Showing 3001 words to 6000 words out of 17169 words
Chapter 2 - KAWAICI Book Free Pages By Zahra Royal Star.txt
kika mallaka ba?, kema kin lalace idonki ya buɗe?".
"Zagina kike neman yi, Ya Shamsu miye haka kuma?".
"Ke dalla can ware ni ki ban waje".
Ya faɗa zai raɓata ya wuce cikin gidan nasu, ta tsaida shi da sauri tana faɗin.
"Baka ji abunda Baba ya ce bane karka sake ka shigar masa cikin gida?".
"Ai ko waye yazo bai isa ya hanani kutsawa cikin wannan gidan ba, ke ko shine yazo billahir azim na ɓarar dashi na wuce".
"Innalillahi yanzu Baban zaka ɓarar?".
"Ke kin fara cika ni fa, ki wuce kawai yawon gantalinki".
"Ya Shamsu karfa a fara jinmu da kai, nima fa na iya tashancin nan a'ato, da ne ka sanni a baya amma ina haɗuwa da wa'inda suka fika ɗanyen kai".
Wani kallo yayi mata yana sakin dariya yana sake binta da kallo sama da ƙasa ya ce.
"Kware kuwa gashi shi yasa naga ai har kin mallaki Mota, dole kice kema dai-dai kike da irinmu, to yayi ya isheki haka, zaki wuce ne ko sai na kikkifa miki mari?".
Ya faɗa yana wani matsowa kusa sosai da ita, idon nasa jawur, da sauri ya matsa tana banka masa hararara, itama duk cika baki ne, amma tasan Ya Shamsu ya shallakema tunaninta, domin duk wata rigima ya sani kuma ya iyata, shine har ƴan siyasa yake ma aiki, itama kawai cika baki ne.
Shigewa motar tayi tana barin wajan.
"Mtsww kai gayu ku tsaya yanzu zan fito mu wafce".
"Sai Oga Allah ya fito da kai lafiya".
Suka haɗa baki wajan faɗa......
*KAWAICI*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*
PAGE 3
*Sabuwar Abuja Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
Da gudu ta shigo gidan tana wai irin hakki.
Aje abinda ke hannunta Ummi tayi tana duban Amna data shigo gidan da gudu.
"Ke wato bazaki nutsu ba ke a rayuwarki?, kece kullum jan faɗa, halama yanzu faɗan kika jawo ko?".
Waige-waige take tana zaro ido waje tana sake duban ƙofar shigowa waje kamin tayi magana taji sallamar Ya Ƙhamis.
Da wani irin sauri ta ƙarasa bayan Ummi tana ɓoyewa.
Binta kawai take da kallo tana ɗan girgiza kanta.
"Hala faɗa taje ta jawo ko?".
Riƙe yake da bulala a hannunsa yana kallon Ummi ya ce.
"Wallahi Ummi wannan yarinyar bata jin magana, kawai ki matsa min na zane ta, wai fa ganinta nayi ta kama wata yarinya tama fita girma nesa ba kusa ba, wai zasu yi dambe. Sai anje an bige bakin rashin kunyar nan wata rana ayi mana maganinki".
"Ai wallahi daka barta an fasa bakin marar jin, ai ni ba kai min dai-dai ba, da baka bari an daketan ba".
Ummi ta faɗa tana waigowa inda Amna take a bayanta Ummi ta ƙara cewa.
"Zaki wuce daga baya na ko sai na mangare ki a wajan nan, ace yarinya kin girma keba ƙarama ba amma har yanzu kina kallon kanki a yarinya ƴar shekara biyar ko goma?".
Turo baki tayi tana kallon Ya Ƙhamis ta bankamasa hararara tana jin mugun haushinsa.
"Ni kike harara ba?, zamu gamu dake ne, zaki zo ki same ni ina zaune ai".
Wuf ta fito daga ɗaki tana duban Ƙhamis ɗaura ɗankwalin kanta tayi tsabar saurin maganar da zata faɗa ta fara cewa.
"Wato Ƙhamis ka fara nuna cewa ban isa da kai ba dai ko?".
Juyowa sukai su duka suna duban Umma data fito daga ɗakinta tana maganar tana bin Ummi da wani mugun kallo.
Ƙasa da kanta kawai Ummi tayi ta kamo hannun Amna zasu wuce subar wajan taji sukar muryar Umma na sake faɗin.
"Wai bance maka ka daina shiga harkar wannan agolar bane shin?, ana dole ne?, na ce bana buƙatar ina ganinka da ita, amma kana nuna kamar ban isa da kai ba".
"Umma miye a ciki dan naga Amna nayin abunda bai dace ba na tsawatar mata?, ai kamar Siya ce da idan na ganta nayi mata faɗa duk ɗaya fa ne nake ɗaukarsu".
"Wato ina faɗa kana faɗa ba?, ka gama raina ni akan wannan Matar da ita da ƴarta?".
Ta ƙare maganar tana nuna Ummi dake gaf shigewa ɗakinta.
Wani irin kallon tsana Amna ke bin Umma dashi, domin Allah ya sani ta tsani Matar nan, da ace Ummi najin maganarta da sun daɗe da barin cikin gidan nan, wadda suke zaune danshi ma Allah ya amshi abunsa, to akanmi za'ace dole sai an zauna a mahalli ɗaya?, itama Ummar kamar munafuka taƙi kama gabanta, ba muguwar munafuka kuma sai Siya duk ita ke haɗa wannan faɗan, tunda Ummi ta shigo gidan a matsayin kishiyar Umma ta kuma zo da ita a matsayin Agola a gidan shikenan Umma ya ɗora karan tsana akanta, sai gashi zaman nasu ma bai daɗe ba Allah yayima Abba rasuwa, shine har lokacin suke tare a gida ɗaya, duk da an raba gado, kowacce taci gado, amma na Umma duk yafi yawa, tunda ita kaɗai keda ƴaƴa da Abba, shi yasa ta cika fariya da ɗagin kai, ƴaƴanta biyu da Abba Ƙhamis sai Siya, Siya irin yaran nan ne masu masifar iyayin tsiya, ga son asani da shegen son jin gulma ga shiga abunda ba ruwanta, akwai ɗaukar kanta nesa inda Allah bai kaita ba, sai dai Ummarta ita ce ta ɗaure mata gindin duk wani abu da take yi, duk wani gayu dama abunda yafi ƙarfin tasa to sai Ummar tayi yadda tayi ta sai mata shi, tana da ƙawaye masu masifar son rayuwar ƙarya, shi yasa itama komai nata na masu ƙarya ne ƴan matan zamani. Ita ko Amna kwata-kwata hakan ba wani damunta yayi ba, rayuwarta kawai take, duka-duka bazasu wuce shekara sha biyar ba, amma idan kaga yadda Siya ke zuba iyayi saika ɗauka wata babbar Mace ce, ita ko Amna ma rashin ji da shegen yawon tsiya bin gidajen ƙawayenta dajan faɗa cikin unguwa ke hanata wani zama ƴan mata bare ta zama ƴar gayu kamar Siya, shi yasa ta ko ina suna da banbancin halayya.
"Kici kanki kisha baƙin ruwa".
Umma ta faɗa tana bin Amna da harara, domin idon Amna irin masu girman nan ne ga cikinsu ba baƙi bane wata irin kala ce dashi har wani sheƙi suke badawa kamar gwalɗin haka saima idan ta shiga rana, shi yasa wani lokacin idan ta ƙurama mutum ido wani sai yaji yarrrr ko gabansa ya faɗi.
"Yarinya sai ido irin na Mayu".
Umma ta sake faɗa tana harare-harare.
Girgiza kai Ummi tayi tana haɗe wani abu a ranta ta sake jan hannun Amna da sauri suka shige ɗaki, dan karma Amnar ta sako maganar da za'a kwana ana faɗa da Umma a gidan, yarinyar tata ce wani lokacin kamar mai shafar jinnu, idan tayi maka wani abun ko wata maganar saika rantse bayin kanta bane.
"Na dawo gare ka, ka buɗe kunnanka da kyau Mlm kaji ni, wallahi Allah Ƙhamis kafa kiyaye ni, ka kiyayi waccar yarinyar mai iskokai a tsakiyar kai, bana son kana shige mata, amma kai kamar wadda aka shanye, shin wai ko an wanke an baka kasha ne ban sani ba?".
Rasa ma abunda zaice Ƙhamis yayi domin maganar Ummar tayi nauyi da yawa, dan haka ya haɗe hannunsa waje ɗaya yana faɗi a hankali kamar wadda baiso aji ya ce.
"Umma dan girman Allah kibar wannan maganar babu daɗi fa idan Ummi taji, kwata-kwata Ummi bata da matsala wallahi kece baki fahimce ta ba".
"Kai dalla can yimin shiru na ce, ta daɗe bata jinba na ce kaji ko?, ka fita idona rufe".
"Shikenan Umma Allah ya baki hakuri".
Kawai ya faɗa yana bar mata wajan, ai saita riƙe baki tana surutu ita ɗaya tana faɗin.
"Wato ni ka bari ma mahaukaciya ina magana ban gama ba, ka barni nan sake da baki wato?".
Sai ƙara banbanmin faɗa take tun tana yi da Ƙhamis harta dawo kan Ummi tana ai duk ita tasa Ɗanta ya raina ta, ta shanye mata Ɗa, amma dole ta miƙe tsaye ta kwato ɗanta bazata bari a rabata da ɗanta ba wallahi.
*Unguwar Dokoki Rimaye, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
Bayan ta gama share gidan tana daga tsaye taji shigowar Ya Shamsu babu sallama sai wani uban fito daya saki, wadda yasa gaban Falmata faɗuwa.
"Ke dalla can ina mutanen gidan?".
Turo baki tayi tana taɓe baki kuma, kamar bazata tanka masa ba, sai kuma ta ce.
"Ba gaka gidan nan ba ka duba mana".
"Kan buh*un uba, keeee ni kike gaya ma magana haka?, kin san da waye kuwa kike magana kai tsaye haka?".
Ya faɗa yana matsowa sosai kusa da ita batai aune ba zatai magana ya ribace ta sai dai taji saukar mari akan kumatunta na dama, ai da wan irin sauri ta saki tsintsiyar dake hannunta tana fasa wata irin ƙara haɗe da sakin kuka, sai hawaye shaaaa kamar an buɗe fanfo, tana yi tana kallon Ya Shamsu cike da mamaki jikinta na masifar rawa.
"Da uban waye kike?, ke har kin isa yaushe aka haife ki ne ma?".
Ya faɗa yana ciccije baki.
Kusan gaba ɗaya mutanen dake cikin gidan suka fito.
Inna ce ta fito daga kitchen tana ɗaure zaninta sosai kamin ta nuna Ya Shamsu ta ce.
"Ai wallahi kamin dai-dai kayi min maganin marar kunya yau ai, saboda naga kwana biyun nan dama rashin kunya take ji dama, da safe ma ina jinsu da Zahariyya so nayi Zahariyyar ta kamata tayi mata ɗan banzan duka, amma naji shiru".
Wata uwar hararara Falmata ta juyo inda Inna take ta zafga mata, tana sake turo baki tana ƙunƙuni.
"Ka gani ba jibi yadda take murguɗa min baki?, dangin rashin kunya".
"Bar wajan nan ko wallahi na ɓarar dake nan".
Ya faɗa a tsawace.
Mama dake cikin ɗaki tana ji amma ta kasa fitowa dan ita kam tama fara gajiya da faɗan da kullum takema Falmata akan ta daina shiga abunda za'ai mata magana, ta rinƙa hakuri tana yin duk mai yiwuwa ta kauda kai, amma bazata iya yin KAWAICIN da Mamar take yi ba, garama Shamsiyya ita ta wani ɓangaren ta biyota ta wajan halayyar kauda kai da hakuri, amma Falmata sai kace ba ita ce ta haife ta ba.
"Ke ina zaki je kuma?".
Mama ta faɗa tan duban Shamsiyya data fito daga uwar ɗaki tana neman fita waje.
"Amma Mama baki jin yadda aka tararma Aunty Falmata ne ana son mata taron dangi?".
"Ba ita ce tajawo hakan ya faru da ita ba?, ai ina jin komai, kinga ni na fita wajen ne?".
Girgiza kai Shamsiyya tayi tana kwaɓe fuska.
"To koma ki zauna bance ki fita ko nan da can ba".
"Amma Mam......
Wani kallo ɗaya ta jefa mata yasa Shamsiyya shanye sauran maganar dake bakinta, ta koma kan kujerar dake kallon ƙofar fita waje ta zauna, tana jin muryar Baba a tsakar gidan, jin abunda yake cewa ne yasa Shamsiyya sauke ajiyar zuciya tana faɗi a fili.
"Gara da Allah ya kawosa yanzu zaiyi maganin Ya Shamsu ai".
"Hayaniyar mi nake ji ne tun daga soran gida?".
Wani kallo Baba yabi Shamsu dashi yana nunasa da yatsa yana sake cewa.
"Wai bana ce karka sake ƙafarka ta tako min har cikin gida ba?".
"A'a Mlm wai ya hakane dan Allah?, ɗan cikinka ne fa shima, ɗa ne a gidan nan kamar kowa fa, sai kuma ka rufe ido kace wai karya shigo gidan nan shida gidan ubansa?".
Faɗin Inna tana duban Baba da ɓacin ran abinda yake ma ƴaƴanta wani lokacin, duk irin taimakonsa da suke idan ya tashi kwashe masu albarka da zagi yi yake babu ruwansa.
"Binta Binta kinji na kira sunanki ko?, ki fita ido na rufe, ai ni na daɗe da yafe wannan a duniya".
"Koma dai miye baka taɓa canzama tuwo suna, dan haka har gobe Shamsu na amsa kiran ɗanka jininka, har gaban abada ba'a canzawa tuwo suna na faɗa na ƙara faɗa yawwa".
"Wato dai Binta bakinki bai mutuwa ko?".
"To wai Mlm na miye ka tsaya kana biye mata, kawai ka ɗauki mataki akansa man, ya za'ai yazo har ƙofar gida yana tara mana ƴan iska suna mana zuƙe-zuƙe".
Umma ta faɗa tana yaye Hijib ɗinta, dan shigowarta gidan kenan taci karo da rigimar da ake yi a tsakar gidan.
"Keee Hansatu hawainiyarki ta kiyaye rama ta wallahi, ki kiyaye shiga gonata nida ƴaƴana, abun magana dai kowanne a gindinsa yake, kema yaran naki wanne irin rashin ji ne basa yi, keda, keda ƴaƴa mata ma gaba ɗaya, ai gara shi ado ne komi yayi".
"Ahab har talle nama audi gori ne dama?, ke kin mance kema duk rabi ƴaƴan naki mata ne, ciki harda mai bi gidajen Karuwai".
"Shikenan ku gama zufda min mutumci kamar yadda kuka saba, ni kenan kullum gidana ace cikin tashin hankali ake da tune-tune, sai kace ba gida ɗaya kuke ba, sai kace kuna ganin hanjin junanku".
"To ai Baba gaskiya Umma ta faɗa da......
"Kee ubanwaye ya kawoki gidan nan kuma?, da har ana magana kina sakowa mutane baki ana magana da ƴan gida uban waye ya sako ki ciki?".
Faɗin Baba yana duban Sa'ade data fito ta tsaya itama.
Sosa kai Sa'ade tayi tana ƙunƙuni.
"Haba Mlm ai nake ganin itama fa ƴar gida ce, dan tayi aure ba wai yana nufin an yafeta shikenan ba".
"Inji ubanwa?, bance ma wai karna sake ganinta ta kwaso ƙafa tazo min gida ba, bazai yiwu na aurar dake ina kuma ciyar dake ba wallahi bazai yiwu ba".
"Ka manta dai Mlm, amma yaushe kike ciyar da ita ɗin?, muma da muke zaune dolenka ka kasa ciyar damu bare ita kuma?".
"Wai ku dalla bazaku daina wannan surutun ba?, kowa yabar wajan nan, ko wallahi yanzu na kira Yara na da Karnukan dake waje su watsa taron nan, tunda idan aka fara cece kuce gidan nan ba'a san a daina ba".
Shamsu ya faɗa yana wani zare ido waje.
"Kai jama'a lallai Shamsu kanka ya fara taɓuwa ba shakka iyayenka kake gaya ma haka?".
Umma ta faɗa tana yin hanyar ɗakinta, taja Ƴaƴanta dake cikin gidan lokacin suka shige ɗaki, ita ko Falmata tuni ta saɓule tayi nasu ɗakin, dan tasan wannan faɗan sai Allah kawai, idan aka tada balli a gidan nasu kamar ana biki idan shaiɗan ya buga gangarsa a gidan nasu ana daɗewa ana abu ɗaya, ko gajiya da cece kuce basa yi........
*KAWAICI*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.........*
PAGE 4
*FALMATA POV*
"Falmata wai ke sai yaushe ne zaki rinƙa KAWAICI kina kauda kai a cikin gidan nan ne?".
Taɓe baki tayi tana turo shi gaba tana kallon ƙasa ta ce.
"Amma Mama ai kin san sai an taɓa ni nake magana fa".
"Bazaki taɓa canzawa ba Falmata Allah ya shirya min ke".
"To ai Mama Aunty Falmata tana da gaskiya, gidan nan namu sai dole kana da baki idan ba haka ba ai ka bani a cikinsa".
Faɗin Shamsiyya tana sake gyara zamanta bayan shigowar Falmata.
Girgiza kai kawai Mama tayi tana ɗan gishingiɗa akan kujerar da take zaune.
Ganin Falmata ta miƙe tana niyar fita tsakar gidan yasa Mama saurin faɗin.
"Ina kuma zaki je ne?, wato sai dai na hanaki fita tsakar gidan nan kwata-kwata wata rana Falmata, bazaki rinƙa jamin masifa ba".
"Mama masifa kuma?, zuwa fa zanyi na manto ɗari biyar ɗita ce a ƙofar ɗakinmu, shine zani na ɗakko karma masu halin ɓera na gidan nan suci karo da ita".
"Tabɗi jam sannu Aunty Falmata ai ko wallahi wannan ɗari biyar ƙila ba rabonki bace".
Shamsiyya ta faɗa tana riƙe baki.
Ɗan miƙewa Mama tayi tana dubanta sosai kamin ta ce.
"Ji wani shirme da wowta, ke har ina barin wani abun amfani a tsakar gidan nan ne?, to karma ki sake naji kinyi magana idan har kika duba babu ita, domin kece kikaja a ɗauketa da kanki, tsabar jan faɗa yau da kikasa gaba kika je kika mance da ita, tsabar faɗa ya miki daɗi ko?".
Sosa kai ta farayi tana shagwaɓe fuskarta Mama bata ƙara magana ba, sai ma komawa da tayi ta kwanta tana nuna mata da hannu alamar taje kawai.
Koda ta fita babu kowa a tsakar gidan sai idonta daya faɗa akan Isma'il da miƙewarsa kenan inda tabar ɗari biyar ɗin tata, kuma tabbas idan ba gizo idonta ke mata ba kamar taga lokacin da yayi saurin zurata a cikin aljihun wondonsa, yana wani tashi idon nan nasa jawur yana wani layi-layi, daka kallesa kasan kwaya ta gama shanye masa ruwan jiki, riƙe yake da taba a hannunsa yana zuƙa yana tafiya yana fiddo hayaƙin tabar ta baki ta hanci.
Ai da wani irin sauri tasha gabansa tana miƙa masa hannu ko tsoron abunda zaije ya dawo bata yi ba, tana jijjiga a gabansa ta ce.
"Ya Ismail bani ɗari biyar ɗita daka ɗauka yanzu a nan wajan".
Wani irin cije baki yayi yana riƙe tabar hannunsa sai da ya sai-saiti fuskarta ya fesa mata hayaƙin akan fuskarta, wani kalar tari ta fara amma duk da haka hannunta har lokacin a miƙe yake tana son ya bata kuɗinta.
Sakin tabar hannunsa yayi ta faɗi ƙasa yasa ƙafarsa ya take sauran ya murjeta.
Dawo da dubansa yayi kan Falmata dake tsaye har lokacin a gabansa tana miƙa masa hannu.
"Ke dan tsohonki ni zaki kalla ki ce wai na ɗaukar miki kuɗi?, ubanmi gare ki da har za'a ɗauka".
"Wallahi Allah kaine ka ɗaukar min kuɗi kuma Allah saika bani kuɗi na".
Ai bai san lokacin daya ɗaga hannunsa ba sai dai taji saukar mari akan kuncinta, ƙara ta saki tana sakin baki sake, yau mari biyu kenan tasha ɗazu Ya Shamsu ya mareta a ɗayan kumatunta yanzu kuma ta samu wani rabon marin a ɗayan kumatun nata.
"Na rantse da wadda yayi ni sai an bani kuɗi na, kuma kaine wadda zaka ɗaukar min kuɗi, duk gidan nan waye yake halin ɓare idan ba kai ba Ya Ismail?".
"Kai wannan yarinyar wuyanki ya isa yanka wallahi, to na ɗauki kuɗin naki, na ɗauki banza kuma, naga ubanda zai tsaya miki na baki su".
"Shin wai ke Falmata idan ba'a jiki kina faɗa da wani ba a gidan nan waike baki jin daɗi ne?, ɗazu fa nan Shamsu da kyar aka kashe wutar da kece kika fara kunna ta, amma sai ma kika saɓe kika shige ɗakinku, kika barmu da masifar da kece musababinta, to wallahi zansa duk wadda kika ƙara ja faɗa ya kamaki yayi miki shegen dukan da zakiyi kwanaki kina jinyar kikinki tunda ke naga kinfi kowa rashin kunya a gidan nan".
Faɗin Inna tana nuna Falmata da yatsa.
Ƙasa-ƙasa Falmata ke faɗin.
"To ba sai asa ɗin ba mu gani".
"Mi kike cewa ne marar kunyar banza?, fitowa zakiyi ki faɗa kanki tsaye ki zage ni, tunda dama ƙarshen rashin kunya ai akanki aka sauke shi".
Inna ta ƙara faɗa a tsawace.
Umma ce tayi wuf ta fito tana faɗin.
"Kefa Binta baki son gaskiya, ai dai