Showing 12001 words to 15000 words out of 17169 words
Chapter 5 - KAWAICI Book Free Pages By Zahra Royal Star.txt
baki shanyayye kawai".
Umma ta faɗa haɗe da ɗaga masa hannu, Siya dake zaune tana shan azabar targaɗe har lokacin tana kallon Amna haɗe da mata wani kallon banza, gani tayi kamar Amna na mata gwalo, ai ko ta fasa ihu tana nuna Amna tana cewa.
"Wallahi Umma gwalo take min".
"Gaskiya ne ba shakka Amna, wato kin mata mugunta kinzo kiga ta mutu shine kike mata gwalo?, to gata nan ras take bata kai da mutuwar ba, ke baki isa ki kasheta ba wallahi, kuma yanzu ta fara saki aiki, idan kinga dama wata rana kiyi mata fatan mutuwa mu gani".
"Aunty kiyi hakuri insha Allah Amna bazata ƙara ba, yanzu ma shigowa mukai ta bata hakuri ta duba ta".
Ummi ta faɗa tana duban Umma, wani irin kallon baki da hankali Umma tabi Ummi dashi tana cewa.
"Ku riƙe haƙurinku bama buƙata, saida ta cutar da ita zata zo tana wani bata hakurii, ai ba har zuciyarta take bada hakurin ba, tunda gashi nan a gabanki take mata gwalo tsabar ta kware wajan shaiɗanci".
"Umma dan Allah kubar maganar nan ta wuce haka, nifa laifin Siya duk nake gani, miye na kawai saita saka Amna goge mata takalmi?, dan kawai neman rigima".
"Kai wai bance ka daina sako mana baki ba Ƙhamis?, ai kai na kusa sallama mata kai, tunda gaba ɗaya an gama min da kai, kwata-kwata baka ganin aibunsu ko laifinsu, dan haka zo ka fice min a ɗaki".
Umma ta ƙare maganar tana nuna masa ƙofar waje, Murmushi ya saki kaɗan ya kai dubansa inda Siya take ya nunata da yatsa yana cewa.
"Daga yau idan na sake ji kinsa Amna wani aiki na rainin wayo irin naki, wallahi wallahi saina miki abunda baki tunani, sakarai kawai".
"Wayyo Allah Umma kinji miye yake ce min a gaban wannan yarinyar Amna?, ni wallahi Ya Ƙhamis ka siya min raini a wajanta wayyo Allah Umma".
Ta ƙare maganar kamar wacce aka kaima duka.
"Ke ke ke yi shirunki, kai kuma fice min a ɗaki na ce, idan ka isa idan na sata aikin ni kazo ka bige ni, ko kuma kace kar tayi aikin nawa, marar kunya kawai".
"Allah ya baki hakuri Umma".
Ya idasa maganar yana juyowa ya fice daga ɗakin yana mamakin Umma da Siya da neman rigima kullum su kar a zauna lafiya.
"Kema kama aljanar ƴarki ku fice min daga cikin ɗaki".
Umma ta faɗa tana nuna su Ummi haɗe da nuna masu hanyar fita.
Ba abunda Ummi ta iya cewa ta jawo hannun Amna dake bin Umma da wani irin kallon takaici haɗe da jin haushinta a zuciya.
*MUHAMMAD POV*
Kallonta yayi yana sauke gilas ɗin dake sanye a idonsa bayan ya ɗauke Computer dake gabansa a hankali ya nuna mata wajan zama yana cewa.
"Ki zauna mana".
"No Doctor Muhammad, mi yasa Matarka take so tafi ƙarfinka ne?, kawai daga na kira ka saita amshe waya ta kama ce min Karuwa?".
"Ki zauna yanzu dai, dama zan baki hakuri a madadinta, ai nasha gaya miki Matana tana da kishi sosai fiye da yadda zan faɗa miki, shi yasa bana so kowacce Mace na kirana mudun ina cikin gida, ina son Matata bana son wani abu ya rinƙa shiga tsakaninmu".
Kallonsa Hanan take da mamaki tana jin zafi da ɗaci a zuciyarta kamin ta ce.
"Ni kenan baka sona Doctor Muhammad?".
"Dama na taɓa faɗa miki ina sonki ne?, bana da ra'ayin ƙarin aure Hanan, shi yasa tun farko da kika nuna kina sona, nayi ƙoƙarin dakatar dake, amma kika nuna ina kefa bazaki iya rabuwa dani ba".
Wata irin ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana faɗar Innalillahi wa'inna alaihir raju'un a zuciyarta, sosai take mai-maitawa, idonta yayi jawur jiri ta fara gani, ganin haka yasa Doctor Muhammad ƙoƙarin taimaka mata ta zauna.
Sauke lumfashi tayi tana ɗan dafe kanta kamin ta ce.
"Baka san irin sonka da nake ba, da baka buɗe baki ƙila kace min haka ba, miye laifi na dan kawai na ce ina sonka?, kai ɗin fa ba kowacce Macece zata iya kallonka lokaci ɗaya ta iya kauda idonta akanka ba, kana kallon kanka kuwa?".
Wani irin murmurshin gefen baki ya saki wadda ya ƙara kashe zuciyar Hanan ta kafeshi da ido, shi ɗin kyawawa ne ba irin kyan nan can ba, idan ka masa kallo ɗaya ma zaka iya ce masa mummuna, wata irin baiwa garesa ta tsantsar kwarji, kyansa mai kwantar da hankali ne, ga wani sansanyen kyau da Allah ya zuba masa, komai yake cike da aji da kuma kamewa, tafiyarsa kaɗai cike da wata irin natsuwa ga wata irin izza wacce ta haɗe da kwarjini take ƙara masa farin jini a wajan jama'a.
"Na gode da soyayya Hanan, amma ki sani kowanne mutum da kalar tashi rayuwar, bana jin zan iya ƙara aure gaskiya".
Kawai sai dai suka ji an buɗe ƙofar da ƙarfi an shigo haɗe da cewa.
"Har sai ka zauna kana lallaɓa Karuwa marar aji da kamun kai?, ke bance miki ki kama kanki ba?, bance miki karna sake ganinki da Mijina ba Mlm?".
"Sakinahhhhh!!".
Muhammad ya faɗa da ƙarfi yana mamakin wacce irin Mace ce ya aura haka mai mugun kishi?, kishin dake rufe mata ido ta kasa gane dai-dai daba dai-dai ba.
"Miye zaka ce min?".
Ta faɗa tana kallonsa babu tsoro.
"Waye ya baki izinin zuwa wajan aiki na?".
"Ai tunda naji wannan ƴar iskar Karuwa ta kira ka tana kashe maka murya, ni nasan dama akwai abunda ta taka, ashe dai nayi gaskiya sonka take, to ki sani har abada Mijina ya zama haramiyarki wallahi".
Sakina ta faɗa tana nuna Hanan data miƙe tsaye tana kallon Sakina, tabbas Sakinar ta fita kyau da diri irin na mata, ga kyau mai fisgar mutum, komai yaji, amma bata jin zata sassuta mata itama sai inda karfinta ya ƙare wajan samun Muhammad.
"Ai ban taɓa sanin ke jahila bace sai yanzu, an gaya miki tsoronki nake ji ne?, to bari kiji idan har ina lumfashi a doran ƙasa ki rubuta ki aje saina auri Mijin naki idan ya so ki faɗi ki mutu".
"Hanan please kije waje".
Ya faɗa yana nuna mata hanyar waje.
"Ke har isa ki kirani da jahila?".
Sakina ta faɗa tana shan gabanta.
Batai aune ba taji saukar mari mai zafin daya gigita tunaninta da jinta da ganinta.
Wani irin zaro ido tayi bayan ta tantance wadda ya mare ta.
"Nika mara akan wannan ƴar iskar?".
"Idan baki shiga hankalinki bama saina miki abunda yafi haka wallahi".
Ya faɗa ransa a mugun ɓace, ganin yadda ransa yayi ƙololuwar ɓaci ne yasa Sakina shan jinin jikinta tana dawowa cikin hankalinta kaɗan, Muryarta na rawa ta nuna Hanan tana cewa.
"Akan wannan?, baka ji abunda ta ce min bane?".
"To ai baki da maraba da abunda ta kira ki dashi, kwata-kwata Sakina baki da hankali da tunani, an gaya miki kishi hauka ne?, kuma idan na tashi ƙara aure ko mutuwa zakiyi an gaya miki zan fasa ne?".
"Na shiga Ukuna an shanye min Mijina wallahi, Innalillahi wa'inna alaihir raju'un na shiga Uku".
Wani irin takaici da baƙin ciki ya ƙara cika Muhammad, hayaniyar da suke ta fara hawa kansa, dan haka ya nunata da yatsa yana cewa.
"Nan da minti talatin tayi miki a gida, daga yanzu idan har kika ƙara taka ƙafa kika ce zaki zo wajan aikina ba tare da na sani ba, to daga lokacin da kika fito ɗin karki sake ki koma min cikin gida, ki wuce kai tsaye gidan iyayenki".
Dafe ƙirji tayi tana mamakin lafazinsa wani irin tsoro ne ya shigeta, tasanshi idan ya ce abu baya canzawa, bare a yadda yayi mata maganar.
Saida ta tabbatar ta bankama Hanan wani mugun kallo haɗe da harara da kallon gargaɗi, kamin ta juya haɗe da sakin tsaki har tana bangaje Hanan saura kaɗan ta faɗi ƙasa, Allah yaso tayi saurin tsayawa da ƙafafunta, tana binta da kallon mamakin hauka da kishin rashin tunani da wasu matan keyi.
Tana fita ta juyo inda yake zatai magana ya ɗaga mata hannu haɗe da nuna mata hanyar fita kawai.
Jiki a sanyaye ta juya tana ficewa itama tana ayyana yanzu ne ma zata fara yaƙin shiga gidan Muhammad ɗin, tunda taga Matar tashi bata da cikakken hankali....
*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai dakata daga na 10 ne insha Allah, biya kuɗinki kawai a tura miki complete nasa yana nan akan Naira ɗari biyar #500 kacal*.
Account number 👉8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank
Shaidar biya 👉08130479973
*KAWAICI*
*©Zahra Royal Star*
PAGE 9
"Baba gani".
Falmata ta faɗa tana turo baki.
"Ke mi akai miki naga kina wani ɓata fuska kamar kinci magani?".
Ƙasa da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta ta ce.
"Babu komai fa Baba".
"Kinga ba wannan ba, kawo min dubu biyar nan wajanki, nasan za'a samu tunda kema kina sana'ar kitso".
Shiru tayi na ɗan wasu sakonni, kamin ta dubi Baba da mamaki, wai dubu biyar?, idan da tana da ita ma da tuni tasai masu abunda zasu ci, bawai ta barta a hannunta ba, hidimar rayuwarsu bama ta bari ta tara ko sisi bare har ta bawa wani, kuɗin kitson da bai wuce a rana ta samu dubi Uku ba ko huɗu, idan an sami Mutane da yawa a ranar.
"Baba wallahi banda ko sisi ni a yanzu".
Riƙe baki Baba yayi yana kallon Falmata kamin ya ce.
"Kawai kice bazaki bani ba, wato kema mugun hali zaka fara?".
"A'afa Baba babu ne wallahi, saboda ni ba wani abu nake samu ba a harkar kitson nan, idan mutum yazo nayi masa bai wuce ya ɗauki naira ɗari biyar ba ya bani, ga masu samun kuɗi da yawa nan Aunty Ma'u a mutum ɗaya kaɗai tana iya samun sama da dubu goma, dubu talatin harda ƴan kai, ni fa hidimar yau da kullum ma bazasu bari na aje kuɗi har sukai dubu biyar bama"
"Ohh ni Binta ina jin magana da iya zance wajan wannan yarinya, lallai ba shakka idan baki nuna halinki ba ta jinin Halima ai an sake miki suna Falmata, yanzu duk miye na ratato wannan maganar har haka?, ina ruwanki da gaya masa nawa ne Ma'u take samu a sana'arta?, ke wani ya taɓa saka miki ido ne iyee?, nifa ko bana son shishshigi da Munafurci wallahi".
Inna ta ƙare maganar tana nuna Falmata da tunda ta fara magana take murguɗa mata baki tana magana ƙasa-ƙasa.
"Ke wai Binta ba damar a faɗi gaskiya game da yarinki ne?".
Baba ya faɗa yana dawo da dubansa inda Inna take tsaye.
"Yo yafa za'ai ta yarda a faɗi gaskiya tunda nata ne ita ta haifa".
Umma ta faɗa tana mata wani kallon uku saura kwata.
"Hansatu wato dai bazaki taɓa daina shiga harkar ƴaƴana ba da ni kaina ko?".
"To Binta miye nayi gaskiya face bakya so, ƴaƴan nan naki fa duk gasu nan a zube sai a slow".
"Inna kiyi shiru kawai barni da ita".
Zahariyya ta faɗa dai-dai ta fito daga ban ɗaki duk taji abunda ke faruwa har Allah-Allah take ta fito domin taga Umma ta fara wuce gona da iri.
"Idan an barki da ita miye zaki mata?, wato dai Zahariyya kema kin koyo rashin kunya ko?".
"A'a Baba nanfa ɗaya gaskiya, ka tsaya inda gaskiya take shine kawai, baka ji miye take cewa bane?, ita bata kalli nata ƴaƴan bane yaya suke iye?, ina ne Asiya bata zuwa bata ga wancan saurayi bata ga wannan saurayi?, ga kuma Amina ita ina ne bata zuwa yawon bin gidajen masu kuɗi?, tsabar tafi ƙarfin gidan nan"
Wata irin shewa Asiya ta saki tana ɗaga labule ta fito itama tana riƙe ƙugunta tana wani fari da ido na tsantsar rashin kunya tana duban Zahariyya ido cikin ido ta ce.
"Ke har akwai abunda zaki iya faɗa a ɗakinmu na Allah wadai wadda baku dashi a naku ɗakin wadda ya take namu ma ya shanye?, ko kin manta ke bin Maza kike yi ne?, ko kin manta duk wani abun kunya da Allah wadai a kanku ya ƙare ne?".
Saukar kyakkyawan mari wadda yasa ta gigice tana sakin ƙara haɗe da dafe kumatunta tana zaro ido waje ƙirjinta na duka, kallon Zahariyya take wacce bata san lokacin data ƙaraso inda Asiya take ba bata san lokacin data ɗaga hannu ta wanketa da wani gigitaccan mari ba.
"Ke miye haka?".
Baba ya faɗa yana nuna Zahariyya.
"Ai wallahi idan baki rama marin da tai miki ba, karki sake ki ƙara min magana".
Umma ta faɗa tana kallon Asiya cike da takaici.
Asiya jin haka ga baƙin ciki biyu ya rufeta, na ribartata da Zahariyya tayi ta mareta, ga furucin Umma akanta, ai kawai saita kamo zanin Zahariyya dake ɗaure a ƙirjinta tana ci mata kwala dashi, Allah yaso ta ɗauresa da kyau, neman kokowa take so tayi da ita, Baba ya kwatsa masu wata irin tsawar daya sasu dawowa hayaccinsu.
"Wai ba magana nake maku bane kun maida ni ɗan iska ban isa ba?".
Tunda suke basu taɓa ganin ɓacin rai a wajan Baban ba sai yau.
"Amma Mlm tsakani da Allah kana kallo ta ɗauki hannu ta mare ta?, miye tayi mata?".
"Bana son jin komai kowacce taja Ƴaƴanta ta ɓace min da gani".
Taɓe baki Inna tayi tana magana ƙasa-ƙasa.
"Hmm ai raini ne dai ƴaƴanka da Matanka sun gama kama shi, duk wannan mazuran da kake yanzu na banza ne, domin dai ba'a dawo da hannun agogo baya wallahi".
"Binta magana naji kina yi?".
"A'ato ni Mlm mi zance ne?, kawai yau sai naga ka koma kamar Mai gidan daya kai ya isa da gidansa, da ace tun fil'azal a haka kake ai da gidan nan bai kasance a haka ba, amma akace tunran gini tunran zane, bazaka taɓa sauyawa ba Mlm ai, duk wannan abun da kake bazai hana gobe kaje kayi abun kunya a gaban ƴaƴanka ba".
"Binta ni kike kallon tsabar idona kina gaya ma magana haka?, miye nayi na abun kunya?, an taɓa kamani ina zina ne da wata?, ko kuwa an taɓa kamani ina sata?".
"Bako ɗaya Mlm, amma tarbiyyar Yaran nan duk ba kai bane kasa gidan nan ya koma haka ba?, ace ka haifi Yara kaine baka san cinsu ba, kaine baka san shansu ba, taya za'ai Yara bazasu faɗa kowacce irin rayuwa bane?, amma da anyi magana baka son gaskiya, kuma ita dai gaskiya ai ɗaya ce, ko ɗan iska yasan gaskiya dai gaskiya ce kuma ɗaya ce".
"To Binta ko zaki zo ki dake ni ne, ko kuma kiyi maganin abun?".
Baba ya faɗa yana basarwa haɗe da borin kunya, babu wata nadama a tattare dashi ko alamar zai daina abunda yake yi.
"Ni na isa Mlm?".
"Har kinyi yawa ma Binta, tunda a gaban Yara kike tona min asiri".
"Hhh Mlm kenan so yaran aka gaya maka basu san waye Mahaifin nasu bane?".
"Kai kowa ya bar wajan nan bana son ganin kowa a nan, tunda an rasa wadda zai fidda ni kunya ya ban dubu goma ko biyar, duk yawanku da kuɗin da kuke samu".
Sakin baki Falmata tayi dake tsaye har lokacin tana mamakin lamarin gidansu, kullum ƙara bata mamaki yake, da halayya irinta Baba, dubi yanzu yadda Inna ta gama gaya masa gaskiya duk da itama bason gaskiyar take ba, yau ta rufe ido ta gaya masa, amma ji yadda ya ture gaskiyar da tsiya, yama mance da abunda take gaya masan.
Lallaɓawa tayi ta shige ɗaki tana girgiza kai.
"Aunty Falmata wai mike faruwa?, Mama ce ta hanani fita".
Harara Mama data fito daga uwar ɗaki ta jefama Shamsiyya dake tabbayar Falmata tana cewa.
"Wato kedai son jin gulma ne dake?, jikinki har kyarma yake idan ana faɗa a gidan nan kice zaki fita ko?".
"To ai Mama kusan duk naji komai kawai gani ne banyi ba, ai gidan nan idan da sabo an saba faɗa kullum, idan ma ba'ai yau to sai kaji anyisa gobe, bafa a tsallake rana ko yini shaiɗan bai sauka a tsakar gidan nan namu ba".
"Hmm Allah ya kyauta kawai, amma ni gidan nan ya daina bani mamaki ma ni, lamarinsa sai ya koma bani haushi kawai, naga ranar da Allah zai kawo gyara a gidan nan".
Mama ta faɗa tana zama ɗaya daga cikin kujerun parlon.
Falmata ta sauke lumfashi kaɗan tana faɗin.
"Ai Mama ba wadda yasa gidan nan ya zama haka sai Baba duk shine wallahi, yanzu ma fa shi yasa wannan rigimar har ana shirin dabbacewa tsakanin Aunty Zahariyya da Aunty Asiya".
"Lallai ita yanzu Aunty Asiya tana ganin Aunty Zahariyya da jiki a murze ita ko da jiki kamar a ƙarya irin nawa, take shirin haye mata?".
"Ai ko yau data sha dukan tsiya Allah yaso Baba yayi masu magana, kin san Allah yau yadda Baba ya tsawatar sai naga kamar wani disfulin Master fa".
Falmata ta faɗa tana dariya suka tafa da Shamsiyya da itama ta saki dariyar.
Girgiza kai kawai Mama tayi tana murmushi tana kallonsu......
*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai dakata daga na 10 ne insha Allah, biya kuɗinki kawai a tura miki complete nasa yana nan akan Naira ɗari biyar #500 kacal*.
Account number 👉8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank
Shaidar biya 👉08130479973
*KAWAICI*
*©Zahra Royal Star*
PAGE 10
*SHAMSU POV*
"Mai gida ya kamata mu hanzarta barin wajan nan, saboda gayu na iya zuwa wajan nan kame".
Wani farin abu yake ta shaƙawa a hancinsa yana jin kansa na juyawa sosai haɗe da ganinsa wata duniyar daban.
Zagaye suke dashi kusan su goma kowanne riƙe yake da taba yana zuƙa, sai shi dake zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana shaƙa abun dake hannusa.
Ɗagowa yayi, sai da kusan suka razana da ganin yadda idonsa suka kai jawur, ganin yadda fuskarsa ta koma. A mamakina kyakkyawan gaske ne domin kyan nasa har yaso yayi yawa, ga wani irin gashi dake garesa kamar wani ba'indiaye, gashin nasa har ya sakko bayansa akan ƙeyarsa, idanunsa masu masifar girma ne, sai ɗan ƙaramin bakinsa wadda ya zama baƙiƙƙirin saboda shaye-shayen da yake yawan yi, saɓanin da, da yake ja jawur, idonsa sanye yake da kwalli wadda ya taimaka masa wajan ƙara fiddo da kamanninsa na ƴan daba, wuyansa sanye da sarƙa, hannunsa da tsintsiyar hannunsa sanye suke da wasu abun hannu, jikinsa ƙananun kaya ne wadda suka ƙara taimakawa wajan fiddo da ainafin suffarsa ta ƙirar ƙarfi, miƙewa yayi tsaye, Masha Allah, domin yana da wani irin tsawo sosai domin duk yafi yaran dake wajan tsawo, ga ƙirjinsa dake da faɗi da girma, ga jikinsa dake murɗe sosai daga gani ada can yana yawan motsa jikin nasa a yadda yake murɗe sosai.
"Sanata Alhaji Sammani, ya ce zai aiko a ɗauke ni, domin yana so ayi masa wani aiki, koda Gayu sunzo nan babu abunda zasu iya".
Ya faɗa kai tsaye yana duban wani wajan daban.
"Amma Mai