Showing 30001 words to 31021 words out of 31021 words

Chapter 11 - SIGN MARRIED BOOK 3 BY OUM HAIRAN .pdf

Advertisement

sauri
ta girgiza masa kai tace “Aa don Allah ba sai na tabbatar ba" tashi yayi ya nufi bathroom yayi
wanka ya fito ya shirya ya sake fita Masallaci ya nufa yayi sallar magrib da Isha sannan ya
koma a ƙofar sashin yake sallamar masu kula da lafiyarsa ya shiga shi kaɗai shidai bai yarda
akwai wata sarauta da zata sanya shi careless da iyalinsa ba part ɗinta ta rinƙa harkokinta a
can da rana but da dare suna tare.
To hakan dole aka barshi da ra'ayinsa sukaci gaba da rayuwarsu ba kamar yanda suka
tsammata ba Granny da tsoho Yanar sune suke koyar da Ma'eesh dabarun mulki kuma cikin
ikon Allah ya samu karɓuwa fiye da Ma'eesh na ɗaya soyayyar gaske dukkan al'ummar da yake
mulka sukeyi masa, wata ɗaya Mom tayi taga daidaiton nutsuwar ɗan nata da iyalansa a Omsk
emirates sannan ta shirya tafiya itadai Batool kamar tace masa zatabi Mom saidai tasan hakan

na nufin faruwar komai domin har yanzu ba ƙaunar mulkin yake yi ba kullum cikin mita yake.





Bayan tafiyar Mom ne ciwonta ya yawaita inda ya gaji da kasalarta gabaɗaya ta zama lazy bata
iya wani moron kirki take gajiya da wannan yasa aka duba masa ita saiga ɓillar sabon ciki a
jikinta a daidai lokacin ne kuma bikin Deen ya tashi da Maryam yarinyar da Innan Batool take
riƙewa da ƙyar Ma'eesh ya barta taje tayi wata guda akasha shagalin biki da ita ta dawo lokacin
cikinta nada wata huɗu, sunci gaba da rayuwarsu me daɗi da Nutsuwa a Omsk duk wata
damuwa da tashin hankali da suka shiga a baya ya shuɗe ya zama tarihi kamar baayita ba
yanda kowa yake nuna mata soyayya ita da yaranta biyu Jany da Aazam abin yana matuƙar
tsuma ta duk da cewa shi mulki ba'a rabashi da yan adawa, watanni suka shuɗe cikin ikon Allah
suna rayuwa cikin so da ƙauna cikin soyayyarsu babu abinda ya ragu abu ɗaya data fahimta dai
Kamar nacin sex ɗinsa ya ragu to ina ma yaga lokaci ashe komai dama yakeyi.
A wannan yanayin ne kuma ta ƙara haihuwar ɗanta namiji wanda aka sanyawa Muhammad
Zahrain daga nan ta dage masa sai ta huta sukayita rigima har saida Granny ta shiga maganar
sannan ya amince ta huta na 3 years itadai tace masa to so tayi tayi planing na zamani amma
ya hanata sai shi da kansa ya rinƙa tsara abinsa sukaci gaba da rainon ƴaƴansu yana tafiyar da
mulkinsa cike da soyayyar al'ummar da yake mulka kowa yana yabawa da salon mulkinsa da
irin zazzafar ƙaunar dake tsakanin ma'auratan.





Ƙawancanta da Samha ya rikiɗe ya zama ƴan'uwantaka duk da cewa itama Samha sun koma
Misra ita da mijinta da zama da ɗansu Jalal sai Batool data haifa tayiwa Aminiyarta takwara
bayan itama Janah tananan a Abuja rayuwar gidan mijin Masha Allah babu wata damuwa
tsakaninta da Alh Ahmad sai damuwar kishiyoyi da suka sanyata a gaba da sahirce sahirce but
abin baya tasiri da yardar Allah tunda ta riga tayi taubatun nusuha ta haƙura da duk yanayin da
rayuwa zata sanyata ta gwammace tasha wahala a gidan aure da tasha wahalar bariki kamar
yanda tasha a baya.
Gashi tana samun taimako gurin Batool ita Samha dake yar halak ce taimako take bata sosai
hakanan Batool ta gina mata babbar makaranta ta mallaka mata don dogaro da kanta, abinda
yake damunta yanzu rashin haihuwa shima kuma sun dage da neman magani tare da nema a
gurin Ubangiji cikin shekarar ta ta sha biyar da aure ne ta haifi yaranta biyu mace da namiji da
Batool taje suna ne suke hirar CEO da Samy nan Janah take faɗa mata ashe suma suna cikin
ƙungiyar asiri lokacin rikicin soyayyarta da King Ma'eesh duk suka rasa rayuwansu.
Ajiyar zuciya tayi tace Allah ya gafarta musu nikam sun gamamin komi tunda a cikin ƙaddararsu
na haɗu da tawa ƙaddarar kuma rayuwata" Tun wannan haihuwar janah bata kuma haihuwa
ba, a lokacin Batool nada yara Biyar uku maza biyu mata Samha ma biyar ita huɗu ne mata

ɗaya namiji, Khazeem mijin Samha shine yanzu babban abokin Ma'eesh suna bawa juna
shawara akan abinda ya shafi mulki yaransu suna ziyartar juna duk lokacin da akayi hutun
karatu, a wannan ziyarar ne Jany da Jalal suka haɗa kansu ashe soyayya sukeyi iyayensu basu
sani ba, sai bayan Jalal ya koma Misra ya sanar da mahaifinsa shifa ƙarfinsa ya kawo aure zai
yi kuma Princess Aysha yakeso zai aura, Aikuwa Khazeem yana sanar da Ma'eesh shima yayi
na'am, dake abin tuwona maina ne cikin ƙasa da wata biyu akasha shagalin bikin da aka daɗe
baayi irinsa a masarautun biyu ba aka ɗauki amarya Jany aka kaiwa angonta Jalal, rayuwa taci
gaba da tafiya yanda akeso cike da Nutsuwa wasu ɓangarorin da ƙalubale.




*_Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah
subhanahu wata'ala, wanda yake wanzar da komai ba tare da jinkiri ba, ina godiya garesa daya
bani ikon kammala wannan ƙayataccen labari me fari jini me taken sign married kuma ina
godiya ga masoyan labarin waɗanda suka samu damar biyana haƙƙina da waɗanda basu samu
dama ba._*




*Note:* *kamar yanda na faɗa a farkon labarin Nan duk wani aure In ba irin auren da Allah da
Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) suka umarcemu da muyi bane to haramun ne a
garemu mu musulmi kuma don Oum Hairan ta rubuta littafin da yake nuni da ɓarnar wasunmu
a doron ƙasa ba yana nufin tace ya halatta bane, not babu ruwan Oum Hairan in kaje kayi kai
ka sani bata gurin sanda zaka amsa tambayar mahaliccinka kamar yanda kaima bakanan
sanda zan amsa tawa.*




*Masu jiran complete book 1-2&3 to ya kammala kamar yanda na faɗa muku complete 1k ne via
9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*


*Contact of evidence 09031307566*



*Sabo yananan tafe 1/8/2025 Insha Allahu me taken *KING ROMANCE Don Allah ina neman
alfarmar yammata su daina karantamin littafi*

*OUM HAIRAN*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login