Showing 1 words to 3000 words out of 17169 words

Chapter 1 - KAWAICI Book Free Pages By Zahra Royal Star.txt

*KAWAICI*

*©Zahra Royal Star*


*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.....*


*TSOKACI*

*KAWAICI*
A cikin gida ɗaya, amma zukata huɗu — kowanne na ɗauke da raɗaɗi, sirri da ƙaddarar da ba ta da kama da ta ɗan uwansa. Gidan da ya kamata ya zama mafaka, ya zama maɓuɓɓugar tsoro da rashin kulawa. Mahaifin da aka dogara da shi, ya zama shinge na zalunci da son zuciya, yana barin ƴaƴansa su nemo mafita a cikin duhu.

*“Kawaici”* ba kawai hali ba ne — wata rufa-rufa ce da kowanne daga cikin ƴaƴan ke amfani da ita don buya daga gaskiyar da ke cin ransu a ciki. A ɓangare huɗu na labarin, kowanne yana bayyana da nasa yunkuri da irin ƙaddarar da ta bayyana wani darasi mai ƙarfi.

*Wane sirri ne ke ɓoye a ƙarƙashin wannan kawaicin? Wane zai tsira daga irin wannan gida?*

Wannan littafi cike yake da jimami, ruɗani da faɗakarwa — yana sa ka kallon rayuwa da iyali da wata sabuwar idanuwa.


PAGE 1

*Unguwar Dokoki Ramiye, LGA, Katsina state Nigeria*


Jiri ne taji yana neman kayar da ita, da wani irin sauri ta dafe kanta tana riƙe igiyar dake sama, dama shinyar kaya take kawai taji kamar wani abu ya gifta mata a tsakiyar kanta.

Fitowa daga ɗaki tayi ganin Mama a tsaye dafe da kanta yasa ta sakin tsintsiyar dake a hannuta ta rugo da gudu gare ta tana faɗin.

"Subhallahi Mama miya same ki?".

Mama ta ɗago tana sauke lumfashi da kyar ta damƙe hannunta tana faɗin.

"Babu komai Falmata, jiri ne kawai nake ji kwana biyun nan".

"Ahayee nanaye a haka zaku ƙare da yinwa, domin idan har zaku tsaya sai Baba yaci daku kuci to kuwa zaku mutu da yinwa".

Kallonta Falmata tayi tana girgiza kanta tana taikacin ƴan gidan nasu gaba ɗaya wa'inda kwata-kwata babu kintsi bare kamun kai a tattare dasu, kowa gashin kansa yake ci, kuma duk laifin yana ga mahaifinsu daya tara iyali sama da Mata Uku amma baida ƙarfin ɗaukar nauyinsu bare kulawa da duk wani al'amarinsu, dole Mace ta nemi sana'a ta rinƙa cida kanta, ko kuma Mace ta fita samarin banza su bata ta kawo gida, kuma hakan baya wani damun Baban, hasalima shi idan zaki samo ki ɗan lasa masa so yake.

Da kyar ta buɗe baki tana duban Hindatu ta ce.

"Ke kanki kin san waye yake jiran abun gidan nan, ya kamata kisan dasu waye kike magana Malama"

Wani kalar baƙin ciki ne ya ciyo Falmata tunowa da irin halayar gidan nasu, wata irin damuwa mai tsananin gaske ce ke rufe ta idan ta buɗe ido ta ga yadda ƙanananta Yayyenta suka zama akan talauci da yanayin rayuwa.

Tasha tabbayar kanta mi yasa Baba yasan baida abinda zai iya riƙe su harya bari ya haife su ya tara iyali masu yawa haka?, gasu nan sun kusa kai su Goma shaa gidan ƴaƴansa, maza harda masu shaye-shaye da ƴan daba a gidan nasu.
Girgiza kanta ta ƙara yi tana kallon Hindatu data yi maganar tana wani taunar chingum, bacci Mama dake wajan yau data ji magana, dan haka kwafa kawai Falmata tayi tana bankama mata harara, itama Hindatun tsaki ta sakar masu tana yin gaba ta fice daga cikin gidan sanye take da wata shegiyar shiga anci wanka sai kace wacce zata je gasar kyau ta duniya.

"Muje ciki Falmata".

Faɗin Mama tana kamo hannunta, dan ita Mama bata cika shiga harkar gidan ba kwata-kwata, dama kuma su biyu ne kawai ta haifa a gidan daga Falmata sai Shamsiyya.

Mata Uku ne a gidan akwai Inna wacce ita ce uwar gida a gidan ƴaƴanta biyar cikin gidan akwai Shamsu shine babba, shi bai cika shiga harkar gidan nasu ba, idan ka gansa gidan to ta ɓaci ne a harkar dabarsu, domin riƙaƙƙen ɗan daba ne lamba ɗaya, duk wata fitini da rigima da ake a cikin garin Rimaye zaka samesa a ciki, sai Zahariyya ita ko tayi shura wajan bin gidajen Gala duk inda gidan Gala yake ta sani, ko wani Alhaji mashahurin mai kuɗi zaka sameta tare dasu a ƙofar gida, kullum ƙofar gidan nasu bai rabo da baƙin Maza, koda Baba ya gani ko a kwalar rigarsa, asalima zuwa yake ya tsaya a lasa masa wani abu shima ya samu, harda su alfahir yake, mutanen unguwar babu surutun da ba'a ma gidan Baba Saminu, wadda da yawan jama'a Baba Saminu suke kiransa dashi, wasu ma Baba kawai, amma kwata-kwata shi hakan baya damunsa hasalima idan ka taresa da magana gaba da gaba tofa zakuyi rabuwar ɓacin rai ne dashi, baya taɓa sauraron surutun jama'a da faɗa masa gaskiya da suke, ga ƙawayen banza masu buɗe mata ido, ita ce ke kawo wani abu a ɗakinsu, daga nan sai Hindatu, ita ko ƴar ƙarya ce ya bugawa a jarida tana son rayuwar ƙarya ga biye ma ƙawaye ƴan ƙarya bata can gidansu ƙawa bata nan, sai tayi kwanaki bata gidan nasu, sai kuma Isma'il, shi wannan ta fannin shaye-shaye shine lamba ɗaya duk wasu ƴan kuɗaɗe nashi wajan caca da shaye-shaye suke ƙarewa, shima ba'a cika ganinsa a gidan ba idan ba ta ƙare masa ba, sai idan baida abunda zaici ko ya saida ya shiga caca, daya zo gidan yaci karo da wani abun saidawa wadda idan ya saida zai masa amfani to sai dai ka nemesa ka rasa, kuma dama da an neme abu an rasa ansan waye yazo gidan a ranar, sai kuma Ma'u, ita wannan ƴar gayun gidan ce ta ɗauki kanta nesa ko rayuwar gidan nasu kullum mita take tana cewa ita fa ba ƴar isalin gidan bace ƙilama a asibiti aka canzata, domin bata dace da rayuwa a gidan ba, fariya gare ta ga ɗagin kai idan ta shiga cikin jama'a saika rantse ƴar gidan wani hamshaƙin mai kuɗi ce, tana kashe ma kanta kuɗi sosai saboda Allah ya bata sana'ar iya lallai mai shegen kyau bata ma ƴan tagajan-tagajan ƙunshi sai Mace ta amsa sunanta Mace, wata irin rayuwa take wacce ta kai kanta ne inda Allah bai kaita ba.

Sai kuma ƴan ɗakin Umma, ita tana da Yara Huɗu, babbar cikinsu ita ce Sa'ade, tayi aure a cikin garin Rimayen, sai dai itama kullum tana kan hanyar zuwa gidan nasu, saboda ta auri ɗan iskan miji, duk ya maida ita wata tsohuwar ƙarfi da yaji, sai kuma Asiya mai bi mata kusan itama rayuwarta ta ɗauki kanta nesa, dan cewa tayi bazata taɓa yin aure yanzu ba, taje ta faɗawa irin mutunan da ƴar uwarta ta faɗa, shi yasa kwata-kwata ta rasa wadda ya dace ta aura, ita ce ka ganta da wannan saurayi gobe ka ganta da wancan, bata da wata matsaya a rayuwa, sai kuma Amina, ai ita wannan magana ba ba damunta tayi ba, sai kayi magana sau dubu bata tamka maka ba, sai wadda ya isa ya kai take masa magana, kawai dai tana son harakar girma, amma bata ɗaukar raini, sai dai akwai shegen yawo da shige-shigen gidajen jama'a masu kuɗin gaske kullum tana kan hanyar zuwa gidajen su ta tayasu aiki, domin ko tuwo akai gidan nasu magana ɗaya ce itafa tafi ƙarfin taci tuwo, shi yasa bata can itama bata nan, neman na kanta kawai tasa gaba, sai kuma autansu wadda suke kira da Baffah, shi bai cika yin magana akan abunda ya shafi gidan ba, neman na kansa kawai yake, domin duk wani aikin ƙarfin da zai kawo masa kuɗi ya sani zai nema da guminsa, shi yasa kamin kaji sunansa a cikin gidan ma aiki ne, sai idan abu ya kwaɓe Baban baida inda zai samo ƴan kuɗi aci abinci zai kama kiransa, dan kusan shike basa kuɗi ba tare da yayi masa gaddama ba koya gaya masa wata maganar marar daɗi, sauran kuwa idan zasu basan sai sun gama gaya masa magana zasu ɗauka su basa.

Sai ɗakinsu Falmata, daga ita sai ƙanwarta Shamsiyya, Falmata a gidan sune kaɗai za'ace ma nitsatstsu, Falmata a gidan wani irin hali ne da ita bata barin ta kwana duk wadda ya ce zai taka ƴan ɗakinsu koya taɓa Mahaifiyarta, to ko za'a jisu, domin ƴan gidan basa da kunya ko misiƙala zarratin, shi yasa a tsaye take, domin Mama irin masu haƙurin nan ne, sai ayima Mama abu sau dubu bazaka taɓa ganin ta ɗaga kai ta tanka ba, Falmata sana'ar kitso take a gidan, ta mugun iya kitso shi yasa kullum gidan ita da Ma'u ke tara jama'arsu ita na kitso Ma'u kuma ƙunshi, Shamsiyya ko dama rainon Falmatarce duk kusan halayensu ɗaya, banbancin ɗaya a tsakaninsu Shamsiyya bata cika faɗa ba, shi yasa ma Falmata ke bala'i idan tazo ta iske ana ma Mama wulakanci a gidan Shamsiyya na gani sai dai tayi ta kuka, abun nacin ran Falmata, sai idan tazo ne za'a kwashi ƴan kallo, shi yasa wani lokacin har Mama bata so ayi wani abun Falmata na gidan, domin duk yadda za'ai idan har harkar ɗakinsu aka shiga ko aka taɓasu tofa sai inda ƙarfinta ya ƙare......

*KAWAICI*


*©Zahra Royal Star*


*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*


PAGE 2


*Unguwar Dokoki Rimaye, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*



A hankali ta gyara kan matar dake zaune ƙasa tana mata ƙitso kanta na akan cinyarta, tana yi duban tsakar gidan nasu babu kowa sai ita zaune tana ma wata makwafciyarsu kitso, sauri take ta gama dan tana son tattare gidan yadda duk yayi ƙura kamar wadda aka shekara ba'a share ba.

Makwabciyar ce tayi gyaran murya tana faɗin.

"Ni ko Falmata wannan tsakar gida naku a rasa wadda zai gyara shi sai ke kullum kike ƙoƙarin sharewa?, ai ya kamata yadda gidan nan yake shaƙe da ƴan mata ana zuwa ana iskesa a gyare, gashi duk an kashe gidan da lallai da ake yi"

Falmata ta ɗan kalli tsakiyar kan matar taɗan tsaya da kitson tana sakin tsaki ciki-ciki ta ce.

"Baiwar Allah kitso kika zo yi ko kuwa namen jin gulmar gidanmu?".

"Ah ah daga magana gaskiya fa ce nake faɗa?, ni ai tausayinki nake ji, ace kullum kice ƴar gyara waje ana ɓatawa".

"Ki riƙe gaskiyarki Malama kinji".

"Allah ya baki hakuri".

Tsaki ta kuma, tana ja mata kai danta fara bata haushi, a rayuwarta bata son zaman gulma da mata keyi, amma mudun za'a zo kitso ko ƙunshi a gidan sai an zauna ana ƙananun surutai da gulmace-gulmace, ita kam bata yarda da wannan ba, amma Ma'u ita da ita da ake zama ana buɗe shafin gulmar mutum idan aka zo mata ƙunshi, daga kiji ana zagin waccar sai kiji ana gulmar wannan.

Kamar an korota haka ta fito daga cikin ɗakinsu tana sanye da wasu matsiyatan kaya ƙananu, sai wata riga data ɗora a saman kayan, saida ta dubi inda su Falmata ke zaune suna kitso tun tana cikin ɗaki take jiyo maganar matar dan haka ne yasa ta fito riƙe da key na Mota a hannunta, dan jiya wani Alhaji yayi mata kyautarta.

"Idan mata bazata iya gani tayi shiru ba, to kuwa zata daina shigowa gidan nan, saiki canza wajan zuwa kitson?".

Wani kallon baki isaba Falmata tayi mata zatai magana Shamsiyya ta shigo gidan tana saurin faɗin.

"Aunty Zahariyya kece kika aje Mota a ƙofar gida nan, naji Baba yana ta santin motar?".

"Idan kece maiyi mata kitson sai ki hanata shigowa gidan nan mu gani ai?".

Da wani irin sauri Zahariyya ta waigo inda Falmata take tana binta da wani matsayacin kallo tana ɗaya key na motarta tana nunata dashi ta ce.

"Ke har wuyanki iya isa yankan da zanyi magana kina gaya min ba daɗi?".

Turo baki tayi na zallar rashin kunya itama ta ce.

"To haka kawai tsakani da Allah, baki ji saida naja mata kunne bane?, da Ma'u ce ke tara jama'arta masu ƙunshi ana gulmar jama'a ai ita baku taɓa shiga harkarta, sai ni haka kawai duk salon a kore min mutane".

"Kinga Falmata idasa min kitso na, na wuce na tafi, kiyi hakuri ke kuma baiwar Allah".

Wata uwar harara Zahariyya ta watsama matar data yi magana, tana sake nuna Falmata ta ce.

"Wallahi ki kiyaye ni".

Zatai magana Mama ta ɗaga labule ta fito jiki a sanyaye domin kwana biyun kwata-kwata bata da ƙarfin jiki saboda rashin lafiyar da take fama da ita, ta ciwon ƙirji, dama kuma ɗan kitson da Falmata keyi a gidan suke samu a ɗakinsu ana ɗora sanwa, domin yanzu kowanne ɗaki girkinsa yake, idan kaga anyi girki gidan gaba ɗaya, takar sa'a akai Baba ya bada wani abun aka dafa gaba ɗaya, to sai ayi wata ma bai kawo wani abu ba, cikin kitson da take yi ba kullum ake samun masu kitso ba, gara ma Ma'u wani lokacin anayin biki ko suna kullum tana samun masu ƙunshi, daga nan idan sun zo ƙunshi sai ta samu masu ƙitso, a haka fa ake rayuwar, shi yasa wani lokacin basa samun abun kirki suna ci, shi yasa ma Mamar ciwon ƙirji ke damunta kuma tasan ba abunda yasa mata hakan sai kwana da suke da yinwa wani lokacin.

"Falmata karna sake ji kinyi magana a nan wajan".

Mama ta faɗa tana kallon Falmata.

"Mtsww aikin banza da anyi magana sai a kama faɗa ma mutum wasu maganganun ban hakuri tsabar ace ma mutum na Allah ne shi".

Zahariyya ta faɗa tana yin hanyar waje dan haushin sanyin da Mama ke dashi take.

Wani kalar baƙin ciki ne ya ciyo Falmata tana bin bayan Zahariyya da kallo, wato ma maganar data faɗa da Mama take kenan ba?.

"Amma Mama dan Allah ki duba fa yadda ta gaya miki magana ta wuce sai kace tana magana da sa'arta haba Mama?, ya kike hanani ɗaukar mataki ne?, ni ce dai-dai da uban kowa a cikin gidan nan wallahi".

Ta ƙare maganar tana idasa ma matar kitson, tana ƙare mata ta miƙe tana miƙa mata ɗari biyar ta amsa tana ajeta akan kujerar da matar ta miƙe tsabar ɓacin rai, matar bata tsaya ba tayi saurin ficewa daga gidan.

"Amma Aunty Falmata kamar dai yadda Mama ta ce ki rinƙa masu shiru, shima ai magana ce, saima kinfi ƙunsa ma mutum baƙin ciki idan har baki biye masa ba".

"Ke da'allah kiyi min shiru kema, ba nan kika wani shigo kina tabbayarta wai Mota a ƙofar gida ba ko tata ce?, ko kallonki ma tayi ne?, baki ga key ɗin Motar a hannunta ba, idan banda abunki da shiga abunda babu ruwanki, ai kema kinsan Mota itace zata zo da ita, duk gidan nan waye yake zuwa da irin wa'innan idan ba ita ba, mutunan dake yawo gidajen ƙaruwai miye Maza bazasu basa ba?, wallahi kin ban haushi".

"Yi hakuri Aunty Falmata".

Mama dake ta kallon Falmata na masifa sai kace ta ari baki, idan kaganta saika ɗauka bazata iya magana mai tsawo irin wannan ba.

Girgiza kanta kawai Mama tayi tana komawa ciki.

"Yawwa ƴar albarka yanzu nake cewa kece kika zo da wagga Mota mai shegen kyau haka?".

Duban Baba Zahariyya tayi tana sake matsawa jikin Motar ta danna key ɗin Motar, Motar ta buɗe ta buɗe gidan gaba tana shiga sai kuma ta dawo da dubanta inda Baba yake tsaye sai washe baki yake ta ce.

"Baba ni ce mana, ai kasan duk gidan nan ba mai iya zuwa da mota sai Zahariyya, wake da alfamar wannan ai sai ni ko?".

Washe baki ya daɗayi yana cewa.

"Ahab kware ko dama na faɗa ai kace da wannan aiki, to yanzu ina za'aje, ina ce dai Motar taki ko?".

Ya faɗa yana sake bin Motar da kallo, dan duk ɗaukarsa ko kawai an bata ne ta hau tazo gida da ita.

"Baba tawa ce mana ko wani ya faɗa maka ba tawa bace?".

"Kai Masha Allahu, kice munyi Mota kawai".

Ya faɗa yana shafa motar bakinsa yaƙi rufuwa.

"Baba na daiyi Mota".

Shiru Baba yayi yana sosa kai ya ce.

"Hakane kam kinyi Mota, to yanzu zan iya samun wani abu?, tun safe bansa komai a ciki na ba, gashi naga gidan duk yau babu wani motsi".

Haushi ne ya ɗan kama Zahariyya tana buɗe jakarta ta miƙa ma Baba naira dubu ɗaya, jikinsa na rawa ya amsa hannu biyu ya fara mata kirari da godiya yadda kasan ba uba ne da ƴarsa ba.

"Wai kai Baba dai a haka zaka zauna ƴaƴa ke ɗaukar nauyinka?".

"Zaka bakkani ne ko kuwa sai kin gama cimun fuska?".

"A'a Baba mi yayi zafi Allah ya baka hakurii amshi gama ƙirin ɗari biyar".

Haba ai sai ya ƙara daɗa washe baki yana dariya-dariya ya ce.

"Ko ke fa da haka kikeyi ai ba'a wani jin kanmu dake".

Ɗanja baya yayi yana matsawa ya bata waje zata tayar da motar kawai sai ga Shamsu sun shawo kwana ta wajan gidan da jama'arsa dake take masa baya.

Baba yana dubansu daga nesa ya ɗaga masa hannu yana barin jikin Motar Zahariyya dake neman tayar da motar amma ganin inda Baba ya nufa yasa ta tsaida motar tana buɗewa ta fito, ganin wadda yazo gidan yau yasa ta nufar wajan itama, dan kwata-kwata basa shiri da Baba da Shamsun, domin duk cikin gidan ba mai ɗakko masa magana harta kai wajan ƴan sadda sai Shamsu, shike sawa ana sake zaginsa a cikin gari, gara daɗawa ma bai basa ko asi sai jawo masa maganar da yake yi.

"Miye ya kawo ka gidana yanzu?, ba na ce karna sake ganinka ko hanyar unguwar nan ba?".

Faɗin Baba dai-dai yazo gabansu, ganin haka yasa Shamsu tsaida jama'arsa yana wani ɗaga masu hannu.

Sanye yake da wasu kaya ƙananu ya jifga babbar riga a sama, kayan duk sun yamutse, fuskarsa ko duk tabo ne wani wajan yankan wuƙa ne, sai idonsa dake shafe da kwalli baki, sanye kansa yake da wata hula ta karkace, bakin nan nasa a karkace yana dubansa cikin Muryar ƴan daba ya ce.

"Haba Father ya kake haka ne?, gidanka fa gidana ne".

"Ta gidan uban waye ya zama gidanka iyee?".

"Wai kai Father ya kake yawa ne?, wannan fa yawa kake yi, ya nida gidan ubana nazo ake min haka ne?".

Baba zai sake magana yana nunasa da yatsa Zahariyya ta ƙaraso wajan tana cewa.

"Please Baba barni dashi kayi tafiyarka kawai".

"To ki tabbatar bai shigar min gida ba".

"Shikenan naji".

Tafiya Baba yayi, Shamsu yana binsa da kallo wato dai bazai taɓa canzawa ba?.

"Mi ya kawo ka?".

Zahariyya ta faɗa tana harɗe hannunta a kirji tana kallonsa.

"Ke bana son iskanci fa, wato shi dai wannan Man ɗin ba zai daina son zuciya ba ko?".

"Uban naka kike cewa ma haka?".

"To duk waye silar shigarmu wannan halin bashi bane, wato kema harda wata Mota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login