Showing 30001 words to 33000 words out of 34919 words

Chapter 11 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt

Advertisement

ma yaran sun ce a ƙoshe suke, don haka ta ajiye kular ita ma ta rage kayan jikinta, yana fitowa daga wankan ita ma ta shiga, kafin ta fito ya dira a kan kular yana cin macaroni, ta yi masa kallo ɗaya ta kau da kai, muryarsa babu yabo babu fallasa ya ce"Sabila kin tozarta ni kin ji daɗi ko?"

Ba ta kula shi ba, sai ma tashi da ta yi ta bar masa ɗakin ta koma ɗakin gado ta zauna, bayan ya gama sai ya shigo ɗakin ya zauna a bakin gadon, ya ce"Ai shikenan ya wuce ko?"

Nan ma ba ta ce komai ba.

Ya janyo hannunta yana cewa"Magana fa nake yi miki".

Ba ta ƙwace hannun ba, amma ba ta kalle shi ba, ya ce"To bari ns tafi wajen bazawarata ita dai na san ba za ta wofantar da ni ba, kin san fa aure zan yi nan da bayan sallah".

Nan ma dai ba ta kula shi ba, ya fice daga gidan.

Da ya dawo wajen sha biyu na dare, cikin baccinta ta ji yana taɓa ta, wajen wata biyu kenan wani abu bai shiga tsakaninsu ba, ita har ba ta so ma ya taɓa ta, saboda tada mata da rashin nutsuwa kawai yake yi, ba ya iya taɓuka uban komai, yau ɗin ma kuwa hakan ce ta faru, ya jagwalgwala ta kawai, har mamakin shi take yi, yadda yana yaro mai jini a jika amma ba ya iya nisan zango, daga yanayin zubin jikinsa kuwa babu kama.




WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, IN SHA ALLAH GOBE ZA MU KAMMALA FREE PAGES.

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

Shaidar biya ta nan
08028966015
[13/07, 2:19 pm] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/IqwGrPcKXM47271YQuTB2R


*AURE A YAU!*



NA
*SADIYA ABDULRAZAK*


*First class writers association*


Page 10


GIDAN YUSUF

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Yusuf yana ta haƙuri da Zubaida da sana'arta, yana ta kuma ƙara shige mata ta WhatsApp, zuwa yanzu dai ya gama gane cewar matarsa ba ta da kamun kai, sannan mu'amala da wasu mazan ba komai ba ne a wajenta, ga kuma ƙarya da take yi na nunawa duniya ita 'yar gata ce s wajen mijinta, suna soyayya suna da fahimtar juna da shaƙuwa, bai taɓa nuna mata ya san abin da take yi ba, kuma wannan waya da aka ba ta kyauta sai ganinta ya yi kawai a hannunta tana amfani da ita, ya same ta da tambayar wa ya ba ta waya? Ta ce siya ta yi da kuɗinta, ya share ta, akwai kuma sanda ta sayi gwal, ta ɗora a status ta ce mijinta ya ba ta tukuicin daren jiya, matan da suke son sanin haɗin da ta yi su biyo ta private, sannan babu jimawa ta sayi mota, ko da wasa ba ta yi shawara da shi ba, sai gani ya yi a status wai mijinta ya siya mata mota, kuma yana dawowa gida ya tarar da motar, ya same ta zaune ta waya, ya zauna ya jira ta ta gama, ya ce"Zubaida wane ne ya siya miki mota?"

Ta ce"Ni na siya da kuɗina, kuɗin sana'ata".

Ya ce"Amma ba ni da darajar da za ki sanar mini kafin ki siya? Ni fa mijinki ne Zubaida, meyasa kike son nesa da ni? Da ba haka zamanmu yake ba, ba na jin daɗin canjin nan naki, ya kamata mu zauna mu gyara zamanmu, mu fahimci matsalarmu".

Ta ce"Ni ba ni da wata matsala da kai, kai ne dai ka ƙwallafawa ranka masifa, idonka yana kaina, komai na yi ba daidai ba ne, sam ba ka son cigaba na, na rasa me yasa, kuma yanzu da ka zo kana zancen mota kai ba abun alfaharinka ba ne a ce matarka ta sayi mota? Na gaji da yadda nake yawo da mai adaidaitasahun haka, sannan motar ma zan ɗauki direba".

Ya ce"Allah Ya sanya alkhairi, amma me yasa kika yi ƙaryar ni ne na siya miki? Me yasa kike yawan ƙaryar na yi miki kyauta?"

Jikinta ya yi sanyi, yanzu dai ta tabbatar da Yusuf yana da lambarta, layinsa guda biyu ta sani kuma har yanzu da guda ɗaya yake yin whatsApp to amma ta ina yake sanin status dinta?

Ta ce"Wane ne ya ce maka ina wannan ƙaryar?"

Ya ce"Ina gani, kullum ina ganin status ɗinki, ni customern ki ne Zubaida, kuma muna chart da ke, idan kina yin daidai a lamarinki da mazan da ba na ki ba kin sani, idan kina kuskure ma kin sani, amma kar ki dinga mantawa da darajar aure, ba ma batun darajar miji ba".

Ya bar wajen ya bar ta da sakakken jiki, tun daga ranar kuma ta shiga fargabar da wace lamba yake yi mata magana? Iya hasashenta ta kasa ganewa, har screening ta yi ta goge wasu lambobin mazan, amma Allah bai sa ta goge tashi ba, duk ta shiga rashin nutsuwa, ta kuma rage ƙaryar mijinta ya yi mata kyauta.

Shi yanzu Yusuf tuni ya sare da sha'aninta, ya kama kan shi suna mu'amala baya-baya kamar yadda ta zaɓa, babbar damuwarsa yanzu bai wuce yadda ba ya samun sakewa a gidansa ba, saboda wannan 'yar aikin nasu, yarinyar tana da rawar kai sosai, yadda take shige masa abun nata ya fara yawa, tana yawan jan shi da fira, sai dai kawai ya ƙi sauraronta, Asabar da Lahadi da yake ɗan zama a gida yanzu ya daina, fita shago yake yi ya wuni, saboda zuciya ba ta da ƙashi, yanayin shigar da yarinyar take yi ya fara isar shi, kuma yana son yi wa Zubaida magana yana fargabar ta yadda za ta kalli maganar, ya san ba lallai ta fahimce shi ba, za ma ta iya yi masa wata fassarar. Ta waje ɗaya yarinyar take burge shi, shi ne tana kula da yaran shi yadda ya kamata, sannan tana da tsafta, tun da ta zo gidan ba za ka ce ka ga wani abu na rashin gyara ba, kuma yana jin daɗin abincinta.

A hankali ya lura ta fara zaƙewa, tana ƙoƙarin wuce gona da iri, saboda yanzu ta kai idan yana gidan ta gama abinci sai ta ɗakko ta kawo masa shi har ɗakinsa, wataran ma yana zaune babu riga a jikinsa, sau biyu yana yi mata gargaɗi a kan hakan, amma sai ta ƙara ta ce mantawa ta yi, ita zuciya ba ta da ƙashi, a hankali ya fara jin baƙon lamari a kan yarinyar amma yana ta dannewa, tun da zuciyarsa ce take sonta ba, gangar jikinsa ce, akwai lokacin da ya shiga ɗakin Zubaida da daddare neman hakkinsa, ya dawo bai samu ba, ya shiga kitchen yana daga shayi ko idan ya sha zai samu sauƙin abun, gajeren wando ne kawai a jikinsa, ya gama ya juyo kawai suka yi kicibus da Fauziya da ke tsaye tun tuni tana kallon shi, rigar bacci ce a jikinta iya cinyarta, rabin ƙirjinta duk a waje, don ma dai ba ta da ƙiba, sai da zuciyarsa ta doka, ya tafi wani yanayi na 'yan sakanni, kafin ya haɗe rai ya ce"Ke lafiya?"

Ta langwaɓar da kai murya ƙasa-ƙasa da kuma sigar yaudara ta ce"Na kasa bacci ne, kai ma haka ko?"

Ya ce"Kamar ya? Dalla ba ni hanya na wuce". Ya faɗa a fusace saboda takaicin ganin shi da ɗan wando da ta yi, ga shi kuma a wani yanayin da duk wanda ya kalle shi sai ya gane.

Ba ta matsa ba ta ce"Dama ina so mu yi magana ne, don Allah zan iya taimakon ka?"

Ya yi mata mugun kallo ya ce"Ba za ki matsa ba?"

Ta ce"Zan iya taimakonka, zan iya ba ka kaina saboda na ganka a buƙace, duk da na san maleji za ka yi, amma dai zan so ka gwada ni ka gani".

Mamaki ya kama shi, ya kalli yarinyar ya ga yadda take wani lanƙwashewa, ya fara tunanin yaushe rayuwar ta zama haka? 'Yar ƙaramar yarinyar nan da a zatonsa ko aure ba ta isa ba, shi ne har take yi masa tayin lalata da ita?

"Innalillahi wa inna alaihi raji'un!" Ya furta a sanyaye, sannan ya hankaɗe ta ya wuce, tun da ta ƙi ba shi hanya, shayin da bai sha ba kenan, ya shiga ɗakinsa ya kwanta yana ta tunanin yadda zamani ya lalace, tarbiyya ta taɓarɓare, shi a zatonsa wannan yarinyar ko aure aka yi mata iyanzu tana nan tana gudun miji, a ransa yake raya ko ina iyayenta? Ko tun yaushe ta lalace har ta yi wannan ƙwarewar? Ko me ya fito da ita aikatau? Hankalinsa duk ya tashi, yau ya gane lallai tarbiyya a yau tana wani hali, haka ya yi bacci rabi da rabi, har mafarki ya yi wai ta shigo ɗakinsa kuma ya amince da ita, ya tashi a firgice kuwa yana istigfari, musamman da ya ga wanka ya tabbata a kan shi, sai ya ga kamar a zahiri ne komai ya faru.

Da safe shi ya tashi Zubaida daga bacci, lokacin yana jin motsin Fauziya a kitchen, ta tashi yana tambayar shi lafiya? Ya zauna a bakin gadon fuska babu walwala ya ce"Zubaida ki sallami yarinyar nan mai aiki a yau ba sai gobe ba".

Ta yamutse fuska ta ce"Kamar ya? A kan me zan sallame ta?"

Ya ce"Saboda ba na ra'ayinta, kuma umarni na ba ki ba shawara ba, sannan ke ba ki kai wacce za ki titsiye ni da son jin dalili ba, ko da dalili ko babu kawai ba na buƙatarta, kar ki sake ta sake kwana a gidan nan".

Ranta ya ɓaci, saboda tana jin daɗin Fauziya, kuma 'ya'yanta ma har sun shaƙu da ita, ta tabbata ba ta yi musu komai na cutarwa sai nuna ƙauna, kawai dai rashin son zaman lafiya ne zai saka ya ce a sallame ta.

Ta ce"Amma dai ka san ba kai ne kake biyanta ba ko? Kuma ba kai take yi wa aiki ba".

Ya ce"Amma gidana ne ba na ki ba, kuma idan ita a ƙarƙashinki take to ke a ƙarƙashina kike, don haka ina da ikon saka ki da hana ki, idan kuma ba ni da shi ki faɗa mini yanzu a nan, sai na san matakin da zan ɗauka".

Har ya fice daga ɗakin ya dawo ya ce"Kar yarinyar ta sake kwana a gidan nan, na faɗa miki".

Ya fice daga gidan, ranar ko karyawa bai yi a gida ba. Da daddare da ya dawo ya yi zaton ta sallame ta ta tafi, duk da ya ga gidan a gyare amma a zatonsa Zubaidan ce ta gyara ko kuma wata ta saka ta gyara mata, bai nemi abinci ba don ya ci a waje, wanka kawai ya yi ya kwanta, bacci ya ɗauke shi, can cikin baccin shi ya ji mutum a kusa da shi, ana taɓa shi kamar ana yi masa tausa, gabansa ya faɗi sanda ya fahimci a zahiri ne ba a mafarki ba, tunani ya fara yi na me ya hau kan Zubaida yau ta kawo kanta gare shi? Tun da suka yi aure daidai da rana ɗaya ba ta taɓa neman shi a shimfiɗa ba, to dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu, shi yasa ya yi lamo yana karɓar saƙonninta.

Daidai nan ita kuma Zubaida ta ji kukan Areef da yake ta cewa ruwa zai sha, tashi ta yi fitsari shiyasa ma ta jiyo shi, ta san Fauziya ba ta da nauyin bacci, tana kula da motsin yaran har cikin dare, ta fita ta ɗauki ruwa a falo ta shiga ɗakin yaran ta ba shi ya sha, sannan ta fito, kamar ta wuce ɗakinta sai kuma ta ji son ta leƙa Fauziya, tana leƙawa ta ga wayam ba ta cikin ɗakin, babu banɗaki a ɗakin ballantana ta ce tana ciki, sai ta yi mamaki, ta leƙa kitchen nan ma ba ta nan, ta fita tsakar gida ta ga shiru.

"Wallahi mata masu ajiye 'yar aiki a gida sai kun dinga tashi tsakar dare kuna zagaye da duba halin da gidanku yake ciki, idan ba haka ba a yi miki kishiya ku dinga rabon kwana ba ki sani ba". Maganar wata mata ta dawo mata rass a kunnenta kamar yanzu take furtawa, a tiktok ne ta gani, ta faɗi hakan kafin ta ba da labarin abin da ya faru da maƙociyarta.

Zubaida ta ji gabanta ya faɗi da ƙarfi, ta koma cikin falon da sauri, kai tsaye ɗakin Yusuf ɗin ta shiga, shi kuma a lokacin Fauziya ta gama caza shi, ya juyo don mayar da martani, yana shafa ƙirjinta ya ji shi wayam ba irin na Zubaida ba, a tare suka zabura su duka ukun, shi ne ya fara tsorata gane cewar ba da matarsa yake tare ba, sai kuma Zubaida da ta kunna hasken ɗakin ta ga mijinta da 'yar aikinta haihuwar uwarta, ita ma kuma Fauziya ta firgita ganin asirinta ya tonu tun ba ta cim ma burinta ba.


GIDAN SUNUSI

Haka rayuwar gidan Sunusi da Sabila ta cigaba da gudana, babu wani cigaba, ya dogara da taimakon da maman Nawal take yi mata, ya naɗe hannu, ita ce omo ita ce sabulun wanka, azumi ya rage sati ɗaya ya zo mata da zancen an saka ranar aurensa, sosai ta ji tashin hankalin da har ta kasa ɓoyewa, ta saka masa kuka tana cewa"Yanzu baban Amal muna wannan halin za ka ɗakko ƙarin aure? Ni ma ba ka iya sauke mini duka nauyina ba za ku ma ka ƙarawa kanka wahala, ni ba kishi nake yi ba, amma ina son nuna maka rashin dacewar haka, wanda ya san zai iya riƙe mace fiye da ɗaya shi ya dace ya ƙara aure ba kai ba".

Ya ɓara rai ya ce"Ke dalla can rufe min baki, ni za ki faɗawa magana saboda kina dafawa ki ba ni? Kafin ki fara ba ni ɗin shekara nawa ina ba ki? To yanzu idan mutum ya ce sai ya yi kuɗi zai yi aure ai ba zai yi ba, kuma da kike wannan maganar wani bai dace ba ce miki na yi shawararki na zo nema? Na faɗa miki ne kawai don ki sani, bayan sallah da sati ɗaya aurena, ki so ko kar ki so ruwanki".

Ta share hawaye tana jin matsanancin kishi yana kama ta, ta ce"Shi kenan, Allah Ya sanya alkhairi".

Ya ce"Alkhairi ai ko ba ki roƙa mana ba mun samu in sha Allah, kuma a gidan nan za ta zauna, don haka ana sallame azumi sai ki kwashe komatsenki na dayan ɗakin".

Ta kalle shi da sauri ta ce"Ina zan kai? Ta ya za ka haɗa mu gida ɗaya? Wannan gidan dai ya yi mana kaɗan, ina zan zuba kayana? Ina yarana za su dinga kwana?"

Ya ce"Kaya idan kin ga dama ki zubar da su, yaran kuma tun da babu inda za su kwanta sai ki mayar da su cikinki kawai, ni dai na faɗa miki don na yi miki adalci, kina da wata ɗaya na neman mafitar yadda za ki yi, idan kuma kin raina arziƙina kina ganin ɗaki ɗaya ya yi miki kaɗan to sai ki yi bayani na sallame ki".

Ba ta sake magana ba, har ya gama mitarsa ya tashi ya fita, ko kwanaki da ya ce mata zai je zance ta yi zaton da wasa yake yi, kuma ba ta taɓa zaton zai ƙara aure a wannan ƙangin da suke ciki ba, tun daga ranar ta shiga sabon halin ƙunci, ta ɗauki kishi ta ɗorawa kanta, 'yan'uwanta kowa ta faɗa masa za a yi mata kishiya, ballantana kuma maman Nawal wacce kullum sai sun yi zancen, ita maman Nawal Sabila haushi take ba ta, saboda ba ta ga wani abun kishi a miji irin nata ba, amma dai haka take ta ba ta haƙuri.

Cikin satin ne kuma take faɗawa Sabila za ta nemo 'yar aiki, saboda aikin azumi yana yi mata yawa, kuma dama tun tuni mijinta yake cewa ta nemo ita ce ba ta bawa abun muhimmanci ba, ta ɗora da faɗin"Duk wata dubu hamsin ya ce zai dinga biyanta, Sabila ban san dai yadda kika ɗauke ni ba, inda ba za ki ga kamar na raina ki ba ai da na ce ki karɓi aikin nan, ki dinga daurewa kina leƙowa muna yin aikin, ba wanda zai gane a unguwar nan tun da kin saba shigowa, dubu hamsin ɗin za ta dinga yi miki amfani".

Sabila ta yi murmushi ta ce"Wallahi maman Nawal na ɗauke ki fiye da yadda kika ɗauke ni, kuma ba wanda zai yi maka wannan tayin sai mai sonka da alkhairi, amma ban sani ba ko mijina zai amince, idan ya amince zan yi in sha Allah".

Da Sunusi ya dawo ta faɗa masa, ai kuwa yana jin dubu hamsin nan take ya ce ya amince, a ransa kuwa har ya fara lissafin yadda za a dinga kasafta kuɗin. Ranar da aka ɗauki azumin farko ta fara zuwa aikin, idan ta je da safe ta gama komai sai ta koma gida ta hau kan ɗinkinta, sai da yamma sai ta koma su yi abincin buɗe baki, haka za ta ciko mata kuloli, har aka gama azumi Sabila abincin sahur kawai take yi, kuma mijin Maman Nawal ya yi rabon kayan abinci ya ba su mai yawa, don haka azuminsu lafiya lau babu rigima da Sunusi, karin aurenss ne kawai yake damunta.

Washegarin Idi ta siyar da kujerunta, ta kwashe komai na falonta, a ɗan filin tsakar gidan ta raba keken ɗinkinta, ta rufe masa ɗakin.

Shi kuwa Sunusi a nashi ɓangaren yana ta shirye-shiryen aure, ya kammala komai, amma fa ya ji jiki, don ba ƙaramar tatsa ya sha a wajen Karime ba, a nata ɓangaren ita ma ta gama shirinta tsaf, iya maganin mata na dubu ɗari ta siya ta saka a gaba tana ta sha babu ƙakkautawa, yanzu har ba ta so Sunusi ya zo zance, saboda ji take kamar ta rungume shi ko ta samu sassaucin sha'awar shi da take addabarta tana hana shi bacci.

A ɓangaren Sunusi kuwa tuni ya fara fargaba, saboda yana tunanin anya kuwa wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login