Showing 15001 words to 17169 words out of 17169 words
Chapter 6 - KAWAICI Book Free Pages By Zahra Royal Star.txt
gida mi ya kamata mu.....
Ɗaga masa hannu yayi yana wucewa yayi gaba yana barin wajan kwata-kwata kamar wadda aka tsikara.
Sakin baki Shamsu yayi yana kallon sauran Yaran ya ce.
"Wai mike damun Mai gida ne?".
Wani dake bayansa ya saki murmushi yana cewa.
"Akwai lokacin da muka biyo ta unguwarku, ya haɗu da ɗaya daga cikin ƴan matan gidanku, har tayi masa rashin kunya, babu tsoro ko shakkarsa duk da yadda garin nan kusan ake tsoronsa, amma ita kamar ma bata san da labarin waye Mai gida ba, tun lokacin sai kaga ya zauna yana murmushi yana dariya ƙasa-ƙasa ko kuma ya zauna yayi shiru kamar mai cikin matsananciyar damuwa, tabbas akwai wani abu da yake so a tattare da yarinyar".
Shamsu bai wani ji komai ba, saima wani ɗan iskan murmushi daya saki yana faɗin.
"A cikinsu wacece haka?, dan kasan ƴan Matan gidan namu kusan ba wani tsoro ne dasu ba, kowacce ta iya tata rashin kunyar, ya kamata ka binciko min wacece ita".
"Shamsu kai ya kamata ka gano wacece ita a yanzu, kazo masa da ita nan".
"Ta yaya zan gane wace?, kawai hanya zanyi masa ya aureta, domin kuɗi kawai zai sakarma Baba billahir azim saiya basa auranta ko bata so".
"Hm zaka gane kawai kaje gidan yanzu, wata ƙila idan magana ta tashi zata iya bada labarin ta haɗu da mai gidanka, tunda sun san ana ganinka kana zuwa inda yake, dama ai bana ji ta wai baza'a basa ita ba".
"Ba lallai ita tasan waye shi ko tasan Mai gidana ne".
Can Shamsu Idi da suke maganar yayi sauran tsaidashi wajan magana yana nunasa da yatsa ya ce.
"Amma zaka iya gane kamaninta yaya take?, duk nasan ƴan gidanmu kawai gaya min kamaninta".
"Yawwa ashe Shamsu kana da kai?".
"Kaifa bana son yawa zaka gaya min ne na taimaka ma Mai gida ko kuwa zaka tsaya min wulakanci?".
"A'a Allah ya huci zuciyar ƙaramin Mai gida".
Ya faɗa yana ɗan jijjina masa hannu alamar girmamawa yana murmushi haɗe da cewa.
"Yarinyar fa gaskiya tayi koni da ace zan sameta so nake, tana ɗan jiki amma kaɗan bata da tsawo sosai ɗin nan tsaka tsakiya take, sai dai akwaita da garin jiki, Mlm komai ga yaji a jikin yarinyar nan kamar wata babbar Mace, amma ba ɓaka bace fara ce ba farin nan sosai ba, tana da manyan idanuwa ga bakinta ɗan ƙarami kamar na tsuntsuwa, yadda take sarrafasa tana ma mutum rashin kunya, ma kaɗai abun birgewa ne, rashin tsoronta shiya ƙara kashe Oga, ya kware mata, amma ganin farko zaka iya rantsewa bata magana ne, gaskiya dai bata tsoro ko kaɗan".
Wani kalar murmushi Shamsu ya saki domin harya gano wacece ma, dan haka ya ɗaga hannunsa yana dafa ƙafaɗar Idi ya ce.
"Idi Falmata ce".
"Kai ka santa, ni dan kasan Mace ɗaya na sani a gidan nan naku Zahariyya domin itama munsha haɗuwa a irin gidajen Gala shi yasa nake gane ta".
"Hhh ka ce Oga ya kamu da soyayyar marar kunya?, anya zasu dai-daita dashi kuwa?".
"Mi zai hana?, zai tafiyar da ita a yadda take wallahi saiya saita mata zama".
Dariya kawai Shamsu ya saki danshi a yadda ya hango abun kawai dama yana so ya huci haushin abunda tayi masa, kuma zai ƙuntata mata ne wajan aura mata Ogansu, baya jin ta Baba da an damƙa masa wasu Manyan-Manyan kuɗaɗe dole ya bada kai bori ya hau.
"Kawai dai zata sha baƙar wahala ne a tattare da Mai gida, domin Mai gida kun san ba'a ɗaga masa murya, bare ya iya jure rashin kunya, wata rana ma ƙila saiya kusan ɓalla yarinyar can, wato duk gidanmu kowanne ya iya rashin kunya, amma ta Falmata ta dabance, kwata-kwata yarinyar akwaita da tsiwa ga hayagaga".
"Allah wallahi dole ta biyu idan tana tare da Oga".
Idi ya faɗa yana wani kalar rangaji sauran suna haɗa baki wajan cewa sun kusa shan biki kenan tunda Oga tsawon shekaru dama baiyi aure ba, kusan shakera talatin da biyar koda bakwai ne ma?, shi yasa daka gansa zaka san ba Yaro bane, zasu sha biki ko ina a garin Rimaye sai an shaida bakin Ogan nasu.
*FALMATA POV*
Tashi tayi zaune tana ɗan dafe kanta dake sara mata tun safen data tashi.
Matar dake tsaye kanta tana dubanta ta ce.
"Falmata zaki iya kitson nan kuwa?, ko dai na tafi sai wani jiƙon?"
Ɗan yamutse fuska tayi tana sauke lumfashi ta ce.
"A'a zan iya kije waje gani nan fitowa".
Da to ta amsa tana ficewa daga ɗakin.
Mama dake zaune tana wuridi da carbi, ta dubi Falmata ta ce.
"Idan kin san ba iyawa zakiyi ba ki sallame ta kawai, ina Shamsiyya ne wai?".
"A'a Mama gara nayi mata ko mun samu kuɗin cefane na yau, naga kayan miyar dana sayo ranar juma'a sun ƙare, ko magi babu fa a ɗakin nan, gara kawai nayi mata. Shamsiyya kuma inaga bata cikin gidan nan".
Falmata ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga ɗakin.
Mama ta ce.
"To ina zata je bata gaya min ba?".
"Inaga ba nisa tayi ba".
Falmata ta ƙare maganar haɗe da idasa fita daga ɗakin.
Tana fita ta iske tsakar gidan da wasu Mata har biyu zaune ƙofar ɗakinsu Ma'u da alama suma ƙunshi ya kawo su, amma Ma'u ta barsu zaune da alama kuma sun daɗe a zaune.
Bata ce ma kowa komai ba ta jawo kujera ta zauna tama Matar da zatai ma kitso alamar ta zauna, tasa mata abun sallah a ƙasa ta zauna suka fara kitson, sai cewa take tayi mata mai shegen kyau Mai gidanta ne zai dawo daga tafiya yau.
Bata ce mata dai komai ba ta fara mata ƙitso ƙananu mai kyan gaske a yadda ta ɗakko kitson kamar ba hannu ke yinsa ba, saida akaci rabin kitson sana suka ji sallamar Ma'u ta shigo gidan.
"Au da Aunty Ma'u baki gidan nan dama?, kin bar masu ƙunshi zaune tun ɗazu".
Falmata ta faɗa tana kallon Ma'u data cire Hijab ɗinta tana zama haɗe da sakin murmurshi tana kallon Matan da suka zo Mata ƙunshi ta ce masu.
"Ku kuwa mi yasa baku kira ni a waya ba?"
Murmurshi ɗayar ta saki cike da wani irin iyayi tana cewa.
"Wallahi bamu da No ɗinki ne shine yasa".
"Ayya a ƙofar gidan nan ai nasa fastar ƙunshi na akwai numberta a jiki".
Ɗayar ce ta amshe da cewa.
"Ayya bamu lura bane, ai da bamuyi zaman nan ba".
Miƙewa Ma'u tayi tana faɗin.
"Ai kuwa bari nazo yanzu a fara".
Ko inda Falmata take bata kalla ba, Falmata data shaƙa danta tsani a disgata amma taga Ma'un yau da wulakanci ta shigo gidan, amma ai zata haye mata ne tana zaune zata ji magana.
Koda ta fito dandanan ta fara ma ɗaya suna yi suna labari ɗayar na faɗin.
"Dan Allah ki tsara min ƙunshi mai kyau, wani bikin ɗiyar ɗan Majalissa zamuje a Kt, so nake mu fito daban wallahi".
Wani kallo Falmata ta jefa masu tana mamakin zantukansu, zata iya cewa tun ɗazu taji suna maganar bikin nan, kamar za'ayi bikin wani nasu, daga gani irin ƴan ƙarya ne masu son asan su waye su.
Taɓe baki tayi tana sake baza kunne jin wata ƙarya da ɗayar ta faɗa.
"Ai bari ke dai so nake kawai na haɗu da wani Sanata a wajan bikin nan na samu kona auresa nima, kin san fa a irin bikin nan na taɓa haɗuwa da wani ɗanɗan Gwamnan jihar Adamawa fa, ya so aure na, ya soni kamar zaiyi hauka bawan Allahn ni ce naƙi kawai".
"Kai jama'a ɗanɗan Gwamnan ne kika bari ya suɓuce miki?, ko dai kin manta dai bawar Allah?".
Matar da Falmata take yima ƙunshi ta kasa hakuri ta faɗa, Falmata ko murmushi ta saki tana cewa.
"Abunda nake tunani kenan, kodai ƙarya yayi miki kika gano ba ɗan Gwamna bane kika fasa, amma ace ɗan Gwamna guda yazo ya ce yana sonki kina haka ai da gudu zaki ce a ɗaura aure".
"Keee Falmata bana son iskanci da wulaƙanci fa, ki kiyayi ni Falmata daga ke har masu zuwa wajanki, kunji an sako daku cikin maganar nan ne?, bana son shiga sharra ba shano, kifa fita idona na rufe Falmata".
Ma'u ta faɗa tana juyowa inda suke ranta a ɓace.
"Allah ya baki hakuri Aunty Ma'u, amma ai gaskiya na faɗa ke daga ji kin san wannan maganar ai ba haka take ba, ta faɗi son ranta ne, ni kuma kin riga kin san ba'a ƙarya a gaba na".
"Ai ko wata rana baiwar Allah idan kina saka baki a irin abunda bai shafeki ba to zaki sha wahala wata ƙilama ayi miki shegen duka".
Ɗayar ta faɗa tana bankama Falmata hararara kamar idonta zasu faɗo ƙasa.
Taɓe baki tayi tana cewa.
"Yo Ohho dai".
"Hmm ke Falmata kike ko waye ma, bana son irin haka kin gane?, daina ganin gidanku nazo zan iya miki rashin daraja wallahi, baki san wacece ni bane, ke kinsan wacece ni kuwa?".
"Riƙe sanayyarki Mlm, wacece ke ɗin idan ba mutum kamar kowa ba?, danni banga alamar ke wata ɗin bace, ai shi arziƙi idan baki sani ba shike nuna kansa, ni kin san wacece ni ɗin kike ɗaga min murya?".
"Ke dalla can Mlm wacece ke ɗin idan ba ƴar gidan Saminu mai matattar zuciya ba, uban waye bai san ƴan gidan nan naku bane, uban naku baida ai..
Kyakkyawan marin data jisa a kwance akan fuskarta ne yasa ta haɗiye sauran maganar da take son furzarwa, a zabure har tana haɗe ƙunshin da ake mata akan fuskarta tayi mata dame-dame duk ta shafa ma fuskar tata ƙunshi, a kiɗime take kallon Ma'u data daddage iya ƙarfinta ta ɗauketa da mari.
"Ma'u...
Ta faɗa da maɗaukakin mamaki.
Ma'u ta miƙe tsaye tana nuna masu ƙofar fita waje jikinta na rawar masifa tana cewa.
"Zo ku wuce mana daga cikin gida, ƙunshi ne bazanyi ba, ke har kin isa ki shigo har cikin gidan Ubanmu kice zaki zage sa ki zauna lafiya?, ke bari kaji bawai Baba ma kaɗai ba idan kika ce zaki taɓa koda Dabbar da ake kiyo ce na rantse da Ubangiji sai na lakaɗa miki na jaki a cikin gidan nan, bare kuma kice zaki taɓo mai gayya mai aiki".
Wata irin dariya Falmata ta saki tana miƙewa ita da Matar data gamama ƙitso yanzu matar na murmushi tana girgiza kai tana alfahari da ƴan gidan akan abu ɗaya, basa barin wani na waje ya shigo ya ce zai taɓa wani a cikinsu, nan ne kaɗai gaba ɗaya ma unguwar suke birgesu.
"Amshi nan Falmata na gode ni na tafi sai wani jiƙon kuma".
Matar ta faɗa tana miƙa mata naira dubu ɗaya haɗe da tattare kayan ƙitsonta ta ƙara gaba. Falmata na murmushi tana dubansu yadda ɗaya duk ta ɓata fuskarta da jan lallai Allah yaso ma ja ne ba baƙi ba, da ba'a san yadda zata koma ba.
"Wallahi Aunty Ma'u kin min dai-dai da ace ma bakiyi magana ba, ni sai na bar yarinya kwance".
Miƙewa sukai a tare cike da wani irin baƙin ciki da ɓacin rai suna dubansu gaba ɗaya wacce aka fara yima ƙunshin ta nuna Ma'u da yatsa tana cewa.
"Wallahi wallahi tallahi Ma'u zaku san su waye kuka wulaƙanta, ku jira sammaci daga Office ɗin ƴan sadda, dan wallahi Allah saina saka an ɗaure ku har igiya tayi saura".
"Ahayee nanaye, dan Manzon Allah kin daɗe baki sa a ɗauremu ba kinji ko?, zaku fitar mana a gida ne ko kuwa saina kira Ya Shamsu yanzu yazo nasa ya sakar maku Karnukansa su rakaku har gida ne ko yaya?".
Ai da wani irin sauri suka kama haɗa kayansu wacce aka fara yima ƙunshi harda gutun hawaye, a zuciyarta ta rantse ko zatai yawo tsirara saita sa an ɗaure Ma'u da Falmata. Da gudu zasu fita daga gidan Falmata ta ɗauki ɗankwalin wata haɗe da jefa masu a baya tana faɗin.
"Allah raka taki gona, ga tsiyarku nan".
"Yo idanma baccin tsaurin ido irin naku da wulaƙanci kuzo har gidan mutane kuce zaku zagi ubansu, kai bari ma na gaya maku idan na ƙara ganinku a gidan nan ko ta unguwar nan na rantse da Ubangiji saina lahira yafi ku jin daɗi, maƙaryatan banza kawai da wofi".
Suna gaf fita ɗayar data ɓata ƙunshinta yayi dame-dame akan fuskarta ta ce.
"Wallahi Allah ku jira irin matakin da zan ɗauka akanku, inaga daga kaina bazaku ƙara yima wani ko wata irin abunda kukai mana ba".
"Na rantse da Allah zanzo har ƙofar gidan inda kike maganar na fasa ma shegiya baki, na zubar miki da haƙora naga bakin magana".
Da sauri ɗayar taja hannunta tana magiyar tazo su tafi daga baya sunyi maganar ɗaukar mataki, dan ita kanta tana jin bazata iya haƙuri da irin cin fuskar da sukai masu ba....
*To laifin daɗi akace ƙarewa, duka-duka a nan na kawo ƙarshen Free pages, yanzu fa aka fara labarin mai dogon zango ne insha Allah, har yanzu ba'a fiddo wasu jarumai daga cikin wannan book ɗin bama tukunna, har yanzu ba'a kamo zaren labarin ba, kai dai kawai ka biya Naira ɗari biyar kaga yadda zata ƙarƙe, a cikin KAWAICI, mi zai faru a nan gaba?, wai shin Gidan Mlm Saminu zai gyaru ne kuwa?, wai ma tsaya Falmata zata auri Mai gidansu Shamsu ne?, kai jama'a nima fa zanso sanin ya labarin zai kaya a nan gaba kaɗan*
*Biya kuɗinki ko kuɗinka kawai a tura maka Complete nasa yana nan akan Naira ɗari biyar #500 kacal*
Account number 👉 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank
Shaidar biya 👉08130479973