani shorck me barazanar katse rayuwa ya kama hannunsa, cikin ƙasa da ƙiftawar idanu
yaji wata murya tana masa amo a kunne tana cewa “Madallah da isowar Muhammad Taheer
magajin Daular Russia kuma jarumin daya gagari matsafan duniya haske takobin datse rayuwar
mushrikai maƙiya Allah!......" Muryar taci gaba da wanzuwa a wannan ɗaki tana amsa amon
sautinta ta kowacce kusurwa ta É—akin inda kowa dake cikin dakin ya shiga firgici.
Daidai lokacin ne kuma wani farin haske me kashe idanu ya keto ta bangon gabas ya zagaye
Batool da ɗanta ya nannaɗesu kamar mosquito yana zagayawa yana ƙara tsiri sama har aka
daina ganinsu, Ma'eesh da aka ƙamar dashi yana tsaye gashi yana kallon komai amma ikon isa
garesu ya gagareshi bare yayi tsammanin kai musu wani agaji shidai a ƙasan zuciyarsa yanata
addu'a haka suka wanzu a gurin kusan minti goma sha biyar sannan wannan haske ya ɓace ɓat
abinda ya dawo da Batool cikin hayyacinta tayi firgigit kamar wacce ta tashi a bacci, ta fara
kallon mutanen dake É—akin ta dubi Ma'eesh daya iso gareta da sauri suka kalli hannunta tare,
maimakon É—anta data rungume cikin jini yanzun wani kyakkyawan Baturen jariri ne a hannunta
me tsananin kama da ita sanye sinkif cikin kayan sanyi sai wani ƙamshi yakeyi me ɗaukar
hankali da sauke kasala.
Da sauri ta janye jaririn a jikinta kamar yanda Likitar data karɓi haihuwar taja baya da sauri cikin
mugun mamaki inda shi kuma Ma'eesh ya matsa da sauri ya sanya hannu ya É—auki yaron
bakinsa É—auke da Bismillah jikinsa na rawa me ban mamaki ya zuba idanunsa kan jaririn ya
lumshe idanunsa tare da durƙushewa ya ɗaga yaron sama yace “Alhamdulillah ya rabbil
azeezul mannah kamar yanda ka bani kyautar Muhammad Taheer yazo a cikin kariyar ka Allah
ka shaida na dawo dashi gareka hadiyya gareka Allah ya zama hadimi ga addininka ya zama
me gudun saɓonka ya zama me gaggawa wajen aikata alkhairinka,
Allah kai ka kareshi a lokacin da bazan iya kare kaina ba bare na kare wanina ya Ubangijin da
baisan babu ba kaci gaba da kareshi ka haneshi shiga shubha bare ta kaisa ga faÉ—awa
haramun" .......
Yana gama faɗin haka yayi masa kiran sallah tare da laƙana masa kalimatusshahada, ya miƙe
idanunsa na zubar da hawaye ya isa ga wani gado na jarirai ya kwantar da yaron ya isa ga
Batool da take zaune Kamar robot ya kama hannunta yace “Alhmdllh Bea kin biyani kin gama
min komai saura na biyaki kema" kwantar da ita yayi ya kira Dr Nadar ta shigo yace ta dubata in
babu damuwa yanason wanketa" fara check É—in ta tayi cikin ikon Allah babu damuwa duk
girman wannan ingarmar jariri da irin wahalar da tasha bata samu ƙari ba ta sauke ajiyar zuciya
zuge mata jinin da wata na'ura sannan tace masa ta gama, taimakawa Batool yayi ta tashi duk
jikinta na amsa mata suka shiga bathroom ya haɗa mata ruwa me sauƙin zafi ya taimaka mata
ta wanke jikinta sannan ya tayata ta gasa kanta sosai duk da tanajin zafin ruwan amma dole
tayiwa kanta gatan da batasan meyi mata ba a wannan ƙasar da basuda kowa.
Kiran wayoyinsa da ake tayi ne yasa shi fita ya buÉ—e babyn da yaketa bacci cikin kwanciyar
hankali ya É—auki wayarsa dake Ring number Deen ya gani ya É—aga da sauri tare dayi masa
albishir yayiwa Allah godiya sannan ne ya kira Mom itama da yaga misscall nata ya sanar da ita
haihuwar nan ta kasa zaune ta kasa tsaye daga ƙarshe ta kirashi tace lallai asan yanda za'ayi
zuwa jibi Batool da jaririn su dawo gida a kula da su.
To shima dake har yanzu a firgice yake baija ba ya koma ya taimaka mata ta fito tana kwance a
jikinsa ya shafa sumarta yayi mata sannu ta jinjina masa kai tace ya kira mata Samha, sai
Khazeem ya kira domin bashida number Samha shi kuma ya kira matarsa ya sanar da ita suna
shirin tafiya gida sai gata cike da farin ciki ta É—auki jaririn tana kallonsa tana kallon Batool tace
“Aa ya haka wannan karon anyiwa Daddyn Jany wayo babyn damu yake kama wannan
koÉ—aÉ—É—iyar fatar ce kawai ta uban Jany" dariya sukayi suka rankaya suka koma gida a gidan ma
suna shan kulawa ita da É—anta Samha kuwa a gidan ta yini sur sai dare sosai ta tafi gidanta
shima don Khazeem yana gari ne, kwana biyu kuwa da haihuwar jirginsu ya É—aga sai birnin
Sudan inda Mom da dukka yan gidan Harda Abbie akazo tarar sabon jika Aikuwa Aazam
yanashan carafke a hannun dangin ubansa harma da wanda Batool bata sansu ba yan uwan
Mom da Abbie.
Washegarin dawowarsu saiga granny ta dira Sudan sunyi murnar ganinta duk da cewa Ma'eesh
bai faÉ—a mata haihuwar ba tsoro yakeji kar saninta ya zama damuwa tunda dai a duniya
damuwarsa É—anta ne wato mahaifinsa Dad, sosai kowa yayi mamakin ganinta tsohuwa me
dattako ga soyayyar jininta ta É—auki Aazam ta zubansa idanu yaro kyakkyawa Masha Allah ta
share hawayen idanunta tace “Mahaifinka naso ya zama sarkin Russia hakan ta gagara
samuwa saboda mummunan ƙudirin mahaifinsa shakka babu Aazam shine zai mulki babbar
masarautata, a wannan karon bayan mun hallaka ruhin ɗana Nazhan da ƙarfin ayar Allah kuma
nasa rundunar dakarun Aljanun Muslunci sun karɓi haihuwar Aazam to kuwa kaima dole ne ka
koma daularka ka mulki mutanenka Ma'eesh waÉ—anda suka shafe shekaru talatin da biyar suna
jiran wanzuwar shugabancin Jinin Zahrain ya mulkesu, ba laifina bane kasancewar mahaifinka
bijirarre hakan ta faru ne daga son sai an rabamu da Mulkin Kasar Russia Ma'eesh mahaifinka
an ɓatar min dashi tun yana jariri kamar yanda hannu yazo don ɗauke Aazam da uwarsa ta
zama raguwa kamarni da tarihi ya maimaita kansa, da yanzu kuna cikin ƙuncin rashin
makusanci kamar yanda na kasance a ciki bayan haihuwar Nazhan, Ma'eesh sun sace min
ɗana sun gurɓatamin shi sun shayar dashi soyayyar addinin yahudanci bayan mun kasance
musulmi tun zamanin Annabi Sulaiman kaico, shekara goma sha biyar na kwashe bansa
Nazhan a idanuna ba, bayan dawowarsa ne na fahimci sun dulmiyar dashi cikin duniyar Tsafi da
addu'a ta ta kasa dawo min da ɗana daidai. Na ɗauki hakan a matsayin ƙaddararsa tun farko Ubangiji bai sanyashi cikin Muminai ba, da
wannan nayi alƙawarin zanyi bakin ƙoƙarina don ganin na tseratar dakai Ma'eesh da zuri'arka
na zaɓi na rasa Nazhan don ka rayu cikin aminci kaida iyalinka.
Sauka tayi ƙasa ta riƙe ƙafarsa Mom ta kamota ta ɗagata tace “Bazaki roƙi abinda kikafi ƙarfinsa
ba Granny indai nice mahaifiyar Ma'eesh kuma ke kika haifi mahaifinsa to bazaki koma Moscow
ba Saida jikanki Ma'eesh da iyalansa nayi Miki wannan alƙawarin"
Ficewa Ma'eesh yayi da sauri zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, part ɗinsa ya shiga ya zube a
kujera jikinsa na rawa yana sharce zufa tunda yake baitaɓa sha'awar zaman Moscow ba kuma
bashida ra'ayin Sarauta, Meyesa Mom tayi masa shigar sauri a rayuwarsa meyesa tayi masa
katsalanta ta yanke masa hukunci batare da ta saurari ra'ayinsa dana matarsa ba? Tashi yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya nufi masallaci ya gabatar da sallar La'asar ya
zauna yana tunanin ƙalubalen dake tunkaroshi taya zai fara rayuwa a duniyar da bai saba ba?
Taya zai saba da ɗabi'un da yake musu kallon baƙi cikin rayuwarsa, sannan taya zai fara
mu'amala da mabanbanta halittu, sarai yasan inda mulkin masarautar Granny yake mulkin
mutum ne da aljan domin kuwa duk wani aljani dake rayuwa a yankin wannan Masarauta
ƙarƙashin kulawarta yake shi ta ina zai fara?"
OUM HAIRAN
[7/22, 7:16 PM] Oum Hairan: *Book 3 page 15-16*
*Oum Hairan*
*Paid book VIP 1k regular 500 via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*
*Send evidence of payment for direct chat me í ½í±‡í ¼í¿½*
https://wa.me/message/FJFZD6227PBYP1
Daƙyar ya iya kai kansa gida bai koma sashin Granny ba ya nufi ɗakin Batool dake kwance ta
sanya Aazam a gaba tana kallonsa zuciyarta tayi mata nauyi masifu sunƙi barin rayuwarsu da
sun fara murna sun fita a wannan sai wata ta kuma Kunno Kai yanzu kuma cikin masifar mulki
zasu shiga?" Hawayen dake Zarya a idanunta tayi maza ta share tunawa da roƙon da Mom tayi
mata na ta rarrasheshi tasan bazai yarda da hukuncin data yankewa rayuwarsu da sauƙi ba,
zuba mata ido yayi yace “Me kikewa kuka?" Cikin son basarwa ta yunƙura ta tashi zaune tana
ƙaƙalo murmushi tace “Na shiga Bedroom ɗinka naga bakanan" zama yayi a saman gadon ya
fuskaceta tare da kana hannunta yace “Me kikewa kuka Uhmm telk to me" batason yi masa
ƙarya sannan batason sare masa gwiwa, yanke shawarar basarwa tayi tace “Ba ina kuka bane
na damuwa inayi ne don farin ciki da Allah ya hana azzalumai ikon rabani da É—ana DaÉ—ina
bantaɓa tausayin wani mutum kamar yanda na tausayawa Granny yau ba, ashe Dad ba
ra'ayinsa bane rayuwar da yayi shima narkar dashi akayi aka dulmiyar dashi“
Ajiyar zuciya ya sauke ya kwanta a gefenta yace “Zuciyata zafi takeyi Bea na tsani mulki
matuƙar bana gidana bane, Ni ina jin kamar ba adali bane Ni akanme zasu zaɓi kaini inda zasu
É—oramin nauyin da idan santsi ya jani zan iya kasa amsa tambayar mahalicci na Batool na tsani
mulki tun ina ƙarami dana fahimci shine Ummul aba'isin wahalolin rayuwata Batool na tsani
mulki tun lokacin dana fahimci a kansa ne ake neman hallakar dani da duk wani abu daya
shafeni, me zanyi dashi? Me nake nema dashi? Suna É—aukaka ko dukiya? Batool wanne ne
banidashi? Wai wanne ne Allah bai bani ba?"
Yanda ya ƙarashe furucin da ƙaraji Saida hantar cikinta ta motsa tunda take dashi sau ɗaya ta
taɓa ganinsa a wannan yanayin lokacin da Lateef ya kusanceta wannan rana taga madarar
tashin hankali sai kuma yau da yake neman birkice mata, kamo hannunsa tayi tace “To ya
zamuyi tunda Mom ta riga ta yanke hukunci Daddyn Jany Wlh Nima banason wannan shirin
kwata² baimin ba sai nake ganin kamar rabani dakai za'ayi...."
Rufe mata baki yayi yace “a'a don Allah saidai a rabani da raina but danasan abinda
dawowarmu zai zama kenan da munyi zamanmu bamu dawo ba, wacce kulawa ce, me a doctor
da zan kasa baki Bea?" Kwantar da kanta tayi jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tace “Kayi hƙr da
abinda Allah ya hukunta a kanka mijina, bazai canzu ba mu jira ikonsa kawai" iska ya furzar ya
miƙe ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa yanajin saukar ruwan kamar yana watsa
tafasasshe a jikinsa, fitowa yayi ya sanya kaya ya fice, bai dawo gidan ba sai cikin dare har
kowa yayi bacci, yana parking ya fito ya nufi part É—insu ji yayi an dafo kafaÉ—arsa ya tsaya cak da
tsananin mamakin waye a wannan daren, ga É—abi'ar gidansu dai yasan kowa yanzu ya kwanta
Deen ne zaka iya samunsa yanzu ido biyu shi kuma bai dawo ƙasar ba.
Zagayowa gabansa Granny tayi ta tsaya tana masa murmushi tace “Nasan abinda ke damun
ɗana har yake fushi dani kayi haƙuri zakaga amfanin wannan tsarin da nayiwa rayuwarka...."
Tayi maganar da harshen Russianci janyewa yayi yayi gaba ta bisa da kallo tana murmushi
tasan dama hakan zata faru, tun yana yaro babu abinda ya tsana kamar sarauta, juyawa tayi ta
nufi sashin da aka sauketa ta ɗaura alwala alwala ta tayar da sallar nafila ta jima tana roƙon
zaɓin Allah akan wannan ƙudiri nata, tabbas lokaci yayi da ya kamata ta haƙura da mulki zuwa
yanzu tsufa ya gama kama dukkan gaɓɓanta tana buƙatar Hutu tana buƙatar itama ta samu
makusanci duk duniya Ma'eesh ne kaɗai magajinta gashi tana ƙoƙarin mallaka masa abinda ya
kasa bawa mahaifinsa shi kuma yana neman butulce mata.
Shikuwa yana shiga ciki ko wanka bai iya ba ya zauna ya rafsa uban tagumi, jiyo alamun
shigowarsa ne ya sanya Batool miƙewa ta ɗauki Aazam domin ko wanka bata yarda ta shiga
tabar É—anta gani take za'a dawo a É—auke mata shi, nufar É—akinsa tayi ta buÉ—e ta shiga ta zauna
a kusa dashi ya ɗago ya kalleta yace “Meye ya hanaki bacci?" Bata bashi amsa ba sai miƙa
masa Aazam da tayi tace "His royal highness ne" kallonta yayi ya kalli yaron yayi murmushi
yace “Na bar masa idan yaga zai iya nikam banaso....." Rufe masa baki tayi tace “Ya jarumin
maza sadaukin duniya gwarzon gwarazan wannan ƙarni zai karaya kuma ya rinƙa tura
hannunsa ga tatsitsin jaririn da bazai iya amfanar kansa da komai ba?"
Zubanta idanu yayi ta karyar da kanta gefe tace “Zani kasance tare dakai a kowanne yanayi
don Allah kayimin wannan alfarmar daɗina kar mu watsawa Granny ƙasa a ido wlh ba ƙinka
takeyi ba itanasonka ne shiyasa ta zaɓeka, kar ka manta kai kaɗai take da kai a duk duniya
bataji daÉ—in Daddy ba kaima ta gaza