Showing 30001 words to 33000 words out of 35767 words

Chapter 11 - BEELAL BUK BOOK 1 BOOK COMPLETE BY MAMAN AFRAH.doc

tsaye tana kallon kowa da kuma abubuwan da ke faruwa da kuma abubuwan da ake tattaunawa, ganin ba a cin zatafin ?ar uwarta hakan ya sa bata fito daga maSoya ba, cikin rashin sa'a sai ta goce daga kan wani burket da ta taka take le?awa aikuwa hakan ya Wauki hankalin gabaWaya waWanda suke falon dan kuwa kowa ya san dai gabaWaya mutanen gidan suna hallare a falon amma waye zai zo gidan nan ya laSe ya ji sirrin gidan saboda kasada.

"Ku bishi ko waye ku kawo min shi nan yanzun nan kar ku sake ku dawo min babu shi duk inda zai shiga ku kamo shi" Cewar Alhaji cikin zafin rai da bada umarni ya faWa yana yiwa gabaWaya ma'aikatan gidan umarni, aikuwa cikin hanzari da son cika umarnin uban gidan masu suka amsa tare da marawa wanda aka jiyo ?aransa baya...


MMN AFRA 09030283375

d'?d'?d'?d'?d'?d'?


*BEELAL*



=???=???=???=???=???=???


NA



MAMAN AFRAH



FCW


Da sunan Allah mai rahma mai jin ?ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.

*This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* =?
?=?
?=?
?



*END OF BUK 1*

Page 2?? 9?? ?'?3?? 0??


GabaWaya haka suka fito suka barbazu a bayan gidan ko ta ina sun kewaye, sai dubawa suke lungu da sa?una na Sangaren Hajiya Nuratu. Fatima da tun lokacin da abin da ta taka saboda tsawon windown da yake daga ?asa akwai zurfi sosai take le?awa ya zame ya yi ?ara, hakan ba ?aramin sanyawa ya yi hankalinta ya tashi ba, hakan ya sanya cikin zafin nama ta fara neman inda za ta Suya waige-waige ta shiga yi hankali tashe dan maganar Alhaji ta sanya ta ji dama bata ma fito ba kamar yadda yayarta ta faWa mata amma ta tsallake maganar tata ta fito. Ganin in bat samu mafaka ba za su cim mata hakan ya sa ta hango wani tsohon tanki na ruwa da ke can bayan gidan wandaba a amfani da shi cikin hanzari ta Wauke murfin da yake yana da babbar ?ofa haka ta ajiye murfinta ta shige cikin tankin.



gabanta na mugun faWuwa tana ta jin wucewar masu nemanta suna ta zuwa da dawo wa tatw da duba ko wane lugu da sa?o na wurin amma cikin iko da hikima ta ubangiji babu wanda ya lura cewa wani zai shiga cikin tankin ya Suya, dan su duk zatonsu ma Sarawo ne. Sai da ta ji sawu ya Wauke bata jin ko motsin mutum Waya sannan ne fa ta lallaSa ta fito gabanta na dukan uku-uku tana addu'a da fatan Allah sa dai kar asirinta ya tonu ko dan yayarra ma da bata ji ba bata gani ba. Wani uban zagaye ta yi kafin ta samu zuwa part Win Yayar tata tana shiga kuwa ta haye sama ta je ta kwanta a kusa da Beelal tana sauke numfashi har lokacin gabanta faWuaa yake dan abu ne ya faru wanda bata taSa zaton faruwarsa ba.



*?angaren Hajiya Nuratu*

GabaWaya ma'aikatan gidan sun karaWe gidan amma babu alamar wani ya shigo ma dan get Win ma kamarbyadda mai tsaron ?ofa ya sanya ?atoton kwaWo ya gar?ame a haka aka samu get Win babu da aka yi amfani da shi aka le?o falo masifa sosai Alhaji ke yi yana basu san aikinsu ba, gabaWaya sun yi tsit suna sauraronsa kamar su ne suka yi laifin a haka dai aka sallami kowa daga taron aka yi al?awarin kyaututtuka masu tsoka da za a rabawa ma'aikatan gidan. Sallamar gabaWaya ma'aikatan aka yi aka bar me gidan da matan gidan nan ma dai ya yi gargaWi da babban murya a kan kowacce ta kiyaye da dokokin gidansa kar a samu wata ta karya doka, sai ya ce zuwa wani lokaci zai iya barinsu su fita tun da matarsa ta haihu sai kuma zuwa gaba idan wata ta samu cikin ya tsufa dole dokar za ta Wora daga inda aka tsaya. Haka dai kowacce ta tashi ta koma Sangarenta aka bar me jego da wacce ta karSi haihuwa da masu mata hidima na Sangarenta dan sai zuwa gobe ne ma za a bar iyayenta da wanda shi me gidan ya ga ya kamata ya barshi daga ckn ?an uwan su zo su ga me jegon da abin da aka haifa.

HAJIYA LA?IFA

Tun da aka ce an ji ?aran wani a bayan window hankalinta ya yi mugun tashi saboda ta san ?anwarta da taurin kai ta san duk iya gargaWin da ta mata kaWan da aikinta ta fito, hakan ya sanya tun da aka fita duba waye ya le?o gabaWaya ta rasa nutsuwarta gabanta ke ta faman lugude tana addu'a a ranta Allah ya sa ba Fatima ba ce duk da zai yi wuya in ba ita Win bace.


Haka ta zauna cikin fargaba tana ta addu'a a ranta a kan Allah ya rufi idanunsu kar su ga wanda suke nema in har Fatima ce. Bata samu nutsuwa ba har sai da ta ga sun dawo sun ce basu ga kowa ba, sosai ta yi farinciki duk da ta san zai yi wuya su ga in har Fatima ce zai yi wuya su ganta saboda shegen wayo dole ta san za ta yi duk iya yinta domin ganin ta Suya ko ta gudu ba tare da sun ganta ba. A hanya ma tana so su yi maganar da Nasira amma hakan ya gagara saboda tare da ma'ailatan Sangarenta suka taho dan haka babu dama sai ha?ura ta yi da yin maganar. Sai da suka zo dai dai ?ofar da za ra sada su da Sangarenta ta sallamesu gabaki Wayansu sai kuma ta ce Nasira ta biyo ta za ta sanyata wani aiki haka suka mata sallama kowa ya kama gabansa ita kuma da Nasira suka shiga Sangarenta, suna shigowa falo cikin tashin hankali ta fara magana.

"Nasira baki zargi wani abu ba game da ?aran da aka ce an ji na wani? "

"Babu zargin da na yi Hajiya menene ya faru?"

"Na shiga Wimuwa wallahi dan na san Fatima za ta iya fitowa kin san wallahi da sun ganta sai an mata lilis a gidan nan dan babu abin da zai sa su ?ylaleta sannan ma duk su Hajiya da sauran abokan zamana sun san Fatima ni wallahi damuwar da na shiga ma ba ta tonuwar asirin ganin Fatima a gida nan bace, damuwata kar idan suka ganta kafin su kawo ta ma wurin Alhajin su mata dukan da za ta shiga wani hali"

"Dan Allah Hajiya ki bar wannan maganar ke da muka bar Fatima a nan sannan kuma kin faWa mata kar wanda ya fito, kuma ita ma ta san matsalar gidan nn ai ba za ta fito ba"

"Baki san halinta bane dole na san za ta iya cewa Beelal ya zauna ta je wani wuri ta dawo, za dai ta masa wayo dan ta je ta ga ko za a ci zarafina kuma da ace ta tarar da abin da take zargi na san sai ta fito daga maSoyarta ta bi min ha??in mutuncina da aka ci sai dai ko me zai faru ya faru"

"Gaskiya ba lallai ita bace kin san fa bada?alar gidan nan, yanzu haka Waya daga cikin matan gidan ce ta shigo da wasu a Soye su ma suka je su baiwa idonsu nama su ga ?wa?waf kar a yi ba su"


"Ni dai yanzu mu je mu gani ko ta samu ta dawo ko kuma tana can wani wajen ta Soya tana tsoron fitowa a gan ta dole in san abin yi " Hajiya ta faWa tana hawa saman Nasira ta take mata baya.

Suna shiga suka a falon saman shiru babu kowa alamar ma basa falon sosai Hajiya LaWifa ta tsorata dan ta Wauka ma Fatima da Beelal ne suka fita a tare kuma basu dawo ba, cikin sauri ta nufi Wakunan ta fara dubawa duk inda ta buWe sai ta ga wayam, duk ta rikice ita ma Nasirar ta tsorata amma suna buWe Wakin da ke can gaba sai suka ga Fatima da Beelal a kwance a kan gado suna ta bacci abinsu.

"Kin gani ko Hajiya dama na faWa miki cewar suna nan gashi dai kin gani da idonki sai zuciyarki ta yi sanyi" Cewar Nasira tana ?ar dariya.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tana sakin murmushin farinciki ta ce

"Kai me za a yi da tashin hankali da fargaba duk sai ka rasa nutsuwarka"Ta faWa tana samun wuri ta zauna.

"Hakane kam tashin hankali ina ya ga daWi yanzu zai sa ka ji komai ya kwance maka"


Fatima da duk tana jin abin da suke cewa dama tun da ta jiyo motsinsu ta rufe idonta. Haka dai suka Wan jajanta Nasira ta yiwa Hajiyar sallama ta tafi Sangarensu.


Haka Hajiya LaWifa ta yi shirin kwanciya ta zo ta shimfiWa katifa a Wakin ta zauna a ka tana ta kallon ?ar uwarta fa Beelal tana jin irin yadda son su da tausayinsu ke ratsa dukkan jiki da jijiyoyinta, tabbas maraici ba ?aramin abu bane da a ce iyeyensu suna raye da komai ya zo musu da sau?i to amma Allah ba ya barin wani dan wani ya ji daWi gashi mutuwa ta musu yankan ?auna ta Wauke iyayensu da kuma Kakarsu wacce ita kaWaice wacce ta rage musu, yanzu kuma su kaWai suka ragewa kawunansu, gashi kuma ?addara wacce ke riga fata ta shiga tsakaninsu na rashin dace da abokan zama nagari dama haka ne rayuwar ?a mace gajera ce shi yasa ake so ta inganta ta, ta kuma tattalata ta kare mutuncinta ?arshe dai abu Waya ne zai kasance jin daWin rayuwarta shi ne dace da samun miji nagari nagartacce wanda zai kiyaye ha??o?inta da na ?a?ansa wannan shi ne kaWai zai sanya ta rayu cikin farinciki saSanin hakan kuma rayuwa ce marar galihu da nagarta haWe da inganci Allah kiyaye.

Haka ta zauna tana ta kallonsu tana sa?a abubuwa da dama ta so a ce ita da ?ar uwarta sun yi dace da samun abokan zama nagari, sai dai kash hakan bai samu ba. Ita ?anwar tata miji babu halin kirki babu kulawa kai shi babu nasa da yawanta, ita kuma ga dai komai na more rayuwa amma kuma sai ta haWu da jahilin miji da kuma jahilar sirika zaman gidan wani irin zama wanda ba a san ha??o?in da za a kiyye ba na aure na baiwa mace kylawa da soyayya, sai dai a bata ci da sha a bata komai ga kuWi nan babu shamaki amma kuma abubuwan da aka rasa sun fi kuWin muhimmanci nesa ba kusa ba.



Kuka take yi ba mai sauti ba amma zafinsa ya fi ma a ce mai sautin take yi saboda yadda ya haWe mata biyu kukan zuci da kuma na zahiri duka biyu abin ke yiwa zuciyarta ga Fatima ga kuma Beelal da a ce tana da dama da ?anci a gidan n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an da kuwa sun dawo hannunta da zama ko dan su samu kulawa su zama basu rasa komai ba ko dan ta zamewa Fatima bango abin jingina ko dan Fatima take ji a ranta cewa bata yi maraici ba, gwara ta zauna da ita a kan zaman auren da take wanda da shi da babu kusan Waya ne dan ba a ce Waya b saboda shi aire ginshi?i ne kuma garkuwa ne ga ?a mace, aure yana Waga darajar mace sama da duk yadda wanda ke da aure zai yi tunani amma wanda bai da aure ya kan gane hakan saboda abubuwan da zai ga ya rasa idan bashi da auren.

Fatima kuwa daga baccin wasa da ta rufe idonta baccin ya yi awon gaba da ita, saboda gajiya ga kuma wunin fargabar da zuciyoyinsu suka wuni a ciki. Haka Hajiya LaWifa ta Saida kanta ta kwanta a kan katifar amma kuma sai ta ji ba za ta iya kwanciya ba ita kaWai tana ganin ?an uwanta haka ta tashi ta koma kam gadon ta gyarawa Beelala kwanciyarsa ta kwanta suka sanyashi a tsakiya haka ta kwanta tana sa?e -sa?e har bacci ya yi awon gaba da ita.

Haka suka kwana biyu kamar yadda suka zo su yi da yake gidan gabaWaya a ruWe yake da haihuwar da aka yi sai ya zamana babu wani wanda zai kawo cewar ma a kwai wasu a cikin gidan haka suka yi kwana biyun cikin soyayya da kulawar junansu Hajiya LaWifa tana ji a ranta ina ma kar su tafi su barta domin u kaWai ne sanyin idaniyarta su kaWai take kalla ta ji daWi marar misaltuwa a ranta. Amma babu yadda za ta yi haka za ta ha?ura su koma gida.


A dai dai lokacin da ake wani taron a lokacin da kowa yana Sangaren Hajiya Mariya a can take taro ita da Alhaji dan haka kowa na gidan yana can bayan Hajiya LaWifa sun yi sallama da Fatima har da kukansu na rabuwa da juna, Beelal ma sosai ya ?an?ameta yana kuka wai ba ya son su tafi su barta, yana ta mata magiya tana zuwa suna ganinta, haka dai ta amsawa yaron cikin jin tausayinsu duk a ta san yanzu komai zai yi sau?i tun da Hajiya Nuratu ta haihu dole za a rage dokar hana fita. Waya sabuwa Hajiya LaWifa ta baiwa Fatima da kuma kayan Beelal na ?an ball da abubuwan wasa da piano na na yara da ta baiwa direbanta sa?o ya siyo mata a Soye sai kuWaWe masu yawa da za su sayi kayan abinci da kuma abubuwan bu?ata. Mukullin get Win da ta karSa a hannun Mai tsaron ?ofa wanda yake datse ?ofa idan za a yi taro shi ya bata a Soye domin su samu su fice ba tare da kowa ya sani ba, suna yin sallama ta kama hanyar Sangaren Hajiya Mariya ta barsu a Sangarenta za su fita sai Nasira ta samesu a bakin get Win dan idan a ka ga Hajiya LaWifa ta fito za a zargi wani abu idan kuma Nasira ce ba lallai a kawo komai ba, dan haka Fatima Beelal Win ta goya a bayanta ta ri?e musu akwatin kayansu da Hajiya LaWifa ta basu suka saka kayansu a ciki har da turamen atamfofin Fatima haka ta Wauka suka baro part Win cikin sauri dan gudun wani ya gan su duk da dai da wuya dan kowa yana wajen taron a haka ta ?araso get Win tana ta hucin tafiya da kuma nauyin akwatin hannunta ga kuma goyon Beelal da take Wauke da shi. Suna zuwa kawai sai ganin Nasira ta yi ta fito daga maSoyarta dan izinin fitowa fitsari ta nema ta fito wannan kasadar. BuWe get Win ta yi sa mukullin suka fita tana Waga musu hannu, da sauri ta mayar ta rufe ta juya abinta, haka ta koma Sangaren Hajiya Mariya ba tare da kowa ya ganta ba, ta koma mazauninta ta zauna, da aka gama faWar ?auli da ba'adin aka sallami kowa ya kama gabansa, a haka ta yi dibara ra baiwa Mai tsaron ?ofa mukullin ba tare da kowa ya gane hakan ba. Haka suka koma Sangaren Hajiya LaWifa ita da Hajiya LaWifar cike da kewar Beelal da Fatima suna musu fatan sauka lafiya.


*Fatima*

Suna fitowa daga gidan ta yi hamdala da wannan tsallaje rijiyar da baya da suka yi, sakko Beelal ta yi daga bayanta, ta kama hnnunsa tana ri?e da akwatin a haka suka Wan fara tafiya kafin suka samu napep suka hau ya kaisu tasha suka hau mota, motar na cika suka kama hanyar Kazaure.




Suna sauka a Kazaure Fatima ta musu siyayar kayan abinci da duk wani abu da za su bu?ata har takalmi na soso ta siyawa Beelal dan dama daga can a kayan da aka siya masa har da takalman kwalliya kala biyu. Dan haka sai da ta siyawa Hameeda ma na kwalliya kala Waya da na soso guda Waya sannan ta yi tsaraba, dan bata samu damar siyowa a Kano ba saboda gani take kamar wani zai je ya faWa cewa sun je gidan Hajiya LaWifa Alhajin ya sa a biyo su. Napep ta samu ya kwaso musu kayansu ya Wakko su zuwa ?auyensu, a dai dai ?ofar gidan ya tsaya ya fito yana fiddo musu da kayayyakin daga can bayan napep Win da aka sanya su da kuma na kan mazaunin kaya ne da ba kaWan ba. Beelal da ke sanye da wando da riga masu kyau ga takalmin kwalliya sai washe baki yake ana fito musu da kayan yana murna yana jin farinciki a ransa su ma sun yi kayan abinci ba za su ke zama da yunwa ba.


KuWi ta Wakko ta sallami mai napep Win, a haka yara suka zagayesu amma ganin Beelal Win cikin shiga me kyau ya sanya yaran tsayawa suna kallonsu da a
mamaki dan ba Beelal kaWai ba hatta Fatima kaya ne masu kyau sababbi a jikinta, hakan ya sanya ma basu tsonani Beelal kamar yadda suka saba ba. Fatima juyawa ta yi da niyyar ta je ta buWe gidan dan ta shiga da kayan amma me kawai sai ta ga ?ofar gidan a buWe tana shirin faWawa Beelal sai zuwa Hameeda a guje ya dakatar da ita dan Hameeda ta samu labarin dawowarsu.

Tana zuwa suka rungume juna Hameeda da Beelal suna ta murna.

"Beelal Babanka ya dawo jiya" Cewar Hameeda da bakinta ya ?i rufuwa ganin Beelal. Gaban Fatima ne ya bada wani rass, jin abin da Hameeda ta faWa, tana shirin furta wani abu aikuwa sai ga Idrisu ya fito daga gidan, ganinsu ya sanya ya haWe rai kamar wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login